Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 79 of 81
*ZUMA A BAKI...!*🌹
{ Painful love Story }
_Shine sabon littafina da ze soma zuwa da zarar na kammale wannan kedai/kaidai maza ka hanzarta ka biya naka domin tun kafin na soma posting ɗinshi zan soma karɓar kuɗin masu son karantawa kai dagajin sunan kasan akwai rikita rikita wadda bazan ce komai ba amman rubutuna ze bayyana muku *Zuma A Baki* comming soon da izinin Allah ƙofa a buɗe take masu soma payment_
*ÆŠAN ÆŠANO*!
_Wannan karon tafiya nai mai mugun nisa har naje na zaƙulo muku ƙayataccen labarin masoya Biyu *Umar Muhammadu Sarkin-Gida* wanda jama'ar unguwa da abokai ke masa laƙani da ( *Cika Daji* ) Eh cika dajin ne mana sabida duk umar ba,a rago to hakance ta kasance ga shalelen inna kuma autanta wanda ya tsunduma a dafkin kogon soyayya da *Aishatul humaira* ɗiyar anty Har soyayyar tasu ta zamewa kowannen su *ZUMA A BAKI* Tabbas tunda nake rubutuna bantaɓa katari da labarin daya kwantamin ya tsayamin kamar ZUMA A BAKI ba! tabbas kodaga jin sunan kasan akwai rikita rikita kuda kawai kubiyoni nasan insha Allah bazan baku kunya ba_
*Hohoho! my fans nace muku painful wallahi da gaske wannan soyayyar mai zafice mai raÉ—aÉ—i ce duk wani masoyi yaci katari da wannan labarin nawa seya dara seya koka seya warwasa labarin ze Æ™ayatar ze tsaya arai ze nishaÉ—antar ze wa'azantar ze ilimantar kudai kubiyoni kawai*💃💃💃💃ðŸ¤ðŸ»
_kai ƙoƙarin ganin kayi payement domin zan soma sakin sane da zarar na kammale wagga_
~N~ *300*# *ta wannan account numbern 0078174806 starling bank show me your evidance of payment ta wagga numbern 08142105218 love you my Æ´an amana my Æ´an iya wuyata*
11/14/21, 3:21 PM - Allah Akbar: *100*
AUREN BARE
*NA*
#AUTAR MANYA
Gaba ɗaya jitayi taliyar ma ta fita daga ranta zuciyarta na wani irin tashi kamar dukkan sauran dataci zata zubo ma'ana ta amayar da ita rantane ke mata masifar ƙuna kamar ana zuba mata gaushin wuta mai zafi cikin zuciyarta.
Bata taɓa sanin ta damu dashiba tana masa wani irin mahaukacin so mai tattare da kishi mai mugun zafi da zugiba se yau, tabbas tana son mijinta tana kishin duk wata macen dazata raɓar matashi musamman ayau data sheda hakan dayay mata halaccin soyayyarshi daya ɗaga martabarta ya nuna yes ita keda muƙami mai girma a zuciyarta, ta yadda agaban dubban jama'a ya nuna yana sonta ze zauna da ita muddin rai.
Sedai kuma kash! yanzu datake jin furucin kanwarsa setaji ya fita aranta setaji tana jin matsanancin haushinsa tare da jin zafin yadda yay ɗin, duk da hakan ba haramun bane domin waccan ɗinma matarshi ce kuma tana da haƙƙi kamar yadda itama take da haƙƙinshi.
Ƙurawa Tv'n dake jikin bangon falon tai batare datasan mitake kallo ba jitake inda zata sami matsera wallahi baze shigo ya tarar da itaba domin zata wucene wurin mamanta amman sanin matakan tsaron dake cikin gidan masu kama da samudawa yasa wannan ƙudirin nata ya rushe.
Su Amina tashi sukai suna mika suka wuce bedroom É—insu suna masu cewa ammi.
"Ammi bara muje muyi sallah muci abinci ƙilafa se gobe dan wallahi bakiji yadda muka gajiba".
Murmushi ammi tai musu cikin kulawa tace.
"Masha Allah, sannunku Allah yay muku albarka Amin seda safen in baku fitoba".
Murmushi sukai atare kuma suka juyo ga Bebi wadda take faman tunani ita É—aya.
"Anty Bebi se Allah ya kaimu"
Firgit! ta juyo tare da ƙaƙalo murmushi dole sabida yadda maƙoshinta yake a bushe.
"Allah ya tashemu lafiya nagode"
Tafaɗa tana mai mayar da ƙwallarta, barin falon sukai wanda yay saura daga Ammi se ita.
Waya ammi ta É—auka, tana kiran nusaiba cikin bada umarni take cewa nusaiban tana son next week ta daure ta shigo kano domin shirye-shiryen biki sannan tazo da lefen bebi da suka haÉ—a.
Sosai suke tattaunawa akan maganar bikin su amina har aka tada sallar magariba.
Bebi ce ta mike ta shige É—akin ammi, tai alwala a toilet É—in ammi sannan ta tayar da sallah.
Bayan ta idar azkar ta zauna tayi sannan ta fito falon wanda bata sami ammi cikinsa ba.
