Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 56 of 81

NAKUÆŠINE

*77*

Tashi yayi jikinshi duk a mace yabi bayan ammi suka fita zuwa falon, Zaune suka tadda Bebi a ƙasan carpet ta zubawa Tv idanu tana kallo ko ƙiftawa batayi.
Dakatawa ammi tayi tana kallon yarinyar wadda sam ita bata san da wanzuwarsu acikin falon ba, tana mamakin yadda akai Aliyu ya auro wannan ƴar mitsilar yarinyar domin ko sa'ar ƴan biyunta batai ba, amman ba,a mamaki da ikon Allah wannan dalilin yasa ta ƙarasa cikin falon Aliyu na bayanta.
Sallamar Ammice ta dawo da bebi daga duniyar kallon datake famanyi É—ago kanta tayi bakinta yana amsa sallamar da matar da ke neman wajan zama takeyi.
Kallon dattijuwar matar bebi take wadda bazata gaza shekaru sittin ba domin ta girmi mamanta nesa ba kusaba sam bebi bata kawo ammi maman Aliyu bace sabida ko a farcen susa basuyi kama ba sabida ammi farace jajur marar girman jiki domin duka duka batada wata ƙibar kirki sedai tanada cikar haiba da kamala wadda kana kallonta kasan mace ce na gartacciya mai yawan ibada tare da tsabta.
Saɓanin shi Aliyu dayake gabjejen mutum dogo kakkaura mai ƙiba da tsaho tare da cikar zati ingarman namiji majiyin ƙarfi baƙine shi amman bazaka sakashi ajerin munana ba domin ko ammi bazata nuna masa kyau ba sedai ta nuna masa jar fata, idanunshi kaɗai masu kyaune bare gashin girar shi daya cure ya cakuɗe ya haɗe dana idanunshi suka bada samfir mai kyau gawani irin gemu na ustazai wanda ya ƙara haska masa fuskar tare da saje mai ƙayatarwa.
Zama ammi tayi tana mai kallon bebi cikin kulawa.
Shima ƙarasowa yayi kusada ammi ya zauna yana ɗaukar remote, Cikin nutsuwa bebi kejan jikinta harta ƙaraso gaban ammi sannan taɗanyi ƙasa da kanta.
"Umma ina kwana fatan antashi lafiya?".
TafaÉ—a kanta a sunkuye sabida yadda ta tsinci kanta dajin nauyin matar.
Cikin murmushi ammi ta saka hannu ta É—ago kan bebi tare da cewa.
"Lafiya ƙalau amman niba umma bace sunana ammi kamar yadda ƴan uwanki suke gayamin kinji ƴar autata"
TafaÉ—a tana kallon fuskar Bebi sannan ta É—ora da cewa.
"Yaya sunanki autata?".
Bebi tsintar kanta tayi dajin daÉ—i yadda matar ta karramata tajata ajikinta batare data nuna mata wani abun ba.
Sannan ta É—ago sosai.
"Sunana Bilkisu, sedai Æ´an gidanmu suna cemin Bebi".
Karaf ya É—ago yana kallonta ashe sunan amminsa ke gareta.
Far'ar ammi ce ta ƙaru.
"Lah....lah ashe takwara tace kai amman nagode da wannan suna bilkisu mai gadon zinare matar Aliyu".
Ammi tafaÉ—a cike da tsokana tana dariya kaÉ—an-kaÉ—an.
Sunkuyar da kanta tayi tana mamakin yadda ammi take janta ajiki.
"Masha Allah bilkisu ga ɗana nan nima nabaki amana kamar yadda mamanki tabawa Aliyu amanarki dan Allah nima ina roƙonki daki masa biyayya kamar yadda na umarceshi akan ya kwatanta adalci akanki, ku zauna lafiya komai yace karki musu kinganni nan nida mahaifinshi shekarunmu 45 da aure tun ina shekara 15 aka auran shi kinga yanzu inada shekara 60 aduniya, bantaɓa yaji ba haka xalika bai taɓa shikana ba yanxu haka ƴaƴana 8 ciff babban su yanada yara 3 mata ɗaya kuma shi kansa ya shekara kusan 41 aduniya amman bamu da matsalar komai nida abbansu dan Allah kema kiyi koyi da mai sunan taki kinji autata matar ɗan autana a maza''.
Ammi tafaÉ—a tana janyota jikinta.
Cikin sanyin murya bebi ta dubi ammi tare da cewa.
"Insha Allahu nagode"
sakin hannunta ammi tayi tare da tashi tayi cikin wani lungu falon yay saura dagashi se ita.
