Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 67 of 81

#kyan alƙawari yasa nayi muku wannan sabida ba kyau saɓa alƙawari amman wallahi banajin daɗi se hakuri#

*Mai son littattafaina complt documents dana gama*
*RABON WANI*
*H A S K E*
*KOBA SO*
*ÆŠAN MAJALISSA*
*DA IZZATA*

*Dukka akan farashin naira 1000, seya neman ta numbern nan 08142105218, suna nan complt a haÉ—e karatu kaÉ—ai ya rage maka*
11/14/21, 3:13 PM - Allah Akbar: *88*

Kallo ɗaya zakama idanunshi kasan cewar sun hau saman network, seda yaɗan kuma gyara kansa sannan ya fita tsakar gidan ya kunna famfo ya wanke idanunshi sannan ya nufi can ainihin ƙofar part ɗin nasu ya buɗe, Goma ne ke tsaye bakin ƙofar hannunshi ɗauke da ledoji manya wasu kuma a ƙasa a zube.
FaÉ—aÉ—a far'arshi yayi tare da fita gaba É—aya.
"A,a goma harka dawo kenan sannu fa angode".
Yafaɗa yana ɗan ɗago ledojin dake ƙasan.
"Wallahi oga na dawo ga kayan nan seka duba daga ciki abinda babu sekamin waya, kayan miyane senaje Æ´an kaba, sannan akwai extra canjinka fa".
Ɗiban lodojin yay guda uku yakai tsakar gida sannan ya dawo ya karɓi na hannun goman kana yace.
"Okey ka zauna ka huta ba matsala zan taho dasu inna fita ai kamayi ƙoƙari nagode".
Murmushi goma yayi tare da cewa.
"Wallahi oga sena ƙarasa ladana gwarama ka barni zan haɗo muku ma harda kayan fruit insha Allah, frij ɗin kuma anjima zan kawoshi bayan an gama chakking ɗinsa".
"To shikenan nagode goma ka riƙe sauran canjin mana ka saiwa yara sweet"
Zaro idanu goma yayi sannan yace masa.
"Haba oga canjin ai ba ƙanana bane bare susha alewa dasu wallahi sunada yawa bara nai maka sending ɗinsu yanzu".
ÆŠaure rai yay sosai tare da tura kofar ya shige.
"Ka zubarsu idan baka buƙata".
Goma yaji muryarshi cikin kunnenshi sanin halin kirkinsa da alkairin sa yasa goma juyawa yana kuma yi masa fatan alkairi tare da É—unbin nasara a rayuwarsa.
Da kansa ya dinga É—iban ledojin yana shigarwa falo harya kammala sannan ya wuce can cikin É—akin.
Yadda ya barta haka yazo ya sameta tayi wani É—ai É—ai a saman katifar hannunta dafe da saman cikinta idanunta a rufe ruff.
Tsira mata idanun wucin gadi yay kana yace mata.
"Ga abincin an kawo ki zuba kici, Seki buÉ—e ledojin dake falon abinda babu kimin magana se a kawo ai kin iya abinci ko?".
Shuru tayi masa duk da tana jinsa amman tsabar yadda jikinta yake amace ta kasa tanka masa.
Wajan sau uku yana mata magana amman ko motsin kirki tagaza yi kuma itama ba laifinta bane laifin gangar jikinta ne datake ayyana mata jin daɗin abinda yay mata aɗazun wanda harya sakata jin wannan baƙon lamarin datake ciki a yanzu.
Takowa yayi har gabanta ya raɓa ya zauna gefen katifar.
Can cikin ƙasan muryarshi yake kiran sunanta.
Ko amafarki baze iya kiran sunan mahaifiyarsa gatsal ba, wannan dalilin yasa yaji ze iya karanta sunanta wadda take a matsayin takwarar sunan mahaifiyarshi shikam bebi yay masa wani daban wannan dalilin yasa ya soma kiranta da.
"Ummi! ummi!! tashi mana ko kinyi bacci?".
Cikin wata iriyar birkitacciyar murya marar fitar amo! taji yana kiranta da Ummi kamar da wata manufa acikin faɗin ummin, sarai kuma ta gane da itan yake amman setai ɗuff addu'a ɗaya take Allah yasa ya taɓata kotaji salama acikin azababban feeling ɗin da gangar jikinta keji.
Kamar yasan ƙudirin dake ranta, Hannunshi ya miƙa ya sauke mata hannunta dake saman cikinta, mirginawa yay ya haye saman ruwan cikinta ya kwanta flate kansa yana saman fuskarta hancinshi yana saman nata bakinsa yana saman nata hannunshi yasa ya zagayeta.
