Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 33 of 81
Shikuwa Aliyu dawani irin mugun gudu yaja motar...............
_duk sanda kuka ga banyi update ba akwai uzurin daya risken musamman a yanzu danake cikin rashin jin daÉ—in jikina sakamakon zazzaÉ“in malerian dake damuna wannan ma nayi sabida masu bibiyata ne amman wlh bana jin daÉ—i kwanan nan_ ðŸ™
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
  { _HOT LOVE_ }
     Â
     NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
           *52&53*
Da wani irin mugun gudu Aliyu kejan motar wanda cikin mintuna kaɗan ta kaishi cikin unguwarsu ta yahaya gusau,Cikin zafin nama da kuzari yake danna uban horn abakin tafkeken gate ɗinsu cikin mintuna ƙalilan sojojin dake tsaron gate ɗin sukai saurin zuwa gaban gate ɗin tare dajanshi suka bude mishi cikinsa.
Hannu suke ɗaga mishi cikin girmamawa alamun suna mishi barka da zuwa kenan,Shiko baima kula da yadda suke ɗaga mishi hannunba, danna hancin motarshi yay zuwa cikin harabar adana motoci tare da fitowa daga cikin motar phone ɗinshi kaɗai ya iya rikewa se keyn motar yana tafe yana hade hanya cikin ƙanƙanin lokaci ya isa part ɗinsu wanda yay amfani da ƙofar baya wajan ɓulla zuwa samanshi domin baison hayaniya a halin yanzu
Acikin ƙayataccen falonshi ya zube saman one seater yana dafe kanshi wanda ke faman sara mishi, duk jijiyoyin kan sun tashi alamun yana damunshi sosai mikewa yay kamar an tsikareshi ya nufi gaban frij ruwa mai sanyi ya ɗauka tare da ɓalle marufin gorar ya kafa kanshi yana faman kwan kwaɗa kamar ze shanye dukkan ruwan frij ɗin haka yakejin maƙogoronshi na faman suya.
"Why Aliyu mike damunka?" haka yake faman faÉ—i a fili bayan ya aje gorar ruwan dake hannunshi wadda take emty domin bai bar komai ba.
Nufar cikin bedroom É—inshi yay batare daya dubi inda ya watsar da phone É—inshi ba.
Sintiri yake acikin bedroom É—in nashi tare da saka hannunshi yana yamutsa sumar dake kanshi wadda batacika yawa ba se saisaye kaÉ—an dayayi.
Tunanin shi ya zurfafa akan wannan ƙaddararran auren daza'ai mishi wanda bai murnarshi ko kaɗan, Wanda damuwar hakan ta haifar mishi da mugun ciwon kai mai zafin gaske ya fuskanci kowa son wannan aure yake amman shikam baiko jin abin a farcen susanshi.
Zama yay saman soparshi tare da kokarin tube rigarshi se a sannan yake tuno wannan yarinyar ta É—azu tsintar kanshi yay da sakin wani murmushi na daban wanda ban san ma'anarshi ba.
Tubewa yay jikinshi yay saura dagashi se dogon wondon rigar daya cire sekuma singlet faffaɗan kirjinshi wanda yake shaƙe da kwantaccen gashi bayyane,ɗora hannunshi yay a saman sopar idanunshi lumshe haƙiƙa yanada damuwa a ranshi amman baida wanda ze fuskanta da ita, gefe guda ga wani haɗaɗɗen ciwon mara dake kawo mishi cafka sakamakon body contact ɗin dayay da wannan ƴar yarinyar amman haka kawai jikinshi ya tashi wanda tun a mota yake faman haɗeshi amman hakan ya faskara, da ƙyar ya mike hannunshi dafe da west ɗinshi gaban cabet ɗinshi yaje tare da janyo drowwer wadda drugs ɗinshi ke ciki ɗaukosu yay tare da komawa ɗan ragowar ruwan dake tsakiyar table ɗin shi ya ɗauka ya balle drugs ɗin ya watsa tare da afa ruwa bisa bakinshi sannan ya koma saman sopar still kwantar da kanshi yay yana saƙe saƙe acikin zuciyarshi.
Ganin time yanaja yasashi tashi tare da nufar bathroom domin yaÉ—anji releife babu laifi ruwa ya watso ajikinshi tare da É—auro alwala, zube kayan daya cire yay acikin washing machine tare da fitowa jikinshi daure da faffaÉ—an blue tawul wanda kuma ya É—auro karami a saman kanshi yana goge saman kanshi dashi.
