Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 40 of 81
*ANZO WAJAN DASU O'O SUKE SO*
_NAGAJI WALLAHI_
*NOTE EDITING AFUWAN*
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }
NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
*58*
Azaune a saman tabarma sune suke amsa mata sallamar gefe guda kuma suna yi mata sannu da zuwa.
Cikin kulawa take amsa musu tare da tube mayafin jikinta ta ratayeshi a saman igiyar tsakar gidan, sannan ta zauna agefen arfa wadda tana ganin mama ta zauna ta haye saman cinyarta tana shagwaɓar auta.
"Mama ina Bebi ko bata biki ba?".
Cewar hassana wadda ta miƙe domin zubowa mama tuwon daren dasuka gama tun ɗazu domin su tunima sunci nasu daga na mama sena Bebi da shahid wanda yake wajan gawayin shi.
"Tana gidan iya wai zata wajan mutuniyarta sadiya suyi magana akan ankon mauludi, tama gama abinta bana banida kuÉ—in anko injima da hidimar saukarta mana".
Tuwon hassana ta kawo mata gabanta ta dire mata sannan ta koma ta É—ebo ruwa a kofi ta aje matashi.
"Aikuwa dai mama dan saukar naji ance kuÉ—in allon nasuma yafi namu lokacin da mukai tsada fa".
Inji hussaina, wadda take riƙe da tourch light a hannunta tana haskawa mama tuwon gabanta wanda zata zuba miya cikinsa.
Sallama sukaji daga ƙofar gida,kafin kuma wani yaro ya leƙo da kansa.
"Assalamu Alaikum, wai ana kiran Balki inji mijinta".
Yaron ya faɗa yana ƙoƙarin juya kanshi ya fita.
"Kaje kace ai babu balki agidan nan matar aure".
Cewar mama wadda ta dakata da cin tuwon nata.
Komawa yaron yay minti uku ya dawo.
"Wai inji khaleepha mai shanawa, É—an gidan mai gwall yace kota fito koya shigo da kanshi ai matarshi ce".
Cikin tsananin takaici hussaina marar haƙuri tace.
"Kace masa ko ubansa isa ya sake ya shigo mana gida semun karyashi bare kuma shi, duk talaucinmu munsan darajar kammu".
Jinjina kai mama tai kurum zuciyarta tana suya tabbas setai da gaske domin taga lamarin yana son zarmewa.
Komawa yaron yay ya sanarwa khaleepha wanda yake fake jikin black CRV ɗinshi wadda taci uban tind babu abinda ke tashi daga jikinshi se uban ƙaurin hayaƙin sigari dana giya wanda daga ganima daga tazubar ɗinshi ya nufo nan.
Tsaki yaja da ƙarfi, shi kanshi bawai son auren nan da dakus ɗinshi ze masa yake ba, sedai ga yadda yaga yarinyar last time zasu fita ita da yayinta yaji yana mugun sha'awarta yana son yaji kalan nata baiwar wannan dalilin nema yasa yay bincike akanta harya gane ƴar ƙanin yaron mahaifinshi ce tasi'u wanda yasan samun ta baze masa wuyaba tunda talakawa ne, baiyi ƙasa a gwiwaba ya sanar da dakus ɗinshi daman abinka da mai neman kukan da aka jefeshi da kashin awaki dama khaleepha ya dameshi da kawo mata da shaye shayen kayan maye,ai tuni haji isa ya kirawo yaron shi tasi'u ya shigar da maganar ɗanshi abin sonshi cikin rawar jiki tasi'un yay na'am daman tunda yaga yarinyar ta tsaye mishi aranshi ya ɗagu daman ya samu su haɗata da ko wanine anan ƴan kusan sabida kyan yarinyar kar ya fisgi hankalin wani mai nerar yazo ya aureta uwarta,ta huta.
