Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 20 of 81
_Awanke hannu a tadani glass_
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }
NA
*AUTAR MANYA*
SADAUKARWA GA
*Kausar Salis Usman aglannissa*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
*25&26*
"Wayyo! zan mutu marata ciwo takemin mutuwa zanyi wayyo Allah nahhhhh", taja maganar da ƙarfi tana dafe marar tata zubewa tayi a wajan numfashinta yana fita kaɗan-kaɗan, cikin firgici ƴan biyu suka ɗagota da ƙyar sabida yadda take da girman jiki, saman tabarma suka kwantar da ita ihsan ce ta wanke bakin rariyar, Sosai suka firgita ga yadda take cije bakinta, Cikin nutsuwa mama ta taso daga gaban murhun kicin duk jikinta yayi wani irin mugun sanyi ƙalau.
Gaban ta tazo ta xauna tana kallon yadda ƴan uwan suka zagayeta"Hussaina miƙomin ruwa a kofi", cikin azama hussainar taje ta ɗebo mata ruwan ta kawo mata, karɓa tayi ta fara tofa mata addu,a acikinsa sannan ta tallafe kanta ta bata a bakinta wani ya shiga wani kuwa bai shiga ba ragowar ta ɗaga rigar uniform ɗin jikinta ta shafa mata,Janyo numfashi tayi kaɗan. tare da juya kanta gefe tana ɗigar da hawaye daga cikin idanunta, "Sannu Bebi, Sannu Bebi".haka ƴan uwan nata keta faman faɗi gaba ɗayansu idan ka cire shahid wanda bai san miyake faruwa ba yana can wajan gawayinshi.
"Kunga kutashi kuje ɗaki ta samu tasha iska kunga nan ɗin baya da wadata sosai".cewar mama wadda takeson taɗan buɗewa Bebi jikinta tasha iska sabida gumin dake zubo mata, Babu musu suka miƙe dukkan su tare da shiga cikin ɗaki jikinsu sanyi ƙalau.
Tube mata hijabin jikinta mama tayi, tare da ajeshi gefe guda sabida daman tunda ta dawo daga makaranta, taje ta kwanta bata tube kayan makarantar ba.
Share mata gumin dake yanko mata ta goshin nata tayi tare da ƙara karanto addu'oi ta tofa mata a saman goshin nata.
Buɗe idanunta tayi tare da mirginawa saman cinyar mama tana cije laɓɓanta kaɗan kaɗan, buɗe matsakaitan idanuwanta tayi waɗanda suka rine sukai wani irin jajur daga gani kasan tana shan wahala.
Ahankali ta furta,"Mama marata kamar zata cire wallahi" a yadda tai furucin maganarma kaÉ—ai ze baka tabbacin tana jin jikinta sabida sam Bebi bata magana a hankali sedai kaji maganar tata tamkar daga nesa amman yau tayi magana cikin nutsuwa.
"Garin yaya hakan Bebi ko zaki soma al'ada ne, shiyasa ya zo miki da haka?" mama ta faÉ—a tana saka hannunta tana gogewa Bebi zubar saman goshinta.
Wata iriyar damƙa takaiwa mama tana furta salati cikin wani irin yanayi kuma jikin nata yay lakwas, kamar mai bacci.
"Mama wani abu yana bimin jikina yana fitomin daga cikin pant ɗina",tafaɗa tana mikewa zaune, duk fuskarta ta jike da hawaye, take mama ta gane baƙon watane ya zowa Bebi, wanda take tunanin ita nata mai azabar ciwon mara ne.
Cikin azama mama ta taimaka mata takai mata ruwan zafi banɗaki bayan ta surka mata shi, ɗaki ta shiga ta ɗauko mata zani da Vest, sannan ta ɗauki naira ashirin ta bawa ihsan akan taje ta siyo mata maganin ciwon mara a chamist, ƙaton fallen zani mai kyau mama ta ɗauko ta fito dashi tsakar gida lokacin Bebi harta tube kayanta ta shiga wanka, hannunta dauke da wandunanta waɗanda suka.ɓaci da jini, itama ƙyamar jinin ne ya kamata gefe ɗaya kuwa tsorone fall ranta ganin yadda wai wannan jinin daga jikinta yake fitowa, aikuwa kafin tagama wankan ta zubar da hawaye yafi kwando sabida tsoratar dake shake a zuciyarta.
