Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 11 of 81
*BONONZA BONONZA ZAFAFAN LITTATTAFAI 5 AKAN FARASHIN 1000 COMPLT DOCUMENT*
*ÆŠAN MAJALISSA*
*RABON WANI*
*KOBA SO.......*
*H A S K E*
*DA IZZATA*
_Idan kin shirya biya hanzarta nemana anan 08142105218_
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }
NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
*Assalamu Alaikum ina yiwa ɗaukacin ƴan uwana musulmi barka da shigowa cikin sabuwar shekarar addinin musulunci ya rabbi ka sadamu da alkairin cikinta kasa mun shiga acikin alkairi da sa,a amin, ya rabbi ka yafe mana laifukanmu kai mana tsari daga dukkan sharri amin barka dai ƴan uwana musulmi 1443AH*🥰
*13*
Ya shiga ɓalle botiran gaban rigarsa dagashi se singlet da wandon shaddar dake jikinsa ya shiga bathroom ya haɗa ruwan wanka sannan ya fito waje arayuwarsa shi mutum ne mai kunyar wani ya ga jikinsa wannan dalilin yasa da wuya kaga Haidara zaune da singlet ko 3qrt sedai tsananin zafin gari ke sakashi hakan kasancewarsa mutum mai yawan gargasar jiki shiyasa yake ma'abocin jin zafi,janyo bathrube ɗin dake hangar cikin bathroom ɗin yayi tare da suturta jikinsa da ita sannan ya jefa kayan daya cire cikin washing machine, ɗin dake bathroom ɗin, Ya jima acikin bathroom ɗin wanda ga dukkan alamu shiɗin yana ɗaya daga cikin maza masu daɗewar wanka, kafin kuma naga ya fito jikinsa rufe cikin rigar wanka tare da ƙaramin tawul akansa gaban wannan madubi ya tsaya tare da goga mai agurguje turare ya fesa cikin mintuna kaɗan ya shirya kansa cikin jallabiya ruwan toka mai yankakken hannu, bayan ya kammala shirinsa ya jefa rigar wankan a acikin injin wankin dake banɗakin tare da fitowa ya nufi falonsa yana faman zuba uban ƙamshi mai sanyi da daɗin ji, gaban Tv yaje ya kunna tare da kamo tashar saudi karatun shaik Abubakar sudais ne ya karaɗe falon, yana tafe yana bi har zuwa jikin wannan ƴar ƙofar dake tsakiyar ɗakunan barcin nan nashi.buɗewa yayi ya shiga babban furjine ƙato a ɗakin se coffee machine dake gefe se jerin cup's dake lulluɓe da farin hanky se sink na wanke-wanke, gaban wannan farin hanky ɗin yaje ya fito ya ɗauki glass cup guda tare da wankeshi acikin sink ɗin sannan ya nufi coffee machine ɗin ya murɗo coffe cikin cup ɗin tare da saka spoon medium bayan ya ɗaurayeshi kana ya fito yana juya coffee ɗin har zuwa cikin falon nashi, xama yayi akan ɗaya daga cikin sitocin falon yana kurɓar coffee ɗinsa yana bin suratul baqra dake tashi ta cikin speaker's ɗin Tv'n.
Yakai kusan mintuna goma a falon kafin aja ƙofar a shigo ciki, sallamar mace ce ta bayyana cikin garɗi da gwalli tare da iyayi, sanin daraja da muhimmancin sallama yasa ya amsa a ƙasan laɓɓansa batare daya ɗago idanunsa dake bisa tv'n sa ba.
"Yaya barka da wuni yaya ka taso daga office" wata ƴar farar budurwa marar jiki ta faɗa tana mai tsugunnawa agabansa tare da tsira masa ƙananun idanunta tana kallonsa kamar zata lasheshi sabida yadda take kallonsa.
"Lafiya Alhamdulillahi, khadija nagode".
YafaÉ—a batare daya dubeta ba.
Sunfi ƙarfin muntuna goma ahaka har ƙafar khadija ta sage amman miskilin bai kuma dubanta ba.
Gajiya tayi da tsugunnen ta miƙe ta masa sallama ta fita tanajin kamar ta kurma ihu! daman tasan kozasu shekara ahaka baze tanka mata ba tarasa wannan musibar son datake wa Aliyu amman shikam kullum hango baƙar ƙiyayyarta take acikin idanunsa.
Share hawayenta tayi tare da sauka ƙasa ta shige ɗakinsu tanajin komai ya fita akanta ita dai shiɗin take muradi har xuciyarta.