Zaro idanu take sabida yadda ya zube mata dukkan nauyin jikinsa gashi babu damar yin ihu! sabida yadda ya tokare mata bakinta da nasa.
Gaba É—aya numfashinta yay wani irin sauyawa sabida azabar nauyinshi zuciyarta na lugude kamar zata tsinko ta fito.
ÆŠan zamewa yayi kaÉ—an yadda bazataji nauyin nashi sosai ba ya É—ora hannunshi a saitin zuciyarta yanajin yadda take faman duka kamar zata faso.
Hawayene ya soma fitowa daga cikin idanunta waÉ—anda suke a lumshe, sosai take zubda hawayen zafin da kirjinta ke mata sabida bakaramin zafi tajiba a É—azun daya haye mata cikin nata.
Miƙewa yay zaune yana mata dariya.
"Raguwa kawai taso kije kici abinci".
Ya miƙe tsayema gaba ɗaya.
"Ni zaki saka na ɓata kayana kuma bani da wasu anan"
Tashi tayi tana tura baki gaba tana share hawayenta.
Dukda bai nuna yana sonta ba kuma bai furta mata hakan da bakinshi ba, amman hakika abinda yake mata yana matukar sakata jin daÉ—in dayasa harta soma jin yana burgeta ba kaÉ—an ba.
Gaba yayi zuwa falo itama mara mishi baya tayi kamar wadda ƙwai ya fashewa aranta take raya daman haka auren keda daɗi amman ta zauna tana kuka! ai wallahi inda tasan haka yake da tuni tace mama tayi mata.
Ahaka ta karasa falon yana daga saman sopa a zaune yawani haÉ—e rai kamar bashi ba.
Zama tayi agaban kayan ta soma buÉ—e komai daki daki.
Ledar farko wani irin kwaline cikinta mai ɗauke da ɗan ƙaramin gas, na girki ajewa tayi bayan ta fito dashi waje, ledar datake ta biyu kuma tarkacen kwalayen su taliyane indomie da sauransu ɗayar kuma ɗan madai daicin bugunne na shinkafa tare da ledojin semo acikinsu,abinka da kayan store wai duk girman kayan nan se an zirasu a leda, ɗayar kuma kayan tea ne cikinta ɗayar kuma su maine da kayan ɗanɗano atakaice dai babu abinda ba,a siyo ba na kayan masarufi.
Seda ta gama fidda komai dake ledar, sannnan ta janyo karamar wadda take É—auke da abincin dayace ya siyo musu tare da wadda ke gefenta ita kuma kajine gasassu cikinta.
Tashi tayi tsaye tana rage kayan tana fita dasu.
Tana shiga kicin ɗin datai mamakin ƙanƙantarsa wanda kuma harda lokoki acikinsa tare da tukwane guda biyu sabbi da plate's ajere da spoons dadai kayan kicin amman bawai masu yawa ba kuma daga gani sabbine wanda take tunanin duk.wannan shirya gidan nasu aikin gomane daya wakilta kafin suzo.
Komai seta ta jera a muhallinsa bugun shinkafar nema dataje zata É—auka sabida karamine seya hanata ya É—auka da kansa ya kawo mata ya aje sannan ya koma.É—aki.
Plate ta É—auka da cokali taje ta wankosu a famfo sannan ta koma ta É—auki kofin data gani kusa da saitin jerin filetan wajan, shima ta wanke tare da cikashi da ruwa ta nufi É—akin bakinta É—auke da sallama.
Ƙoƙarin zama take ta zuba abincin taji muryarshi.
"In kika tafi can wajan kofar fita akwai abin zuba datti ki É—auki tsintsiya ki gyara wajan mana inkin gama seki ci abincin a nutse a tsabtace ai yafi"
Yafaɗa yana mai ɗaga wayarshi dake ƙara tare da furta.
"Hellow usman ya ake ciki?".
Bata gamajin abinda yake faÉ—i ba ta fita daga É—akin, seda ta tsaya a gaban famfo tasha ruwa ta É—an huta sannan ta nufi wajan É—aukar tsintsiyar tanajin dik ta gaji( hmm Aliyu baka san madam É—in taka madam Æ´ar madara bace ba inaga bata son aiki fa)
Lokacin data dawo ya gama wayar yawani kwanta a saman sopar idanunshi rufe harara ta ɓalla masa ta wannan sakata aikin dayay kana ta zauna ta soma sharar.
"La'ila haba ummi shara a zaune kamar wata raguwa ko dai yunwar ce ta saka haka kinsanfa ni bana son ganda"
