Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 61 of 81
Ƙafafunta ta ɗora akan wani lallausan carpet wanda ke maka wellcome a bakin bedroom ɗin ammi wanda ya sami damar isa har cikin bedroom ɗin tsananin laushinsa yasa Bebi shagala batare datayi yunƙurin ɗaga ƙafafunta ba.
Har ammi ta ƙarasa cikin room ɗin kafin Bebi tayi ta maza ta kuma saka ɗayan ƙafar ta cigaba da tafiya cike da tsananin mamaki wato su masu kuɗi komai nasu yana da matuƙar bam-banci danamu.
Acikin katafaren bedroom ɗin ammi Bebi ta yada zango wanda ko iya nan ammi ta karrama Bebi kuma tabbas ita kanta ta yarda da gaske Aliyu ɗan gatane na gasken gaske a wajan mahaifiyar tasa duba da yadda ammin take nan-nan da ita tare da tattali da lallashinta kamar ƙwai daga ƙarshema take kiranta da *Autar ta* a tsakiyar room ɗin ta dakata tana kare masa kallo babban ɗakine sosai wanda ya sami damar lamushe ƙaton royal bed mai uban girma tare da babbar wadrov duka masu kalar golden se ƙaton dressing mirrow tare da wata kujera doguwa daga gefe se sallaya tare da hijabi na sallah a nannaɗe daga can ƙuryar ɗakin se wata golden ɗin kofa wadda take a rufe daga hannun hagu.
A saman wannan sopa É—in ammi ta zauna sannan ta kalli Bebi a tsanake.
"Buɗe wannan ƙofar ki shiga zakiga tawul a saman ƙofar ciki kar ki shiga ta farkon ki shiga ta biyu akwai ruwan wanka na haɗa miki sekiyi wanka in kingama ga kayanan a gefen gado ki saka".
Ta faɗa mata cikin bada umarni kana ta mike ta nufi wata ƙofar daban ba wadda suka shigoba wadda se lokacin Bebi ta lura da ashe kofofin ukune a cikin ɗakin kenan ba iya wannan bane kaɗai akwai wasu aciki lallai inta nutsu seta leƙa tagani.
Gaban madubin ta nufa tafara tube kayanta tana kallon kanta amadubin tana É—an xaro idanu kaÉ—an kamar wata yarinya.
Tana gama tube kayan ta ɗauki hijabinta ta ɗaura a ƙugunta tare da ɗaure kanta da ɗan kwali kana ta nufi cikin kofar ta murɗa ta shige abinta.
Yadda ammin tace da ita hakan ta aiwatar wani farin tawul ta ɗaura wanda daga ganima sabone kuma babu laifi ya rufe mata cinyoyinta, tana shiga cikin bathroom ɗin ta tarar an haɗa mata ruwa a tap na wanka wanda tunda ta shiga taji mugun ƙamshin turaren wanka ya cika mata hancinta.
Cire tawul ɗin tayi tare da farayin wankan cikin tsananin jin daɗin ruwan duba da yadda yake bin fatarta yana wani irin sulɓi yana gudu, ga kuma sabulun wanka na ruwa wanda taita makashi a sumar kanta tana wankewa domin ita ta ɗauka shampo ne na wanke kai daman ƴar kalabace hassana tai mata wadda tuni ta tuje amman dayake Bebi batada wani gashin kirki yasa bata dameta ba.
Bebi wadda ko a gida bata haura mintuna biyar a bayi amman yau bebi kusan awarta guda tana cuÉ—e jikinta abinka da farar fata tuni fatar ta kuma haske takuma yin kyau gwanin sha'awa domin har É—aukar idanu takeyi.
Tashi tayi tsaye bayan ta gama wankan É—an kallon kirjinta tayi sosai suka bata tsoro sabida yadda sukai wani irin cukowa kamar da gayya sunyi wani irin kyau,Tura bakinta tayi gaba kamar agaban wani tare da É—aura tawul É—in kana tace.
"Ni wannan nonon kafa ishen kullum kaita cukowa kamar wata uwar garke".
TafaÉ—i hakan tana goge kanta da hijabin data cire kana ta fito waje É—auke da Æ´an kayanta a hannu.
Abakin ƙofar ta dakata seda ta ɗaura ɗankwalin a saman jikinta ta kare kanta yadda ba mai ganin kirjinta sannan ta fita zuwa cikin ɗakin.
Kamar kwa tana da masaniya domin da ammi taci karo a zaune gabanta wani irin kaskone wanda aka haÉ—a masa gaushi yana ta faman ci se wata jarka dake gefenta.
"Yauwa autata kin kammala wankan to maza zona haɗaki kafin ya ƙaraso zoki tsugunna akan kaskon nan amman kafin nan zona fara baki zuma kisha wallahi ta nusaiba ce ma ta manceta Allah yayi rabonki ce zuma ce mai kyau sabida tana gyara kuma akwai sinadaren maganin sanyi acikinta".
Ita dai bebi bata fahimci abinda ammi take nufi ba sabida ƙarancin shekaru wadda ita kuma ammi ta faɗa mata hakanne domin yanzu ta shiga sahun manya bayan haka kuma ta ƙara gogewa wajan gyara jikinta.
