Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 18 of 81
NA
*AUTAR MANYA*
*Siyan nagari mayar da kuɗi gida ga arha ga ƙarko kudai maza ku garzaya ku nemi taku Suna sayar da MTN data akan price Mai sauki 1gb 300 2gb 600 expire 30 days ga masu bukata suna iya tuntuɓarsu akan wannan number din 08066268951*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
*21&22*
Hassana ce ta juyo wajan hussaina tare da ce mata"Hmm wannan bawan Allah baya da matsala jiba kamar ba mai kuɗiba yadda ko ƙyamatarmu bai ba".tafaɗa tana ɗan kaɗa idanunta kaɗan,"To ai daman wasu mutanan zakiga Allah ya zuba musu sauƙin kai tamkar bamasu kuɗiba aidaman ba duka aka taru aka zama ɗaya zakiga ai ko a talakawan akwai masu izza to kuma suma haka masu dashi ɗin akwai masu izza da ƙi faɗi", hussaina tafaɗa tare da mikewa sabida zuwan wani ma'aikaci zesai dambu bayan ta zuba mashi ta dawo ta zauna tana cigaba da hirarta da ƴar uwarta, cikin ikon Allah ahaka akaita zuwa wajan siya wasu sukan zuba musune a packet wasu kuma anan zasu zauna saman bancinan wajan suci su ƙara gaba abunsu.
_CIKIN BABBAN ÆŠAKIN TARO NA MUSAMMAN DAKE CIKIN KAMFANIN MAI ATAMFA_
Sosai suka zauna tare da manyan cikin kamfanin suka tattauna akan abubuwan cigaban da kamfanin nasu ya samu duk da kasancewar kamfanin sabone amman kuma ikon Allah haryaso yafi na *mundaɗu* samun jama'a sosai kuma duk ba kowane yay silar haɓɓaka wannan kamfaninba kamar *Aliyu Idiriss Mai atamfa* wanda shi kanshi usman ɗin ya jinjinawa ɗan uwan nashi yakuma san dukkan wata nasara da kamfaninsu na nan dama sauran suke samu tofa tare da taimakon ɗan uwan nashine saninsa mutum mai ɗan banzan naci tare da mayar dakai akan dukkan abinda yasaka agabanshi tofa da zarar ya kafe babu zancen bari, duk da kasancewarshi mutum mai wuyar sha'ani amman hakan bai saka ya samu miskila wajan iya hulɗa da mutane ba wanda hakan ya kuma jawo mashi ƙara samun tarin mutane yadda ba,a zato sosai mahaifinsu yake alfahari da Aliyu sabida yadda yake bashi gudunmawa fiye da sauran ƴan uwanshi.
Sun kammala taron su cikin awowi biyu kacal wanda aka tashi cikin farin ciki gami da fahimtar juna, anan usman ya ƙaddamar da abinda ze ƙaddamar kafin kuma mai gayya mai aiki director manager ya dawo, sosai.
_BAYAN KAMMALA TARO_
Zaune yake cikin offishinsa, asaman kujera irin wadda take kaÉ—a mutum tana juyashi batare dayay tsammani ba.Kiran masijanshi yayi tare da bashi umarni akan yaje yazo mashi da Salihu( baban nazir ) cikin mutuna biyar masinjan nashi ya shigo bayanshi baban nazir ne wanda wannan kiran na oga usman ya firgitashi addu,a yake kada Allah yasa oga usman yace.
Su hassana su daina kawo abinci kamfanin, sabida yaran suna bashi matukar tausayi ba É—an kaÉ—anba, sannan kuma su kansu sunajin daÉ—in taimakon abinci ko banxa ka huta shan lemo da burodi.
"Haba kaiko kamar ba namiji ba, daga aikawa kazo kazomin kana muzurai nanfa ba office É—in dodonku bane".
Muryar usman ta sauka cikin dodon kunnen baban nazir wanda tun zuwanshi daya rissuna yake faman tunani shi É—aya bai kuma É—agoba seda yaji muryar usman É—in data katse mishi tunaninshi.
Sosa kanshi yay kaÉ—an tare da kallon oga usman É—in tare da cewa.
"Ai oga bansaba jin kana kirana haka kurum bane harga Allah naji wani abu acikin zuciyata har ina addu,a Allah yasa ba dakatar da yarancan zakai ba".
YafaÉ—a kanshi tsaye sabida duk tunaninshi ya riga ya tafi akan hakanne.
