Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 43 of 81

Su usman kuwa daga wajan É—aurin auren...........

*LITTAFIN KUÆŠI*
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *PART*

NA KUÆŠINE

*62*

Su usman kuwa daga wajan É—aurin aure kai tsaye gida sukai sabida ranar sunday ne babu aiki, suna tafe ya abbakar yana jajanta abin yana kuma daÉ—a gargaÉ—in usman akan komai ze biyo baya kada ya sake ya ambaci sunanshi.
Dariya usman É—in ya saki kana yace.
"Haba magajin abba kaima kasan babu kai acikin wannan badaƙalar ai ka gama mana komai ALLAH dai ya raya zuri'a amin".
Cigaba yayi da cewa..
"Amman gaskiya dattijon akwai karamci Aliyu ya ɗauko ƴar gidan masu karamci Allah dai yasa komai yazo cikin sauƙi".
Usman ne yace.
"Insha Allahu, muna fatan haka yaya".
Suna tafe suna tattaunawa har suka karasa gida, lokacin wajan 12 na rana ya abbakar part É—inshi ya nufa bayan ya kashe motar shima usman nasa part É—in yay domin yay break fast.

Nasan fans zaku so jin tarihin Aliyu wanda ban riga dana feÉ—eshi a part one ba amman yanzu insha Allah zakuji.
************
Mai atamfa family.
Asalin tarihin shi kansa mai atamfar kakan Aliyu kenan mahaifin Alhaji idiris mai atamfa abban Aliyu, sunan shi Marigayi Alhaji Ali mai atamfa haifaffen garin kano ne shi cikin wata ƙaramar hukuma wai ita ɗan batta.
Alhaji Ali É—ane ga sarkin kasuwar garin É—an batta waishi malam usman, shi kanshi Alhaji Ali ya gaji kasuwanci ne wajan mahaifinshi marigayi malam usman É—in, tun yana yaro malam usman ke tafiya dashi kasuwa wajan sayar da kayan sakawar dayake kasuwanci, wanda malam usman bai saida komi se atamfa acikin kasuwar.
Marigayi Alhaji Ali shi kaÉ—ai mahaifinshi malam usman ya haifa kamar yadda shima malam usman É—in ya taso baida Æ´an uwa na ciki É—aya sedai Æ´aÆ´an dangi.
Gatan duniya Malam usman ya nunawa Ali shida matarshi hajjo..
Lokacin da Ali ya taso, yazama saurayi se malam usman ya ɗauki ƴar gidan ƙanin shi wanda mahaifansu suke ciki ɗaya ya bashi yace ya aura mai suna salma, tunda shi Ali bai sami yin karatun boko ba, sedai harkar kasuwanci daya saka gabanshi kamar yadda yaga mahaifinshi yana yi.
Batare da musu ba Ali ya amshi auren salma hannu biyu cikin ladabi da biyyya, hakan bakaramin daÉ—i yaywa mahaifanshi ba cikin kankanin lokaci aka saka ranar biki, wanda iyayen Ali sukai rawar gani wajan nunawa É—an nasu gata.
saka ranar aure da wata biyu.
Allah yaywa Malam usman rasuwa batare daya ga auren ɗan nashi ba, zokuga tashin hankali wajan Ali kamar zebi uban nan nashi haka yayta kuka sabida sun shaƙu, ganin babu ran mahaifinshi yasa ya mayar da hankalinshi baki ɗaya akan harkar kasuwancin mahaifin nashi harma yaso yafishi yawan jama'a.
Bayan rasuwar, malam usman da wata É—aya aka É—aura auren Ali da salma wadda ta kasance Æ´ar uwarshi ce ita ta jini.
Gida guda suke zaune da hajjo iya ladabi da biyayya salma tanayi wa uwar mijin nata.
Aurensu da shekara É—aya Allah ya azurta salma da haihuwa ta haifi É—anta namiji mai kyau dashi, ranar suna yaro yaci suna Ayuba, tun daga nan kuma se haihuwa ta buÉ—ewa salma atakaice seda salma ta haifi Æ´aÆ´a shida maza biyar mace É—aya.
Ayuba, Salmanu, Idiris, Yusufa, Shu'aibu, karimatu.
Lokacin da aka haifi karima ne Allah yaywa hajjo rasuwa gidan seyaywa salma faÉ—i sam bata jin dadin zaman musamman idan yaranta suna makaranta sabida haihuwar tata akufi akufi ce shiyasa yaran suka taso kusan kansu É—aya.
Ganin haka yasa Alhaji Ali ya tattara nasa ya nasa, ya baro É—an batta ya dawo nan cikin kano da zama inda ya sai gida a wata anguwa wai ita yakasai, anan suka cigaba da zama har xuwa sanda komai ya dai daita gareshi ya sayi shago anan cikin kasuwar kantin kwari yacigaba da sabgarshi ta sayar da atamfofin shi.
