Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 29 of 81
Riƙe haɓa hussaina tayi tare da kallon Bebi, "Malama wayace ki zuba dambu?".
Ta jefa mata tambayar cike dajin haushi.
"Babu wanda yacemin na zuba nice nai niyya sabida motama bata tashi seda mai bareni kuma Æ´ar adam".
"Ai shikenan shegiya jaka ko kunya bakyaji ki xauna kina cin abu a bainan nasi sabida kawai kija wani yace bamuda tarbiya mtswwwwwww!".
TafaÉ—a cikin jin haushi sannan ta nemi gu ta zauna.
"Duk wanda yay min wannan kallon yaje can dayawarshi haka kurum yunwa zata halakamin hanjina kurum senai sanya kema kinsan babu amana a tsakanina nida yunwa".
Miƙewa hussaina tayi ta soma zuba alalen a wani ɗan madaidaicin flate mai ƙaras, yaji ta zuba agefe tare da wadataccen manja.
"Ai sekiyi Bebi, ni banida lokacin shirmenki mike kibi waccan hanyar zakiga step ɗin bene kibishi sosai zakiga hanyoyi sun raba akwai lifter daga hannun dama babu ruwana idan kikai gangancin shiga kika maƙale danta manyan wajan nan ce kaɗai".
TafaÉ—a tana nuna mata hanyar
"Idan kika hau saman benen sosai ze kaiki har inda yay mana kwatance É—azu inma baki gane ba ki tambaya ko a reception ne".
Tafaɗa tana miƙo mata flate ɗin data rufe mata shi.
"Nidai kawai ke kije mana seni nifa bazan gane ba".
"Aidaman baxaki gane ba, sabida bakya gane komai ke! seci dan haka wallahi sekin É—auka kinkai konaci ubanki".
Hussaina tafaÉ—a cikin daure fuska wadda tasaka Bebi É—aukar alalen sabida tasan halin tijarar hussaina wataran daman batada daÉ—in sha'ani.
Ɗauka tayi ta riƙe da hannu biyu ko kallon ƴar uwar batai ba ta soma tafiya seda tai nisa hussaina tai dariya "Ja'ira aike zuma ce naga seda wuta" tafaɗa tana cigaba dayin cinikin kafin Bebin ta dawo.
Tsorata bebi tayi da yadda taga tanata ratsa hanyoyi konace ƙofofin glass manya kafin ta hango step ɗin daga can gefe yawani raba hanya baki ɗayanshi yaji wani irin tiles kamar ruwa ga wani abu nan wanda shitake tunanin koshine lifter ɗinma.
Hanyar step ɗin tabi ta hau saman benen sosai take nishi sabida tafiyar tai mata yawa, da taimakon masu tsaron ƙofofin wajan ta kai har babban reception ɗin saman kafin ta kuma miƙar hannun daman dayace mata ɗazu dayana mata kwatance.
Ita sam bataga wani office ba se guda É—aya jall, cikin hanzari taga wani mutum kamar security ya taso daga saman wani chair zuwa gabanta.
"Hy meya zo dake nan ko baki san dokar wajan nan ba?"
MurguÉ—a baki tayi.
"Toni ina ruwana dawani dokarku,ni gafara na wuce ogan naku dakanshi ne yace na kawo mishi abinci".
TafaÉ—a tana tureshi.
"Ke! Ke!! Ke!!!".
Yake faman faɗa bayan yabi bayanta amman ina Bebi bata jiyowa ba sabida harta kai ga buɗe ƙofar ma tuni ta kutsa kanta.
Shiko sakataren Aliyu mamakine ya kamasa yasan badai Yallaɓai bane zece da wannan tsagerar yarinyar ta kawo mishi abinci ba.
Yasan halin ogan nasu da kamewa baya tunanin yanada lokacin ma kula wasu matan a waje bare wannan, kuma tunda yake dashi baitaɓa siyan abincin waje ba, soyake yay mata bayani ko wajan oga usman tazo seyay mata direction ɗin office ɗinshi tunda nan site ɗin office ɗin MD ne kaɗai a wajan wato Aliyu, wanda yake da comfirm ɗin bashi da yawan surutunma daze jawo wannan mara kunyar wajanshi, komawa kawai yay ya xauna yana mamakin jimawarta bata fitoba tunda yaga ogan bai nan yana son yaje ya fito da ita yana kuma tsoron karyaje koshi ɗinne dai ya ce takai masan tunda yaga yarinyar mai kyau ce, duk da yasan ogan nasu kula mata baya cikin tsarinsa dan kullum lina da kuka take fitowa daga office ɗinshi idan ta shiga to yanzuma ya hana shi barin lina wucewa bare ta shigar mashi office.