Ɗan tsaki yaja kaɗan tare da furta "Yara tunkafin ku tafasa zaku ƙone mtssss se son auren tsiya wanda idan aka musunma basu san yadda zasuyi da mijinba".yafaɗa a fili tare da faɗawa tunani na daban.
Shi haryau baiga muradin ransa ba, ma'ana wadda tai dai-dai da tsarinsa shi baya son auren yarinya ƙarama sabida gani yake bazata iya da buƙatarsa ba, yafi son babbar mace wadda tasan metakeyi wadda zata kula dashi wadda zata kular mashi da yaransa domin shi burinsa yaga ya tara zuri'a mai yawa da albarka, khadija babu laifi tana da shekaru domin takai kusan 27 da haihuwa dan yanzun haka tana shekarar ƙarshe a BUK amman yanayin tsarin jikinta da yadda take yasa shi sam batai masa ba ace mace kamar tsinke kullum se tsabar iyayi da jida kai amman kamar ka hureta ta faɗi shikam sam khadija baya mata kallonso sedai kallon ƙanwa kuma shi har yanzu baitaɓa jin wani alamun feeling akan soyayyar wata budurwar mace ba, kodan batasu ɗin yake ba oho?
Katse tunanin daya faɗa yayi tare da miƙewa bedroom ɗinshi ya shiga xama yayi akan bedset drowwer ɗin dake gefen gadonshi tare da ɗaukar wayarshi guda, number dr jalal ya shiga nema ta jima tana ringing kafin ya ɗaga,dr jalal abokinshine school guda sukai sedai bam bancin course haka zalika kuma cousins bro ɗinshine kuma surukinshi domin yana auren ƙanwar Aliyu mai binshi Nusaiba yanzun haka suna Abuja da zama sabida aikin daya kaishi can ɗin, ɗaga wayar dr jalal yayi tare da fara yiwa haidar tsiya"A,a tuzurun amminmu barka da warhaka".haɗe ranshi yayi tamau "Kai banson shirme nifa surukin kane yakamata ka dinga darajani, hope ya yarana suna lafiya?" yafaɗa cikin barkwanci, atakaice dai sun gaisa cikin barkwanci kasancewarsu abokan wasa, sannan Aliyu yaɗan nisa"Dr babu wasu tablet ɗin da suka fi waɗancan ƙarfi wallahi jiya da ƙyar nayi barci yanxun haka still ƙasan marata ciwo yakemin sosai ataƙaice yau ko break wallahi banyi ba kawai ina daurewa ne".yafaɗa yana lalubar leɓansa na ƙasa yana tsotsa tamkar sweet.
Dariya dr jalal ya saki kaɗan"Haba bro kaida naji ance an maku baiko da dija kawai kacewa su abba su ƙara yo maku zooming ɗin aurenku sabida kaifa sparm yay maka yawa".yafaɗa yana dariya,haɗe rai Aliyu yay"Malam kaga in bazaka gayamin ba wallahi zan katse wayana banson shirme yadda kuka ƙaƙabamin ita haka zaku gaji ku rabamu".yafaɗa cikin tsantsar takaici.
"Gaskiya Aliyu wannan karon bansan wanda xan kuma tura maka ka siyaba tunda wanda na baka yafi kowanne ƙarfi amman ina baka shawara kawai kai aure shine kaɗai solution ɗinmu,kokuma a wannan karon wallahi i will tell to su abba su san komai kawai tun kafin ka kai kanka lahira".
Furzar da zazzafan huci yayi tare da rintse idanunsa yana kuma tsotsar laɓɓansa shikansa wannan lamarin ya ishesa, kullum daren duniya da ƙyar yake barci sauƙinta ma ɗaya azumin dayake yawaita yi shine kaɗai yakejin ɗan samun nutsuwa amman yana adduar Allah ya rabashi da faɗawa halakar kusantar zina domin muninta.
"Hellow bro kana jina kuwa?" cewar Abdul-jalal ta cikin wayar"Eh inajinka bara kawai zan cigaba da shan wannan ɗin kafin muga abinda Allah zeyi Tnx".yafaɗa tare da katse wayar zubeta yay bisa gadon tare da sauka ƙasa wajan Amminsa..............
**********
"Bebi ke Bebi tashi kada kiyi lattin sallar asubahi".cewar mama wadda tafi mintuna biyar tana tashin Bebi a bacci amman Bebi ko gezau.............
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.