Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 78 of 81
*ZUMA A BAKI...!*🌹
{ Painful love Story }
_Shine sabon littafina da ze soma zuwa da zarar na kammale wannan kedai/kaidai maza ka hanzarta ka biya naka domin tun kafin na soma posting ɗinshi zan soma karɓar kuɗin masu son karantawa kai dagajin sunan kasan akwai rikita rikita wadda bazan ce komai ba amman rubutuna ze bayyana muku *Zuma A Baki* comming soon da izinin Allah ƙofa a buɗe take masu soma payment_
*ÆŠAN ÆŠANO*!
_Wannan karon tafiya nai mai mugun nisa har naje na zaƙulo muku ƙayataccen labarin masoya Biyu *Umar Muhammadu Sarkin-Gida* wanda jama'ar unguwa da abokai ke masa laƙani da ( *Cika Daji* ) Eh cika dajin ne mana sabida duk umar ba,a rago to hakance ta kasance ga shalelen inna kuma autanta wanda ya tsunduma a dafkin kogon soyayya da *Aishatul humaira* ɗiyar anty Har soyayyar tasu ta zamewa kowannen su *ZUMA A BAKI* Tabbas tunda nake rubutuna bantaɓa katari da labarin daya kwantamin ya tsayamin kamar ZUMA A BAKI ba! tabbas kodaga jin sunan kasan akwai rikita rikita kuda kawai kubiyoni nasan insha Allah bazan baku kunya ba_
*Hohoho! my fans nace muku painful wallahi da gaske wannan soyayyar mai zafice mai raÉ—aÉ—i ce duk wani masoyi yaci katari da wannan labarin nawa seya dara seya koka seya warwasa labarin ze Æ™ayatar ze tsaya arai ze nishaÉ—antar ze wa'azantar ze ilimantar kudai kubiyoni kawai*💃💃💃💃ðŸ¤ðŸ»
_kai ƙoƙarin ganin kayi payment domin zan soma sakin sane da zarar na kammale wagga_
~N~ *300*# *ta wannan account numbern 0078174806 starling bank show me your evidance of payment ta wagga numbern 08142105218 love you my Æ´an amana my Æ´an iya wuyata*
11/14/21, 3:21 PM - Allah Akbar: *99*
Rana ɗaya kuma ta mai kaya inji bahaushe, zama yayi a bakin katifa tare da saka hannunshi guda ɗaya ya dafe saman kanshi gaba ɗaya tashin hankali yagama mamaye zuciyarshi arayuwa baya son ɓacin ran mahaifinshi ko kaɗan tabbas yasan a wannan karon sesun sami gagarumar matsala da abban nashi, sharce zufar data karyo mashi yayi tare da furta.
"Innalillahi wa'inna'ilaihirrajun, ubangiji ka kawomin sassauci acin wannan cakuÉ—aÉ—É—an lamarin" yafaÉ—a tare da mikewa tsaye.
Ya soma shirya kanshi cikin wani brown boyel mai yankan manyan sukari tare da É—ora hula a saman kanshi takalmi ya saka mai kalar kayan jikin nashi, turare ya fesa mai daÉ—in kamshi tare da É—aukar wayarshi da makullin motarshi ya fita daga É—akin.
Bebi tana falo a zaune tana shan tea wanda ko sugar babu acikinshi sabida yadda bakinta yake babu É—anÉ—ano ko guda dan ko abincima a wannan lokacin se Ali yayi mata jan ido take turawa tana kuka! wanda baya minti É—aya kuma seya dawo tass.
Akanta ya tsaya tare da kallonta fuskarshi babu sukuni.
"Tashi ki É—auko hijabi zamu fita"
Da kallo ta bishi tana nazarinshi amman ganin yadda ya haɗe girar sama data ƙasa babu alamun wargi yasa tai maza ta janye tea ɗin daga gabanta tana yatsine fuskarta daman tunda taga suna tare an kirashi a waya ya tashi yabar falon ya koma ɗaki tasha jinin jikinta abinda yasa bata bishi ba dan karyace tana masa bin diddigine.
