Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 41 of 81

*IDAN NAGA RUWAN COMMENT*
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }

NA
*AUTAR MANYA*

_Bakina yagaza furta irin godiyata agareku masoyana sedai naita binku da ɗinbin addu,a tare da fatan alkairi a kullum ina kuma gaya muku inhar kukaga banyi update ba, to kufara min uzuri kafin komai mussamman yanzu da lafiya tai ƙaranci anata fama da zazzaɓin maleria, tare da mura nima jiya nayi zazzaɓi amman yanzu kam Alhamdulillahi naɗan ji dama-dama, shine nace to bara na baku koba yawa, Godiya mai tarin yawa ga ƴan COMMENTS BOX ɗina inajin daɗin yadda kuke nuna goyon bayanku akan wannan littafi, Godiya mai tarin yawa ga masu tayani SHARE zuwa sauran wasu group's ɗin tabbas na shaida soyyyarku gareni Nagode! nagode!! Allah ya saka da alkairi amin ONE LOVE_

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

*59*

Tana faman kuka! kamar wadda ranta ze fita.
Yajima yana tsaye batare daya ƙarasa gab da itaba kuma bai mata magana ba domin yana tunanin ma bata ji takun ƙarasowar shiba.
Kallonta yake tundaga sama har ƙasa tacikin hasken farin watan daya haska masa ita.
Gyaran! Murya yay kaÉ—an yana naÉ—e hannayenshi a saman kirjinshi tare da kafeta da idanunshi masu mugun dafin hukunta marar jin magana.
Cike da zallar tsoro firgici Bebi ta juyo sanin hatsarin lungun domin bama abinshi da daddare sabida ƙwacen da akeyi acikinshi baya da haka har shaye shaye maza ke zama suyi acikinsa itama yau gudun khaleepha ne yasa ta gwammace ta shigo cikin layin akan tabar shi yacimma burinshi akanta.
Sedai kuma duk da hakan akwai É—unbin tsoro da firgici mai yawa acikin ranta wanda ya bawa jikinta damar rawa kota ina kamar mazari.
Jada baya ta somayi kaɗan-kaɗan duk tunaninta khaleephane sabida duhun datake ciki bai bata damar ganin kowaye ba, Sedai ga yadda taga tsayin na gaban nata yakuma firgita ta domin ko kusa khaleepha bai kai wannan na gaban nata ba, Jin ƙamshin sassanyen turarenshi datayi ya kuma bata tabbacin bashi bane kuma ba, ƴan shaye-shayen da suke zama bane.
Ɗaga idanunta tai still taga har yanzu bai matsaba kuma bai ƙaraso inda take ba.
Tsugunnawa tai awajan tare da cusa kanta a tsakankanin cinyoyinta tana ambatar sunan ubangijinta, Kukan ma yatsaya mata cak! sabida tsoro domin batai tunanin bil adam bane sabida tsananin ruÉ—in data shiga.
Ganin zata ɓata mishi lokacine yasa yaja ƙafarshi da ƙyar sabida ƙyamar kwatami, agabanta ya tsaya tare da ɗan rage tsayinshi kaɗan ya rissuna yana binta da idanunshi.
Jin mayen ƙamshin takumayi yana tunkarota kafin ta ɗaga kanta daga cikin cinyoyinta ta zuba idanunta akanshi yana rissune gabanta yaɗan ranƙwafo da kanshi gareta kaɗan.
Bushashshen miyau ta haÉ—iye mai zafin gaske tanajin wani mugun fitsarin tsoro ya taho mata.
Sam bata gane fuskarshi ba sabida duhu atunaninta wani ɓata garin ne yabiyo ta yay mata illah!.

Cikin dauriya take jada bayan a yadda take,Gam! taji anriƙe mata tsintsiyar hannunta,Wanda hakan yabawa fitsarin datake maƙo damar zubowa babu shiri baki ta ɓare mai zata zunduma ihu! yay saurin saka tattausan hannunshi ya danne matashi cakk, ya ɗagata yabar wajan da ita.
Wutsil wutsil take tana ƙoƙarin ƙwace kanta amman bai direta ba se a bakin layinsu alokacinne hasken farin wata yabata damar kallonshi a tsorace, take tasoma jada baya tana mamakin tayaya yazo nan?.
Babu mai bata amsa se mayun kaifafan idanunshi dasuke mata yawo akaf ilahirin jikinta.
Cak ta tsaya ta kasa jan ƙafafunta ta tafi sabida yadda sukai mata nauyin ja.
"Malama tafi kiban wuri konai ƙwallo dake kowama yaganki a wannan shigar ai baze gaza yin lalata dake ba"!
Kallon kanta tai se lokacin ta tuna da shigar datai a ɗazun har hassana tana mata magana akan tazo ta saka hijabi taƙi.
Jitai ta muzanta da wannan kalamin nashi.
"Nace ki wuce kibani wuri, ai wancan wawan ne dai-dai dake tunda baki da kamun kai yarinya kamarki kin fito da wannan tsakar daren".
Ya kuma faÉ—i adake.
Yana É—an jan tsaki! sabida yaga har tara ta gota ga usman shuru.

