Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 2 of 81
*AUTAR MANYA*👉👈
_LITTAFIN KYAUTA NE BANA SAIDA WA BA AMMAN RASHIN COMMENT ZE SAKA YA KOMA NA KUÆŠI, INA MATA MASU SON A TALLA MUSU HAJARSU, ZASU IYA NEMANA TA WATSAP NUMBER TA_
11/14/21, 3:05 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
  { _HOT LOVE_ }
     Â
     NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
           Â
             *002*
Tsaye tayi abakin titin ruwan yana kuma jiƙa mata jikinta, ganin yamma tana kumayi magariba tana kawo kai, yasa ta yanke shawarar bita lunguna, hakance ta faru ta lunguna tabi har zuwa cikin layinsu wanda yake da tazara sosai a tsakaninsu da wajan dasuke kai awarar.
Nufar bakin wani ɗan ƙaramin gida tayi wanda katangar gidan take ƴar ƙarama domin batafi taku uku ba, yaye labulan buhun da aka rufe ƙofar gidan dashi tayi, tare da ɗanyi ƙasa da kanta gudun bugewa domin tsayinta yaywa. ƙofar kaɗan, karo sukaci da wani ɗan matashin namiji wanda baifi shekaru goma sha bakwai ba, kallo ɗaya zaka masa ka gane shiɗin yayanta ne, da kallo ya bita"Kedai kinji kunya wallahi kullum cikin saka mama a damuwa kike, to yanzu ma wai daga gidan ubanwa kike, kin ɗagawa kowa hankali?" yafaɗa yana kawo mata hannu kamar ze bugeta, da gudu tai baya tana watsa masa harara" wai kai shahid ɗin nan meya ruwanka dani ne kuɗin awarar uwata akacinye shine naje nabi bashin tunda ƴan biyu su baxasu iya ba".......,"Seke tsagera?" yafaɗa yana zabga mata harara, bata bi takansa ba tai cikin gidan, shima sabida yasan bazata raga masa ba yasa yay wajan gawayin sa dayake saidawa acan bayan layinsu.
Wani ɗan mitsitsin tsakar gida ta shiga tare da fara kiran "Mama! mama!! mama!!!, kina ina ga ƴar albarkarki ta iso" tafaɗa da ƙarfi tare da tsayawa ƙyam a tsakar gidan batare data shiga ɗakinsu ba.
Cikin sauri wata farar mace tas ta fito daga cikin ɗakin dayake ƙwaya ɗaya tall acikin gidan, kallo ɗaya zaka mata kagane ita ɗin mai kyauce kuma mahaifiya ga bebi domin ga kama nan kamar an tsaga kara,da sauri ta ƙaraso gabanta tare da riƙo hannunta tajata zuwa cikin ɗakin data fito daga cikinsa , wanda yake shinfiɗe da ledar, tsakar ɗaki tare da ƙatuwar kafita se sip ta kaya, ƴan biyu suna zaune akan katifar suna kallo a ƴar wayar mama, se arfa da ihsan a gefe suna cin taliya, suna shiga ta saki hannunta tare da haɗe ranta kaɗan "Yanzu bebi kullum sekin ɓata min raina kike jin daɗi?" tafaɗa muryarta tana karkarwa, da kallo bebi.