"Lafiya dai ko? naganka ba kamar É—azuba?"
TafaÉ—a cikin kwantar da murya kamar yadda umman mufida ke gaya mata aduk sanda zakaiwa mijinka magana yazama ka tausasa lafazinka tare da kwantar da muryarka.
Agogon dake É—aure bisa tsintsiyar hannunshi ya kalla.
"Kinga 1:00pm dan Allah kiyi sauri ina mota ina jiranki"
Ya fita da saurinshi.
Cikin mutuwar jiki ta mike zuwa bedroom wani coffee hijab ta ɗauka har ƙasa ta ɗora saman doguwar gown ɗin material ɗin dake jikinta tare da saka plate shoe ta fito cikin sauri tana tafiya kamar iska zata ɗebeta cikin tsanaki ta mika hannu ta bude marufin motar ta shiga wanda shi harya ma kunnata domin ita kaɗai kawai yake jira.
Revars yayi kana ya nufi wajan gate ya fita daga gidan.
Redion motar ya kunna batare daya mata magana ba, ta kula yau Æ´an shariyar nashine suka motsa masa kokuma akwai abinda ke damunshi acikin zuciyarshi.
Sosai yake falfala gudu a saman kwalta har ya sami zarafin barin arean unguwar ganin ya É—auki hanyar da gidansu yake yasa komai nata ya tsaya cak.
Har lokacin daya ƙarasa cikin unguwar tasu, abakin gate ya dakata tare da danna horn masu tsaron gate ɗin sukazo suka bude masa suna masa barka da zuwa.
A harabar wajan adana motoci ya parker motar ya kashe tare da balle murfin ya fita.
Haɓa ta riƙe tare da gyara zamanta batare datayi yunƙurin binshi ba, har ya kusan ɓacewa daga gurin ya juya yaga bata biyosa ba tsaki! yaja a fili tare da komowa kansa ya zira ta cikin glass ɗin motar.
"Kifito mana ya kike ɓata min lokacina"
Da sauri ya saka hannu ya buÉ—e murfin motar yana tsaye ta fito a wannan karon yaÉ—an sassauta saurin nasa suna jerawa tare sedai bai ce mata komaiba.
part É—in alhaji babba ya nufa dukkan ilahirin jikinshi yayi sanyi amman dayake shiÉ—in namijin duniyane babu ta yadda zakai ka gane halin dayake ciki sabida ko saman fuskarshima bata nuna hakanba.
Kofar babban falon alhajin ya bude wadda daman anan ake tattauna dukkan wani important issues na cikin zuri'ar tasu.
Zare idanunshi yay lokacin dayay katari da mutanan dake falon domin babu wanda bai sami zarafin halartar wannan wuriba hatta zee datake jego seda ta amsa kira, sedai su umar da basa gari.
Sallama yayi kanshi sunkuye ya kutsa cikin falon wanda ƙannenshi suka sada kansu ƙas sauran iyayenshi kuma suka zuba masa idanu.
Bebi na biye a bayansa wadda ilahirin jikinta yake rawa musamman yadda taga idanun kowa yayo kanta caaaa akai mata da ido ana kallonta.
Abba wanda tun É—azu ya kasa zama se faman kaiwa da komowa yake wayarshi ahannu cikin sauri ya juyo ga Aliyu dake kokarin gaisar da abban bauchi.
Tas! tas!! tas!!! falon ya É—auki sautin tagwayen maruka uku ciff da abba ya wankewa fuskar Aliyun dasu.
Cikin wani irin yanayi bebi ta silale a jikin bango ta raɓe tana rintse idanunta sabida yadda taji marin kamar ita akaiwa.
Itako khadija tun shigowar bebi takejin gabanta na wani irin bugawa sam bataji marin mijin nata ba gaba É—aya hankalinta da idanunta yana kan bebi tai mugun zuba mata idanu ko kiftawa batai.