Ko cream bai shafa ba turare kawai yaɗan fesa kaɗan tare da nufar gaban close set ɗinshi shirya kanshi yay cikin ash jallabiya tare da fita zuwa falo lokacin anata kiran sallar magrib dan haka phone ɗinshi kaɗai ya ɗauka.tare da sauka ƙasa, Falon ammi ya shiga bakinshi dauke da sallama wadda yayta ciki-ciki, Ammi ya samu zaune akan sallaya tana lazimi gyaran murya kawai tai mishi dan haka bai zaunaba seya fita domin yaji ana kokarin tayar da sallah ya bari idan ya dawo ɗin suyi magana.
Har zuwa sallar isha'i yana cikin masallaci kasancewar shike jan limancin masallacin time to time idan yana available, bayan an idar da sallah tare suka jero da usman suna tafe usman na addabarshi da labarin yadda É—azu sukaje wajan da zasuyi taron wunin bikin Aliyun wanda shi baima san da hakanba bada ban usman É—in ya gaya mishi yanzu ba.
Taɓe bakinshi yay batare dayace uffan ba, kusan a tare suka shiga cikin babban falon abbansu wanda yake a farko kafin ka kai ga shiga ainihin falon ammi.
Usman ne ya zube a ƙasan carpet yana faman mayar da numfashin gajiya kamar wanda yay wani abun sakamakon ƴar ƙibar dayake da ita, shiko Aliyu daga ɗan wani saman stoll na table ɗin tsakiyar falon yaja ya zauna yana ɗaukar wani ɗan littafi daya gani a saman table ɗin, idanunshi kafe akan littafin har abba yay sallama ya shigo bayanshi yaya abbakar ne, se nusaiba wadda take biwa Aliyu, tare da ƴan ƴaƴanta ƴan biyu a bayanta.
Cikin sauri ya juyo cikin ɗubin mamaki yake bin nusaiba da kallo na yaushe kikazo? amman seya bar abin can ƙasan ranshi tare da mayar da hankalinshi kan yaranta ya saka hannu ya ɗagosu yana manna musu kiss a saman goshinsu.
Gaba ɗaya ya mayar da hankalinshi kan yaran seda ya gama wasanshi da ƴan biyun waɗanda basufi shekaru ukuba, kuma dukkansu matane masha Allah, kyawawa dasu, sannan ya riko hannunsu sukai wajan abba wanda ya zauna akan lallausar darduma yana bawa ya abbakar umarnin ya haɗa mishi tv,gab da ƙafafun abbansu ya xauna yana aje yaran a saman carpet tagumi ya zuba tare da ƙurawa abbansu ido kamar bai taɓa ganinshi ba.
Sarai abba yana lura da yadda yakeyin ɗin kuma yasan da abinda yake bukata sedai zurfin ciki bai barinshi ya faɗi abinda ke ranshi, sedai abba da ammi suna yawan gano idan yay hakan tabbas yana cikin damuwa wanda daman can tun yana ƙarami da haka suke gane yana da matsala ko damuwa cikin ranshi.
Nusaiba ta zauna daga É—ayan side É—in cikin girmamawa tace.
"Yaya haidara ina yini kai kaÉ—aine yau ban gani ba, yaya aiki ya shirye shirye?" tafaÉ—a cikin mutuntaka.
"Lafiya alhamdulillahi! ina su amir?" ya bata amsa idonshi na kan abba.
"Suna school kasan ba,ai hutu ba, na barsu da abbansu kawai se masu aiki".
Zaro idanunshi yay waje waɗanda suke ƙara mishi madarar kyau ɗan gaske, yana mata kallon bakida wayo.
"Kina nufin kin barosu acan tare da wasu kika kwaso ƙafafu kika tawo ke?".
Murmushi tai tuna yadda yake mutuwar son yara tasan idan shine baze iya ba.
"Eh! mana bikin yayana guda wanda nakeji dashi duk duniya aiko cikine idan da damar na aje sena aje bare kuma yaran dazasu iya yiwa kansu tsarki".
Dariyar usmance ta karade wajan.
"Gaya masa dai Æ´ar nusai angaya mishi kowa mayen yarane irinshi".
