Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 6 of 81
*VOTE*
*COMMENTS*
*SHARE*
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: I just published "PART 6" of my story "AUREN BARE". https://www.wattpad.com/1109538150?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=autarmanya&wp_originator=ikpMILhK1zeHxV6QZZRcPLMlWp3agsPzqCYNmA9e%2Flr1pMRPEIDwqDYFHx678GsZUFu89NFvDx2V8kClj9MowWZ2YZGRT49eaLvHxUCfU2RB6QQ1iZHpLSXGr09bVAPw
*AUREN BARE !!*🌹
  { _HOT LOVE_ }
     Â
     NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
               *006*
Abba ya ɗauki son duniya ya ɗorawa Bebi wadda ta taso cikin gata, Bebi tafi duk sauran ƴan uwan nata kyau gata da shiga ran mutane sedai fa tun tana ƙarama ta taso a son rigima rashin haƙuri da faɗa.
Sedai kuma tana da son Æ´an uwanta musamman abbanta da mama, lokacin da aka haifi Bebi tana da wata biyu iya hansatu matar malam ado wadda tun daga kan mazan Æ´aÆ´anta biyu bata kuma haihuwa ba, se a wannan lokacin Allah ya bata ciki ta haifi Æ´arta mace wadda taci suna sadiya wadda suka taso kusan kai É—aya da bebi.
Bebi ta bawa ihsan mai sunan gwagwgwo aya shekara biyu, daganan se arfa wadda taci sunan mama aisha wadda da cikinta ne Allah ya É—auki ran Abba shida amininsa malam ado wanda agarin tafiyarsu ta hanyar saro katifa Allah yay musu rasuwa ta hanyar hatsari.
Baƙaramin girgiza waɗan nan iyalan bayin Allah'n sukai ba Bebi batafi shekara huɗu ba lokacin amman har suma ta dingayi tana kiran abbanta, abinda ze baka mamaki shine kaf su Rabi'u babu wanda yazo wa mama ta'aziya se ƴaƴan baba ado ne maza awajan da dangin sa tare dasu malam se ƴan uwan mahaifiyar mama dasuka zo daga ƙauye.
Haka akaci gaba da ƙarɓar gaisuwar Abba tare da amininsa baba ado kowa yaga halinda mama da iya hansatu suka shiga tare da ƴaƴansu seya tausaya musu, sabida tsabar tausayi yasa baba lado ( malam ) ya ɗauki nauyin dukkan abinda za,aci na waɗannan gidaje biyu har zuwa tsahon kwanaki bakwai.
Cikin kwana na bakwai Allah ya nufi su Tasi'u zuwa gidan ɗan uwan nasu waɗanda sukaita ɗaga kai suna watsawa, mama da yaranta kallon banza.
Mariya ƙanwarsu ita ta dubi mama a sheƙe tana cewa....
"Kukuwa a wannan matsiyacin gidan kuke rayuwa kamar dab.......,
Bata ƙarasa ba Bebi wadda take raɓe a bayan mama tana kuka ta cafketa tare da katse ta hanyar furta.
"Ai seki kawo mana na ƴan gay......, itama bata ƙarasaba mama ta kwaɗa mata mafici da kallo mariya tabi Bebi wadda lokacin take ƴar micila tare da maka mata harara gami da jin tsanar yarinyar tashi ɗaya hartana ƙudurar wani abun aranta.
Haka suka gama habaicinsu mama bata tanka musu ba har suka tafi wanda Bebi seda tasan yadda tai tabi bayansu ta watsa musu ƙasa ta ɓuya haka suka juyo suna masifa amman basuga kowa ba.
Lokacin nema mama takejin wai ashe baba suwaiba bata da lafiyar ƙafa yanzu ita kuma inna hasiya bata da lafiyar idanu.
koda bebi ta shigo gida jin ranta take sakayau ko banza taci uban masu gayawa mamanta magana duk da lokacin bata sanma kosu waye ba.
Su abba sunada kwana ashirin da rasuwa mama ta haifi arfa haka tacigaba da raion Æ´aÆ´an nata cikin tsananin dauriya sabida bata da matallafi se Allah.
Malam yakan É—an tallafa mata to kuma shima ga tsufa yasoma kamashi gashi baya da É—a namiji bare ya sami matallafi.
Haka zalika itama iya hansatu take fama sedai ita nura da aminu sun kawo ƙarfi kuma bata kai mama yawan iyali ba sedai itama ɗin maleji take sabida nura da aminu karatu suke dole wani abun setai da gaske kuma duk da haka tana ƙoƙarin ganin ta tallafi maman ƴan biyu da wani abun haka xalika suma su nuran suna tallafawa mama, ita daman Bebi ƴar gidan iya hansatu ce bacci kaɗai ke kawota gida sabida shaƙuwarsu da sadiya ƴar baba hansatu.
