Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 47 of 81

*NA KUÆŠINE*
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *PART* 2

NAKUÆŠINE

                            *67*

Babu abinda kakeji acikin ƙayataccen falon nasu, face ƙarar na'urar sanyaya ɗaki tare kuma da ƙarar cokalin da khadija ke ɗiban dankalin turawan dayake cikin plate ɗin gabanta tana ci ahankali ciki nutsuwa tare da tsantsar iyayi.
Yana shan tea ɗin yana lumshe idanunshi yana jin daɗin yadda kayan kamshin cikinshi ke ratsa mishi maƙogoronshi yana jin daɗinshi sosai musamman yadda kamshin ke dukan hancinshi.
Harya kammala ya dire cup ɗin idanun khadija yana bisa kanshi hamdala tayi ga sarki Allah sannan ta miƙo mashi dankalin data zuba mishi cikin plate wanda yace bazeci ba seyasha tea tukunna.
Ɗan ƙyafe bakinshi yayi kaɗan batare daya kalli plate ɗin ba, sabida yadda yaji cikinshi ya ƙoshi.
"Yaya kaci wannan É—in".
Muryarta ta dokin kunnenshi, É—an juyowa yay kaÉ—an.
"Am ok"
Abinda ya faÉ—i kenan yana juya kanshi yana kallon side É—in Tv.
"Please yaya kaɗan ci koyaya danfa kai na tashi tun six nayi maka break fast mai ƙayatarwa haba mana my cwt man dan Allah kaci".
Tafaɗi maganar cikin sigar shagwaɓa.
Bayanson hayaniya hakanan kuma bayason watsa mata ƙasa bisa idanunta sabida shi mutum ne dayasan ƙimar ɗan adam sam baison yay mata abinda bazata ji daɗi ba, musamman yanzu datake ƙarƙashinsa, duk da bai sonta ko kaɗan amman bai tunanin ze iya cutar da ita ko ƙuntata mata domin shi lamarin aure na Allah ne.
Jan plate ɗin yay gabanshi sannan ya tanƙwashe ƙafafunshi abisa ƙa'idar tarbiyar cin abinci.
Batare daya É—auki spoon ba, ya É—anja hannun rigarshi sannan ya saka hannunshi na dama yay bisimillah sannan ya soma cin abincin, Cike da nutsuwa.
Ta cikin ƙasan idanunta take kallon yadda yake cin abincin nashi cikin nutsuwa yanayi kamar baison cin abincin wanda hakan kamar acikin tsarinshi yake.
Yakai kusan mintuna biyar yana cin abincin amman kuma baifi loma uku ba, sannan ya ɗan janye plate ɗin daga gabanshi, ya miƙe tare da shiga cikin kicin ɗin dake falon, ya wanke hannunshi, ya ɗauki tiesue ɗin dake saman frij ya goge hannunshi da bakinshi ya jefa a dustbin ɗin dake gefen frij amman bawai irin wanda ake zuba shara bane ba, wanda ake ɗan zuba tarkacen dattin dake falo ne, sannan ya karasa saman seater ya zauna ya ɗauki remote control, yana serching channel, tashar saudi ya kamo tare da ɗan kwantar da kanshi yana kallonshi.
Itama khadijan miƙewa tai daga wajan cikin nutsuwa ta kwashe kwanukan tanajin ranta yay mata sanyi ganin yadda yaci abincin nata, kaiwa kicin tayi sannan ta koma ta ɗauko kayan gyaran waje ta gyare wajan tas duk daba datti yay ba sabida cin abincin nasu cikin nutsuwa sukai, sannan ta ɗauko room freshner ta fesa, wanda nan da nan ƙamshi mai sanyi ya ƙara cika falon, Seda ta tabbatar da tsaftar wajan sannan tazo kusada shi ta zauna daga saman ɗayan seater ɗin dake kusa dashi.
Itama tana kallon amman rabin hankalinta yana wajanshi tana kuma sake tsinkewa da lamarinshi na rashin maganarshi ace mutum kamar bebe.
"ÆŠaukomin wayata acan".
Ya nuna mata can wajan center carpet inda sukai break fast.
Cikin sauri taje ta É—auko mishi ita sannan ta miko mashi cikin nutsuwa.
Amsa yay yana kunnata.
Yana ƙoƙarin ɗorata a gefenshi yasomajin ringing! Cikin nutsuwa ya duba saman screen ɗin wayar sunan usman ne ya fito ɓaro ɓaro.
Mr Man.
Serving É—in dayay ma usman kenan acikin wayar tashi, Cikin É—an sakin fuska ya É—auki wayar yana karawa a kunnenshi.
"Hellow kai wai wani irin mutum ne anata kiran wayarka tun safe akashe ina ka shigane?".
Murmushi yay na gefen baki wanda ke ƙara mishi tsabar kyau sannan yace.
"Bashinka naci koko a haya nake kabani notice".
Yafaɗa yana sakin ƙayataccen murmushi yana ɗan shafo gemunshi.
"Ban saniba É—an rainin wayo dalla malam ina son ganinka in kana kusa mu haÉ—u a parking space".
"Bafa zan fito ba ko gidan baƙonka ne, ina cikin falona a zaune ka shigo mana".
Wata dariya usman yay harda ƙyaƙya tawa.
"Kaga farin shiga ungozo mar wake, seka gayawa wanda baida falon, Angon kwana biyu".