Wannan karon murmushi yay tare dajan bakinshi yay shuru.
Ya abbakar ne yagama haÉ—a kallon bayan ya kamo tashar CNN zama yay shima daga gefe tare da É—aukar remote control domin ya rage volume É—in tv'n.
Ammi ce tai sallama ta shigo se Æ´an biyunta da amina waÉ—anda hannayensu yake É—auke da manyan farantai na sliver guda uku waÉ—anda aka jero kayan abinci a samansu ajewa sukai daga gefe bayan sun gaisar da yayin nasu guri suka nema suka xauna, kowa ya halarta a wajan idan ka cire umar wanda ke legos, amman akwai abbakar, usman, aliyu, nusaiba, amina, hassana,hussaina, se ammi tare da abba, se Æ´an jikokinsu waÉ—anda nusaiban tazo dasu daga birnin tarayya.
Gyaran! murya abba yay sannan ya dubi usman.
"Shehu fara bude mana taro da addu,a".
YafaÉ—i hakan cikin bada umarni.
Batare da bata lokaciba usman ya mike ya jagoranci addu,ar kamar yadda abban yace bayan ankammala aka rufe da salatin annabi (s.a.w) se suka shafa sannan usman ya koma ya zauna, kowa ya bada hankalinshi akan abba.
"To Alhamdulillahi! muna godiya ga Allah mai kowa mai komai tsira da amincin Allah,su ƙara tabbata ga annabi muhammad ( s.a.w ) amin, kamar yadda kuka sani ban taraku anan domin komaiba sedan murnar sha'anin bikin ɗan uwanku dazamu fara nan da kwanaki biyu, to Alhamdulillahi ranar da kowa acikin wannan zuri'a yake fatan tazo tofa gatanan Allah ya nuna mana fatanmu Allah ya basu zaman lafiya da iyalai masu albarka".
Yaja fasali wanda ya bawa iyalan nashi damar amsawa da.
"Amin".
Sannan ya cigaba.
"Muna fatan Allah ya sanya alkairansa acikin wannan zama ya ƙara mana danƙon zumunta da kaunar juna amin, Aliyu kamar yadda ka sani, ina son kaima ka zauna anan cikin gidan acikin ɓangaren dana mallaka maka bana son zuri'a ta tabar cikin gidan nan dan haka kowannenku na sama masa inda ze zauna, sedai kuma bayan aurenku da wata guda, zan turaka legos kucigaba da xama da umaru nan kuma ze koma hannun usman da fahad da mansur insha Allahu".
(fahad da mansur Æ´aÆ´an Alhaji babbane yayan abba).
Nisawa ya kumayi inda falon yay tsit kamar babu kowa se saukar numfashinsu.
"Abbakar ya baka gudun mawarshi amatsayin shi na babban yayanku magajina, yayi maka lefe akwatuna seti biyu, umar ya ɗauki nauyin yiwa ita wannan yarinya jeren kayan ɗaki shiko shehu ya ɗauke nauyin komai wanda za,aci za,a sha acikin wannan taro, nusaiba, ta ɗinko maka kayan dazaka saka tundaga ƙasar sinigal, amina ta cika muku store da kayan abinci suko ƴan auta, lemuka da ruwa suka siyo maka, nagaya maka hakane domin kaiwa ƴan uwanka godiya sannan kuma kaima ka ƙara akan alkairin da kake musu na zumunci fatanmu Allah ya ƙara haɗe mana kanku".
Gaba É—aya kanshi ya É—auki zafi inama auren so yay da anga rawar kai duk da yaji dadin yadda Æ´an uwan nashi sukai mashi amman abin bawani ratsashi yay ba sabida baya É—aukin auren ze daurene kawai dan kyautatawa mahaifanshi.
"Bakace komai ba, babana?".
yaji saukar muryar ammi akanshi.
"Hajiya kinsan É—an nawa da kunya fa, yaudai burinki ya cika É—anki ze aure sekibar yimai lissafin shekaru".
Abban ya faÉ—a cikin barkwanci.
Murmushi ammi tai tana nazarin ɗan nata wanda yaƙi koda ɗago kanshi bare yay godiyar da aka ce.
Kamar ze kuka ya É—ago jan idanunshi yana fesar da zazzafar iskar baki.
