Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 23 of 81
*RABON WANI*
*H A S K E*
*KOBA SO*
*DA IZZATA*
*ÆŠAN MAJALISSA*
_DUK ÆŠAYA DOCUMENT AKAN FARASHIN NAIRA 300 AMMAN MAI SANSU BAKI ÆŠAYA ZE BIYA 1000 MAI BUKATA SEYA TUNTUBENI 08142105218_
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }
NA
*AUTAR MANYA*
*HAJIYA AISHA NAGA SAƘON ALKAIRIN KI GARENI NAGODE ALLAH YA ƘARA GIRMA WANNAN SHAFIN NAKINE NAGODE SOSAI ALLAH YABAR MUTUM DA MAI SONSHI HAƘIƘA NAJI DAƊI ƘWARAI NAGODE ALLAH YA ƘARA GIRMA TARE DA BUƊI, YA RAYA ZURI'A AMIN*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
*31&32*
Yajima acikin motar yana saƙawa da kwancewa baki ɗaya zainab tagama tashin kanshi, shi kanshi dana sani yakeyi akan shishshiginshi na kai mata wannan dambu dayay, inda bai kai mataba yasan da duk hakan bazata taɓa faruwa ba, amman yanzu ga yadda yaga yanayinta kamar jira take ƙiris ta fashe yasan idan bai zo mata dashi ba akwai ƙura!.
Ganin har 9 ta wuce yasashi tada motar tare dayin revars ya ɗauki hanyar gate, cikin azama masu gadi suka buɗe mishi gate ɗin suna ɗaga mishi hannu alamun adawo lafiya, yana kan titin yahaya gusau wanda ze bida kai har wajan sharaɗa kwanar ganduje,yaji wayarshi tana ringing! da baze ɗaukaba domin ya zataci ko Aliyu ne ya sauka ze addaba mai, dan haka yana ɗaukar wayar domin yay rejecting kawai seyaga ashe madam ɗinshi ce ke mishi wayar, cikin fargaba ya ɗaga cikin muryar magagi tace"Darling dafatan dai bazaka manta da abinda Bebeyn keso ba?". Bata jira cewarshi ba ta katse wayar, wata ƙwallar takaici ce tazowa usman wuya, tayaya a wannan daren kusan goma saura ace ana son dambu, to wama ze masa?, yasan ammi koze mutu bayajin zata dafa mishi wani dambu,hajiya mahaifiyar zainab ba lafiyar ƙafa gareta ba, bare yaje yace ta taimaka tai musu itama ɗin na masu aiki take ci.
Jim yayi da ranshi yana tunanin mafita wata ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke yana haɗa yadda ze aranshi tare da rage gudun motarshi gudun kada wani ya taɓashi sabida baki ɗaya tension ɗin zainab na yau ya hanashi gudanar da komai, wato rigimar wasu matan idan sunada ciki duk yadda kake xatonta ta wuce tunaninka.
Still wayar shi ya kuma ɗagawa yana kuma addu,a cikin ranshi Allah ya bashi sa,ar abinda yake shirin aikatawa domin shine ƙarshen wani tunani nashi akan dambun zainab.
Numbern wayar Malam salihu ya kira, cikin sa'a ta shiga kuwa,baban nazir wanda ke zaune a kan dakalin ƙofar gida yana sauraran labarai a redio shine yaji wayarshi tana ƙara duba saman screen ɗin wayar tashi yayi ganin sunan oganshi usman yasa ya mike da sauri tare da ɗagawa cikin rawar jiki.
"Assalamu Alaikum".
Cewar usman wanda yana tafe a hankali akan kwalta yana magana da baban nazir É—in.
"Amin wa'alaikkassalam".
Cewar baban nazir wanda ya zaƙu yaji ko lafiya?.
"Malam salihu kai haƙuri na kiraka da wannan tsohon dare wallahi madam ce ta murza kambun, wannan dambun na ɗazu................,"Tas ya kwashe komai ya gayawa baban nazir akan rigimar datake mishi tun magariba akan dambun, wai itafa ala dole setaci wannan dambun sannan hankalinta ze kwanta.
Murmushi baban naxir yayi tare da tuno shima yadda yake azabtuwa idan madam É—inshi tana da ciki akan yawan tsurfarta.
"Karka damu oga usman yanzu bara na turo maka da number wayar matar datake dambun nasan maman biyu akwai tausai zatayi mata ko kaÉ—an ne tunda akwai kayan sarrafawar a gidan, amman kafin nan ni xan soma yi mata waya sabida ta sani".
Mayar da ajiyar zuciya usman yayi tare da hamdala, sannan yace.
