Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 19 of 81
_DAGA WAJANSU HASSANA_
Lokacin da masinjan usman ya kai musu flaks É—in sosai sukai mamaki ganin dalla dallan kuÉ—in daya zaro ya miko musu tsorata..........
*MATA DA MAZA ƳAN KASUWAR DAKESON NA TALLATA MUSU HAJARSU A SAMAN SHAFUKAN LITTAFINA CIKIN FARASHI MAI SAUKI ZASU IYA NEMA NA TA NAN 08142105218*
*MASU SON LITTATTAFAINA DANA KAMMALA KAMARSU*
*ÆŠAN MAJALISSA*
*HASKE*
*KOBA SO*
*RABON WANI*
*DA IZZATA*
*DUKKANSU AKAN FARASHIN NAIRA DUBU ÆŠAYA,1000 IDAN KUMA ÆŠAI ÆŠAI KIKE BUKATA 300 DOCUMENT A HADE SE KARATU ZAKI TUNTUBEN ANAN 08142105218 DOMIN KI BIYA KI MORE KARATU*
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }
NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
*23&24*
Cikin mamaki mai ɗauke da tsoro hassana ta dubi masinjan ayayin dayake Miƙo musu kuɗin hannunshi tare da cewa,"Gashi inji oga usman yace ku zuba masa dambun, amman kada a saka yaji".Karɓar flaks ɗin hassanar tayi ta soma zuba masa harse da ta cikashi damƙam har baki sannan ta rufe, kuɗin ta amsa a hannunshi ta ƙirga iya wanda tasan yakai adadin na dambun ne sannan ta mikawa masinjan ragowar canjin, wanda shi harya soma tafiya tai saurin binshi, sakato yayi tare da cewa"Ai yace kada na karɓi ragowar na baku duka", ɗan jim kaɗan tayi tare da kallonshi"A,a dan Allah kace masa yabarshi sabida mamammu zata mana faɗa idan taga kuɗin ya haura".tafaɗa tana miƙa masa kuɗin kana ta koma wajan sana'arsu, miƙawa hussaina kuɗin tayi tana mata bayani, zaro idanu hussaina tayi tare da cewa,"Lallai wannan mutumin yau soyake mama tai yanka yanka damu kenan",dariya sukai atare "Aidaman shiyasa nayi saurin dakatar dashi tun wuri" cewar hassana wadda ta mike zuwa wajan zubawa wani alala.
Shiko masinjan usman yana komwa office ya tarar da ogan nashi yana amsa waya, dakatawa yayi harya kammala sannan ya rissuna ya mika mishi tare da cewa...........
"Oga wallahi fafur sunƙi karɓar kuɗin wai mamansu zata musu faɗa idan taga kuɗin ya haura, wallahi oga babu yadda banyi dasu ba, amman sunƙi amsa".
Yakai maganar yana rissunar da kanshi a ƙasa.
Ƴar dariya kaɗan usman ya sauke tare da jinjina wannan lamarin.
Daman ana samun yara masu tarbiyar nan har yanzu? tabbas duk lalacewar zamani ba'a taɓa haɗuwa a zama ɗaya dole akwai nagari sannan kuma akwai ɓata gari.
Sau tari wasu yaran tsananin babu takansa su sallama kansu wa mazan banza domin su sami abinda zasu ci, wasu kuwa tsabar kwaÉ—ayine ke rufe musu idanu, harsu faÉ—a halaka, wasu kuwa laifin iyayen sune.
Amman su waÉ—annan yaran kana kallonsu, dai kasan bamasu wadata bane, amman daga gani sunada tarbiya sannan kuma mahaifiyarsu a tsaye take domin ganin ta basu tallafi ta ko'ina.
"Oga ga dambun fa".
Yaji muryar masinjan a saman dodon kunnenshi.
ÆŠagowa yayi fuskarshi É—auke da murmushi kamar koda yaushe sannan ya dubi masinjan nashi.
"Ok ka ajemin saman frij nagode kaje da ragowar canjin kasayi wani abun".
Cikin rawar jiki masinjan ya dubi usman tare da rissunawa sosai gabanshi.
"Kai oga bansan dame zan maka godiya ba, amman ina roƙon Allah daya saka maka da mafificin alkairinshi amin nagode ƙwarai".
DaÉ—ine ya kama usman na wannan godiya murmushi ya saki tare da É—agawa masinjan hannu batare daya ce mashi komiba.
Aikin dake gabanshi ya cigaba dayi batare daya kumabi takan zancen Æ´an biyuba, amman yana ji aranshi tabbas ze duba lamarin yaran yanajin ze tallafesu da wani abun.
Ya jima a office É—inshi yana aiki har aka kira sallah, bai samu fita masjid ba amman yayi acikin office É—inshi sannan ya É—auki flate ya zubo dambun da masinjanshi ya aje masa shi bisa frij,
Tun kafin ma ya kai lomar cikin bakinshi yaji wani sihirtaccen kamshi mai É—aukar hankali ya shiga cikin hancinshi.
Wani irin ƙamshin attaruhune tare dasu albasa, ga gyaɗa tabi lafiyar saman dambun ga wadataccen zogale malam, tuni usman ya soma haɗiyar miyau jikinshi yana mazari, ya koma saman raising chair, ya zauna kana ya ɗora ƙafafunshi ɗaya kan ɗaya, ya fara da bisimillah a cikin bakinshi sannan ya ɗauko spoon ya soma ɗibar dambun.
