Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 22 of 81
_KANO_
Babu laifi Bebi ta sami bacci sosai dan har akai kiran sallar magariba bata tashiba seda mama ta saka ihsan taje ta tawosa............!
*KUYI HAKURI KU ƘARA HAKURI AKAN WANDA KUKE ALLAH YA BAKU IKON BANI ZAFAFAN COMMENTS NIKUMA YA BANI IKON BAKU ZAFAFAN PAGE AUTARKU CE* 👉👈
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
  { _HOT LOVE_ }
     Â
     NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
            Â
            *29&30*
Babu laifi Bebi ta sami bacci sosai domin se dama aka kirawo sallar magariba sannan mama tasa ihsan taje ta tasota, murza idanunta tayi tare da mikewa zaune duk jikinta yayi sanyi ƙalau haka ta tashi ta fito tsakar gida, seda ta shiga bayi ta wanke jikinta sannan tazo gaban mama saman tabarma ta zauna.
"Ke malama tashi kije ki É—auro alwala ki gabatar da azkar É—inki, bana son sakarci ta haka shaidanu ke shigar macen datake haila bata yawaita alwala da addu'oin tsari".
Babu musu ta mike taje ta É—auro alwala ta wuce É—aki sabida tsakar gidan duk su mama sun shinfiÉ—a katuwar tabarma suna sallah.
Zama tayi tare da fara gabatar da karatun azkar É—in maraice, tana kammalawa ta fito tsakar gida lokacin suma sun idar da sallar bataiwa kowa magana ba taja ta zauna tare da zuba tagumi, itafa Bebi wannan tsumman na jikinta duk shine ya dugunzuma mata hankali( wayyo! cikina dariyar bebi karki kasheni ) da kallo mama ta bita kana tace.
"Waini yau meya sami uwata ne?, naga tun ɗazu taƙi magana ya Allah ya ubangiji kasa sanadin wannan girma dayazo miki yasa sanadin samun nutsuwarki ne kamar haka".mama takai maganar ƴan biyu suka cafe da "Amin mama wallahi yau gidan sakayau".murguɗa baki tai hartana danna shi gaba"Nifa mama wannan tsumman ya ishan wallahi yarda shi zanyi na huta haba abu se soken.........",Batara ƙarasa ba mama tace.
"Kull nakuma jin kin faɗi haka wallahi kika yarda se ranki ya ɓaci dan ubanki haka zaki dinga yawo jini na ɓata miki jikinki Eye?"tafaɗa mata fuskarta a daure domin tasan halin ƴar tata da wauta zata iya yardawa ɗin.
"Nidai Allah kuwan".ta faÉ—a fuww ta mike tayi cikin É—aki tana gunguni itafa ya dameta da haka wani baccin ya kuma fisgarta sabida har yanzu jikin nata bai wani yi garau ba, ko abincin dare bata ciba mama tace su barta kawai tasan halinta tana tashi tsakar dare setaci.
Suma sunayin sallar isha'i sukai cikin ɗaki sabida hadarin daya haɗo a garin koda suka shiga ɗaki hussanai ce ta dubi mama tare da cewa.....
"Mama goben dai sedai ni inje É—in naga Æ´ar taki babu lafiya?".
TafaÉ—a tana kwanciya gefen hassana.
"A,a idan ta warke sesuje ai babu wani damuwa Allah dai ya nuna mana goben".
Mama ta faÉ—a itama tana kwanciya a gefensu hassanar abinka da jikin talaka na gajiya ko cikakken minti goma basuyi ba bacci yay awon gaba dasu.
Shahid ne kaÉ—ai ke budurinshi a tsakar gida yana É—an dafa indomie É—inshi harya kammala yaci shima ya kwanta a É—an shagonshi na soro.
_YAHAYA GUSAU_
*GIÆŠAÆŠO MAI ATAMFA ESTATE*
Cikin harabar estate É—in motar usman take danna kanta wanda ya baiwa masu tsaron gidan damar tawowa aguje! zuwa gaban mahaukacin katon gate É—in gidan suka budewa usman gate É—in cikin barkwanci yake gaisawa da sojojin waÉ—anda sune ke tsaron gidan sannan yaja motarshi a hankali har cikin parking space, revars yayi kafin ya gyara parking É—inshi sannan ya kashe motar tare da fitowa yana xagayawa ta baya ya É—auko jakarshi ta office tare da kular dambu, ya dauki hanyar gate É—insu wanda shine daga gefe, turashi yay tare da bude kofar part É—inshi ya shiga cikin babban falonshi bakinshi dauke da sallama.
