Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 16 of 81
"Bakace min komai ba Aliyu?"! Alhajin ya faÉ—a yana kallonshi"Alhaji babu abinda zance Allah ya kaimu".yafaÉ—a tare da mikewa yana sosa keyarshi kana yaja ya bar sitroom É—in bai kuma bi takan alhajin ba.
Murmushi Alhaji yayi tare da mayar da kanshi ya kwantar yana jan carbinshi.
Shikuwa kai tsaye ɗakinshi ya koma ya watsa ruwa again tare da kwanciya saman gado yana naxarin abinda ke gabanshi har wajan 12 bai rintsaba alwala ya mike yaje yayi kana ya tada sallah har wajan 3 sannan ya sami bacci, kiran sallar farko ya tashi ya bada raka'atul fijir kana ya sauka zuwa masallaci har wajan 6 yana can daga nan wajan dayake motsa jiki ya nufa wajan 7 ya gama komai ya sauko sanye cikin yadin kufta yana zuba kamshi ammi ya gaisar rannan a hade tare da mikewa ze fita"Bazakai break ba?" ciki ciki ya bata amsa daya makara sabida yana son yay landing komai sabida tafiyar dazeyi, "OK Ga Khadija nan zaka ajeta a skull tana shirin fitowa yanzu".harya mike ya koma ya zauna tare da dafe kanshi mintuna uku ta fito jikinta sanye da after dress ammi taiwa sallama kana ta gaisar dashi, bai amsa mata ba"Ammi na wuce office" "Nace zata bika ka sauketa a skull".girgiza kanshi yayi"Ammi nai latti sedai ta nemi driver".yana gama faɗin haka ya dauki car key ɗinshi ya kama hanya ze futa,"Yaya pls ko a jection ka saukeni zan sami napep" tafaɗa tana mikewa da jakarta a hannu ta bishi, adai dai corridow ya tsaya yana aika mata da mugun kallo"Ni sa'anki ne dan ubanki ɓacemin anan" yabuga mata tsawa kana yabar wajan yana huci wata motar ya shiga sabida tasa tana wajan gyara koda yaje aikin rannan nashi a hade yake wajan 4 ya tashi zuwa yay wajan bokking na jirgi kana ya koma gida ya soma shiri, wajan magrib yay wa su ammi sallama ya wuce airport jirgin dare yabi zuwa garin na legos wanda yabarwa usman ragamar komai na kamfaninsu na kano.
Washe gari bakwai Bebi tai makaranta, wanda hakan ya baiwa kowa mamaki agidan haka rayuwar bebi tai ta tafiya cikin wannan satin bata wani magana seta skull sabidama kada mama ta sakata a lissafin tafiya tallan kamfani, yau takama asabar tun wuri mama ta kammala komai ta haɗa musu abin bukata cikin tsafta ƴan biyu suka shirya kansu haka shahid ya samo musu mota har ƙofar gida ta ɗauki kayan nasu zuwa bakin tafkeken kamfanin na mai atamfa dake sharaɗa, da taimakon baban nazir suka shigar da komai cikin kamfanin daga gefen masallaci dakwai wata ƴar rumfa mai dauke da bencina da tebur a saman teburin ya aje musu kayan abincin nasu wanda tsananin mamakin girman kamfanin da yadda yake a tsare ya daskarar dasu hassana, zamansu da kamar mintuna uku ciniki yace salamu alaikum domin tuni har an cinye damubun har ana neman kari.
Kayansu suka haÉ—a wajan karfe 3 sukayo gida cike da tarin nasara.