Ko kallo bai isheta ba ta kare sharar tare da fita ta zubar ta dawo ta zauna tana faman huci.
Ledar abincin ta jawo zata zuba.
"No ke baki san akwai bacteria, ba yakamata kije ki wanko plate ɗin kafin ki zuba abincin aciki sabida gudun ƙwayar cuta".
A wannan karon jitayi kamar ta kurma masa ihu amman tsoro baze barta ba.
Tashi tayi fuww taje ta wanko ta dawo ta xauna ta soma bude abincin tana zuwaba.
Tanaji yana tambayarta meye babu akayan abincin tayi masa banza sabida haushin aikin dayake sakata.
Aɗan zaman da sukai ta fahimci tsananin tsabtarshi tare da tsantsenin shi uwa uba kuma taga baida son jiki saɓanin ita da inda ze mata wanka ma sotake.
"Ummi"
Taji ya faÉ—i wannan sunan daya raÉ—a mata yau.
"Ummm".
Ta faÉ—a lokacin datake kai loma abakinta fuskarta a É—aure.
"Ni bazaki min tayi ba, kofa break fast banyi ba".
Haushine yazo mata wuya jiba yadda yake wani abu kamar karamin yaro zesha mama.
"Ai É—auri biyune abincin".
Ta bashi amsa kai tsaye wadda take da manufa biyu.
Murmushi kawai yay kana ya koma ya kwantar da kansa, lallai samun mace kamar khadija se antona se yanzuma tunaninta ya faÉ—o mashi aransa.
Idan itace bazata taɓa cin abinci gabanshi ta hana shiba idanma baici ba setai kokarin yi mashi kuka! amman ita wannan kanta ɗaya ta sani.
Tunanin halin khadija ya faÉ—a ita ko Bebi abincinta takeci hankali kwance ta gama ta É—auko kaza guda wadda ke cikin leda.
Ta soma yaga tana ci tana lumshe idanu sam ta manta dashi awajan seda ta gama cin abincinta tsaf sannan ta shanye ruwan dake kofin gabanta sabida babu pure water agidan kana taja ƙafafu ta naɗe batare data ɗauke plate ɗinba.
"Madam a É—auke kwanukan mana, kefa banason son jiki wallahi akan wannan halin zamu soma faÉ—a da wuri".
Taji muryarshi akanta.
Banza tai masa ta É—ebe kayan takai kicin ta dawo.
"Jeki wankosu mana ki kife tunda ba yawa,Kuma naga akwai omo akayan daya siyo".
Kamar kububuwa haka ta koma ta wanke plate É—in amai makon ta koma É—akin setai zamanta aka dakalin famfon batare data koma cikin É—akin ba.
Shiko abbane yay mashi waya cikin sauri ya ɗaga wayar sukai maganar dazasuyi kana ya miƙe, ya fito hannumshi riƙe da key.
Tana ganin ze ɗaga labule ya fito ta miƙe tsaye.
Kallonta yay kaÉ—an ya kauda kanshi.
"Zani gida amman ƙilan zan dawo anjima pls ki samu kiyi wanka kafin na dawo akwai kayan brush a toilet sekiyi"
Juya masa baya tayi.
"Bazaka ci abincin ba?".
Murmushi yayi tare da shafa sumar kanshi.
"Bantaɓa cin abincin waje ba zanje ammi tamin nata naci tunda ke nasan bazaki min ba".
Dariya tai kaÉ—an tana rufe idanunta.
"To adawo lafiya Allah ya tsare inkaga yaya usman kace nace ya gaisarmin dasu Æ´an biyuna inya gansu a kamfani".
TafaÉ—a muryarta tana rawa kaÉ—an alamun xatai halin.
Tausayi yaji ta basa amman bai nuna mata ba.
"Zan gaya masa insha Allahu kona zo dasu nan?".
Girgiza kanta tayi.
"Karka gayawa mama amman dan bazata bari suzo yauba nasani".
Dariya yayi.
"Bama yanzu ba senan gaba zasu zo kedai kiyi wanka kafin na dawo".
"Nifa bana wanka biyu sabida murace dani kamar kaza".
Dariya yayi sosai dajin maganar tata.
"Drama gel! karkiyi wallahi na dawo da kaina zan miki a tsakar gidan nan"
ai da gudu ta faila tayi ɗaki tana sheƙa masa dariya.
Shima dariya yake harya fice yaywa goma waya akan ya tura mata su mufida shikuma ya wuce yanajin zuciyarsa fresh.
Direct motarshi ya buÉ—e ya shiga tare dayin revars yabar layin................

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.