Gaban ammi ta ƙarasa bayan ta aje hijabinta a gefen kayanta data cire lokacin dazata shiga wanka ɗazu.
Cikin sauri ammi ta saka hannu ta ɗauko pillow daga saman sopa ta aje mata a ƙasan ta zauna sannan ta miƙa mata jarkar.
"Amsa maza shanye".
Karɓa tayi tana bisimillah! tare da kaiwa cikin bakinta.
Jin wani irin ɗan bauri da garɗi da dabino da kwakwa da tarkacen kayayyakin zaƙi yasa Bebi iyayen ƙwaɗayi aka gyara zama har tana lumshe idanunta seda ta shanye tas duk yawan zumar kana ta mikawa ammi jarkar.
"Yawwa autata nagode to zo matso da jikinki kinajina ko ki ware ƙafafunki sosai yadda hayaƙin ze shiga jikinki maza amshi ki zuba ina zuwa".
Ta miƙa mata wani ɗan ƙullin turare ɗan mitsil, tare da turo mata gaushin gabanta wanda tuni cinyar Bebi ta ɗauki zafin azaba.
Amman tsabar ganin girman ammi wadda ta cika idanunta yasa ta ware kafar sosai sabida lokacin ammi ta miƙe tabar wajan.
Sosai ta buɗe cinyoyin ta saka kaskon a tsakiyarsu sannan ta kunce turaren dake cikin wani irin leda mai ƙyalli ta zuba ciki aikwa nan da nan ƙamshi na azaba ya cika hancinta.
Daɗa turawa tayi cikin cinyar tata hayaƙin na shiga jikinta har wani zufa ya haɗa sabida azaba, amman haka Bebi ke ƙara ƙaƙaba turaren wanda har fatar cinyarta ta soma ɗaukar zafi alamun zata ƙone( kai bebi wauta zata saka Ali jinya)
Cikin sauri Aliyu ya haura samansa bayan ya shiga part É—inshi lokacin wajan karfe takwass na safiya, falon sama babu kowa alamun matar gidan bata rigada ta tashi daga bacci ba, Bedroom É—inshi ya buÉ—e ya shiga domin yay wanka...............
#Autar Manya.
*Afuwan* !
*Afuwan* !!
*Afuwan* !!!
*Wallahi bani da caji awayata nima banso na tsaya anan ba amman Allah ya kaimu next*
11/14/21, 3:13 PM - Allah Akbar: *82*
*wannan na gobe ne insha Allah sabida gobe bazan samu damar yi muku typing ba sabida haka ga shinan a taɓa babu yawa nagode*
Tuɓe kayanshi yayi cikin sauri ya ɗaura white towel a west ɗinshi ya faɗa cikin bathroom ɗinshi cikin mintuna ƙalilan ya haɗa ruwan zafi acikin tap wanda ya wadatu da kayan ƙamshi na wanka, yajima yana cuɗe jikinshi kafin ya kammala wankan ya naɗo kanshi cikin towel ya fito zuwa cikin room ɗinshi.
Seda ya goge jikinshi tsabb da ƙaramin towel sannan ya ƙarasa gaban dresing mirrow ya ɗauki lotion ya shafa sama-sama a saman fatarshi ya ɗauki turare mai daɗin ƙamshi ya fesa ajikinshi seda yayma kanshi ɓarin turare mai kwantar da hankali sannan ya taje gemunshi mai bawa mata tsoro.
Baya da yawan wannan ƙaƙale ƙaƙalen na maza daman shi tin fil azal bai daɗewa ashiri, dan haka cikin mintuna kaɗan ya gama kammala gyara kanshi kana ya koma gaban jerin kayanshi.
Wani black jeans ya ɗauka wanda yaɗan ɗameshi kamar trouxer ya haɗeshi da white shirt mai hannu iya gwiwar seda ya shirya cikinsu tare da ƙara gyara kanshi sosai kana ya kuma komawa gaban mirrow yayma kanshi ɓarin turare still, sannan ya kwashi wayoyinshi da car key yabar ɗakin tare da ƙamshin sa.
Wayyo zokuga Aliyu yadda yay wani irin kyau seya fito kamar ɗan saurayi mai kimanin shekaru 30 sabida kyan dayay sabida ƙananun kaya suna haska guy ɗin ba kaɗan ba saidai shi a tsarinshi yafi son manyan kaya.
Yana fitowa falo ya hangi giftawar madam dija tana kaiwa da komowa a tsakanin daining area da kuma kicin, taci gayunta cikin ƙananun kaya masi bin jiki su kwanta luff.
Ɗaga kanshi yay ya kalli agogon dake bangon ɗakin, ƙarfe tara da kusan rabi, zama yay saman one seater tare da ɗaukar remote yana sauya channel.
Har dija ta kammala setting daining sannan ta karaso wurinshi ta rissuna.
"Good morning my hony ".
Ɗan kallonta yay ta ƙasan idanunshi sannan yace.
"Morning dear"
kamar an mishi dole.