Karuwarshi ko matarshi no karuwa dai domin tasan zuri'arsu basa AUREN BARE! rintse idanunta tai gam tana kiran sunayen Allah.
Kafin maganar alhaji babba ta karaÉ—e wurin.
"Kaimin dai-dai idiris daka mari shasha Aliyu muzaka zubarwa da ƙima muzaka tozarta muzaka kwancewa zani a kasuwa muzakaiwa abin kunya a cikin zuriya?"
YafaÉ—i hakan cikin cakuÉ—aÉ—É—iyar hausar data saka kowa cikin zulumi wanda tuni zuciyar wasu ta soma raya musu Aliyu karuwa ya aje agidansa.
"Dakata Alhaji"!
Ammi ta mike a matuƙar fusata wadda tunda abba ya aurota bata taɓa yin irin wannan maganar ga dukkan ahlin nashiba.
"Ta yaya kake jefarmin É—a da irin waÉ—annan munanan kalaman waÉ—anda suke kaman ceceniya da zaman dadiro...........,
"Bilkisu koma ki zauna kada in kuma jin maganarki in ba hakaba ranki ze mugun ɓaci"
Abba ya faÉ—a cikin zafin rai.
"Wallahi idris bazan komaba ta yaya kai kana gani za,a lalata auren ɗanka sabida wata banzar al'adar daba addiniba sannan kai shuru to wallahi senai magana koda zakace yau ƙarshen igiyoyin aurenmu dakai ya ƙare Aliyu auren sunna, yayi da sanin ƴan uwanshi abubakar da usman su'suka wakilci aurensa kuma abubakar shiya miƙa sadakin auren nasa sun ɓoye mukune sabida banzar ɗabi'arku ta rashin AUREN BARE! Wadda nake addu'a Allah ya rusa wannan al'adar kowa ya sami ƴancin kanshi".
"Dakata bilkisu!
Alhaji babba ya faÉ—a tare da mikewa.
Shiko abba ƙasa yay da kanshi yasan ran ammi ya ɓaci tunda tace abbakar kai tsaye tace idriss kai tsaye wanda bata taɓa faɗin sunanshi ba tunda ta haifeshi sabida alkunya ta ɗan fari hakanan bata taɓa faɗin sunan shi abban ba sabida alkunya itama abba take faɗa mai kamar yaranshi ammi macece mai kawaici da hakuri yadda yaji yau ta mike tana wassafa magana yasan ranta ne ya ɓaci.
"AUREN BARE Baya cikin tsarinmu dana iyayenmu sabida kina ganin kin isa kin kai kin kawo shine zaki dubi idanuna ki gayamin wadda duk ta fito abakinki ko? madallah to nagode amman ki sani wannan aure dashi da babu duk É—ayane a wajanmu sabida haka a yanzu base anjima ba kai tsageri marar mutunci inason ka saki waccan yarinyar ka bata takardarta ga matarka nan hadiza Æ´ar uwarka ta jini da ita muke son ka zauna ba BARE ba! domin bazamu lamun AUREN BARE a mai atamfa family ba"
Alhaji babba ya kare maganar yana mikawa Aliyu takarda da biro, Bebi kafe tsohon tayi da idanu tana kallonshi maganarshi ta ƙarshe tafi kalmar sakinta dayace zafi acikin zuciyarta.
Lallai namiji munafuki ne au ashe daman yana da mata yake wannan rawar jikin akanta jar bura'uba! lallai ya gama da ita ƙarewa ma matar tashi ƴar uwarsa ce lallai ya cuceta!!!
Falon ne yay tsit illah sautin kukan dija dake tashi sannu a hankali tanajin duniyar tana juya mata Aliyu yayi aure? da wadda take hango tsantsar sonta a gareshi wayyo taga takanta itakam.
Haka zalika umman khadija datai zaman dirshan tana share zufa.