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }
NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
*18*
Abakin layi mai baburin adai daita sahu ya sauke su, saukar da manyan kulolin dasuka fita dasu sukai zuwa waje kana suka biyashi kuɗinsa, sannan suka dauki kulolin suka shiga layin gidansu, a soro suka aje suna mayar da numfashi sannan suka kuma ɗauka sukai sallama acikin gidan, "A,a har kun dawo?" cewar mama bayan ta amsa musu sallamar, tare da matsowa ta kamawa hassana babbar kular dake hannunta wadda aka zuba dambu acikinta, jinta sakayau yasa mama mamaki, seda suka kai kulolin gaban rariya sannan mama ta kawo masu tabarma ta shinfiɗa musu, kana ta kawo musu ruwa a moɗa tare da abincin ranarsu data aje musu, Hassanace ta mika wa mama kuɗin dake hannunta waɗanda zasukai kimanin naira dubu huɗu,"Mama wallahi akwai sa,a acikin wannan sana,a duba fa gaba ɗaya mun siyar da dambun alalan ma haka kumafa har ƙari suketa nema".murmushine a saman fuskar mama tana karbar kudin tana lissafasa su,"Masha Allah ai inaga gobe semu ƙara kaɗan koya kukaga?" ta tambayesu cikin kulawa, abincin data kawo masu sukeci sannan hussaina ta dubeta"Eh amman fa amfi son dambun kada ki daɗa alalan barshi a na rabin kwanon kawai", tafaɗa tana kai loma bakinta"to shikenan babu komai Allah ya kaimu bari shahid ya dawo seya koma janguzan ya siyo mana abinda babu nacikin kayan haɗin dambun".tafaɗa tana mikewa ta shiga ɗaki.Abincin suka cigaba daci har suka kammala sukai sallah sannan suka nufi ɗaki ƴar hutun tana kwance saman katifa tana sharar bacci ranta fess, da kallo suka bita kowacce ta kama sabgar gabanta.
Se yamma ta tashi tana raba ido sabida rashin sallar la'asar ɗin da batayiba cikin azama ta mike tana musu barka da zuwa sannan tayi tsakar gida tayo alwala, sallah tayi sannan tahau tambayarsu harsun dawo da wuri haka, ganin basuda wani aiki yasa suka zauna suna bawa Bebi labari."Hmm Bebi bakiga yadda kamfanin yayi kyau ba, wajan aje motoci daban wajan aje babura daban , gefen masallaci muka zauna awajan wani tebur bakiga yadda ake ciniki ba, sabida mukaɗai ne masu abinci awajan, amman inaga zamu sayi pure water muna saidawa dan naga babu mai kawowa" cewar hussaina kenan"A,a da akwai kanti fa daga bayanmu kuma nasan ƙila yana saida ruwan".cewar hassana tana dariya,sosai suke hira awajan har wajan magariba sannan shahid ya dawo wanda daman daga dawowarsa daga skull mama ta aikasa janguza, shinkafa dasu zogale da mai ya siyo masu, a tsakar gida ya dire wanda su mama suka fito suna masa sannu, da zuwa harda Bebi ake aikin zage zogalan shinkafar mama ta haɗawa ihsan ta bata ta kai mata ɓarza, sukuma suka cigaba da haɗa kayayyakin dambu da alalan gobe, har zuwa magariba sannan, suka ɗora abincin dare kana kowa ya tafi yay sallah yaudai bebi akwai abin arziki sabida ta xage ta tayasu aiki sedai ko aranta batajin zata je wannan waje sabida bataji ranta ya kwanta dashi ba.
Har dare suna Æ´an aikace aikacensu, abinci sukaci suka wuce makarantar dare bayan sun dawo suka kwanta bacci dabida shirin fitar gobe.
Tunda ya sauka A legos yake gudanar da ayyukanshi cikin nutsuwa sabida ya riga ya saba da nan ya kuma san jama'a sosai, agidan abba nacan wanda suke zama ya sauka, da safe ze fita office da yamma ya tashi, ya umar daman tunda Aliyu ya je shikuma ya dawo gida, waya kawai yake da ammi wadda kullum zancenta akan lefe yake wanda tuni tabayar da order kayan lefen nashi sabida bikin harda na Amina za,a haÉ—a.
Yau takama sunday wanda ya rage kwanaki biyu ya dawo kano zaune yake a saman sopa system É—inshi aje bisa cinyarshi, jikinshi sanye da jallabiya milik aikine gabanshi sabida yana turawa wani kamfani achaina wasu samfur waÉ—anda sukeson a shigo masu dashi, wayarshi dake yashe a gefece take faman ringing! wajan sau biyu yana dubawa baya É—auka ana ukunne ya É—aga"Assalamu Alaikum" yafaÉ—a batare daya duba sunaba, jin muryar lina yasaka shi dawo da wayar ya katse tare da wullata saman gado ya jima yana aiki akan system É—in tashi kafin ya gama ya É—auro alwala ya fita.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.