Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 49 of 81
****************
Yau kam babu uwar da aka tsinana agidansu bebi sabida yadda ta É—agawa kowa hankali hatta shahid dake wajan gawayinshi seda Tasa ihsan ta kira mata shi yana zuwa ta dubeshi.
"Shahid ka yafemin kaga yadda rayuwata zata koma ko? na tashi bada shirin aure ba yau an É—aura min aure zanje nai zaman da bani da masaniyyar yadda zan kasance ko zaku sake ganina a raye ko rasuwa zanyi oho?".
TafaÉ—a tana kwanciya a saman cinyar hussaina wadda itama kukan take.
Kai jama'a nimafa kaina seda nayi kukan sabida su bebi yadda suka taso bacci tare komansu tare bada ban auren ko mutuwa ba meze rabasu da junansu musamman ita da bata san waye mijin nataba batasan yaya zata tarki zaman auren ba infact ma bebi yarinya ce batada wani ilimi akan rayuwar aure ga auren nata yazo mata a kurewar lokaci batare da mama tai tunanin sanar da ita komai ba ya ALLAH ka bawa ALIYU ikon riƙe marainiyarka da amana amin, wannan itace addu,ar daya kamata muyiwa bebi kenan.
Cikin sanyin jiki shahid ke dubanta yana ayyana wannan lamari mai sarƙaƙiya shi kansa da mama ta gaya masa maganar auren bebi seda jikinshi yay sanyi.
"Ki kwantar da hankalinki ai xamuke zuwa sannan kuma bazaki mutuba insha ALLAHU ina miki fatan alkairi acikim zama aurenki shikuma ALLAH ya bashi ikon riƙeki da amana amin".
YafaÉ—a yana share hawayenshi.
"Kaima haka zakace shahid yanzu shikenan na daina ganinka nadaina faÉ—a dakai nadaina cinye maka indomin ka"!!
Se ta kuma fashewa da wani irin kuka daya saka mama ta tsaya cak da haÉ—a mata kayan datakeyi a cikin jakarta.
Tasowa tai tana rarrashinta da ƙyar ta samu tai shuru sannan hassana ta fita dan ɗora girki ganin magariba ta ƙarato.
Ana idar da sallah mama tasa bebi ta shiga wanka...................
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *PART* 2
NAKUÆŠINE
               *69*
Da kuka da gaddama mama ta samu bebi ta yarda ta shiga wankan domin seda ta haɗa mata da jan idanu sannan ta shiga tana dira ƙafafunta a ƙasa kamar wata ƙaramar yarinya.
Bata wani jimaba ta fito ƙafafunta ma basusan mai tai ba, mama tana tsakar gida agaban murhu tana firfita gawayin data ɗiba ciki ta zuba acikin kaskon turaren wuta, itace ta ɗauko ta dubi Bebi da mamaki kafin ta ɗaga murya ta kira "Hassana! zo maza ki ganemin kafafun ƴar nan ni kada tace ban gani ba sosai gwarake ƴar zamani ce baki tsufaba" cewar mama tana makawa bebi harara.
Cikin dariya hassana ta fito daga É—aki jikinta sanye da hijabin sallah tana cewa.
"Kai mama dan Allah in wani yaji base yazata ke tsohuwa bace duka dukafa mune na farko kuma.mudin nawa muke?" da sauri mama ta kwaÉ—o mata É—an maficin dake hannunta cikin wasa da barkwanci tana ce mata.
"Ke banson shirme mukam ai shekaru sunja sekuma fatan cikawa da imani".
Murmushi hassana tayi tana furta amin sannan tabi kafafun bebi da kallo tana ƙunshe dariyarta.
"Haba hajiya bilkisu mai gadon zinare in bada ban abinki ba tayaya wannan kafa taga ruwa nima dai mama banga komai a wannan ƙafarba".
Tafaɗa tana ƙara bin ƙafafun bebin da kallo.
"Karki ɓatamin rai maza ki koma kije ki dirjen ƙafafun nan banson shirmen banza da wofi".
Tura baki tai ta kuma danna shi gaba kamar zata taɓo ƙofar gidan sannan ta dubi mama
Tare da zubo da hawaye sannan ta shiga banɗakin aikuwa ta bugo ƙofar da ƙarfi kamar zata ɓallata.
Watsa ruwa tai tare da saɓawa soson data haɗa da sabulu ta wanke ƙafar, tare da watso ruwa samanta sannan ta fito gaban rijiya taje ta ɗibi ruwa tai alwala batabi takan kowaba ta saka doguwar rigar da ko arzikin bra da pant babu haka ta zir ƙaton hijabi ta tayar da sallar tana idawa ta soma azkar har akai sallan isha tana kan darduma.
Tana sakawa da kwancewar Æ´an gidansu sun tsaneta gwarama ta tafi gidan mijin ko yankata ze ta zauna sabida yadda suka shareta sukai zamansu a tsakar gida.