Zuwan Aliyu wajan shiya dawo da sakataren daga dogon tunanin daya faÉ—a.
"A,a bala yada wannan nazari haka?" yafaɗa yayin dayake kokarin kai kanshi bakin ƙofar office ɗin nashi wadda inda bebi ta lura zataga an rubuta MD ALIYU IDRISS MAI'ATAMFA! a saman kofar, amman sauri da tsautsayi bai barta ta fahimta ba.
"Yallaɓai amman akwai bakuwa fa aciki".
Yafaɗa yana sada kanshi a ƙasa.
"Bance kada ka kuma bari wannan yarinyar ta shigarmin office ba"! ya faɗa ranshi a matukar ɓace.
Sosa kanshi yay tare da rissunawa.
"A,a ba ita bace wannan wata marar kunyace babu yadda banyi da ita akan kada ta shigaba amman kamar zata zagen ta wuce".
YafaÉ—a muryarshi tai kasa sosai.
"Kai miya xaunar dakai anan miye amafani office ɗinka na farko kafin a shiga nawa inda kana zaune wata ƙazamar bazatai gigin shigar min office ba, Bala! wannan yaxama first and last dazaka kuma barin wata ta shigar min office with out my permission"!!
yafaÉ—a yana wucewa daga wajan fuwwww! yakai bakin kofar ya murda handle ya shiga cikin katafaren office É—in nashi.
Akan desk ya aje tarin takaddun hannunshi tare da file ɗin daya fita dashi, ƙoƙarin nufar special room ɗinshi na ciki yake wanda yake hutawa acikinsa, idan ya gaji, wanda kuma yay dai-dai da lokacin da Bebi ta gaji da tsaiwar jira ta ɗago ƙafafunta zata fita sabida tun zuwanta tana tsaye a bakin frij ta kafe duk tunaninta ko wani uzurinne ya hana usman fitowa shiyasa ta dakata sabida karta koma hussaina ta balbaleta tace mata batada hakurin jira.
Duk sanyin Ac ya gama kashe mata jikinta gefe ɗaya kuma tsananin santin kyan office ɗin take wanda taga tarin computer's kamar me a zube a saman desk kai haɗuwar office ɗin kaɗai ta shagalar da itane harta kasa yunƙurin fita akan kari.wanda hakan ya hanata jin bude kofar tashi, ɗago idanunta, tai waɗanda take kokarin kaisu ga ƙofa sedai mugun ganin datai yasa jikinta yahau rawa harma da mazari.
Cakk! ta tsaya ganinshi tsaye hannunshi aje bisa kan wata system yana kokarin ɗauka xe wuce cikin wannan special room ɗin, hannunta rawa yake wanda ya bata damar sakin flate ɗin dake hannunta jin ƙarar dayay yasashi ɗagowa shima karaf ya sauke idanunshi akanta, kafin kuma tallatsin manjan ya sami damar fallatsa har zuwa saman wandon farin yadin jikinshi.
Cike da wani irin mugun tsoronsa wanda ya kusan sakata suman wucin gadi tai ƙasa da kanta sam baxata iya jurar wannan kallon ƙasƙancin dayake mata ba, tabbas! ta shaidashi wannan shine wannan na jiyan daya bata tsoro ɗan uwan wannan mai kirkin sabida tanada rike abu wannan dalilin yasa bata manta shiba dukda bata da tabbacin kamanninshi amman dai ta shaidashi shine dai!.
Wani irin kallo yake aika mata dashi wanda duk yadda naso na haskoshi nakasa fahimta.
Kafin ya aje system É—in hannunshi bisa desk É—in.
Takowa yake zuwa gabanta idanunshi bisa kanta inda ita kuma take ƙara yin ƙasa da kanta tana kuma jada baya, jikinta yana rawa kamar xata shiɗe, seda takai ƙarshen bangon wajan sannan ta dakata jikinta yana kuma kaɗawa kamar kirjinta ze fito ya faso wani irin mugun fitsarine taji ya kunno mata kamar ze zubo mata tsabar tsoronsa ya saka numfashinta sauka da sauri da sauri, a iya tashinta zata iya cewa bata taɓa ganin mahalukin dataji tana mugun tsoronsa kamar wannan bawan Allahn ba wanda tun daren jiya data ganshi taji batada sukuni gashi yau ma tsautsayi ya kawota har inda yake.
