Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 31 of 81
_Alƙwari na cika sabida nace zan baku na dare amman ban so na tsaya ananba dan dai karkuji shurune_
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
  { _HOT LOVE_ }
     Â
     NA
*AUTAR MANYA*
_Wannan shafin na sadaukar dashi ga duk wani ɗan team Bebi da Ali, da kuma masoyana kuyi yadda kukeso dashi kai sekunga damar bawa ma wanda kuke so musamman ƴan comment box ɗin auren bare_ 💃
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
           *47&48*
Cikin mamakin yadda tace ƙanwarta ce waccan ɗin yake dubanta tsaf yaga basa wani kama idan bata jini ba, sannan kuma yaga hussaina ƴar ƙarama ba kamar waccan marar kan gadon ba.
"Ok to kije gida mana ko ƙila tayi gaba tabarki sekima mamar bayani tunda ita bataji".
Ya fusgo maganar kamar an tilassa mishi dole yayita.
Hussaina ƙasa tayi da kanta sosai kamar maijin sanyi sabida yadda ƙwarjininshi ke ƙara ratsa mata jikinta sannan ta soma magana a sanyaye.
"Ai faɗa zatamin akanme na barta wallahi ni tsoron mama nakeji, yanzuma nasan duk inda take hankalinta yana kammu sabida tace kada mu wuce ƙarfe uku koda bamu siyar duka ba, to muyo gida".
Tunda ta fara maganar yake kallonta amman tacan ƙasan ido irin kallon nan wanda kaida akewa shi bazaka fahimta ba seshi wanda yake makan ne ze gama kallonka tsaf.
Haka kawai yaji ta bashi tausayi ganin yadda take kuka! yana son yaga mutum mai son nashi, uwa uba kuma yadda yaga ta firgita da tsoron faɗan mahaifiyarsu tabbas! yaji tausayi mai girma aranshi.
"Jirani anan zanyi sallah ina zuwa karki damu".
Yafaɗa batare daya jira cewarta ba sabida jin ana ƙoƙarin tayar da sallah wanda yawanci shike jagorantar limancin amman yau ya makara ta dalilinta cike da wani irin sauri kamar ze tashi sama yake tafiya harya samu damar ƙarasawa cikin masallacin yahau sahu shima yabi jam'in sallar.
Bayan sun idar addu'oinshi yay kamar yadda ya saba sannan ya fito sabida hankalinshi dayay gida yana sauri sabida wannan lissafin daza suyi shida abbansu gudun yawan gaisuwar staff ɗinsu yasa yabi ta ƙofar bayan masallacin.
Cikin wani mugun shorck yay saurin jan birki tare da goya hannunshi a gadon bayanshi.
Jada baya yay tare da tsugunnon dabai shirya ba.
Gurfane yake agabanta wadda take kwance tana baccinta ranta fess har wani munsharin daÉ—in iskar wajan takeyi.
"Innalillahi wa'inna ilahirraju'un"!!! kalmar data fito a bakinshi kenan yawun bakinshi ya ƙafe ƙaff babu alamun danshi cikin bakinshi tsananin firgici da mamakine suka rifushe, wanda seda yayta ambaton sunan Allah sannan ya dawo dai dai.
Wannan waccen irin hatsabibiyar yarinyace? ya jima baiga sakarai irinta ba gabas yamma gudu arewa ya duba akwai ciyayi wajan bata gudun wani mugun ƙwaron bata gudun ɓata gari? tunda ko ina akwai nagari akwai mugu.
Watsar da wannan tunanin yay yana aiyana ballagazancin ta.
Wani irin shu'umin kallo yake aika mata dashi wanda nakasa ganeshi sabida yadda ranshi ke a haÉ—e tamau.
Ilahirin rabin kirjinta yana waje baccinta take babu alamun damuwa tsira mata manyan idanunshi yay yana kallonta a wannan karon ya mata kallon tsaf ya kuma fahimci ƙarancin shekarunta, wadda ko sa'ar ƴan biyun ammi bata kai ba, wato wannan ita ake kira da girma ya riga hankali, miƙewa yay ya taka zuwa gaban famfon da ake ɗiban ruwa akai cikin toilet ɗin masallaci hannunshi ya tara ya ɗebi ruwan cike da zallar mugunta ya nufo inda take kwancen wadda alamu suka nuna ma bata san da wanzuwarshi a wajan ba, zube matashi yay tass asaman fuskarta tare da ƙara tsugunnon agabanta yana kallon yadda ta zabura tana wata iriyar miƙa wadda sauran kaɗan ta sumar dashi, bakinta ta turo gaba kamar wata ƙaramar yarinya kafin kuma tai wani irin juyi wanda ya bata damar samun babban muhalli a saman jikinshi ta saka hannunta ta janyoshi kamar pillow, batare data buɗe idanunta ba take yawo da hannunta zuwa saman face ɗinshi jin gashi kwance bisa fuskarshi ya bata tabbacin a jikin namiji take wani irin tsalle zuciyarta ke mata kafin ta samu ta juyo da ƙyar tare da kici-kicin neman tsira sedai ta makaro sabida ya riga yay mata riƙon tsauri kasancewar shi namijin duniya yasa ya gama janyota zuwa saman cinyarshi ba tare kuma daya zauna ba, a yadda yake a tsugunnen haka yake riƙe da ita ajikinshi saboda idan ya saketa tabbas xatai mummunar faɗuwar da setaji mugun ciwo, jin ƙamshin shu'umin turare mai azababben ƙamshin da tunda mama ta kawota duniya bata taɓa jin irinshi ba yasa ta soma ƙoƙarin bude madai daitan idanunta waɗanda suka ɗan kumbura sabida bacci.