Tura baki tai gaba tana tuna rashin kirkin daya karta mata kwanakin baya shine yanzun ma yakeson karta matashi, gashi tanajin tsoron karta tanka mishi ya duketa a banza.
"Nifa ba wani wuri naje ba Ehe! dan kar aje aimin kallon ƴar iska daga gidan iya nake kuma idan ƙarya nake kaje ka tambayi mama! bakuma wani abunne yasa na gaya maka hakan ba sedan kar wataran ka ganni kaimin wani irin kallo".
TafaÉ—i maganar da sauri sabida tsoron karya masgeta.
Tunda ta soma magana yakafe bakinta da ido yana kallo first in history mace tagaya mishi magana a dake batare datai shayi ba, ko manyan mata suna rissuna mai bare wannan dayake zaton inda yay auren wuri dafa tuni ya haifi kamarta.
"Shigar jikin kifa itama mamar tasani tabarki?".
Shikanshi bai san yay wannan katoɓarar ba seda yay maganar sannan ya tuna yay taɓargaza, amman Bebi dayake akwai ƙuriciya yasa bata wani fahimta ba.
"To ina ruwan......., Baiji abinda zatace ba ya kwaɓe bakinta da bayan hannunshi yana mamakin tsiwar yarinyar.
Dira ƙafafunta ta soma a wajan tana dafe bakinta da hannunta.
"Nifa marainiyace kuma bani da lafiya É—azu har asibiti aka kaini amman shine zakazo kana duka na, kai kullum na haÉ—u dakai sekaimin mugunta jiyafa haka kaitamin masifa ka É—aukoni a motarka yayan babana yaga nafito daga motar ya biyoni yana cemin karuwa harya zagi mama, daga nan kuma yakawon wannan na É—azun yace se anÉ—aura mana aure, kuma Allah ze sakamin tunda ni marainiyace.......".

*NAKASA WALLAHI ZAZZAÆI WALLAHI ALLAH BANA JIN DAÆŠI KUYI HAƘURI SE GOBE*

_Albishirinku masu son littattafaina Document da page toga dama ta samu gareku ga duk mai son karanta books É—ina page ko documment kamarsu *ÆŠAN MAJALISSA* *RABON WANI* *KOBA SO* *HASKE* *DA IZZATA* duka akan farashi mai rahusa guda 5 É—in a naira 1000, in kuma É—aya kakeso a naira 300, maiso seya neman ta wannan number 08142105218 sena jiku masoya suma dukansu akwai daÉ—i da ratsa zuciya_
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }

