Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 30 of 81
_karkusa ran ganin wani anjima gaya nan har na dare_
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
  { _HOT LOVE_ }
     Â
     NA
*AUTAR MANYA*
_Assalamu Alaikum my fans saƙon godiya marasa adadi gareku haƙiƙa naji daɗin yadda kuke nuna min ƙauna kuma alhamdulillahi jikina ya samu sauƙi masu kirana da masu ajemin msg ta inbox ina godiya Allah ya bamu lafiya da abinda lafiya zataci amin summa amin ONE LOVE_
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
            *45&46*
Jikinta har rawa yake sabida tsorata a iya tasowarta bata taɓa ganin wanda take mugun jin tsoro kamar shiba, sassanyar iskar dake kaɗawa awajan ga kuma gajiyar gudun datayi daga saman benen zuwa nan da kuma kukan! datayi shiya bata damar jin wani shegen bacci wanda batai tsammaninshi ba kuma daman jiya batawani samu baccin kirki ba, uwa uba kuma yadda tacika cikinta da dambu kunsan mai hali bai fasa halinshi, daman ita tun fil'azal idan ta ƙoshi tofa seta matse takejin daɗi wannan dalilin yasa kallo ɗaya zakayi ma Bebi kaɗauka daga gidan manyan mutane ta fito sabida fatarta kalar hutuce sabida babu laifi tana bawa jikinta haƙƙinshi, daɗi kuma da jikin nata bamai son wahala bane ba.
Domin aiki kaɗan zatai jikinta yahau ciwo,Waigawa tayi gabas yamma kudu arewa taga babu kowa wajan wannan dalilin ne ya bata damar tube hijabin jikinta ta shinfiɗa a wajan tare dayin kwanciyarta sam tama manta dawani zancen alalen usman data ɓarar a office ɗin yallaɓai ALI! Cikin mintunan da bazasu haura biyarba bacci mai daɗi ya sureta wanda iskar dake kaɗawa awajan itace takuma bata goyon bayan sake bajewa ranta fes take sharar barcinta babu sanya.
Daga cikin kamfani ko, tun hussaina tana ƙirga lokuta hartazo tana ƙirga awanni lokacin da wani staff yazo siyan alale takuma tambayarshi don Allah karfe nawa?Cemata yay karfe biyun rana da rabi, Cikin fargaba tagama zuba masa alalen wanda inda staff ɗinma ze kula tofa dase yaga hannu hussaina yana rawa sabida lokacin ilahirin jikintama rawa yake sabida kaɗuwar jin shurun Bebi datayi.
Bayan wannan staff ɗin mutum ukune sukazo siyan dambu babu ya ƙare dan haka alalen dayay saura suka siye sabida shi daman na rabin kwano mama keyi domin anfison dambu awajan fiye dashi.
Hannunta ta wanke tare da haɗe kulolinsu, waje ɗaya sabida tasan duk inda drivern dake kaisu ya ɗauko su gida yake yana hanya domin bai wuce ƙarfe ukun yamma kamar yadda mama ta gaya musu baki ɗaya tace koda abincin bai kareba kawai idan uku tayi suyo gida domin yanayin garin yadda yake, idan yaso sesu cinye abinsu da daddare to barema kuma cikin hukuncin Allah tunda suka soma bai taɓa kwantai ba.
Hasalima duk inda biyun rana tai zuwa da rabi sedai kaji ana cigiya domin abin kamar wawarsa ake Allah ya saka musu nasibi acikin sana'ar tasu, _daman munsan shi Allah haka yake Arrahamar-Rahimin neshi mai rahama maijin ƙai ga kowani bawansa dan haka komai na rayuwarmu idan muka miƙa masa toshi ɗin yasan yadda zeyi damu domin shine mahalicci ma'mallaki wanda babu kamarshi tsarki ya tabbata agareka ya ubangijin halitta Allah muna godiya agareka_  Bayan tagama haɗe komansu waje ɗaya sintiri tahauyi a tsakanin hanyar word ɗin da office ɗinsu usman yake dakuma hanyar wajan da kulolin su suke ganin time yana ja yasa ta leƙa har wajan masallaci wajan da provision store ɗinsu yake amman still babu Bebi babu alamunta.
Sosai hankalinta ya tashi zuwa lokacin babu tunanin ma dabai zo cikin brain É—inta ba.