"Nagode Allah ya saka da alkairi".
Abinda ya iya faɗi kenan murya a shaƙe kamar wanda yaci wani abun ya tsaya mishi a makoshin sa.
Hirar yadda lamarin bikin ze kaya ita tacigaba da wakana acikin falon wanda Aliyu yay gum kamar ba shi za,a yiwa bikin ba.
Har wajan 9 suna faman tattaunawa kafin amina ta mike ta soma zuzzuba musu abincin da sukazo dashi acikin flate, koda ta mikowa Aliyu girgiza kanshi yay bai amsa ba, sema saɓar ƴaƴan nusaiba da yay yabar musu falon.
Zama sosai su ammi sukai suna hirarsu tare da yaransu kamar wasu abokai daman wannan ce al'adar abba yana son yaga ya tara yaranshi tare da Æ´an jikokinshi sun xauna suna hirarsu kamar babu gobe, haka xalika suna da kyakykyawar fahimta da surukansu matansu ya abbakar waÉ—anda suma suke kyautata musu sosai musamman anty zee matar usman wadda take Æ´ar É—akin ammi.
Sun jima kafin mazan suyiwa su abba sallama suka bar falon suko su nusaiba zama sukai suna hirarsu da abba da ammi har zuwa wani lokaci kafin suyi sallama sabida dare yaÉ—an ja.
Aliyu yana fita bedroom ɗin ammi yaje kwantar da ƴaƴan nusaiba yay sannan ya fito cikin falonta ya xauna ƙafafunshi zube bisa table, hannunshi ya ɗora akanshi.
Har tsawon lokuta yana xaune seda yaga shigowar su ammina sannan ya É—aga kai ya dubi agogo wajan karfe goman dare dan haka ya mike ya koma falon abba.
lokacin dayay sallama ammi tana zubawa abba black tea a cikin cup, da hannu abba yay mishi alamun dayazo gareshi.
Babu musu ya nufi gaban abba ya ɗanja baya kaɗan ya zauna yana tanƙwashe ƙafafunshi.
"Babana waya taɓamin kai naga tun ɗazu ran ƴan mazan a haɗe yake gajiyar office ce ko?".
Abba ya faÉ—a cikin kulawa.
Sunkuyar da kanshi yay kasa yana ayyana damuwar auren nan tafi gajiyar office dubu amman sabida tsabar zurfin cikinshi seya cewa abba.
"Naxo muyi wannan lissafin wallahi baccine a idanuna abba daman na jira kane harka nutsu".
Murmushi abban yay.
"Kai wannan baban nawafa akwai tsabar kaf kaf da kudi wato ashe kai zaman jira kai to maza ina jinka".
Abba ya faÉ—a yana mayar da hankali kansa lokacin ammi ta mikowa abba cup É—in tea, sannan ta kuma haÉ—o wani ta miko wa ali.
"Amshi maza shanye ban kofin domin nasan bakaci komai ba ka tsaya bakin rai".
Cikin damuwa ya amshi kofin yakafa bakinshi tass ya shanye sabida babu zafi sosai.
Sannan ya mike tsaye mintuna biyu yaje gaban frij saman yaÉ—an laluba ya É—auko white papper wadda ya ajeta gaban abba yazo da ita dalla dalla yake zayyanewa abba abinda yake cikin takaddar wadda babu komai cikinta face tsantsar lissafi na cigaban da aka samu acikin kamfaninsu na wannan watan.
Abba yay farin ciki yaji daÉ—i sosai wanda murnar harta kasa buya.
Duk yaranshi babu wanda yakejin daÉ—in tafiyar da business É—inshi kamar Ali sabida yasan kanshi abba yana jin dadinshi yana kuma alfahari dashi over.
"Haƙiƙa ina godiya ga Allah daya azurtani dakai babana Allah yaywa rayuwarka albarka kaji".
"Amin abba sedai kuma......., yakasa karisawa.
"Sedai me? faÉ—i mana komeye zan maka matukar baifi karfina ba, kuma matukar ba zancen fasa aurenka da khadijaba domin kasan wannan aure babu fashi sedai idan babu raina kona alhaji babba".
"Abba seda safe Allah ya bamu alkairi".
Yana faÉ—in hakan yay saurin tashi yabar wajan ranshi na suya.
"Amman Alhaji yakamata fa aduba lamarin yaronnan".