NA
*AUTAR MANYA*

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

*60*

Durƙushewa tayi a wajan tana masa kuka! kamar ranta ze fita zuciyarta tana mata zafi jitake kamar ta mutu,Dawani irin yanayi na tsantsar sanyin jiki ya bita shima yay tsugunnon a gabanta yanajin wani irin mugun sanyi na ratsa jikinshi, kalaman rarrashi yakeson arowa amman yakasa kalma ɗaya data faɗi ita ta sanyaya mishi jikinshi, datace yaja mata yayan babanta yana kiranta da karuwa har ya kawo mata mijin aure, shi mutum ne mai tausayawa ɗiya mace yana da mugun rauni akan su musamman idan yaga mace tana kuka yanajin zuciyarsa na mishi suya.
"Jiya kuma? jiya da yaushe na kawoki gida?".
YafaÉ—i maganar a rarrabe, jin sautin muryarshi adai dai saitin kunnuwanta yasa tai maza ta É—ago se asannan ta manta cewar bafa jiya bane tun wancan satinne data raka hussaina talle kamfani, tsabar ruÉ—une yasa tace mishi jiya wanda su kansu sun jima basuje tallen ba.
Ɗan jan jikinta tayi ta matsa daga saitinshi tana kokarin miƙewa domin bazata iya tsayawa a yadda suke ɗin ba.
"Jeki gida! Yanzu yaushe ne bikin sukace?".
Yafaɗi maganar yana miƙewa tare da zuba hannunshi acikin aljihun wondonshi.
"Nima ban saniba amman ɗazu yacemin ko gobe ko ranar friday mai zuwa wai don ya nunamin ƙarfin ikon kuɗinsu, amman mama taje gidan baba malam ɗazu sunyi magana".
Tafaɗa tana miƙewa tsaye.
"Waye haka?"
YafaÉ—a yana kallonta.
"Shine kakanmu a bayan layinmu yake".
Shafa gemunshi yay yana kuma jefa mata wata tambayar.
"Ke kina son auren?".
Zaro ido tai waje tare da cewa........
"Tabb wallahi bana sonshi sabida kowa yasan ba ɗan arziƙi bane kuma mama bayanzu xatamin aure ba, nifa ban isa aure ba".
Dariya yay marar sauti wadda ita bata ganta ba.
"Nidai yanxu nina ja wannan aure ni kike xargi kikace nina ja maki?"
Tura bakinta tai gaba..........
"Da ina xamana lafiya babu wanda yazomin dawani maganar aure seda akaga ka saukeni a motanka" tafaÉ—a tana share hawayenta.
"Jeki gida nagode".
YafaÉ—a yana barin wajan.
Da sauri tai cikin gida gabanta yana faÉ—uwa, da usman taci karo ze fita suna sallama da mama, da sauri ta gaisarshi sannan ta wuce É—aki tana jiran faÉ—an mama akan daÉ—ewarta.
*****************
Usman ne ya fito bayan sunyi sallama da mama sannan ya ƙarasa gaban motar ya bude ya shiga ya zauna.
A zatonshi Aliyu ze mishi faÉ—a amman seyaga bai mishi ba sema tada motar dayay tare dayin revars yabar layin titin kabuga ya É—auka domin isa murtala suya domin ya siyowa madam khadija kaza.
"Kaga najima ko kai hakuri hirace taÉ—auki daÉ—i".
cewar usman yana kallon wayarshi ganin time yay karfe goma saura.
"No babu matsala, ina son neman shawararka amman dan Allah bana son shirmenka magana zamuyi serious".
Murmushi usman yay tare da cewa ina jinka.
Babu wani ɓoye-ɓoye Aliyu ya fara yiwa usman bayani hankalinshi yana kan kwalta.
"Kasan wannan yarinyar Æ´ar gidan daka fito yanzu ba Æ´an biyun ba".
Da mamaki usman yace.
"Ok Bebi naji suna kiranta kasan sunan ammi gareta".
"Koma miye sunanta nidai mafita nike nema sabida banson na mutu da haƙƙin wani akaina"...........tass yagama kwashe duk abinda ya faru dashi da yarinyar tundaga haɗuwarshi da ita a kamfaninsu har zuwa yau datake gaya mishi za,a mata auren dole.
"But ni abinda yake damuna yadda ta É—oramin laifin danna É—aukota a motana ne ya haifar da haka, se abu na biyu yaron dasuke son bata baya da kirki, abu na uku ina tunanin basa shiri da dangin mahaifin nasu shine yasa sukeson yi mata wannan auren domin su tozarta mahaifiyar yaran".
YafaÉ—a yana É—an huci! kaÉ—an tare da dafe sitiyarin motar tashi.
Cikin tsananin mamaki usman yake duban Aliyu lallai Ali ba karamin zurfin ciki gareshi ba tayaya duk akai wannan bidirin bai sanar da usman É—in ba?
Yaso yay mishi cari amman gudun zuciyarshi yasa ya mayar da hankalinshi gareshi domin yasan yana fara dariya maganar xata watse dan baze kuma tanka mishi ba.
"Shawara ta gareka shine ka AURE TA"