Rayuwa tana tafiya waÉ—anda cikin amincin Allah mama ta soma saida kayan miya ganin babu wata riba ta koma yin adashi wanda shiya jamata yin suna acikin unguwar wanda anan tasan mutane sosai kuma suna zaman mutunci da kowa.
Su hassana sun shiga makaranta waɗanda iya kacinsu jss 3 ta ciresu sabida halin rayuwa sedai kuma sun sauke alkur'ani mai girma.
Shahid ne yanzu ze xana neco ita kuma Bebi tana jsss three ita da sadiya su arfa kuma suna primary.
Ganin yadda jama'a suke cinye mata kuɗi ga rigima yasa ta soma yiwa ƴan biyu awara tana kasa musu suna kaiwa can kasuwar kai da ƙafa ada Bebi take ɗorawa to ita kuma Bebi da zarar an kasa mata seta wuce wajan sadiya suje suyo tsokanarsu daganan a zubar suci taci, ta dawo tana raba idanu, gata da mugun tsoron duka sedai tsabar rashin ji.
Ganin haka yasa mama ta soma haÉ—ata da Æ´an biyu kuma ba dan taso ba inda asonta ne tafison yaranta su zama masu ilimi kamar kowa amman babu hali,da magariba kuma zata kasawa shahid tuwo shima ya fitar da rana kuma in babu makaranta ya tafi wajan gawayinsa.
Su ihsan kuma tana ɗora musu kayan miya still su kai cikin unguwa da wannan mama take samun na cefane harma taiwa malam alkairi sabida ya tsufa, su Bebi sun ɗauki malam kakansu ada kafinma su san komai sun zata shiya haifi abba seda suka girma suka gane komai wanda Bebi taji duk duniya bata da maƙiya kamarsu Baba tasi'u.
Su Aminu da Nura kuwa Æ´aÆ´an baba ado su suka zamewa su Bebi yayye kuma dan dai suna karatune basuda yadda zasuyi amman sam basa son wannan tallan nasu Bebi.
Rayuwa tana tafiya lokaci yana ja Bebi yarinya ce mafaɗaciyar gaske gata da rashin kunya se tsabar tsoron duka se nace tunda mama take bata taɓa ganin abunda ya baiwa Bebi tsoroba haka zalika bata da saurin kuka duk abinda Zebawa Bebi kuka abun babbane amman ko dukane sedai ka gaji amman bazatai kuka ba sedai fa da zarar taga abin dukan zata gudu.
Gata da mugun kwaɗayin nama haka zalika ko ciwo take bata kasa cin abinci sabida Allah ya zuba mata baiwar son kai loma abaki wataran idan mama batai girkiba haka zata sakata agaba tai ta mita, itafa Bebi ko ƙofar gidane ya bugeta setaje ta rama haka xalika ko arfa ƴar autar mama ce ta bugeta bata saniba seta rama bata da haƙuri ko kaɗan.
To gwarama Æ´an biyu takan É—an raga musu amman ba can ba shahid kuwa yazama kamar sa'anta dan wataran har dambe ake sedai kuma idan suna Æ´ar daÉ—i dashi watakan wajan dahuwar idomin dayake kawowa ta dafa masa anan xakaga bebi tana yaya shahid sabida ze bata lasar tukunya.
Batada aminiya kamar sadiya, Bebi yarinyace mai garin jiki dan idan ka dubeta sekace gaba take dasu hussaina sabida tun tana ƙarama can kirjinta ya soma cika dalilin haka yasa kullum mama cikin zulumin fitar Bebi take sabida ɓata garin samari, shiyasa ta dafe mata da saka hijabi koda yaushe.
Sedai kuma inda Allah ma ya duba mama sam hankalin Bebi bayaga kula saurayi ko an biyota xagi ke rabata da mazan kota saka gudu! itafa haushi maza ke bata sam idan taji su sadiya suna zancen samari setai ta ƙunci wannan dalilin ne yasa suke faɗa da salisa sabida tana haɗata da habu mai itace wai saurayinta wannan kalmar har ƙwalla take saka Bebi dan tsabar takaici.
Haka zalika suma su hassana mama bata barinsu zance sabida acewarta komai dama ne bata son yaran nata su buÉ—e idanu da soyayya sabida gudun matsalolin rayuwa tafison koda ma auren ne Allah ya kawo musu kwatsam batare dajan lokaci ba.
Su siba a wajan saida awara suka san su Bebi sabida wani zubin suna kai musu wajansu su siya to sabida tsaftar su yasa daga sun fita da ita ake siyeta wani zubin ma har gida ake zuwa
To ashe shi siba akwai wata aƙasa domin tunda ya ƙyalla yaga Bebi yaji yana sha'awarta wannan dalilin yasa yaci awararta ya hanata kuɗin toya zata irinsa ce ashe rabon a ɗauko masa officer ne, wannan dalilin yasa kukaji yadda Bebi suka ƙarke da siba agaban officer tun a shafinmu na farko.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.