Ƙitt ya kashe wayar.
Murmushi yayi tare da miƙewa takalminshi ya zira a ƙafafunshi sannan ya ɗan tsaya gabanta.
"Zan É—an fita sena dawo".
Tashi tayi cikin sauri, few mint ta É—auko turare a É—akinta, gabanshi ta tsaya a tsorace ta fesa mashi kaÉ—an a gaban rigarshi ta gaba.
"Allah ya tsare min mijina ya kareka daga dukkan sharri, ya hana idanunka kallon kowacce mace inba niba My nawa ni kaÉ—ai".
Shikam dariyama tabashi ya raɓeta ya wuce yana yaba yadda take riritashi kamar ƙwai.
Sauka yay ƙasa tare da bude kofar falonshi ya fita harabar gidan.
Gate É—in gidan ya buÉ—e ya fita part É—in ammi ya nufa kanshi tsaye, a babban falo ya zauna a saman seater yana kallon tashar aljazeera.
Jin shurun yay yawa ya miƙe tare da buɗe kofar falon ya fita sabida yasan ƙilan ko bata tashi daga baccin data koma bane ba, sabida yau sunday babu aiki kowa yana gida shiyasa ko ina tsitt a gidan da alamun kowa yana hutawa ne.
A parking space ya tsaya tare da fiddo da wayarshi ya niman layin usman, cikin sauri usman ɗin ya ɗauki wayar bayan ya miƙe daga kishingiɗan dayake.
"Ganifa kona koma ban gankaba".
"A,a kajirani dan Allah yanzu xan bullo".
Katse wayar yayi yana ɗora hannunshi akan kirjinshi tare da ɗan kurawa gate ɗin usman idanu,mintuna kusan goma sega usman ya ɓullo, cikin mamaki Aliyu kebin usman da kallo ganin yadda yake sakin far'a fiye da wadda yasansa da ita.
Musabaha sukai sannan usman É—in ya kalli Aliyu.
"Yaya maganarmu ta jiya a ina muka tsaya?"
Jimm yayi Da alamun ya manta sannan ya kalli usman É—in.
"Ban fahimceka ba wace magana ce?".
Cikin É—an zafin rai usman yace.
"Maganar ubanka banza marar mutunci to maganar Æ´ar mutane daka saka a tension".
Tsaki yaja É—an kaÉ—an
"Lallai shehu kaci tuwo akaina yanzu akan maganar can kake zagina tnx".
YafaÉ—a yana É—an haÉ—e ranshi kaÉ—an.
"Kaga ba wannan ba yanzu kai mikake gani akan lamarin?".
Shafa gemunshi yay.
"Na ware kuɗin dazan bawa mamanta takaita bording school sabida no need mu ɗauko ƴar mutane batare da wani ƙwaƙwƙwaran hujjaba domin nasan maman tata ma bazata bamu ba".
Dariyar baka da wayo usman yay mashi.
"Ƙurun ƙus! inji tatsuniyar gizo da ƙoƙi".
Inji usman sannan ya dubeshi.
"Kaga dan ALLAH É—auko kuÉ—in semuje da wuri mukaiwa maman tata kawai, kaga zuwa gobe monday se a sama mata makarantar".
Zaro idanunshi yay.
"To sarkin azarbabi tayaya zamuje gidan mutane da wanna ranar dake kawo kai nikam bazan fita ba gaskiya".
Murmushi yadda ze mar ram yay usman sannan yace.
"Ok zuwa dare insha Allahu semuje can gidan pls dan Allah karka ɓatamin lokaci".
ÆŠan nazarinshi yake sannan yace.
"Wai nikam kodai da wadda ka haskone agidan kakeso irin wannan rawar ƙafa haka, kamar kai abin yashafa naga kawani damen wallahi inda nasan akan wannan shirmen nakane da babu abinda ze saka na fito da wannan ranar".
Gaban usman ne ya faÉ—i yana gudun kada shirinshi ya watse, amman daya tuna yadda ze masa zarge yasa yaÉ—an saki fuskarshi.
"Cool down karka damu koni ka bawa kuɗin sena kai musu can ɗin babu matsala, ai amman da amutunce kazo mukai masu tare kadama kuma ka kaiwa mamanta kudin muje gidan wannan kakan nata semu kai mashi tare da damƙa masa komai daga karshe muyi mashi bayanin yadda ze sakata a makarantar kwanan batare da kowa yajiba bare a damesu".
Kallon kana shirme yaywa usman amman bai ce komai ba.
"Nidai ga abinda nai niyya kaga ni se anjima" yafaÉ—a yana barin wajan.
Gumi ke tsirgawa usman kota ina.
Abinda yasa bai gayawa Aliyu haƙiƙanin gaskiyar lamarin ba sabida gudun rikicinsa ze iya tarwatsa wannan lamarin tunkafin abu yay nisa yafison ya ribace shi suje gaban malam, tare sannan malam ɗin ya damƙawa Alin amanar bebi daga nan kuma yasan komai zezo masa cikin sauki amman a haka akwai rikici idan yace ze gaya masa kai tsaye dan haka shima nufar part ɗinshi yay yana ayyana insha Allah ayau zasuje gaban malam maɗaurin auren bebi inda yuwuwa su tawo da ita yau in kuma Alin bai yarda ba abarta har zuwa wani lokacin kafin suga abinda Allah ze xartar.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.