Da hannu usman ya sallami masinjanshi dake tsaye awurin batare daya juya ba.
Sannan ya gyara muryanshi tare da kallon baban nazir.
"Malam salihu idan babu damuwa ina bukatar daka zauna akan É—aya daga cikin waÉ—annan kujerun mana".
YafaÉ—a tare da zube dukkan hannayenshi asaman teburin gabanshi yana kallon baban nazir da tausayawa.
Cikin sauri baban nazir ya miƙe tare da komawa saman emty chair ɗin dake cikin office ɗin wadda ta kasance ta silver, sannan ya mayar da hankalinshi kan oga usman ɗin.
Gyaran murya oga usman yayi tare da kallon baban nazir.
"Ai malam salihu ina zaton kai da kanka zakaje kana bada labarin halinmu kaf! bama ni kaɗai ba wallahi ko Aliyu da kuke ganinshi haka bani zaton ze iya wulaƙanta ɗan adam bare kumani, saboda me?, dukkaninmu bamusan me rayuwar zata kaimu gaba ba.to dan haka ina son ka cire kokonton wani abu daban acikin ranka wallahi ka ɗauka kamar nan ɗin kaima wajanka ne, sabida haka ina musu fatan nasara acikin sana'arsu ni babu ruwana da wani danyazo yaci arzikinmu nai masa ido ko bakin ciki,
Sabida haka ni ba wannan tasa na kiraka ba, daman tambayar ka zanyi idan babu damuwa.
Kasan madam É—ita se ahankali kwana biyu bata cika lafiyaba wallahi kullum problem É—ina abinda zamuci, na break na lunch dinner, kuma kaga dai rayuwar yadda take kuma kasan mata nan idan sunada juna biyu se addu,a shine nace idan babu damuwa kozaka tambayamin mamar yaran nan akan tabani guda É—aya inje gida da ita sabida ayyukan gidana da girki?".
Zubafe ta ketowa baban nazir wannan shine ga ƙoshi ga kwanan yunwa yasan ko ana yaki bayajin maman ƴan biyu zata bada yaranta aikatau sabida tunba yauba ake wannan mujadalar amman tace ita bata yardaba tafison ko tsakuwa a misali zataci tofa taci tare da yaranta.
"Ban musa makaba oga amman gaskiya mahaifiyarsu ce batada ra'ayin hakan amman zan tambayeta ko Allah zesaka ta yarda".
Cewar baban nazir wanda kawai yafaÉ—i hakane amman yasan hakan bamai yuwuwa bace.
Cikin ilimi tare da nazari usman yagama fahimtar baban nazir shi daman bawai matsuwa yay sosaiba tunda akwai masu aikin sedai kawai yadda yaga tsarin yaran da tsaftarsu yakeson ya daukesu ko girkine kodan ya sami kafar taimaka masu amman tunda abin bazai yuwuba kawai ze hakura.
"No Salihu karka matsa kanka amman pls dan Allah inason ka tabbatar min da tsaftarsu kawai sena dinga order dambun ma kawai is ok domin madam tana son dambun sosai".
Dariya baban nazir yay.
"Tabb oga ai wallahi ko madam baxata nunawa maman biyu tsaftaba amman kaima zaka tantance ko yadda kaga yaran da yadda komai nasu yake a tsaftace".
YafaÉ—a yana dariya shima usman É—in dariya kurum yay yana cewa"watakan dannafi yadda yasa ka haÉ—a harda madam É—ita lallai malam salihu ka rainani da yawa" yafaÉ—a yana kiran masijanshi.
Wata babbar kula wadda yake zuwa da abinci cikinta ya baiwa masinja sabida daman kwana biyu ba,a zuba komai cikinta sedai ai masa take away a waje,"Je wajan yarancan su bani dambu" yafaÉ—a wa masinja tare da buÉ—e locar ya fiddo sabbin kuÉ—i ya bashi"Kada ka tsaya amsar canji kaji kavar masu duka kace inji yayansu" yafaÉ—a yana dariya"Malam salihu ka iya tafiya kawai, bama seka je ka gaya mataba barshi na dinga siya kasanmu Æ´aÆ´an ammi Allah ya É—oro mana san dambu kaf É—inmu" yafaÉ—a yana fiddo wayarshi daga aljihun wandonshi sallama baban nazir ya mishi ya fita.shiko madam ya kira ya sanar mata maganar dambu aikuwa abinka da mai ciki tahau murna nan da nan tace zata aiko driver ya bata kasonta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.