Saukar hannunshi a gefen hijabinta yasa tai wani irin juyi tare da ɗago da fuskarta ta sauke. akan tashi kallo ɗaya tai mishi tai ƙasa da kanta sabida yadda ta hango tashin hankali da rashin mutunci acikin fuskar tashi, rannan nashi a haɗe yake tamau babu alamun sassauci, hannunshi ya kange a gefe da gefenta inda gabaki ɗaya yay mata wani irin rumfa da jikinsa, jitai duk ya cika office ɗin tsananin kamshin mayen turarenshi shiya kuma haifa mata da jin wani iri adukkan ilahirin jikinta.
"Bakida kunya ko?".
Yafaɗa cikin wani irin murya can cikin maƙoshinsa wanda bada ban tsananin kusancin dasukai ba da baxata taɓajin abinda yace mata ba.
Sabida yadda sauran kaÉ—an ya rungumeta, mamakin wannan iskancin nashi take yawani xo yay mata wannan rumfar sekace ya sami Æ´ar iska amman tsoronshi ya hanata tanka mishi.
ÆŠago idanunta tai sega hawaye shaaaaa!!
Duk jitai ta shiga matsi wannan shine farkon kusancinta da É—a namiji a rayuwarta, Rintse idanunta tai wanda ya bashi damar kare mata kallo musamman lashish É—in, daya kwanto saman idanunta, matso da fuskarshi yayi gab da ta'ta har yana fesa mata É—umin numfashinsa wanda yake É—auke da wani irin mayen kamshi na musamman.
Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi jikinta ya kara rawa fiye dana da, wani irin ɗaurewar mara taji wadda take gab da sakin xawo aranta tana dana sani tafi cikin kwando wannan horon nashi yafi duka zafi!
"Waya baki izinin shigomin office? ko nan ma wajan rashin ɗa'a ne"!! taji saukar muryarshi acikin kunnenta ƙoƙarin zamewa takeyi tai ƙasa amman yaƙi bata damar aiwatar da hakan, sema kurawa kirjinta idanu dayay yana kallon yadda yake fat! fat!! alamun takai ƙololuwar ƙarshen jin tsoronsa.
Murmushin geben baki yay yana kuma hukuntata da idanunsa kafin ya kuma cewa.
"Nisa'anki ne banson nai maimaicin magana wallahi maganata ta biyu bara tai miki daÉ—i ba".
Cikin rawar murya wadda take rarrabewa.
"Dan...dan...Allah....kai....kai...ha...ha..ƙu..ri..".
TafaÉ—a tana janyo numfashinta wanda takejin ya gauraye danashi, zuwa lokacin kukanta ya soma fitowa fili.
Nikaina mai rubutun nayi mamakin kukan bebi mai taurin zuciya amman takewa kallon Aliyu kaÉ—ai kuka! wanda ko ciwo take bata masa kuka amman yau iya kallon Aliyu kaÉ—ai ya É—aga mata hankali lallai Ali mazan fama ne!
"Nibance kimin kuka ba malama tambayarki nike maye ya shigo dake office É—ina, har ana miki magana a waje kikai rashin kunya ko?"
YafaÉ—a yana É—an jada baya kaÉ—an yana kuma kallon yadda take faman sheko hawaye kamar famfo.
"Kayi haƙuri wannan farinne yace na kawo mishi alale".
Ya fahimce ta tsaff amman seya basar.
"Ai office ɗin baƙin kikazo ko baki kula ba, to danma ke sakarai ce tayaya baki san waje ba zaki shigo kanki tsaye agarinku na marasa kan gado ake haka? keba mace bace koko haka kikaga mata na shiga wajan namiji kansu tsaye?".
YafaÉ—a yana matsawa daga inda take sosai ya basu tazara yana kallon yadda taki É—ago idonta.
"ÆŠago ki dubeni shashasha wannan yazama karo na karshe dazan kara ganin wannan jar fuskartaki anan arean"!!
Saurin É—agowa tai sekuma tai saurin mayar da kanta sabida ganin yadda ya zaro mata manyan idanunshi duka waje waÉ—anda suka kusan sumarta.
kafin taga ya juya bayanshi cike da zafin nama yabar wajan ya shiga ɗayan ƙofar wanda hakan ya bata damar tattare rigarta ta bawa wondonta iska aguje ta fita daga office ɗin tana haki, hamdala tai ganin bataga wannan na ɗazun ba, seda ta sauka ƙasa sannan ta sami wata kwana ta zauna dabar tana mayar da numfashi mai haɗe da hawaye da majina sabida takai kololuwar tsorata........................
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.