Hawaye ta soma wani nabin wani tayi data sanin zuwa da Bebi yafi cikin kwando ganin babu wani alamun Bebi wajan yasa ta nemi guri adai dai saitin step ɗin Benen ta zauna ta rafka tagumi tana kuka kan jiki kan ƙarfi kuɗin cinikinta yana hannunta tanajin komai ya fice mata akanta takai lokuta masu tsaho awajan tana kuka har fuskarta tai jajur abinka ga farar fata.
Shiko Ali yana nufar cikin special room ɗinshi direct madai daicin toilet ɗin ciki ya shiga ya sami sabulu mai kyau ya wanke ƙafar wandonshi aranshi yana raya irin haukan yarinyar tare da giggiwarta sedai akwai ɗan banzan tsoro, tsaf ya gane ƴar gidan mai dambun jiyace marar kunyar nan dasuka gani jiya, fitowa yay yana yarfe wajan da man ya ɓata mishi, gefe ɗaya hannunshi namasa masifar zugin rashin sabo da wankin, ya jima yana yarfe wajan kafin ya gama shan iska, da kanshi ya fito zuwa wajan data ɓata ya sami mopar ya goge wajan ya ɗauke fasashshen plate ɗin ya zuba a tousbin, sannan ya koma ya cigaba da aikin dake gaban shi na tarin takaddun daya shigo dasu ɗazu daya zube akan desk.
Sakataren shi daya aika tun É—azu garage shike faman danna nocking alamun, yana niman izinin shigowa.
ÆŠago da kanshi yay a miskilance tare da cewa.
" Yes! Come in".
Sannan ya cigaba da aikin dake gabanshi.
Cikin ladabi tare da nutsuwa wadda duk wanda ze raɓeshi tofa koda baya dasu seya arosu dan Ali mutum ne wanda baya shiri da mutum mai baragada ko rashin nutsuwa, Sakataren yay sallama daga ɗan nesa dashi ya rissuna tare da miƙo masa keyn hannunshi.
"Yallaɓai an kammala gyaran yanzu haka motar tana can wajan adana motoci".
Fuskarshi kamar koda yaushe kadaran kada hakan ya É—an dubi sakataren tare da cewa.
"Ok thanks, ajemin nan".
YafaÉ—a yana cigaba da rubutunshi.
ÆŠan sosa kanshi yayi sannan ya kuma cewa.
"Yallaɓai madam lina tana reciption tace wai don Allah tana son ganinka to........",
"Stop!".ya buga mashi tsawar data saka nakusan yarda birona cikin É—an zafin rai kaÉ—an yace.
"Mena gaya maka? nace kada ku kuma barin wata mace ta shigomin office ko? duk abinda zasu ce su gaya maka tun a office É—inka na falo kada ka kuskura wata ta kuma shigomin nan dafatan kaji abinda nace?".
YafaÉ—awa sakataren yana zaro masa fitinannun idanunshi masu girman da kyau.
Rintse idanu sakataren yay kana ya soma bashi hakuri in full respecting, bai sami zarafin magana ba illah hannu kawai daya É—aga mishi domin wannan maganar dayake harya soma haddasa mishi ciwon kai mai zafin gaske.
Cikin sauri sakataren ya fita inda shikuma ya koma baya ya lafe yana dafe kanshi.
Wannan rayuwa tana bashi tsoro ta yadda wasu matan ke tallan kansu wa mazan waje, waÉ—anda wasu tsantsar so kan saka suyi hakan wasu ko tsabar son kuÉ—in jaraba ne ke saka su yin hakan.
Cikin haka usman ya turo ƙofar ya shigo inda bada ban sallamar dayay ba da Alin bazeji shiba sabida zurfin tunanin daya faɗa na lamarin wannan rayuwa da wasu matan suka jefa kansu irinsu lina masu tallar kansu wa mazan waje dan parsonal issue nasu.
"Man yane na ganka haka lafiya ko tunanin dije ake ne?"
YafaÉ—awa Alin haka yana dafe saman desk É—in da Alin ke rubutu akanshi.
Bai tanka mishi ba sema aikinshi daya cigaba.
"Kai bakajin yunwa?"
Ya kuma jefawa Alin tambaya?.
Se a sannan ya É—ago kanshi yana kallon usman da idanunshi dasukai ja kaÉ—an.
"Banjin yunwa nasha coffee, halan ƙureni kazoyi?".