Tsakin ya kuma ja akaro na biyu ransa idan yay dubu ya ɓaci sintiri yake famanyi a kofar gidan jiyake kamar ya faɗa ciki bayajin yau ze iya bacci idan bai taɓa nonon yarinyar nan ba, sabida yadda zubin halittar ta ya tsaya mishi arai yana ƙoƙarin fiddo da wayarshi dan ya kira tasi'u yagaya mishi halin da ake ciki idan da halima ai ɗaurin auren nan gobe ko jibi danya nuna ƙarfin kuɗinsu babu abinda baze iya karɓo musu ba.
Hasken wata shegiyar haÉ—aÉ—É—iyar mota yagani wadda taiwa tasa gudun wuce sa'a a kuÉ—i yaga ta haske masa fuska kuma abin takaicin motar tana kallon saitin tasa ta riga ta bake wajan ga kuma lungun daman bawani mai girma ba.
Takaici biyune ya hade mishi sema ya kasa kiran wayar yana son yaga wani É—an rainin wayon ne yazo ya tokareshi haka kamar hanyar ta ubanshi ce.
Cikin jin haushi Ali ya dubi usman "Na baka minti, Biyar Allah ka ƙara zan saita layi dan kasan inada abinyi" shiko usman tsabar mamakin brain ɗin Ali yake shifa koyasha giyar wake baze iya kawo kanshi layin ba bare gidan amman tsabar fasaha da riƙe abu akai irin na Aliyu batare da tambaya ko shakkuba ya kawo su layin wanda tsabar ƙwarewama baibi dasu ta wancan layin na farko dasuka kasa shiga da mota ba, wannan karon ta bayan layin ya shiga inda suka samu babbar hanya har kofar gidan ya sami ƙarasawa da motar, sedai CRV ɗin da suka gani a ƙofar gidan yasa basu ƙarasa dab da gidan ba seyay parking daga ɗan gefe kaɗan, amman yarasa mai yasa Aliyun ya haske Crv ɗin?.
Fitowa usman yay yana cewa.
"Afuwan ango yanzu zan leƙa na fito".
Tsaki! Ali yaja yana mamakin shishshigi irin na usman yanzufa gidan yakeson shiga sekace na ubanshi bai kashe motar ba sema ƙara hasken fitilar motar tashi dayay tare da tsirawa waje ɗaya idanunshi.
Usman sallama yay a bakin soron gidan tare da ambatar sunan hassana.
Dayake babu wata tazara da tsakar gidan yasa mama jin sallamar dan haka ta É—an É—aga murya tana cewa.
"Waye?"
Batare data bar wani ya fita ba sabida tsaro, daman duk suna cikin damuwar lamarin wancan shaiÉ—anin yaron.
"Nine mama É—anki usman mai dambu".
YafaÉ—a cike da barkwanci.
FaÉ—aÉ—a far'arta tayi tana cewa.
"To hassana maza shinfiÉ—a masa sallaya acan shigo mana kaida gidanku".
TafaÉ—a tana jan mayafinta wanda ta ciresa É—azu ta rufe jikinta tsaff.
Sallama usman yay tare da shigowa ciki.
Zama yay akan sallayar yana gaida mama.
suma ƴan biyu dasu ihsan suka gaidashi tare da miƙewa suka bar wajan.
"Mama lafiya kwana biyu ƙannena basa fitowa, nima dayake na kwana biyu banje ba sabida anyi bikin wannan ƙanin nawa wanda mukazo dashi kwanaki, toseda na koma jiya malam salihu kecewa basa zuwa to Allah sadai ba laifi mukai ba?".
YafaÉ—a cikin nutsuwa.
"Lahh É—ana wallahi babu komai kasan garin damuna se ahankali, amman insha Allah zasu dawo ne".
Sannan ta numfasa kana ta É—ora da cewa.......
"Allah sarki ashe biki kukai? to Allah yasanya alkairi aikuwa na shaidashi wannan marar maganar ko dakuka zo kwanakin baya?".
Dariya usman yay "Eh! fa shine to mama kinsan sha'anin biki duk gajiya ta hanamu, fita office ni se jiya na koma ma".