tabi mama tare da cewa"Mama kuɗin awararmu fa na tsaya na amsar mana idan kuma ƙarya nake gobe muje dake wajansu"girgiza kai mama tayi tare da cewa"Bana son jin ba,asi kullum ina gaya miki cewar duk wanda yaci awarar nan bai baku kuɗi ba to ku barshi da ALLAH, ke mace ce bebi bana son wannan faɗace-faɗacen naki sabida baki san bakin wani ba".dira ƙafafunta tafara a ƙasa tana ƙoƙarin sakin kukan shagwaɓa, "Haba mama idan nabar musu kuɗin dame zamu dinga cin abinci wallahi mama indai akan haƙƙina ne se inda ƙarfina ya ƙare", da kallo mama ta bita tana mamakin halin ƴar tata, sam batayo halin kowa na gidanba, mama bata ƙara shan mamakin bebi,
ba seda ta zayyane mata yadda sukai har zuwa wajan ƴan sandan datayi sannan ta fito da ɗari biyun data amso ta miƙa mata sannan tai rau rau da idanunta"Mama dan ALLAH kibani ɗari aciki anjima na siyo nama wallahi miyauna har tsinkewa yake sabida ƙwaɗayi". cikin mamaki mama tace"Kice zuwa kikai wajan maza kika nuna rashin tarbiya harda tube hijabi wato haka na baku tarbiya?,haka kikaga ƴan uwanki sunayi BILKISU soki ke kijamin maganar dangin ubanku ko?, dasuka zuba mana ido suga gudun ruwanmu?" tafaɗa tana kokarin kai mata hannu, da baya tai waje tana furta"Mama bazan kuma ba" tana yarfe hannayenta.
Zama mama tayi a bakin katifa tare da kallon Æ´an biyu dasukai tsuru batare dasun cigaba da kallon da sukeba suna sauraran dramar bebi da mama, suna kuma tsoron suyi magana tai musu rashin kunya.
"Ya salam ni Aishatu ALLAH ka kawomin sauƙi cikin lamuran wannan yarinya, na haifeki ban haifi halinki ba" ta faɗa a fili, hassana ce ta dubi mama, tare da ɗan matsowa gabanta kaɗan bayan ta taso daga kwanciyar datayi, dafa hannun mama tayi tare da cewa.
"Mama kiyi haƙuri haƙiƙa Bebi tana buƙatar addu'arki, ta uwa mama ki ɗora akan wadda kike insha Allahu babu abinda ze faru se alkairi".
TafaÉ—a cikin nutsuwa, É—an murmushi mama ta saki, kaÉ—an tare da kallon hassana tana yaba irin baiwa tare da hankali irin ta Æ´an biyun, nata, kana tace.
"Hakane Allah ya rufa asiri". daga haka ta miƙe ta fita zuwa tsakar gidan tsugunne taga Bebi, ga ruwan yanata faman dukan jikinta, sabida da yaɗan tsagaita amman yanzu ya dawo da ƙarfinsa, ruwan taɗan sharce daga fuskarta, wanda yake faman zubowa tamkar da bakin ƙwarya, itama mama duk yabi ya jiƙa mata jikinta.
"Watakam so kike ki sakani cacar siyan maganin zazzaɓi ko Bebi?" tafaɗa tana kallonta.
Cikin tsoron dukan mama Bebi ta É—ago idanuwanta da suka firfito tare da cewa"Dan Allah mama kada ki dakeni, wallahi yunwa nakeji rabona da abinci tun safe". tausayin Bebi ne ya kama mama.
Da kallo tabi Æ´ar ta'ta tare da cewa.......
"Bazan miki komai ba bebi maza ki tashi ki shiga cikin ƴan uwanki, amman ki tuɓe kayan jikin naki tukunna".
Mama ta faɗa tare da shiga cikin wani ɗan ƙaramin kicin wanda baze ɗauki mutum biyu ba, ko mutum ɗayan nema seyay da gaske, irinsu bebi masu ƙiba kuwa ma yay musu kaɗan.
Cikin rawar ɗari Bebi ta ƙarasa cikin ɗakin nasu harara! ta watsawa hussaina wadda take baje a katifa tana kallo, sannan ta bugawa su ihsan tsawa! "Dalla ku rufe idanuwan ku zan tube kayana".
Cikin sauri yaran suka rintse idanuwansu, janyo marufin sip É—insu tayi tare da kare rabin jikinta, sannan ta tube kayan jikin nata waÉ—anda sukai sharkaf har É—iga suke.
Ko ɗaɗɗiyar atamfa riga da zani ta ɗauko wadda da ƙyar ta saka rigar sannan ta ɗaura zani ajikinta wanda kayan ya sami damar kama mata jiki ɗam ɗam.
Hijabi ta É—auka ta saka sannan ta É—ebe kayan data cire ta fita waje, igiya taje ta shanya duk da ruwan har yanxu yana sauka.