"To amman baka ganin aini ban san gidan ba? tayaya zanje na amso?".
Murmushi baban nazir yayi akaro na biyu sannan ya soma yiwa usman kwantace sabida gidansu Æ´an biyu bashida wahalar ganewa, aikuwa cikin sauki usman yama gane wajan sabida yanada aboki awajan arean shiyasa yay saurin gano gidan kai tsaye batare da kwano kwano ba.
Sosai usman yayta zubawa baban nazir godiya wadda har seda baban nazir yaji wani iri sannan sukai sallama mintuna kaÉ—an baban nazir ya turawa da usman number maman biyu, inda shi kuma baban nazir É—in ya soma kiran maman biyu.
Wayar tana gefen pillown mama tana jin labarai da ita, wanda har sun soma baccima jin karar! wayarta yasa hassana ta mike cikin bacci ta É—aga wayar gananin baban nazir ke kiran yasa ta mikawa mama tana gaya mata wanda ya kira É—in.
Cikin fargaba mama ta É—auka tare da sallama.
"Maman shahid kinjini da wannan dare haka?".
Cikin nutsuwa mama tace.
"Ai daren bai nisaba da saura tukunna dan har yanzu goman dare batai ba".
Murmushi yayi tare da soma koro mata bayanin uban gidan nasu sannan daga karshe ya haÉ—ata da Allah akan kozasu samu?.
A wannan karon mama seda tai dariya tare da furta.
"Haba baban nazir ai ko shiɗin ka turo kai tsaye batare dakayimin wayaba wallahi zan masa bare kuma kai da kanka aikafi ƙarfin komai wajena wallahi karka damu insha Allahu yanzu zan samu na ɗora masa akan gaushi ba matsala".
Wani irin daÉ—i baban nazir yaji atake ya dinga jero mata godiya, har sukai sallama ya katse wayar.
Murmushi mama tayi tare da furta "Haba ai shege shike manta alkairi, abinda kukai mana ai kunfi karfin komai wajena".
Tafaɗa tana miƙewa zuwa tsakar gida da wayar a hannunta, cikin sa,a shahid ya gama dafa indomein sa da ragowar gaushi, ga garin hadarin ya baje se wata sassanyar iska da aketa xubawa, cikin axama ta ɗebo tsakin shinkafar tare da sauran kayan haɗin dambun ta soma aikin yadda zata sarrafashi.
Usman wanda ya kusan ƙarasawa airport shine ya soma kiran layin mama yana addu,ar samun nasara.
Mama tana wankin tsakin shinkafa taji wayarta wadda take kan gujerar tsukunno tana kara.
Dawowa tai da baya ta É—aga, tare dayin sallama duk tunaninta baban nazir ne sabida bata iya karatu ba, yasa bata fahimci cewar number bakuwa bace.
Daman kuma akasari se idan Æ´an biyu ko bebi ko shahid na gida suke mata save sannan idan an kira suke gaya mata wanda ya kira, ko number baban nazirma data amsa kwanakin baya wajan matarshi rahine ajeta tai seda Æ´an biyun suka dawo sannan sukai mata save É—inta.
Jin bakuwar murya yasa mama ta ƙara nutsuwa tare amsa sallamar.
"Mamammu dan Allah ki taimakamin nasan malam salihu yay miki bayani wallahi ta riƙen wuta".
Cire wayar tai daga kunnenta tana mamakin wannan bawan Allah mai barkwanci da saurin sabo haka jiba kamar yasan haka Æ´aÆ´anta ke ce mata.
Jin magiyarshi yasa ta mayar da wayar tana É—an murmushi kaÉ—an.
"Karka damu É—an gidan mama yanzu ma haka dambun Æ´ata yana kan wuta insha Allahu nan da Æ´an mintuna zan kammala seka zo ka amsa kaji É—ana ka bita a hankali kasan mata da ciki se hakuri".
Wani irin kunyar matar usman yaji ta rufeshi tare dajin ƙaunarta dama akwai mutane masu saukin kai kamar haka lallai wannan matar tana da matukar kirki over.
"To mama ta nagode! yanzu haka ina bakin gate na airport zan ɗauke brother na yazo daga legos, in xamu wuce gida sena biyo na amsa, nagode mamata Allah ya ƙara girma Allah ya jikan abbanmu, ki gaisarmin da ƙannena ƴan biyu".
YafaÉ—a tare da kashe wayar.
Murmushi mama tayi batare data ce komai ba ta aje wayar inda ta É—aukota tare da É—auko gyaÉ—a domin ta gyarata.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.