Muryar mama taji daga bakin kofar bayin, tsumman data yanka da pant take miko mata ta ɗan bular jikin kofar bandakin,"Maza kiyi ki gama wanka ga shinan na ninka miki seki saka tadai gaya mata yadda zatai a takaice sannan ta dawo ta zauna, itako Bebi acikin bandaki kukan ta cigaba dayi da ƙyar ta iya saka tsumman a jikinta tanajin duk ya cika mata hq, haka ta rufa zani ajikinta sannan ta ɗauraye wandunan dasuka ɓaci kana ta fito waje tana harɗe ƙafafunta kamar ƴar........, Seda ta zo gaban mama sannan ta ɗauki Vest ɗin ta saka batare data saka bra ba sabida daman ita ba damunta tai ba, sallamar ihsance ta katsewa mama hanzari amsa mata tayi sannan ta karbi sakon maganin, hassana ta kira daga ɗaki tazo tace ta zubowa Bebi ɗan ruwan shayin da ake ajewa arfa ƴar autar mama sabida tana sonshi sosai, zubowa tayi acikin kofi tare da cokali, ta mikawa Bebi sannan ta kuma mata sannu ta koma ɗaki, bayan ta amshi kofin ta kafa abakinta tana kurɓa tana hawaye, ƙura mata idanu mama tayi tana addu'a acikin ranta Allah ya kawowa Bebi miji ta aurar da ita sabida koga yanayin girman jikinta kaɗai ka gani seta baka tsoro kullum ka ganta kamar hurata ake seka ɗauka rainon madara ce duba ga yadda tsarin cikar halittarta yake bazaka taɓa ɗauka anan gidan takeba, kirjinta kamar na ƴar shekaru ashirin babu mai kallon Bebi kace mata shekarunta sha shida sabida yadda take kamar zata fashe, wannan girma na Bebi yana ɗagawa mama hankali, musamman idan ta duba taga yadda rayuwar nan ta koma wasu mazan basa tsoron Allah suna ganin yarinya kamar Bebi wadda babu laifi tana da kyan sura tofa idan mai kwaɗayi ce xasu ribaceta ne suyi lalata da ita, wannan yana ɗaya daga cikin abinda yasa take ɗan tsawaita tsaronta akan Bebi fiye da sauran sabida ita Bebi surarta a bayyane take komai zafa ta saka danta rufe jikinta sefa ta bada sharp,duk da ita bata isa ta hana Allah ikonshi akan ƴar tata ba amman tana iya kokarinta dantaga ta killaceta bama ita ba harma sauran ƴan uwan nata wallahi wannan tallan dan babu yanda zatayi ne amman da tuni ta yanke shi amman tana addu,a Allah ya kawo masu mafitar alkairi baki ɗaya.
Kukan! Bebi dake fitowa da sauti a wannan karon shiya dawo da mama daga duniyar tunanin data afka, cikin sauri mama ta furta"Ciwon marar ne ya dawo?". girgiza kanta take tana kuma zubar da hawaye kamar ba Bebi ba wadda kafin kaga kukanta se antona ko ciwo take bata kuka ammam wannan karon kukan! take sosai.
"Mama jinine fa ke zubomin ga wannan tsumman sukarmin jikina yake na shiga ukuna!!!" tafaÉ—a tana zubar da hawaye!.
Dubanta mama tayi da nutsuwa ganin yadda taÉ—an faÉ—a yau É—aya tabi ta É—agawa kanta hankali, wanda ba wai iya ciwon marar kaÉ—ai bane ya sakata yin hakan harda ma tsoro wanda ya bayyana a saman fuskarta.
"Kinga ki kwantar da hankalinki kinji ko ina anyi muku karatun jinin al'ada a makarantar islamiyya?, ko.wace mace tanayi bake ɗaya ba, sedai wadda Allah bai ƙaddara zatayi shiba yana xuwar mana ne a kowani wata wata tsakiyar wata, wata farko wata kuma karshe, watama batayi baki ɗaya wanda wannan kuma anfi danganta hakan da lalura..........., Sosai mama ta xauna tana nunawa Bebi yadda zatai tare da yadda zata gyara jikinta komai dai ta zauna ta nuna mata hartana mata misali ga su hassana wanda tsabar tashin hankali ya hana Bebi fahimta ada, sam tama manta anyi musu wannan darasin a makaranta seda nutsuwa tazo mata sannan ta kwantar da hankalinta amman dai har yanzu marar tana yi mata suka, dama kuma taga Sadiya tana ce mata wataran bata azumi dadai sauransu, sam bata ɗauka haka abin yake ba seda yazo kanta anan karatun malam hadi na islamiyya ya dawo mata kanta, wanda ya bayyana musu hukunce-hukuncen jinin haila, dai dai sauransu.
Sosai mama ta zauna ta kuma yi mata nasiha mai ratsa jiki hartana tsoratar da ita akan nisantar wani namiji sabida gudun shigar ciki, daman kuma tasan Bebi inda Allah ya tai maketa ko Æ´an yaran da suke cewa suna sonta bata kulasu bare kuma ta tsaya da wani amma me yanzu baka shaidar mutum, Gwara dai ta kuma tsoratar da itan kamar yadda take haÉ—asu tai musu hakan tun kafin wannan lokacin yazo, sannan kuma ta kara yi mata nasiha da kula da sallah sannan ta nuna mata dukkan abubuwan da suka halarta akanta sosai ta nuna mata jin tsoron Allah fiye da komai a rayuwa sabida littafinta yanxu a bude yake dukkan abinda tai xa,a shigar dashine.
Jikin Bebi ne yay luɓus wata irin nutsuwa tazo mata haka sukaita hirar fahimta da mama har lokaci yaja sannan tace mata ta koma wajan ƴan uwanta ita kuma tayi kicin wajan aikin gabanta.
Koda ta shiga É—aki kwanciyarta tayi a saman katifa tana tsuke jikinta waje É—aya tana jin yadda mararta take É—an lafa mata a hankali hankali sabida karfin maganin datasha kafin kuma bacci ya kamata wanda aikin wannan maganin data sha É—inne.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.