Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 65 of 81
*86*
Nan da nan idanunta suka cika da mugun tsoro sedai kuma babu damar tayi magana sabida dodon nata yana wajan amman a zahiri inda dafa hali daseta turje taƙi shiga cikin gidan sabida furucin dataji wanda ya kira da goma yayi yanzun.
Ɗan jimm yay kaɗan yana kuma nazarin gidan sosai yake mamakin yadda ze iya kwanan cikinsa idan hakan ta kama, lallai rayuwa babu tabbas duba wai shine ze zaman gidan nan wanda bai kai part ɗinsa na gida girma ba, shi seyau ma yake kuma ƙarewa gidan kallo sabida tunda ya ginasa baifi sau ɗaya yazoba shima kuma lokacin yana hidimar ginin kamfanin shine shine ya biyo yaga gidan sabida ya riga da ya gama bawa masu kwangilar ginin gidan komai.
To sekuma yau da wannan ƙaddarar Auren ta kawoshi yay zaman wucin gadi kafin suga kuma mai Allah ze musu nan gaba.
"Amman goma tayaya macizai suke shigowa nan É—in hakan ai kamar da akwai matsala?".
Sosa kai goma yay kana yace.
"Wallahi oga duk haka aketa fama kasan in akace maka waje da ƙarancin mutane baya ga nan kuma waɗannan ciyayin na nan suke kawo su".
YafaÉ—a cikin ladabi da biyayya.
"Okey yanzu dai kanemo masu cire ciyayi sannan ai feshin maganin sauro sekuma a samo mutane dazasu zauna a waÉ—annan ragowar biyun kaga kunyi ciki da ita kuma yarinya ce kaganta zataji tsoron zama ita kaÉ—ai anan side É—in, inda hali ma asa ma mata mai tayata hira".
Yakai maganar yana kallon Bebi wadda tai ƙasa da kanta tana nanata.
"Kuma yarinya ce kaganta"!
Acikin ranta tana mamakinsa wani zubin idan yay magana kamar da biyu.
Dariya goma yay kana yace.
"Babu matsala oga ai tunda madam É—inka ce babu komai akwai yarinyata ta farko sunanta mufida zata dinga zuwa suna hira shekararta sha huÉ—u ai ta isa base an kirawo kowa ba,sannan ta É—an dinga shiga suna hira da matar gidan nawa".
Murmushi yayi kaɗan tare daɗan sosa kanshi da keyn mota.
"No ita É—iyan taka dai ta shigo amman bani son yawan fice fice tai zamanta a wajanta nagode".
YafaÉ—a babu kunya bare kara.
"Okey to shikenan babu matsala oga ai kawuce komai wajanmu alkairin dakake mana.......".
"Is ok goma muje ko? dafatan an É—an gyara nan É—in?".
Ya dakatar da goma akan maganar dayake son yayi kana yaja ƙafafunshi suka nufi gaban ƙofar part ɗin wadda take ta zallar baƙin ƙarfe.
Da azama goman ya saka keyn ya buɗe ƙofar goman shiya soma shiga kafin Aliyu yabi masa baya se Bebi wadda take sauri kamar wani abun ze kamata sabida itafa tunda taji an ambaci maciji shikenan fa sinadarin tsoronta ya ƙaru fiye dana da.
Sallama goma yay a ɗan ƙaramin tsakar gida, tare da tsayawa yana yiwa Aliyu magana.
"Oga ga wannan"
Ya miƙa masa wani extra key daban sannan yace.
"Wannan key É—in room&parloun, ne amman kasan babu wadatattun É—akuna ina ganin É—aki É—ayane se falo ga toilet kuma anan tsakar gida se kicin, kasan tsarin gidajen arean nan se ahankali".
Karɓar keyn yay tare da cewa.
"Nifa goma nayi mamakin tsarin ginin gaskiya yayi ƙunci ahaka Allah ya kyauta".
Dariya goma yay.
"Ai oga shiyasa lokacin da ake ginin naso kana zuwa sabida kozaka sauya fasali rashin zuwanka yasa sukai maka ginin gidajen haya se haƙuri fa duk haka muke fama musamman kai oga daka saba rayuwar sakewa nan ɗin ze maka zafi".
Dariya yayi a wannan karon wadda ta saka Bebi ta saki baki tana kallonshi ashe haka dariya take mugun yi mashi kyau, sannan yace.
"Toya za,ai Goma damafa in baka mutu ba ai baka gama ganin rayuwa ba hakanma ai mungode Allah".
"Hakane oga yanzu bara na koma sabida na samo masu aikin ciyayin akwai ruwa a toilet cikin famfo ga kuma na tsakar gida, sedai wataran idan ya ƙare se an fita ɗiba, sannan duka nasa an gyara cikin room ɗin nepa kuma babu matsala muna samu sosai".
Goma yakai maganar yana ɗan sada kanshi a ƙasa.
"Okey nagode goma am pls nace zan maka transper yanzu dan Allah kaje store kai mata ɗan shopping ka haɗo da ƙaramin gas komai dai na buƙata sabida ni zan koma can gidane abba yana jirana".
"Angama oga babu matsala ni zan juya Allah ya tsare mana kai".
Murmushi yayi tare da ce masa.
"Nagode se anjima".
Harya juya sekuma ya juyo ya kalli Bebi.
"Madam se anjima"
Cikin siririyar muryarta mai kama data yara tace masa.
"Nagode amman ka turomin mufidan".