Zama tai a ƙasa tare da rafka tagumi ta zubawa ƙofa idanu.
Anan tai sallar isha'i tana idarwa ammi ta fito daga wani lungu, zama ammi tayi cikin kulawa tana kallon Bebi kafin a nutse tace mata.
"Kin gaji da zaman kaÉ—aici ko auta?"
Murmushin dole tai mata.
"A,a ammi daman zanje wajan Anty zainab matar yaya usman naga boy".
FaÉ—aÉ—a far'arta ammi tayi tare da ce mata.
"Zaki gane wajan ne?".
Da sauri ta É—aga mata kanta.
"Eh! Ammi zan gane in Allah ya yarda".
"To shikenan amman ki maza sabida mijinki nasan yana tafe".
"Insha Allahu" tafaɗa a fili amman ƙasan ranta cewa take.
Tab yayta zuwan mana ni ina ruwana dashi.
Tashi tayi ta gyara hijab É—inta sannan taiwa ammi sallama kana ta fita daga falon.
Da sauri take nufar part É—in usman É—in, kamar daga sama ta hangi tsaiwarsa gaban motar da sukazo É—azu daga gani kayansu yake É—iba yana bawa wasu ma'aikatan gidan suna mika masa cikin part É—insa.
Cikin azama ta É—auke kanta tai kamar bata ganshiba damma Allah yasa shiÉ—in bai gantaba.
Gate ɗin ɓangaren usman ta bude ta shiga cikin falon.
Usman zaune da jinjirin a cinyarshi zee tana gefe tana shan tea sallama tayi tare da fara gaisar da usman tana masa barka.
Sosai yake janta da wasa yana tambayarta ina Aliyun?
Basarwa tai bata basa amsa ba ta koma kusada zee ta zauna wadda take tambayarta yaya fama da jiki?
Sosai usman ya sake yana mata hira tun tana jin kunya harta sake nanfa hira ta É—auka har zee batare data san lokaci yana jaba.
ÆŠaukar yaron tayi tana yaba kyansa babu ta inda yabar usman.
"Lah yaya usman kamarku É—aya"
TafaÉ—a tana dariya.
"Yes aimu ƙarfin jini garemu kema nasan Aliyu zeyo ɗan naki"
Dariya ta saki tana kunshe fuskarta a hijabi.
"Anty zee zan tafi se gobe"
"Tsaya amarya ina zuwa"
Zee tafaÉ—a tana mai tashi ta shiga É—akinta mintuna uku ta fito hannunta É—auke da littafi guda biyu.
"Ga wannan ze rage miki kewa nasan zaki gaji da zaman kaÉ—aici wannan na farkon girke-girkene tare da gyaran jiki na mata,wannan kuwa littafin karatun hausa ne na soyayya da faÉ—akarwa na marubuciya Autar manya sunanshi HASKE na tabbata kika karanta Haske sekin nemi KOBA SO, uwarsu ubansu kuma ÆŠan majalissa labarin Muhammadu Anwar Sameer( mai girma Mas ) tare da nafisa Fk, tabbas litattafan zasuyi matukar tayaki hira"
Zee ta faÉ—a tana mai zama akan pillown data tashi.
"Umm kudama mata hirarku kenan na littafi wai dan Allah bakwa gajiya da karatunne?"
Usman ya faÉ—a yana dariya.
"Haba cwt heart ka manta kwanaki yadda ka dinga cewa Auta kuwa ta fara sabon littafi zaka biya ka sai mana sabida yadda kacemin kaji daÉ—in RABON WANI wanda nake karanta mana kullum da daddare koka manta?"
Washe baki usman yay yana mai gyara xamanshi.
"Yes my heart ai har yau labarin ya kasa barin zuciyata shine wanda yayansa saddiq ke auranta ko? ashe shi kuma tun tana karama yake sonta amman yayansa yay masa shigar sauri, seda ta haifi tagwaye sannan Allah yaywa sadiq É—in rasuwa shikuma ALIYUN ya aure tako? kai haryau my love na kasa manta RABON wani na Fatin inna da Aliyu cousin brother É—inta ko?"
YafaÉ—a yana dariya.
Dariyar itama zee tai.
"Ai wallahi auta babu laifi inajin dadin book's É—inta shiyasa na matsu ta soma sabon datake mana tallenshi"
Da sauri usman ya mike.
"Wanne kenan kina nufin Auta zata kuma yi mana wani book É—in bayan AUREN BARE?"
Murmushi zee tayi.
"Koma ka zauna oga! ai auta a shekara daman tana yin book ne guda uku to wannan shekarar ma gata tazo mana da DA IZZATA, labarin ɗiyar sarki Memah asma'u masu dukiyar gado tare da sahibinta shahararren ɗan ƙwallon ƙafar nan wato ABDUL-NASEER ALIYU ADAM DAULA! sannan tazo mana da AUREN BARE labarin Aliyu idriss mai atamfa, to yanzuma naji ana cewa, zatayi mana sabo wanda tun kafin na karanta shi naji sunansa ya burgeni bara na nuna maka tallen nashi".
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.