Daga can tsakar gidan kuwa mama ta ƴan biyune zaune da arfa da ihsan da shahid sun zagaye kwanon gyaɗa suna ɓareta suna cin kayarsu, sabida mama taga take taken Bebi inta cika shiga harkarta damula komai zatayi wanda daman koda batai wannan auren bama ai aure yazama dole su kansu ƴan biyun nan da watanni ne sun tafi gidajen su, dan haka ta tattare kan ƴaƴanta suka barowa bebin ɗakin ita ɗaya suka baje a tsakar gida suna sharafin gabansu.
Wanda wannan shariyar ta kusan saka bebi bindigar zuci.
Sallamar malam lado itace ta katsewa mama labarin datake bawa Æ´aÆ´an nata sannan ta amsa cikin sakin fuska tana ture gyaÉ—ar gabanta.
Cikin sauri shahid ya samasa tabarma daga gefen ɗakin mama sannan suka gaisar da malam ɗin suka tattara suka bar wajan suka shiga ɗaki dukkansu sabida a tarbiyar data basu bazama agabanta in tai baƙo ko wani irine kuwa baƙon.
"Malam ina wuni ina gajiya yaya hidima kuma angode ALLAH ya ƙara girma amin".
TafaÉ—a tana É—an gyara mayafin dake jikinta.
"Alhamdulillahi mijin nata basu ƙaraso ba, naji shurune nima yasa nace bara na shigo sabida, halin rayuwa ALLAH yasa dai lafiya danni bana ƙaunar gobe waɗancan azzaluman su tarar da ita a gabanmu sabida zasu iya yin komai domin ganin sun hana tariyarta".
Gaban mama ne ya tsinke ya faÉ—i nan da nan wata zufa take kara kaini bisa goshinta shaff ta manta da wannan cakwakiyar seda malam É—in ya sanar mata dan har tana cewa bebi bazata tare ba setayi É—an taronta ko iya yinin uwane, bayan haka kuma tana son amsar adashinta taÉ—an saiwa bebi kayan É—aki dana tsakar gida sabida babu lefe kuma itama komai yazo mata a kure bare tai shirinta irin na uwa mace.
"Basu zoba malam amman meze hana mu kaita ko gidansu iya ne in yaso duk sanda yazo semu É—auko ta ni wannan masifa dame tai kama"!
Murmushi malam yay irin nasu na manya sannan ya dubi mama yace.
"Haba Aishatu ai zancen masifa ya kare sedai duk wanda ya É—auko da zafi ta faÉ—a masa, itadai yarinya ALLAH ya rufa mata asiri".
Yan nisa da maganar sannan ya cigaba da cewa...........................
"Abu nagaba kuma shine dagani harke a yanxu alhakin haƙƙin bilkisu ya sauka daga kammu yana hannun shi mijin nata dan haka bazamu zartar da komaiba harse munji daga bakin shi mijin nata sannan semuji abinda yake da akwai, amman ni a tunanina mu miƙa yarinyar nan gaban mijinta yafi inyaso komi ze faru daga baya semuji".
ÆŠan nazarin maganar malam mama tayi sannan ta É—ora da cewa.
"Hakan yafi ai duk abinda kace babu fashi malam ina laifinka daka tsaya mana kafa tuna wannan gidan damuke ciki kai kabamu me muka haÉ—a dakai inba mutuncinba tabbas kaimana abinda ALLAH ne kaÉ—ai ze biyaka badai mutumba, haka zalika iyalanka suma sunyi mana domin komai na rayuwa baya faruwa seda sanadi tare da sila, yau inda rahinatu É—iyarka ta farko batazomin da maganar cinikin kamfaniba da tayaya wannan yaro zega bebi aikwa kaga komai ya faru damu na alkairi kaine sanadi malam ni mutum ce wadda tasan alkairi komai kankantar sa hakanan komai girmansa wallahi yadda mahaifinsu ze zartar da komai akansu batare danai musuba tofa kaima É—in hakane dan haka waÉ—annan yara nawa jikokin kane halak malak malam se yadda kace kuma nagode da yadda ka nunamin akan yaran nan ALLAH yasa ta dalilinsu a rayuwa ka huta kaji daÉ—i fiye da wanda kake ciki yanzu".
Murmushi malam yay tare da furta.
"Amin Aishatu!Ai kinsan rayuwar duniya inji ɗan hausa yace inkaji wane ba banza ba, in bai sha wuyar dare ba tofa yasha ta rana! dan haka kowa kagani da arziƙinshi, sefa yasha wahala kafin ya sami arzkin, shi kansa mahaifin yaron daya auri balkin ai ɗan ƙauye ne!a ɗanbatta yake bakiga gwaramar dayasha ba kafin yazama hakan, wallahi bantaba ganin mutum irinshi ba yasan darajar ɗan adam akwai alkairi inkinga yadda yake taimako agarin nan se ALLAH shiyasa nai farin ciki da balki ta auri ɗansa na cikinsa ko badan arzkinsuba wallahi iya karamcinsu ma da tarbiyrsu abinso ne".
Cikin mamaki mama ta dubi malam tana tambayarshi daman yasan gidansu Usman?.
Sosai malam ya gyara zama yana fayyace mata kyawun hali irin na mahaifin Aliyu.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.