FaÉ—aÉ—a far'arshi yayi tare da cewa
"Angama madam insha Allahu".
Kana ya juya ya fita cikin nutsuwarsa wadda Aliyu yake dubawa akullum shine ma yasa ya aminta dashi sabida goma irin mutanan nan ne masu gudun duniya yana da matuƙar kirki sosai kuma shima ɗan ɗambattane domin ga gidan mahaifinshi ga gidan marigayi Alhaji Ali kakansu Aliyu kenan.
Gaban ƙofar yaje ya zira keyn ya buɗe ta sannan ya tako gabanta.
"Kishiga ciki bara naje mota na É—auko miki jakar kayanki".
Ya faÉ—a mata idanunshi na yawo a saman fuskarta.
Sunkuyar da kanta tayi ƙasa tana wasa da yatsun hannunta batare datace masa komai ba.
Juyawa yayi ya fita daga gidan tana jin sautin tura ƙofarshi aikwa a 360 tabi bayanshi sabida bazata iya zama ita kaɗai ba.
Daga bakin gate ta tsaya tana hango sanda ya buÉ—e boot yana fito da kayan nata harya gama ya rufe sannan ya turo gate É—in ya shigo.
Kusan cin karo yayi da ita wadda take kokarin juyawa ta bishi.
Haɗe ranshi yay tamau tare da raɓeta ya wuce.
Bin bayansa tayi har suka koma cikin part É—in nasu.
Wannan ƙofar ɗakin daya buɗe ɗazu ita ya shige itama tabi bayanshi madaidaicin falone wanda babu komai acikinsa se doguwar kujera wadda daga ganima sabuwa ce domin ga ledarta nan, se ƙaton carpet ɗin da aka shinfiɗa acikin falon se fankar sama sabuwa dall se labulan daya ke a ƙofar ɗakin dana window da kuma ƙofar bedroom ɗin, wuce nan yay ya shiga cikin room ɗin itama ta bishi abaya, nan ɗinma carpet ne aka shinfiɗa acikinsa se ƙatuwar katifa sabuwa wadda aka shinfiɗa katon bedshit se ƙaton bargon rufa a gefenta daban tare da pilow guda biyu da aka jera a gefen katifar bayan nan ko sip babu bare kuma madubi nan ɗinma akwai fankar sama acikinsa, aje jakunkunan hannun nashi yayi agefen katifar sannan ya zauna shima daga gefen yana mai sunkuyar da kansa ƙasa alamun gajiya sun bayyana ƙarara a saman fuskarshi.
Takowa tayi sannu a hankali itama ta zauna a ƙasan carpet ɗin dab da ƙafafunshi seta ɗora kanta a saman katifar sabida itama ta gaji kuma lokacin 12 na rana ma ta kusa sabida haka itafa cikinta ma yasoma kiran chiroma.
Tsitt É—akin yayi bakajin sautin komai sena fankar dake famanyi sakamakon wutar nepar dasuka kawo yanzu.
ÆŠago da kanshi yayi tare da zuba mata idanu yana kallonta.
"Kinga dai yadda tsarin gidan yake kuma ni ba mazauni bane ba, sabida yanayin aikina ki dinga rife ƙofarki inna zo zanna saka extra key ina buɗe wa sannan kuma bana son fita kinsan Allah ko nan gidan goma nazo na tadda kin shiga sena ɓata miki rai duk abinda kike so kidinga gayamin, zan sai miki waya ki dinga kiran mamanki tare da ammi sannan nima zan sa miki numberta".
YafaÉ—a yana son ya tashi tsaye.
Cikin aro jarumta Bebi ta saka hannu ta dafe saman cinyarshi sannan ta dubeshi.
"Nifa baxan iya zama anan ba salon macijin yazo ya saremin jikina".
Tafaɗa tana kuma raɓa jikinta sosai ajikinshi alamun tsoro sun nuna atare da ita.
Zame hannunta yayi daga jikinshi sannan ya zamo daga saman katifar shima ya zauna saman carpet É—in ya jeru da ita.
Tsintar kanshi yayi da kamo hannunta guda É—aya, wasa yake da yatsun hannayen nata sannan taji muryarshi acikin dodon kunnenta.
"To yanzu idan ban tafi ba, da yaya zanna samo miki abinci kina ci?".
YafaÉ—a mata hakan muryarshi da zubin rarrashi.
"Neman abincifa zan tafi".
Ta kuma jin maganarshi ahankali kamar da wasu awajan.
"Nifa bacewa nayi karka tafi ba, amman kanafa ji ance maka akwai maciji agidan sannan kuma ni seka barni ni É—aya?".
Ta faÉ—a tana turo bakinta gaba kamar zata tsinkoshi.
Kallon yarinta yake mata jiba yadda take acting kamar wata yarinyar goye tsintar kansa yayi dajin dukkan zafin É—azu ya gushe agareshi sabida yadda take fici-fici da idanun rigima tsira mata idanu yay tare da saka hannu ya tallafi kumatunshi dasu alamun tagumi batare daya tanka mata ba.
"Sabida haka sedai na shiga gidan wancan Baban mufidan koka kiramin ita kaga har yanzu bai turo ta ba kuma ina jin yunwa sosai".
Takai maganar tana turɓune fuska alamun zata yi mashi kuka!.
Can cikin ƙasan maƙoshi muryarshi cike da zallar gajiya taji yace.
"Pls kada kimin kuka malama me zakici yanzu?". yafaÉ—a yana sakin hannunt.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.