"Amsa nace"
Alhaji babba ya dakawa Aliyu tsawa wanda ko motsi ya kasayi illah kansa daya sunkuyar kuma har yanzu yana duƙe ne agaban abban bauchi wanda tun fara maganar baice komai ba, usman kwa ji yake kamar yaje ya naushi Alhaji haka zalika ya abbakar hankalinshi yay matukar tashi,gaba ɗaya falon tsitt ya ɗauka.
ÆŠago da jajayen idanunshi yayi waÉ—anda suka kuma girma jijiyar kanshi ta mike tai wani irin ruÉ—u-ruÉ—u zubawa alhaji babba idanu yayi batare dayay shakkarshi ba yace.
"Alhaji kayi hakuri wallahi bazan saketa ba sabida inason matata! kuma ai AUREN BARE ba haram bane bafa zan saketa ba wallahi kozaka mutu haka nan addini ya haramta sakin mace mai juna biyu akan me zan saki matata da cikin sati biyu ajikinta?"
Yafaɗa yana mai miƙewa tsaye yana jefawa alhajin wani irin kallon raini.
Gaba É—aya falon hayaniya ya É—auka kowa yana na'am da maganar Alin domin daman yawanci mazan biyayya suke bawai son wannan auren haÉ—in suke ba.
Gyaran murya abban bauchi yay wanda daman shi baice komai ba tun farkon maganar.
"Zauna babana, ya dubi Aliyu a tsanake.
Zama yayi cikin na'am da maganar abban bauchin sabida mutum ne shi mai feÉ—e gaskiya wannan dalilin ne yasa ma suke yawan samun matsala da alhajin.
"Haba yaya ta yaya zaka ringa tilaswa yara Auren da basuyi niyya ba wannan fa abun ba addini bane ba yanzu hakan ku bai ishemu ishara ba? yanzu inda karuwa ya ajefa dafa haka za,a kawo mana ɗan shege mu goya amman ku duba auren nan nasa abubakar da usman su suka goya masa baya yayi akanme zakace ya saki matarsa ita khadijan da kuka liƙa masa ai ya amsa yay muku biyayya ku ba seku goya mai baya a binda yake soba kuduba isharar Allah auren da kwana goma sha biyar har Allah ya basu rabo toni dai babu ruwana sabida haka inma zaku aje wannan makaman yakin naku seku aje, kai babana tashi kaja matanka Allah ya baka ikon yin adalci sannan daga yanzuma duk mai son AUREN BARE yaje yayi matukar zeyi adalci Allah ya bashi tagari amin"
Abban bauchi ya faÉ—a yan mai tashi yabar wajan daman shi abinda alhajin yake yafa isheshi yana musu wata isa da gadara kamar shine ubansu ai wa ba uba bane.
Falon ne ya dauki hayaniya nan da nan kowa ya soma tofa ta bakinshi mazan familyn kwa ihu suke suna cewa.
"Well done yaya Aliyu Allah ya biyaka ka kwato mana Æ´anci" haka suketa faÉ—a wanda hatta Æ´ammatan ma ba,a barsu abaya ba domin yawanci da samarinsu amman tsoro yake hanasu kawosu gaban iyayen nasu.
Gyaran murya alhaji babba yayi.