Wani sassanyan daÉ—i taji adukkan ilahirin sassan jikinta lumshe idanunta tayi kana ta waresu bisa kanshi sannan tace.
"Wow amman naji daÉ—in wannan suna cwt ga abincinka a daining kona kawosa nan?".
TafaÉ—i tana wani yin fari da idanunta tana juyasu kamar da gayya.
Lumshe mayun idanunshi yay batare dayace mata komaiba sedai ya fesar da wata irin sassanyar iska ta cikin bakinshi.
Hannunta wanda yaji jan lallin bikinsu ta zube bisa saman cinyarshi kafin ta sami nasarar É—ora É—ayan cikin nashi tana matsawa sannu a hankali tana wani irin lumshe idanu kamar maijin bacci.
Sosai yaji shakkar hakan aranshi yana mamakin ƙarfin halin yarinyar.
"Dija mi kikeso dani ne nifa bana break da sassafiya haka kamar wani gara dan Allah kibarni na huta".
YafaÉ—a yana zare hannunshi daga cikin nata.
Jada baya tayi kaɗan tana ƙwaɓe face ɗinta zata masa kuka!.
"Amman dai yaya kasan yadda nakeji dakai acikin zuciyata danme zakana katseni aduk sanda zan raɓeka why inda kace zan maka fyaɗe ai yanzu ina matsayin matarka ne kuma inada cikakkiyar lafiyar dazan buƙaci mijina".
Kalamanta su suka hargitsa masa lissafin dake kansa, tabbas baya son yazama daga cikin maza masu tauyewa iyalansu hakkinsu amman kuma shi gaskiya zafin dayaji rannan yake tsoro sabida shi Allah yayoshi cikin mutane masu gudun abinda ze taɓa lafiyarsu.
Amman ganin yadda taja baya tana kuka kamar wadda akama rasuwa yasa yaÉ—an sassautawa zuciyarsa ya saka hannunshi ya É—aukota kamar wata Æ´ar beby dayake khadija batada wani girman kirki ya É—orata a saman cinyarshi.
Tsira mata narkakkun idanunshi yayi masu tsananin dafin zafin so agareta yana kallonta yana noticing É—in mood É—inta.
"Dija ya kikeso nayi dake ya maganarmu ta jiya?".
YafaÉ—a yana É—ora gemunshi adai dai gefen wuyanta yana son yaÉ—an rage mata zafi koda kaÉ—an ne.
Ƙoƙarin magana takeyi amman jin tsinin gashin gemunshi yahanata tayi maganar sema wani irin nishi dataja tana ƙara kwanciya a cinyar tasa.
"Ina magana kinmin shuru".
YafaÉ—a mata yana shin shina mata cikin kurmin wuyanta da hancinsa baki É—aya ya gama kashe mata jiki tun a iya nan kaÉ—ai.
"Naiwa anty ruma magana tace ba damuwa zuwa next week in sha Allah".
Tafaɗa murya a shaƙe kamar zatai kuka sabida duniyar daɗin datakejin kanta cikinta.
"Okey kice next week zamu angwance"
Yafaɗa cikin son basar da abin domin koda wasa baya zaton a yadda take ɗinnan ze ƙara gigin kai jikinshi gareta gwara in Allah yasa ta samu gyara to komai ze koma dai dai ta yadda shi bai cutu ba itama kuma bata cutu ba.
Kwantar da kanta tayi cikin kirjinshi ita É—aya keta faman cusa kanta cikin kirjin nashi amman shikam kallonshi ma yake batare dayaji wani feeling akan abinda take masan ba.
Cikin son dakatar da ita a fitinar datake son kunnowa kanta yace mata.
"Goma tayi tashi ki kawon black tea kaÉ—ai".
Kamar karta mike haka takeji amman hakanma tagode cikin sauri ta mike ta nufi gaban daining inda shikuma yabi cilai cilai ɗin ƙafafunta da kallo yana ayyana sirantar ta kamar wadda batacin abinci acikinta.
Harta kawo masa yana nazarin tsarin ta wanda sam batada wani na jan hankali ajikinta inka cire iyayin tsiyan dake gareta.
Karɓa yay tare da furta.
"Thanks".
Kana ya É—ora agefen shi kan wani É—an madai daicin table sabida akwai zafi cikin tea É—in.
Ƙoƙarin sake hayewa saman cinyar tashi kum takeyi.
a nan kam haɗe rai yay tamau ta yadda batada space ɗin yin hakan kana ya mayar da kanshi ga tv, Itama anata ɓangaren ganin ya koma mata Aliyun shi sakk nada seta kama kanta ta zauna waje ɗaya tana kallon tv ɗin kamar yadda taga ya mayar da hankalinshi ga tv.
ÆŠaukar cup É—in yay tare da kaiwa bakinshi yanayin bisimillah.
Cikin tsanaki yake kurɓar shayin wanda yakejin daɗinsa domin ta ƙayatashi da kayan ƙamshi masu daɗi da ƙayatarwa kota nan yana jinjinawa dija domin koda girki kaɗai zata iya siye wanda take tare dashi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.