Murmushi mama tai tana yaba karamcin usman tare da saukin kanshi.
"Aikuwa dai abubuwan biki se hakuri yawa garesu, hassana! zoki kawo mishi tuwo"!
"lahh wallahi mama yau cikina a koshe yake amman watarana naci insha Allahu".
Hira suka cigaba dayi.da usman akan tsadar rayuwa da ake ciki wanda mama ta sake sosai dashi kamar sun jima jitai hirar usman ta wanke mata damuwar wancan mara kunyar yaron, su hassana suna daga É—aki suna sauraran hirar sunata mamakin shakuwar mama da usman É—in suma.......
Bebi tunda ta shiga gidan iya suka ƙule a ɗaki suna hira ita da sadiya seda aka soma labaran ƙarfe taran dare sannan iya ta kwaɗa musu kira.
"Bebi zoki wuce gida kinsan mamanki bata son fitar dare".
Tura baki Bebi tai gaba.
"Iya ni kibarni na kwana wallahi gidanmu sauro".
Dariyar sakarcin Bebin iya take.
"Maza xona sakaki a hanya ki karasa dan bana son wannan shirman naki".
Kamar zasuyi kuka! iya ta saka Bebi gaba seda suka rakata har bakin layin sannan sukai sallama iya da sadiya suka koma ita kuma Bebin tacigaba da tunkarar gida.
Gabanta ne taji ya faɗi lokacin dataga hasken fitilar mota ya haske hanyar datake harya bata damar kallon gabanta bata kuma kaɗuwa ba seda taga wata bakar ƙatuwar mota still a dab da gidansu.
Tana kokarin hawa dakalin kofar gidan nasu taga mutum kamar bugagge akanta.
ÆŠago kanta tai tana ambatar sunan Allah a zuciyarta.
"Malam lafiya zakawani zo katsayamin kamar ka bugu?"
TafaÉ—a cikin fitsara.
Tare da saka hannunta ta kare idanunta sabida hasken ɗayar motar dake oposite ɗinsu ya kuma ƙaruwa.
Sautin dariya taji kafin taga ya dawo gabanta ya bake hanyarta ta shiga gida se asannan hasken daya haskashi yabata damar ganin koshi É—in waye.
Ɗan gajere ne marar jiki farine tas idan bata manta ba taɓa ganin wannan mutumin lokacin da zasu fita itada da ƴan biyu abakin wani shago yana zaune yana shan sigari ƙwarai ta taɓa.ganinshi.
"Balkisu zinariyata haba nima mijin se ammin tsiwa to angonki ne na jibi ko gata, naxo zance ne muƙarasa mota" yafaɗa yana kokarin kai hannu saman nata.
Jada baya tai sabida ƙaurin daya bugeta wanda ta tabbata na kayan mayene.
"Wallahi tallahi ka kuskura ka taɓamin hannu sena baka mamaki banza gaja kawai".
Tafaɗa tana harararshi kamar idanunta zasu faɗo ƙasa.
Dariyar basawa yay.
"Ke dakata mahaukaciya nixaki mannawa hauka kinsan waye ni kuwa to in bakida labarina kije ki tambaya waye mai shanawa nine wanda idan akacewa mutum yaje ya gani to ni ze gani tantirancina ya wuce tunanin karamin kanki wawiya kawai"!!
Murmushi Bebi tayi tana masa kallon wanda ya sami matsalar ƙwaƙwalwa.
"Ayyah kace bariki ce da kanta agabana to Allah yay min tsari da shaiÉ—anin mutum irinka"
TafaÉ—a babu tsoro atare da ita tana jada baya sabida tunkarar ta dayay.
"Zaki gane baki da wayo yayin da jibi ko gata na turmushe ki na goge bakin tsiwa inma bakida masaniya kije ki tambayi kawunanki waye ya bada sadakin ki yarinya zan nuna miki karshen iskanci".