Cikin wani irin ƙarfi yaja burki ya dakatar da driving ɗin yana kallon usman.
"What in aureta fa kace usman are you in sense?"
Murmushi usman yay.
"Wannan shine only solution da xaka fidda yarinyar daga cikin sarƙar datake shirin shiga rayuwarta sannan zaka ceci maraicinta".
Lumshe mayun idanunshi yay yana jan huci mai zafi yana dafe kanshi tare da bude idanun tar ya zubawa usman su, wanda shi kansa usman seda ya firgita da ganin yadda idanun Aliyun suka sauya launi.
"In auri yarinyar da zan iya haifarta sabida ƙarancin shekarunta? in auri yarinyar da babu abinda ta sani se cin abinci ƙilanma raino kawai zanyi ina nidai ka sauya wani abun sabida kasan wannan baze yuwu ba, dani naso kawai na maka uban yaron a kotu idan yaso kotu ta hana auren faƙat".
Dariya usman ya gintse tare da kallon Aliyun.
"Cewa kai zaka iya haifarta sabida karancin shekarunta, ai ba haifar tata kaiba ko? sannan raino ai anfison waɗannan sabida sune masu sugar, kawai dai kai tunani amman nidai a shawarce kai wannan yaƙin ka taimakesu dan Allah ka aureta, koba ka sonta kai yaƙi da zuciyarka gaba xatai maka rana".
Kallon kaci kai yay wa usman.
"Yaufa kwana na ɗaya dayin aure? sannan na ƙara? tayaya zan fiskanci abba akan ina son *AUREN BARE* Wanda kasan haka baya cikin tsarin familyn mai atamfa?".
Dum! dum!! gaban usman ya faÉ—i shifa yama manta da wannan tsarin na zuri'arsu seda Aliyun ya faÉ—i yazun.
"Eh! Aurenka da ita shine mafita amman babbar matsalar itaɗin BARE CE! amman ban tunanin abba zeƙi yarda sedai matsalarmu Alhaji babba domin ka tunamin lokacin da ya umar yaso auro wannan ƴar legos ɗin alhaji fa cewa yay sedai ya umar ya bar musu gidan indai baze auri jininshi ba".
"Mafita ta gaba duk da ban tsoron yin auren domin ba haram bane".
Murmushi usman yay.
"Ka auretan ko Allah xesa ka fara rusa wannan shegiyar al'adar da wannan tsohon ya kafa mana ƙiri-ƙiri muna ganin mata muna son aurowa amman a takura mana seta family kai ɗaya zaka iya rusa wannan shirin nasu ZAKIN AMMI".
Murmushi Aliyun yay a ƙasan ranshi tare da tuno abubuwan da suka shude aranshi.
"Ok toyaya lamarin ze kasance kasan kona sha giyan wake bazan tunkari abba da wannan É—anyen aikin ba".
Dariya usman yay kana ya jawo kunnen Aliyun yay mishi raɗa, ɗan ware ido Aliyun yay tare da girgiza kanshi kana ya tada mota suka wuce suna tafe suna hirarsu harya ƙarasa wajan siyo kazan ya futa ya siyo komai tare da nufar mota suka tafi gida lokacin da sukaje gida ƙarfe shaɗayan dare sallama sukai da usman shiya wuce part ɗinshi.shima Aliyun mota ya kashe ya kwashi kayanshi daya siyo yay nasa sashin.
Lokacin dayaje khadija tai bacci abinda ya siyo mata ya aje mata a saman madubi kana yay nasa ɗakin ya tube kayanshi ya shiga wanka yana fitowa ya sauya kayan bacci ya haye gadonshi ya kwanta yana tunanin maganar usman tabbas akwai aiki gabanshi sabida su abba basa ƙetare maganar alhaji babba wanda yanajin a wannan karon shi ze soma watsi da maganar shawarar usman ce take.masa yawo azuciyarshi ahaka bacci ya kwashe sa.
********
Tun kafin mama tashigo Bebi tai baccin ƙarya wanda kiran duniya mama tai mata amman taƙi tashi harya zarce xuwa na gaske, washe gari tun asubahi Bebi tayi wankan tsarki tai sallar ta, kana ta koma gado ta naɗe ta cigaba da sharar baccinta.
*********
Ƙarfe bakwai na safiya tayiwa malam a ƙofar gidan marigayi alhaji mai katifa amininshi ɗan gidan rabi'u yagani zefita ya kirashi yace yay mishi sallama da iyayenshi.
Mintuna biyar Rabi'u Tasi'u Sani suka fito ganin baba lado (malam) yasa suka É—anyi jim sabida basa kaunarshi sakamakon yadda yaja É—an uwansu babansu bebi ajikinshi.
A É—age suka gaishe shi tare da kallonshi "Muna sauraranka malam".
cewar sani wanda yake kallon malam.lado.
"Dama maganar auren nan da kuka zo yiwa wannan yarinyar shin kunyi binciken halaiyar yaron da sauran abubuwan da shari'a ta umarta a yi ayayin da ake neman aure?".
Dariya suka saki mai tattare da ranin hankali.