Wayyooo! tuni usman ya soma mazari kunnenshi ya soma rawa at list usman seda yay flate biyu na dambun da ƙyar madam ɗinshi ma ta samu ɗan kaɗan wai hakan ma sabida darajar cikin jikinta ne yasaka ya rage mata shi,Sosai yaji daɗin dambun seyace idan ba ammi ba babu wadda takai wannan matar iya dambu,ruwa ya buɗe yasha tare da hamdala ga sarki Allah kana ya koma gaban aikinshi yana ayyana yadda ze ringa bada kuɗin nashi na mussaman sabida matukar daɗin da dambun yayi mashi.
Wajan karfe ukun rana Allah ya taimaki su hassana dambun nasu ya ƙare tas! har ana nema shima alalen babu laifi ya kare yau ɗin sedai baikai dambun kasuwaba.
Na baban nazir dasuke ware mashi hassana ta É—auko tana kallon hussaina"Tomu yanzu yaya zamuyi da dambun baban nazir kinga har mun tashifa bai zoba", cikin kulawa hussaina ta dubeta tare da cewa"Ki bawa mai gadi idan ya fito seya bashi kawai" wannan shawarar ta karba haka ta kaiwa mai gadi dambun baban nazir sannan ta koma wajan Æ´ar uwarta suka haÉ—a kayansu, aka suka É—ora kulolin har zuwa bakin gate yau sun É—anyi jinkirin samun abin hawa, kafin kuma Allah ya basu iko wani yazo sukai ciniki suka hau suka wuce gida.
Cikin mintuna talatin suka isa gida a bakin layi suka tsaya tare da sauke kayansu, yauma kamar kullum shahid ne ya taimaka musu da É—aukar kayan zuwa gida, bayan suma sun sallami mai napep É—in suka wuce cikin layin su.
Cikin farin ciki mama take musu barka da zuwa yauma kamar kullum ta taresu da ruwa tare da abinci,"Mama banga Bebi ba tana ina?" cewar hussaina, murmushi mama ta saki"Tunda ta dawo daga makaranta ta shige ɗaki ko hijabi bata cire ba naga dai ta kwanta". tafaɗa tana mikewa zuwa bakin rariya"Mama kodai mutanan natane zasu hauro?".cewar hassana,"A,a inaga ko baccine yaci ƙarfinta kinsan fitar sassafan data tsira gudun karta fita talle".dariya hussaina tayi"Aikuwa mama ta shirya inaga ranar lahadi tunda basu da school ita zatabi hassana".juyowa mama tayi tare da kallon hussaina"Akan wani dalilin ke zaman me zakiyi agidan? tunda ku kunyi Candy base ku fita ba ita kuma da Allah yasa yanxu ta mayar da hankalinta ga karatun nata seku barta taje kafin mugani itama idan ta gama ɗin me Allah ze mana".
Turo baki hussaina tayi sega hawaye nan shaaaa! sun wanke mata fuskarta"Haba mama yanzu tsakani da Allah ita kullum sedai taci tai kashi ta kwanta mu zamu fita ita bazata iya kama mana ba", tsame hannunta tayi daga ruwan wankin shinkafar gabanta ta dawo gaban yaran nata, tagumi tayi tana kallon yadda hussaina take kuka!
Hassana kuwa tai kicin-kicin da ranta kamar kace mata kat! tasaka ihu! daman tasan halinsu tun tana goyonsu É—aya baya abu É—aya yay shuru.
"Kinga daina kuka! akanme zakiyi kuka? indai akan tallan Bebine yi haƙuri kuma ku daina gaba ɗaya mu haɗa kai mu zauna semuci abinda zamuci a ahaka, kunsan dai halinta bana son ta fita taje ta ɗauko mana abinda yafi karfinmu ko, kuma bawai bana sonku ko neba bakuma bam-bamci yasa nake cewa kukai ba duka-duka idan kuka kwantar da hankalinku kwana nawane kun daina ma gaba ɗaya, bana son Bebi taje musu waje tai abinda ze jamana matsala, tunda Allah yasa ta koma makaranta shikenan zancen rashin aikin da batayi agida kuma wannan kanta dan akwai lokacinda setai kuka da takaicin haka bawai ina mata baki bane, Ai ita ƴa mace indai tace son jiki da rashin aiki xatai wallahi to tana tare da muguwar matsala Allah ya gani ina yi kokarina akanta amman tunda ita haka Allah yayita ina nan ina addu,ar Allah ya haɗa ta da miji mai tsafta.
Mai kuka ce ta fashe da dariya hartana kifawa"Mama miji mai tsafta fa?", cewar hussainar tana dariya kamar ba ita ke kuka! ba.
"Eh mana, ba shine maganinta ba".
"Daman mama tun É—azu mukai maganar da hassana ranar lahadi su fita da BeBi nikuma senayi mana wanki sabida ko hijabin fita bamu dashi gobe, wallahi duk sunyi datti amman idan baki so mama na hakura sena fitan Allah ya baki hakuri".
Kallon su tayi da kalar tausayi sannan tace, "Nifa duk ba wani abu bane hakan kuma banji haushinku ba sabida kuma mutanene kamar kowa sabida Ki zauna Allah ya kaimu se taje É—in"
TafaÉ—a tana tashi daga wajansu.
Aguje sukaga Bebi ta fito daga É—aki tana rike cikinta.
Bakin rariya ta tafi tana sheka amai! tana dafe da mararta wadda take kokarin tsinke mata sabida azabar ciwo.
Cikin azama hussaina tayo kanta"Ke BeBi miya sameki haka?,
"Marataaaaaaa wayyo zan..za....zan.............
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.