"Tabbas maganar Abban bauchi ta sanyaya mun jikina kuma auren baba Ali yazaman ishara tabbas rabo ma kaɗai ze iya kasheni dan Allah ƴaƴan nan kumin afuwa waɗanda na tursasa sukai auren dole duka kuyi hakuri daga yau najanye wannan al'adar tawa kowa yana da damar AUREN BARE! amman nagartacciya mai tarbiya, tabbas idan har iyaye zamu dinga tilasawa yaranmu auren da basa so tofa za'a iya haifar ɗan da baida idanu, tabbas wannan ma isharace gamu iyaye mu dinga yiwa ƴaƴanmu adalci sabida tsanani tilasawa yaro yana sakawa ya bujirewa mahaifa musamman Aliyu wanda ban taɓa masa magana ya musan ba bantaɓa ganin ɗan albarka kamarshiba baya musu haka nan baya saɓa mana amman yau harni ze duba yace kozan mutu baze saki matarsa ba ya kalli idanun ubansa baiji kunya ba lallai soyayyar shi da wannan yarinya takai ta kawo wallahi inda ba'ai auren bama za,a iya haihuwa a titi, kai idriss karkai fushi da ɗanka maza kai masa afuwa Allah yay muku albarka gaba ɗaya, haka zalika kema bilkisu nasan rankine ya ɓaci har kika jefamin kalamanki na ɗazu abinda baki taɓa min ba tun aurenki agidan nan kikemin biyayya duk tursasawar dazanwa ƴaƴanki baki taɓa ɗaga ido kin dubeni ba sabida haka ban rike ki araina ba Allah ya baki hakuri yayi maki albarka keda zuri'arki Amin"
Amsawa dukkan mutan falon sukai gaba É—aya. alhaji babba yaji jikinshi yayi sanyi, daman shi abba marinma dayay wa É—an nasa dan dai kar alhajin yaga kamar ya daure masa gindine amman shi tun kalaman alhaji isyaku yaji jikinshi yay sanyi tabbas yayi godiya ga Allah dayasa ba É—an shege aka kawo masa ba.
"Zonan ƴar albarka kiyi hakuri do Allah kada ki rikeni akan nace asake ki kiyi haƙuri ɗiyata"
Alhaji yafaɗawa bebi haka yana kallonta wadda tun ɗazu ta raɓe tana jin duk maganganun nasu bata ɗago ba sema kasa data kumayi da kanta domin ita kaɗai tasan a halin data ke ciki.
Abba ne ya É—ago kansa batare dayace kamai ba.
Yadai zubawa Aliyu idanu yana kallon yadda gaba ɗaya hankalin Aliyun na kan matar tashine data sada kanta kasa taƙi kallon kowa.
Addu'a abba yayi tare da sallamar kowa ya kama gabansa amman yacewa iyalinshi su samesa a falonshi harda surukanshi kaf.
Kowa tashi yayi yana murna, ammi da kanta tazo gaban bebi ta É—agata suka wuce can part É—inta.
Abakin kofa dija ta tsaya tana turawa umman ta baki.
"Nace ki kwantar da hankalinki ko? wannan marar kunyar yaron tunda ya furta maganar dayaso agaban alhaji wallahi akan waccan Æ´ar ze iya sakinki kinafa kallo ciki gareta ke bazaki kwanto ki samuba,so kike ki É—aga hankali mu tashi a tutar babu? akanta fa yau Alhaji ya rusa al'adar da aka gina sama da shekaru ashirin a wannan zuri'a tamu"
"Amman umma kishiya fa nidai ina son mijina ina kishinsa"
Murmushi umma tayi.
"Kamar yaya kenan ban fahimta?"
"Ina son ya Aliyu tun farko sabida Allah wallahi umma na yada makaman yaƙina na cewar dan dukiyarshi zan zauna dashi nidai kimin addu'a domin yanzu zan fuskanci ƙalubale akanshi Allah yagani inason sa dukiyarshi bata gabana nagane so yanzu na kuma gane son kuɗi"
Mamaki khadija ta bawa, umman tata wadda tsabar zafin maganar yasa umman jan tsaki tabar mata wajan.
Part É—in ammi dija tayi duk tanajin babu daÉ—i aranta.
Gaba ɗayansu ta samu a falon abba,hadda bebi datake raɓe jikin ammi taki kallon kowa ma a falon.
Gyaran murya abba yayi sannan ya dubi Aliyu.
Cikin tsanaki yagama masa nasiha tsaf sannan ya nusarshi kuskuren dayay akan maganganun shi na gaban alhaji daga karshe ya ce masa lallai koyau ko gobe yaje ya bawa alhajin hakuri.