"Malam lado daman mutum da kayanshi har wani daga can ya isa yazo yay masa ƙarfa ƙarfa akanshi? shin ina ruwanka kana bare ina ruwanka da shiga tsakanin jini da jini?, To bari kaji wannan yaro ubansa uban gidanana ne kuma nina jagoranci auren dan haka babu fashi"!!
Cewar tasi'u.
"Eh muda kayanmu yau ko gobe ko jibi xamu daura a huta da wannan jaraba".
Cewar sani.
"Allah sarki au ashe fa malam musa ɗan uwankune ai ban saniba, ku dan Allah inba jahilci irin nakuba duk irin ƙiyayyar da kuka nuna mishi har kunada damar yiwa ɗanshi aure to bari kuji ni ɗinnan ni zan ɗaurawa kowacce a ƴaƴan musa aure kuma wannan auren nina gaya.muku baze yuwu ba gaba ɗayanku na isheku muxuba dani daku".
YafaÉ—i hakan tare da barin wajan da sauri yana huci.
Jikinsu ne yay sanyi suna tunanin yaya xasuyi cikin haka kiran haji isa ya shigo wayar tasi'u da rawar jiki.ya É—aga yana faman kirari.
Umarni ya bashi akan anjima.ze aiko da akwatunan lefe gobe za,a É—aura auren sabida khaleepha ya bukaci haka.
Ajiyar zuciya tasiu ya saki yana ayyana faÉ—uwa tazo dai dai da zama tare dayin na'am da maganar kana ya kashe wayar yana duban Æ´an uwanshi.
"Kurabu da wannan tsohon damu yake xancen inya san wata ai bai san wata ba gobe ma daganan zamu É—aura auren muga ta tsiya sedai kawai yaje ya É—auki abarshi".
Dariya sukai kana suka watse akan gobe zasuyi fin karfi.
********
Kai tsaye malam lado gidan mama yaje lokacin suna karin kumallo shinfiÉ—a tai masa ya zauna anan yake wassafa mata komai.
Cikin tsoro mama tace"karfa suje su mana ƙafa ma'ana suyi ɗaurin auren nidai dan Allah malam ko wani ne ka samu ka haɗata dashi insha Allahu kafin suyi mai yuwuwa".
Jimm yay yana nazari secan yace.
"Karki damu ai ALLAH ya fisu".
Sallamar yaroce ta katse musu maganar.
"Assalamu alaikum.wai usman yana sallama agidan".
Cewar yaron.
Jimmm mama tai kana tace.
"Kace masa ya shigo"
Sallama usman yay tare da neman guri ya zauna cikin ladabi ya gaisar da malam shuru wajan yay daga mama se usman tare da malam a tsakar gidan domin Æ´an biyu suna É—aki kuma sun kunna redion data hana suji abinda ke wakana.
"Mama nida babban yayanmu ne munzo neman alfarma in bazaki damu ba sabida jiya naji komai daga bakin wannan ƙanin nawa akan auren bebi dazakuyi mama in babu damuwa muna son ayau a ɗaura auren da Aliyu ga yayanmu can a mota yaxo da sadaki sedai angon baizo ba muke wakiltarshi mu ƴaƴan alhaji idiriss mai atamfa ne.mama kowa yasan sunan mahaifinmu koda zakuyi bincike".
Malam ne ya zubawa usman idanu yana kabbara ga sarki Allah, mama kam tsabar mamakin wannan lamarin ya hanata magana.
"To babu laifi domin a shari'ar aure daman shedu da waliyai akafi so to muna godiya ga Allah dayasa kuɗin kuka kasance shaƙiƙan shi Aliyun kuma waliyanshi domin kace harda babban yayanku babu matsala ni xan zama waliyin ita bilkisun idan yaso se aje can kofar gidana ai shela, in aka ɗaura kafin bisani daga baya yazo ya ɗauki matarshi a hannuna mun gode da wannan karamci".
Cikin sauri usman ya fita ya sanar da ya abbakar wanda ke cikin motarshi malam ne ya fito suka wuce can kofar gidanshi atare.
Sosai malam lado yay shela harda mai unguwa da manyan dattijai na cikin anguwar yaya nura da ya aminu ma seda suka zo duk mamaki ya ishesu lokacin dasukaji sakon kiran malam, amman ƙarancin lokaci yasa basuyi binciken komai ba.
Ƙarfe tara da rabin safiyar lahadi 1/3/ ɗunbin jama'a suka shaida ɗaurin auren ALIYU IDRIS MAI ATAMFA da BILKISU MUSA MAI KAFITA! cikin sadaki mai daraja wanda ya abbakar babban yayan Aliyu ya miƙa kuma shiyay wakilcin ango ya tsaya a matsayin mahaifin ango, inda usman kuma yazama shaidar ango malam lado kuma yazama waliyin amarya tare da sauran shedun dasuka tsaya wajan ɗaurin auren harda su mai unguwa da sauran jama'ar unguwa.
Bayan shafa addu'oin dasuka fito daga bakin mai anguwa taro ya watse su ya abbakar sukaiwa malam lado sallama suka wuce da É—unbin farinciki hakanan shima yay gidanshi da sadakin bebi a hannunshi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.