Ya rigada yaywa kansa alkawarin bawa yaranshi karatu mai inganci sabida shi bai samu yayi ba wannan dalilin yasa baya tafiya da É—ansa ko É—aya kasuwa suna makaranta suna karatun su.
In akai hutu yakan tarkatasu sutafi can É—an battan wajan dangisu suyi hutunsu acan su dawo suma kuma Æ´an uwan nacan É—in sukan tawo nan yakasan suyi kwanakin su sukoma gida wannan dalilin yajawo shakuwa mai yawan gaske a tsakanin Ali ( baffa )da danginshi nacan haka xalika itama salma wadda Æ´aÆ´anta ke ce mata ( inna ) tana kwatanta janyo nata Æ´an uwan ajikinta sosai sabida ita suna da yawa bakamar Ali dayake shi kaÉ—ai ba.
Rayuwa tana tafiya shekaru naja, lokacin Ayuba shida salmanu sun kammala karatunsu na secondry, Seya samar musu makarantar ABU zariya, suka cigaba da karatunsu acan wanda kowa da fannin daya karanta, Ayuba accounting yake karanta shikuma salmanu yake karantar mass com, gidan ya rage daga idiris se ƙannenshi idiris yana ƙyalla idanu yaga babu ƴan uwanshi seya soma bin ubanshi kasuwa tun inna tana faɗa harta gaji wataranma a bakin shagon ze raɓe, Alhaji Ali na korarshi amman kamar cigam seya xauna.
Abokin Alhaji Ali ne yake ce masa kaga tunda É—annan naka yanason harkar kasuwancin nan kabarshi ko naira hamsin kana bashi babu mamaki akwai abinda Allah ya boye akan harkar tashi.
Fafur baffa yaƙi yace shifa baze yarda idi ya xauna babu karatuba yanzu zamani ya sauya rayuwa idan babu ilimi fanko ce suma dan dai sunzo acan dane amman inda yanzune babu abinda ze saka yaki makaranta koda kuwa a boye ne seya jeta.
Babu yadda abokin baffa baida shiba amman yaki yarda.
Da ƙyar abokin nashi ya shawo kanshi akan shi ya yarda yana zuwa shagonsa in antashi daga makaranta seyana bashi ɗari biyu, dayake abokin baffan yana da yara a shagonshi
Dan dai babu yadda zeyine yasa ya amince wa abokin nashi.
Tun daga wannan lokacin idi ke zuwa shagon abokin baffanshi yana miƙa kaya ana bashi kudinshi yana tarawa, ranar asabar da lahadi da wuri yake zuwa ranar makaranta kuwa baya zuwa se antaso ahaka har ya kammala secondry lokacin, su ayuba sukuma sun shiga level 2 suma in sukazo hutu sukan bi baffa can kasuwar amman basa mayar da hankalinsu akan haka hartaja baffa yace sudaina zuwar masa shago.
Ganin Idi ya gama makaranta yasa abokin baffa ya kuma kara masa kudin biya sabida ya kara shekaru da hankali shikuma baffa lokacin yana cuku cukun samarwa idin makarantar gaba da sakandire sabida yafi masa son karatun fiye da komai, lokacin Allah bai ze samu jami'a ba shi se baffa ya samar mishi poly, inda yake karantar bussiness accounting, cikin haka shima mai binshi yusufa ya sami gurbin karatu anan poly É—in amman shi yana karantar hausa islamic ne.
Shekarar su ayuba huɗu a makaranta sukai passing out suka tafi service, ayayin da baffa ya samarwa kowannen su macen aure kuma dukkansu sun kanace ƴaƴan ƙanin shine da iyayensu suke ciki guda, bayan dawowarsu daga service baffa ya bawa kowanne gida, tare da damƙawa kowa matarshi ahannu, bayan fitowar result Allah ya taimaki shi ayuba ya sami ikin banki shikuma salmanu ya sami aikin gidan redio amman ba anan ba acan jahar bauci, dole tasaka baffa ya saka haya a gidan salmanu ya tarkata masa matarshi suka wuce wadda ita da matar ayuba suke ciki guda kuma duka ƴan uwan inna da baffa ne.
Shikuma ayuba ya zauna anan gidan da mahaifinshi ya bashi tare da matarshi.
Adaddafe idi ya gama poly bai tsaya karbar kwalinshi ba ya bazama kasuwa cikin yardar Allah ya haÉ—u da Æ´an chaina waÉ—anda suke bashi kaya yana sayar masu ya É—ora nashi.................
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *PART* 2

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.