Muryar ammi ta karade falon cikin nutsuwa.
"Dakata! Balkisu banson zancen banza duk duniya bamuda kamar alhaji babba tunda ya bada umarni bamu isa muce damme ba, dama naga take takenki wallahi harda hannunki wajan kara tunzurashi a ƙin wannan aure".
YafaÉ—a yana huci.
"Allah ya baka hakuri ni ban isa na hanashi aure ba tunda nima fatana kenan kullum Allah ya sanya alkairi amin".
Tana faÉ—in haka ta mike tabar falon sabida tasan halin abba yanzu se iya rufeta da faÉ—an tana É—aurewa Aliyu gindi.
ÆŠakinta ta koma tai kwanciyarta tana addu,ar Allah ya basu zaman lafiya.
Washe gari dawani irin ciwon kai aliyu ya tashi wanda ya hanashi fita office sannan ya kulle kanshi a É—aki, sabida hayaniyar Æ´an biki da suka soma cika gidan.
Se wajan dare ma ya kunna wayoyinshi anan yayta cin karo da sakon taya murna wanda abokanshi da sauran jama,a ke mishi wanda yasan usman ne yayta yawo da zancen auren nashi.
Wajan taran dare gidan yay tsit saukowa yay xuwa falon ammi wanda babu kowa ciki se masu aiki,yana kokarin fita sabida tun jiya da daddare rabonshi da wajen ko sallah ma yau a É—aki yaytayin abarshi wayarshi dake cikin aljihun wandon jeans É—in dake jikinshi ce take faman ringing dubawa yay yana kokarin fita ganin bakuwar number yasa yay banza da ita haka aka cigaba da kira kamar babu gobe.
Khadija wadda taci kwalliya ta alfarma tana gidan make up tana jiran angon nata yazo su wuce wajan event ɗin da tun ɗaxu suka ɗai ake jira ita ke faman doko mashi kira da ɗayan sim ɗin nata, gefe guda ƙawayenta na familyn su, sun zagayeta suna faman zuba mata hotuna sabida khadija ita sam bata da yawan kwashe kwashen kawaye yawanci ƙawayen nata ƴan gidane sa'anninta na familynsu.
Ido jajur take kallon jawa É—iyar alhaji babba.
"Jawahir kinga yaya bai É—auka ba kodai bazeje vane tun É—azu su umma kemin waya".
Murmushi jawahir tai tana cewa.
"Haba dai yayafa usman ya bamu tabbacin xuwansa kinga kawai mukira ko yaya fahad ne yazo muwuce tunda time yana ja kawai ma hade acan".
Tura baki khadija tai.
"Nikuwa nafison naga gani gashi muna tafe ana ƙyasamu a hoto".
TafaÉ—a tana lumshe idanu.
Seda jawahir tai da gaske sannan khadija ta yarda suka kira fahad yazo ya daukesu lokacin da sukaje waje ya cika makil da É—an adam.
Hotuna akaita faman yiwa amarya da kawayenta.
Zama tai a high table tana kuma kiran layinshi sedai wannan karon swich off usman ma bata sami damar ganinshiba sedai matarsa zee take faman barin kudi, haka akai taron aka gama khadija na kukan zuci.
Ganin an dameshi da kira se kawai ya kashe wayar ya koma É—akinshi tea ya haÉ—a daÉ—an biscut ya zauna yasha sannan yay wanka ya kwanta.
Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya.
Yau ta kama ranar juma'a É—aya ga watan É—aya dubban manyan mutane na cikin kasarnan dama kewayenta suka shaida É—aurin auren ALIYU IDRISS MAI ATAMFA! DA KHADIJA YUSUF MAI ATAMFA! cikin sadaki mai daraja can na hango usman yana faman baza babbar riga kamar angon, se faman baje baki yake ransa fess kamar shi akewa bikin.
Sanye ike cikin É—anyen boyel royal blue anmasa É—ikin half body, se hular daya saka wadda tai marching da kayan jikinsa yay mugun kyau duk da rannan yana haÉ—e amman bai gaza fita da tsantsar kyawunshi ba.
Zamewa yay sabida kanshi daya soma ciwo yabar usman da tarin abokanshi ya gudu gida samanshi ya hau yasha magani ya kwanta.