YafaÉ—a muryarshi aÉ—an kausashe amman kaÉ—an.
"okey nima tun ɗazu nacewa waccan ƙanwar tawa ta, kawomin alale amman najisu shuru kuma nama leƙa naga bangansu ba duka ƙilan ko sun mantane dan nagama kamar sun haɗe kayansu".
YafaÉ—a yana wucewa gaban frij É—in dake office É—in Alin tare da budewa ya É—auko molt guda É—aya ya balle saman ya soma sha batare daya zauna ba yace.
"Zan koma office sabida xanyi sending cash É—innan da mukai maganar da abba na waÉ—ancan Æ´an kasuwan, yaufa inaga baxanyi off da wuriba yaya zamuyi da tafiyar kenan?".
Yafaɗa yana ƙoƙarin kai kanshi ga waje.
"No karka wani damu ai nasa an kawon mota ta, ni ina sallah ma zan wuce gida wallahi duk jikina ciwo yakemin".
Aliyun ya faÉ—a tare da É—an juya idanunshi kaÉ—an.
"Aikam gajiya yanzu ka somata malam domin nan da kwana uku mun soma shagali kaga ango ina yaga ta zama" usman ya faÉ—a aguje yabar office É—in sabida yasan yay tsokana.
Shiko Ali murmushin da baida ma'ana a wajena yay kana ya miƙe jin ana kiran sallah.
Alwala ya ɗauro acikin toilet ɗinshi kana ya fito, hularshi ya ɗora a saman kanshi tare da haɗe system ɗinshi cikin jaka tare da key da phone's ɗinshi kiran masinjanshi yay in few minutes ya shigo bayan ya rissuna agabanshi sannan yace "Yallaɓai gani", umartarshi yay akan ya kai mishi tarkacen shi mota haɗi da miƙa mishi keyn motar sannan shima yay abinda ze sannan ya fita waje hannun rigarshi a tattare alamun a wajan alwala ya tattareshi, kwantaccen gashin dake gefen fuskarshi ( saje ) duk ya jiƙe da ruwa yay wani irin luff hakama na hannunshi duka ya jiƙa da ruwa cikin sauri yake tafiya akan ƙafafunshi ko ina yay staff suna zubewa suna gaisar dashi cikin ladabi da ban girma.
Lipter ya hau wadda ta taimaka mishi zuwa ƙasan benen hawa na ƙarshe sannan ya sauka ya taka da ƙafafunshi har zuwa ƙasan daga bakin step yaga matashiyar budurwa zaune ta cusa kai tsakanin cinyarta tana kuka! domin ga sautin kukan! yana fita a fili.
Harya yi gaba sekuma ya duba agogon rolex ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hannunshi, ganin da sauran wajan 30 minutes kafin a tayar da sallah dan haka yaja ya tsaya cikin nutsuwa ya ƙaraso gaban ta.
Ƙamshin mayen turarenshi shine ya baiwa hussaina damar ɗagowa da sauri tare da saka hannu ta share hawayen dake zubo mata.
Binta da kallo yay na É—an wani lokaci yana noticing É—inta sannan yay mata sallama.
Acikin ƙasan maƙoshinsa kamar anyi mishi dole fuskarshi babu alamun dariya bare sassauci yake kallonta kafin ya fara jefa mata tambaya akan kukan datake a ƙasan ransa yana mamakin ƙarancin shekarunta.
"Ƙanwata ce mukazo tare tunda na aiketa ta kaiwa yaya usman alale har yanzu ban ganta ba, kuma na koma gida nasan mamammu faɗa zatamin". ta ƙarasa maganar tana sakin kuka!sabida haka kurum taji mutumin yay mata wani irin ƙwarjini a idonta taji tana ganin ƙimarshi da girman shi infact ranta ya aminta dashi sabida nutsuwarsa tare da tsantsar kamala da kamun kansa datagani acikin tsakiyar idanunshi, wanda kallo ɗaya tai mishi ta iya ɗauke idonta sabida tsabar ƙwarjininshi.
Tsaff yagama gano komai kasancewar sa mai saurin É—aukar abu aranshi, amman yay mamakin ina yarinyar nan tayi wadda yake da comfarming ta fito daga office É—insa tuni to ina tayi? yafaÉ—a aranshi.
Amman afili seya dubeta yana jin ransa yana taɓuwa da kukan nata................!
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.