Gabantane ya faÉ—i har tsoronta ya bayyana hankalinta ya tashi nan da nan in kuwa har aka aura mata wannan tabbas angama da rayuwarta waye bai san iskancin shiba seda yafaÉ—i sunanshi tama kuma shaidashi dama akanta É—azu wannan baffan nata yazo gidansu.......
Jikinta na rawa take kokarin shiga gida domin ta ƙarajin komai sabida ɗazu sama sama taji maganar dan tana tsaka da zazzaɓi.
Caraf taji hannunshi saman nata yana kokarin haɗata da jikinshi cizo ta gantsara mashi agigice ta juya da gudu amai makon ta koma gida tsabar ruduwa seta koma bayan layinsu cikin wata kwana ta raɓe tana kuka!
Duk abinda suke Aliyu yana kallon su kamar a tv sedai baijin abinda suke faÉ—a amman ga yadda yake hango waccan marar kunyar yaga kamar fitsara takewa gayen, bai kaÉ—u da lamarin ba seda yaga gayen yanason rungumeta wanda tsabar kaÉ—uwa yasa shi balle marufin motar batare daya shirya ba ya fito tare da nufar wajan dasuke.
Yana zuwa tana guduwa wannan gayen kawai yagani wanda yay mishi kama da ƙazami.
A ƙyamace Aliyu ke kallon khaleepha kamar yaga kashi.
"Ƙaddara ƙanwarka akazo yiwa wannan iskanci xaka yarda nace zaka yarda dan ubanka"!!
Khaleepha yaji murya dakakkiya ta doki kunnenshi.
Kafin ya É—ago kanshi ya zuba su akan tsayayyen namiji É—an gayu wanda babu wargi atare dashi,Cikin tsoro da kuri khaleepha yake cewa.
"To kaikuma waye kuma.mai ya ruwanka da matata itafa zan aura nan da ƴan kwanaki ina ruwan.......,Bai ji karashen maganar ba ya kwaɓe bakin khaleepha da gefen hannunshi.
"Ko mijinta ne kai zan iya hukunta ka sabida su mata killacesu akace ayi ba watsasu ba bare kuma.kai daga duk inda ka fito.kai ba É—an kirki bane wawa kawai ubanka ne ze aura maka ita dalla ja gwangwanin motarka kabarmin nan kona saka hukuma ta kama min kai"
Aliyu ya faÉ—a ranshi na suya.
"Zan tafi amman kasani in ka hanani taɓata anan wallahi baka iska ka hanani auranta cikin satin nan ba domin tuni sadakina ya riga komai isa gidansu".
YafaÉ—a da sauri ya faÉ—a mota yaja a guje jikinshi na rawa kar wannan mai kama da samudawan ya zaneshi.
Dariyar rainin hankali Aliyu ya saki tare da kaiwa iska naushi yana mamakin wautar wasu iyayen da basa tsayawa wajan binciken suwa Æ´aÆ´ansu zasu aura, sunfi daraja kuÉ—i akan cancanta, wannan yaron daga duk inda ya fito É—an mai kuÉ—ine amman sangartacce marar tarbiya, to ita kuwa tayaya babar waÉ—annan yaran xata haÉ—a Æ´arta da wannan yaron marar tarbiya kuma inba mantawa yayba yaji kwanakin baya tace yaran marayu ne.....
Mai makon ta tsaya ta zaɓa musu majazen ƙwarai shine zata haɗa ƴarta da wannan shikam dan dai baya da son shiga hurumin daba nasa bane amman tabbas daseya magantu akan wannan lamarin dan yana tausayawa duk wadda xa,a haɗa aure da wancan ɗan ƙwayar.
Hanyar databi ya tsirawa ido............
Yana ayyana tsabar duhun hanyar tare da ƙanƙantar ta domin garin babu wuta shikanshi dalilin dayasa ya kunna fitilar motarshi kenan.
Cikin nutsuwa yake taka kafafunshi harya karasa cikin lungun mai uban kwatoci.
Raɓe yaganta ajikin bango tana..............
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.