Matarshi Zainab tana zaune a ƙasan carfet tana kallo a tv shigowarshi yasata tashi da ƙyar tana mishi barka da zuwa cike da tattali da kulawa.
Cikin wani irin salo ya jawota hade da cikin yawani rungume batare daya aje kayan hannunshi ba, seda taÉ—an zame tare da karbar kular dambun da jakar hannunshi ta shige gabanshi tai masa jagora zuwa É—akinshi, yanayin yadda usman yakewa zainab dolema ya dinga baiwa Ali haushi konima nace anya.....!
Bai samu tayin wankan ba yau, illah haɗa mishi ruwan dumi datayi kaɗai sabida hankalinta na wajan dambu wanda tun a cikin ɗakin ta soma kaishi bakinta tana yi tana lumshe ido jitake kamar karya kare amman lomarta batafi biyar ba taji wayam babu dambun babu alamunshi.
Cikin kwaÉ—ayin shi taja ta zauna ta rafka tagumi har seda usman É—in ya fito ganinta babu yadda take yasaka shi saurin karasowa gabanta.
"Sweet heart what wrong with you?".
YafaÉ—a yana tallafota zuwa jikinshi har yana goga mata ruwan daya rage jikinshi na wanka.
Turo bakinta tayi gaba sega hawaye nan shaaaa!!
"Ni wallahi wannan dambun bai isheni ba Allah senaci zan iya bacci, kuma bana ammi kona hajiya ba, na waÉ—anda naci yanzu nikeso".
Dum!Dum kirjin usman ya bada sautin tare da zamewa ya zauna.
sunayen Allah ya shiga jerowa dama haka mata masu cikin suke?.
Shi yanzu an riga anyi sallar magariba ta ina ze, iya tunkarar gidan wasu?, infact ma ta ina yasan gidan.
Marairaicewa yayi tare da cewa.
"Kiyimin hakuri Cwt gobe insha Allahu zanxo dashi mai yawa amman yanzu kinga Aliyu zanje na É—auko a airport sannan kuma banje na gaisa da abba ba".
Tashi tayi daga wajan tana jin wani iri aranta batajin zata iya kai haƙarƙarinta gado in bata kuma kai wannan dambun bakinta ba
Agurguje ya shirya kanshi cikin manyan kaya tare dayin alwalar magariba ya fita masallaci.
Koda ya dawo ma part É—insu ya koma anan babban falon ammi ya sami abbansu yayi mishi barka da hanya sannan ya nemi guri ze Zauna sabida ammi ta dakatar dashi akan maganar bikin Aliyu wanda za,ai next week.
Ganin ankusa kiran sallar isha'i ga maganar taki ta kare tsabar complain ammin ke mashi akan halin É—an uwan nashi,yasa abba katse wa ammi hanzari"Kai shehu maza ni kaje airport ka É—aukomin babana idan yaso ka dawo kucigaba daga inda kuka tsaya".
Murmushi usman yayi tare da mikewa yana jinjina girman soyayyar abbansu da Aliyu.
Sallama yay dasu ammi kana ya koma part ɗinshi ganin yadda zainab matarshi ta hade kanta da gwiwa yay matukar girgizashi, cikin sauri ya karasa gareta yana yi mata magana kasa kasa, duk yadda yakai ga dadin bakinshi taƙi bashi haɗin kan magana itafa dambun nan dai zata kara ci.
Aranshi jaje yakewa kanshi na kaika jawa kanka amman a fili, lallaɓata yake yana kuma ce mata insha Allahu zega yadda zeyi ta samu taci ɗin da ƙyar ya samu ta saki ranta sannan ya ɗansha tea kana ya dauki keyn motarshi ganin 900:pm ta kusa kuma jirginsu Aliyu sauran mintuna kaɗan ya sauka.
Har waje ta rakashi.
Sannan ta jawo jikinta ta koma falon shikuma ya karasa parking space ya shiga motarshi.
_AYI HAƘURI A ƘARA HAƘURI A KUMA YIN HAƘURI AKAN WANDA MUKE BAKI ƊAYA ALLAH YA ƘARA MANA HAƘURI DA JUNA AMIN_
_MASU MIN MAGANA AKAN BOOKS ÆŠINA DANA GAMA COMPLT DOCUMENT GASU KAMAR HAKA_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.