Bayan ta kammala ta nufi cikin ɗan madai daicin banɗakinsu wanda yake wanke ƙar ƙar, kama ruwa tayi tare da fitowa ta dauro alwala, shiga ɗakin ta kumayi ta shinfiɗa sallaya tare da tayar da sallar la'asar wadda ta makare mata.
Bayan ta idar ko hijabin bata cire ba tayi waje lokacin an ɗauke ruwan dan duk su hassana suna tsakar gidan har sun gyara shi sun goge ruwan daya jiƙa tsakar gidan.
Duk suna zaune hussaina tana tankaɗen garin tuwan dare wanda shahid ke fita dashi can cikin kasuwar sharaɗa kai da ƙafa.
Hassana kuma tana daka kayan miya danginsu daddawa da sauransu, ihsan wadda bazata wuce shekaru goma sha biyu ba, tana faman wanke Æ´an kwanika a bakin rariya.
Kanta tsaye ƙofar kicin ta nufa tare da tsayawa"Mama abani abinci yunwa nakeji".
Juyowa mama tayi duk fuskarta tagama haɗewa da gumin haƙayin itacen dayabi ya addabi kicin ɗin, ni kaina seda nabi fuskar mamansu bebi da kallo sabida yadda take da tsananin kyau ɗan gaske farace jajur kamar ka taɓa jini ya fito sedai kuma wahala ta saka duk jan maman ya du sashe sedai kuma tsantsar kyanta ɗan gaske! har yanzu yana nan bai gushe ba.
"To Bebi baki ga yanzu nake kici-kicin na haÉ—a ruÉ—en tuwan ba?, ai kya jira na gama ko?".
Zaro idanu Bebi tayi waje wanda hakan yake acikin al'adar rayuwarta muddin zatai magana seta zaro su duka waje, sannan ta haÉ—e ranta tamau kamar kace mata kat! ta fashe, sannan ta soma magana muryarta tana rawa kamar zatayi kuka!.
"Mama yunwa nakeji wallahi tun safe dana sha koko har yanzu ban kuma kai mai É—umi cikina ba".
Ta ƙarasa maganar tana zubo da hawaye! shaaaaaaaa, kamar famfom.
Mama bata kula Bebin ba illa cigaban datayi da tuƙa ruɗenta harta kammala sannan ta fito waje ta wuce Bebi wadda take ta faman kukan yunwa.
Abakin Æ´ar tabarmar da su hassana ke kai mama ta xauna sannan ta É—an É—aga murya kaÉ—an.
"Wai ke! Yaushe zaki hankaline?, Nace yaushe zaki hankaline?, idan da abincin nan me zanyi dashi dazan aje naƙi baki?".
Ta kalli Bebi cikin jin haushinta.
"Wallahi tunda kuka tafi tallah ban ɗora ko ƙwayar hatsi acikin gidan nan ba, ina zaune ina jiran ikon Allah, shahid ne yazo da taliya leda ɗaya, ita na dafa na zubawa, su ihsan shima na zuba masa, ina jiran ku dawo naga abinda Allah ze mana, sam hankalina ya tafi ga inga na haɗe kuɗaɗan nan na shahid ya zana jarabar wannan kema na baki kuɗin jarrabar shiga aji huɗun nan amman har yanzu abin yaƙi tafiya, seki zauna kijira in gama tuwo kici tunda ke har yanzu baki san abinda yake dai dai ba".
Mama ta ƙarashe maganar tana jin ranta na mata suya na halin kunci da rashin da suke ciki.
"Mama dan Allah ki rabu da ita, ga ruwa can a randa tasha ta jira tuwo".cewar hussaina wadda taÉ—anfi hassana zafi.
Wata uwar harara! Bebi ta makawa hussaina tare dajan tsaki! batare datayi magana ba taja ƙafafunta zuwa cikin ɗakinsu.
Rufda ciki tayi tare da sakin kuka! "Ya Allah ka kawo mana É—aukin ka na alkairi a wannan zamanin talaka yana cikin matsala...............
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.