matsawa tayi jikin kujera ta raɓe sabida yadda taga ya haɗe ranshi tamau yana kallon tv kamar baisan da biladam a falon ba.
har ammi ta dawo falon bayanta Æ´an aikine mutum biyu kowanne hannunshi É—auke da tiren sliver,agaban bebi suka aje tiren sannan suka gaisar da Aliyu kana suka juya suka bar falon.
Zama ammi tayi tana kallon bebi.
"Auta ga abinci nan kici ki ƙoshi in kin gama ina ɗakina kizo ki sameni, kaikuma kaje kai parking komai zuwa 12 Zaku wuce".
Tana gama faɗin haka ta miƙe tayi cikin ɗakinta.
Zumɓura baki yayi gaba tare da takewa ammin baya yabita ɗakin kamar jela.
Ita bebi ma dariya ya bata jiba kamar wani É—an yaro yabi ammi yana tura baki lallaima wannan man É—in.
Jawo tiren abincin tayi tana buÉ—e fulasan kai.
ɗayan farfesun farin kifine ɗayan kuma soyayyar doyace fara tas babu ƙwai se ɗayan kuma farfesun kayan cikin ragone.
Babban fulas É—in tean ta buÉ—e shikuma kunun gyaÉ—ane wanda yay fari tarr alamun anzuba madara aciki se cokula da plate tare da kofi.
Ƙwalla ce mai zafi ta zubo mata sannan ta dubi farfesun.
"Allah sarki mama dasu hassana da arfa da shahid inama zakuzo damunci tare ALLAH sarki mama koyau me zataci oho wallahi inda babu masu tsaron gidannan dase na boye wani na gudu nakai masu suma sunci sunji daÉ—i".
TafaÉ—a tana maijin kewar mahaifiyarta da Æ´an uwanta.
"Hmm koda yake mama ta hanemu da ɗaukar abinda ba namu ba nidai tunda iyani suka bawa naci kawai inyaso sena basu labari in sunzo, kona tambayi Boss nace masa ya tambayi ammin ta bani na kaiwa mama oh! koda yake babu kyaufa roƙo ba ɗabi'a bace mai kyau sannan kuma babu kyau ɗaukar kayan miji kayi kyauta dasu musamman in bai sani ba wannan ba ɗabi'a bace mai kyau ina dai fatan Allah kabani sana'a mai kyau wadda zan tallafi ƴan gidanmu amin".
Tafaɗa tana mayar da ƙwallarta wadda ta haɗe da miyan ƙwaɗayi domin tuni miyan mutuniyar ya tsinke sabida ganin hadaya agabanta.
Ƙamshin farfesun shiya hanata magana lokacin da Aliyu yazo ze gifta ta gabanta ya fita daga falon.
"Ni zan koma ki tabbatar kinyi wanka kafin na dawo kiyi brush kafin kici abincin".
YafaÉ—a yana kokarin fita.
Wani irin wullll tai da idanu kamar na farar kura tana kallonshi batare datayi magana ba still hankalinta yana kan fulas É—in dake gabanta.
Dariya yarinyar ta bashi harya fita yana yinta daga gani yarinyar kurace za'ai daru da ita wajan cin nama.
Mayar da ajiyar zuciya tayi tana shakar kamshinsa tare da maida kallonta ga fulas É—in gabanta.
Hannu na rawa ta ɗauki plate guda ta kusan juye rabin doyar sannan ta kwaɓe farfesun kifin kaff akai tana cewa.
"Tabb loma ba in carry yaushe gamon ƙauna ai wallahi Allah bantaɓa cin irin wannan farin kifin ba gwara naci na donge".
A bayyane take faÉ—in hakan.
Sannan ta janyo kofi ta zubo kunun gyaɗar cikin fulas wanda yaji suga ta ɗaga kofin ta kurɓa tare da zaro idanu.
"Kai lah ashe da madara aciki ina tsoron haÉ—a madara da kifi kar cikina yay ciwo".
sekuma tayi dariya kamar sakarai.
"In zakasha giya shata dubu inji bahaushe bara na aje wannan kunun agefe gwara naci kifin na haƙura da shan kunun duk da farin kifine babu ƙarni amman dai sabida tsaro gwara na hakura".
Ta janyo plate É—in tareyin bisimillah ko cokalin bata saka ba tafara cin abincin kunnenta yana tsalle kamar ze faÉ—i.
Gyara xama tayi tana ci tana kallo wayyo ran bebi ze fita dama akwai abu mai daÉ—i kamar wannan na gaban nata..............

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.