Karaf ta sauke akanshi wani tsalle cikin zuciyarta yay wanda hatta shi seda yaji yadda bugun zuciyar tata ke mugun tsallen, kafin ta soma ruwan hawaye kamar famfo tana kuma ƙoƙarin dira sedai ta makaro, abinda ya bata mamaki sema ganin datai ya miƙe da ita a tsaye a hakan, ilahirin jikinta rawa ya cigaba dayi, kafin ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ganin ya direta a gabansa wanda ta koma ƴar firit agaban nashi sabida yanayinshi na ingarman namiji, taga-taga ta somayi zata faɗi sabida yadda kanta yake neman juyewa, karaf ta kumajin taci karo da tattausan kirjinshi wanda babu abinda take shaƙa se ƙamshi gefe guda kuma ta sami guri mai kyau domin har wani nutso tai acikin kirjin nashi.
Wani irin zirrrrrrr yarrrr zuuuuuuuu!! yaji adukkan ilahirin gangar jikinshi har zuwa yatsun hannunshi tun sanda ya ganta a haka yaji wani zazzafan zazzaɓi yana son rufeshi batare daya shirya ba, lokacin daya karata jikinshi tabbas yay namijin ƙoƙari kafin ya sami nutsuwarshi ta dawo dai dai, still yanzu datake maƙale a ƙirjinshi jin wani mugun fitsari yake yana taho mishi wanda bai san dashiba, cikin tsantsar kamewa ya sami damar tureta daga jikinshi nashi tare da maka mata wata razananniyar tsawar! data saka Bebi zubewa tai zaman da bata shirya ba, tare da saka hannunta tana rufe kunnenta, baki ɗaya ta firgice ta susuce ta tsorata kamar xata shiɗe.
"Dan gidanku haka aka koya miki, rungumar maza!! ya daka mata wannan tsawar tare da furta mata wannan maganar wadda baisan da fitowarta a bakinshi ba.
Bai jirata ba yaci gaba da cewa........
"Kinzo nan kina shashanci da daƙiƙanci kinbar ƴar uwarki tana bilayin nimanki sabida ke bakkida nutsuwa ko?".
A wannan karon sosai yayo gabanta kamar ze duketa cikin sauri tai baya tanajin wani irin mugun tsoro aranta tana ayyana wannan wata sabuwar jarabarce kenan babu dangin uwa bare na uba daga haduwa yau ze nemi shiga rayuwarta.
Amman a fili kuka take sosai tana haÉ—e hannunta guri É—aya tana boyesu a bayanta dan duk tagama tunanin zaneta zeyi wata muguwar faduwar gaba takeji har shakewa take sabida tsabar kuka!.
Jada baya yay yana kallon tsoronshi a saman fuskarta, murmushin da bansan ma'anarshi ba,naga yayi tare da kallonta da fitinannun mayun idanunshi dasuka É—anyi ja! kaÉ—an.
"Maza biyoni wawiya, idan kika batamin lokaci zan saka karnukan bayan can na masu gadi sumin kaca-kaca da naman jikinki".yafaÉ—a yana juyawa tare da gyara jikinshi sosai yawani tamke fuska kamar koda yaushe.
Lokacin daya karasa inda yabar hussaina yay mamakin rashin ganin ta dabai yiba, wanda ita hussaina ganin ya jima bai dawo ba yasa kawai tai tunanin maganarshi ta farko wadda yace ko Bebi tai gida, shiyasa tai tafiyarta tana ayyana yadda xata karta ma bebi rashin m.
Tsaki! yaɗan ja baison mutum marar yarda, kafin ya karasa gaban motarshi wadda taci black tinted, a window's ɗinta yay mata key ya bude tare da shiga ya xauna yana addu'a kafin ya kunnata, haryay revars yana kokarin tada motar bata karasoba seda ya juyawa sannan ya hangota yaga yadda take tafe kamar wadda ƙwai ya fashewa aciki duk ta cure kanta da hijabin jikinta dayake tunanin bayan tawowarshi ta sami zarafin sashi, tsayawa tai cike da tsoro! tana waigen hussaina amman wajan wayam haka zalika bataga hussainar ba, jin ƙarar horn a gabanta yabata tabbacin wancan masifaffen ne kamar yadda ta saka mishi, cike da firgici ta karasa gaban motar ganin, yadda motar take da wani irin kyau kamar babu gobe yasa taja ta tsaya jikinta yana faman rawa.
Cike da masifa ya turo marufin kofar tare da firfito mata da manyan idanunshi yana mata nuni data shigo cikin motar.
Cike da tsabar tsoro ta shiga wajan daya bude mata inda yake emty site na kusada driver site hannunshi ya É—ora saman cinyarta ya tura murfin ya rufe motar kafin yaja ya tafi wanda yabata damar sakin wawiyar ajiyar zuciya............
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.