Itama ammi nasihar yay mata tare da cewa taje ta bawa alhajin hakuri sannan yahau ya abbakar da faɗa sosai akan kuskuren da sukai shida usman itama khadija nasiha yay mata sannan ya kirawo bebi itama kamar yadda yaywa khadija nasihar zamansu lafiya haka yayi mata, daga ƙarshe yahau yima su usman tsiya harda cewa daman rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya.
Addu'a akai aka shafa daga karshe kuma aka hau hirar bikinsu amina tashi abba yayi yana duban Aliyu.
"Babana tashi muje asibiti zanga likita nifa nagodewa Allah dayasa ba ɗan shege aka kawon ba Allah yay muku albarka ya ƙara haɗa kanku ami"
Dariya suka saka gaba É—aya sukwa Æ´an biyu saka bebi agaba sukai suna damunta da surutu.
Watsewa akai daga falon dija ta kama hanyar part É—inta tana nanata maganar abba na cewa.
"Amina dasu hassana zasuje part É—in khadijan sauran extra room É—in dake saman za,aiwa bebi jere zuwa anjima gobe zata koma can da zama domin yafison ya haÉ—e iyalanshi waje É—aya daga yau maganar rabuwa ta kare"
Yanzu shikenan zata zauna guri É—aya da kishiya damma Allah yaso kowa da toilet É—inshi amman kicin a haÉ—e falo a haÉ—e damma dai kowa da falonshi a bedroom É—inshi spare guda É—aya, yanzu yakama su suka saka Aliyu a tsakiya kenan domin É—akin bebi yana gefen na Aliyu na dija na É—aya gefen shima.
Haka ta koma É—aki duk jikinta sanyi kalau.
Ammi da kanta ta haÉ—awa bebi ruwan wanka tanayi ta kwanta saman gado ba jimawa bacci ya kwasheta.
Shima daya dawo daga kai abba asibiti wajan sayyyar kayan ɗaki suka wuce da amina wadda ita taiwa bebi zaɓen kayan ɗaki white colour masu kyau.
Daga nan can tokarawa ya wuce yaywa su goma bayani akan sun bar nan É—in kayayyakin shi mai amfani ya É—auko da nata sauran tarkacen kayan abinci kuma ya bawa su goma haka ya baro tokarawa yana kewar gidan domin anan yasan bebi a cikakkar mace anan sukai rayuwa mai tsayuwa arai tabbas wannan gida ya shiga kundun tarihinshi na rayuwar shi da bebi.
lokacin daya dawo gida part É—inshi ya wuce anan ya tarar dasu amina da Æ´an biyun ammi da sauran cousins É—inshi sunata faman gyara É—akin da bebi xata zauna sun jera kayan É—aki yanzu falon suke haÉ—a mata sosai tsarin wajan ya burgeshi wajan khadija ya wuce wadda ta yada fushinta ta zage ta ringa basa kula ta musamman anan yay sallah yaci abinci ya kwanta saman gadonta wanda shine farko tun aurensu.
Har su amina suka gama basuga gilmawarshi ba haka nan dijan bata fito ba itama sauka sukai suka fita lokacin magariba tayi falon ammi suka yada zango.
Lokacin bebi ta tashi tana zaune a carpet tana cin taliya.
Ammi tana zaune saman kujera tana jan carbi.
"Washh Allah ammi yunwa mun gama amman munci ubanmu"
Da mamaki ammi ta kallesu.
"A,a kar ku gayan zancen banza tun wajan 2;00pm ku tafi jere amman dija bata baku abinci ba? ina baba Alin yake naga abbanku tun É—azu yana falon shi?"
Dariya hussaina ta saki.
"Taɓɓijan ammi tunda fa muka bar gidan nan muke aiki dasu hidaya,wallahi anty khadija bata leko ba shima yaya Aliyun daya shigo tun la'asar yace mana sannu ya shige ɗakinta har muka fito basu leƙo muba sun kulle kansu a ɗaki"
Hussaina ta faÉ—a cike da wauta.
Dum! dum!!dum!!! gaban Bebi yay wani irin faÉ—uwa wani irin zazzafan kishine...................
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.