Sosai akai taro na bikin wanda ya cika da manyan mutane ammi ma tai rawar gani sosai wajan kawata bikin É—an nata sedai hankalinta yan wajanshi sabida ta jima bata ganshiba.
Se dare Jama,a suka É—an lafa sosai umman khadija tai mata huduba wadda sam khadija bata hau kan ko guda ba, haka anty karima kanwarsu abba tazo taja hannun khadija har part É—in alhaji babba yay mata nasiha mai ratsa jiki, sannan aka kaita wajan abba shima, zaunar da ita sukai, gabansu sannan abba ya dauki waya ya kira gogan.
Yana zaune ya dafe kanshi yana mamakin waishi akawa auren dole, kiran abba ya dawo dashi daga duniyar tunaninshi.
Babu yadda ze haka ya zira black jallabiya akan boxern jikin nashi, sannan ya É—auki wayoyinshi ya sauka zuwa falon abba.
Ammi da abba zaune se wadda yagani tana zaune gabansu ta rufe fuskarta.
Sallama yay tare da zama gabansu kana ya gaisarsu.
Cikin tsanaki abba ya dubi Aliyu tare da fara yi mishi nasiha mai ratsa jiki wadda rabinta akan rayuwar aure take tare da rikon amana na aure, daga karshe ya riƙo hannun khadija ya damƙawa Aliyu.
"Ka riken ita amana da mahaifinta dani uwarmu É—aya ubanmu É—aya ka rikemin É—iyar yusufa da kyau! domin katayamu rike amanar daya rasu yabar mana kaji babana".
Abba yafaɗa idanunshi yana kawo ƙwalla.
Sannan ya juya ga khadija itama yay mata nasiha sosai wadda babu abinda take se faman kuka!
Yana kammalawa ya dubi Aliyu.
"Tashi kuje ɓangarenku akwai key jiki komai yana kintse office daman nace ka huta duk sanda kai ra'ayi ka koma".
HaÉ—e ranshi yay tamau.
"Abba ko kayana banyi parking ba pls ta kwana anan gobe insha Allah semu koma can É—in".
A zafafe ammi ta É—ago kanta.
"Ban amince da shiga haƙƙin iyaliba,a matsayina na mahaifiyarka wadda take da hakki akanka wallahi idan yau baka saukewa marainiyar nan ta gabanmu hakkinta na auratayyaba ban yafe maka ba, sabida nasan halin taurin kanka ƙila yadda zaka jeda ita haka xaka barta ko kallo".
Dum! Dumm!! yaji gabanshi yay mugun faÉ—uwa akanta mahaifiyarshi ke faÉ—in haka.
Amman ammi ta É—ora mishi mugun nauyin daya xama dole ya saukeshi.
Ita kuwa ammi ta faÉ—i hakanne sabida kwaÉ—ayin kota dalilin hakan Allah ze karkata hankalinshi kan khadijan su zama masoya na hakika amman har cikin ranta kawai tafaÉ—i hakanne da wannan manufar bada wata ta daban ba.
Shikanshi abba yay mamakin furucin ammin amman baice komai ba.
Itako khadija shiwa ammi albarka take sabida ta matsu matuka.
Da sauri yace.
"Zanyi ammina kimin gafara karki sake dan Allah kimin mugun baki".
Nisawa tai.
"Allah yay maka albarka maza tashi kaja matarka kutafi Allah ya sadamu da alkairinshi amin,".
Wuff ya mike yabar falon yana tafe yana hada hanya.
Ta kofar baya yabi sabida har yanzu akwai Æ´an biki.
Daga part É—in ammi zuwa nasu akwai tafiya yana tafe kamar marar lakar jiki.
Ita kuma tana bin bayanshi kamar cingam ranta fari fess yau xata kwana kan faffadan kirjinshi datake mugun marmari.
Ƙayataccen part ɗinsu ya tura gate ɗin ya shiga da sallama sannan ya karasa gaban katuwar kofar glass ɗin da aka kawata, babban falonsu ya shiga yana sallama abakinshi.
Sosai yay mamakin yadda aka kashewa part É—in kuÉ—i ba kaÉ—an ba,sama ya haye inda bedroom's É—in gidan suke still tana biye dashi abaya.
Cikin bedroom guda ya shiga tare da faÉ—awa daman babban bed É—in dayaji white bedshit yay mugun kyau.
Akanshi ta tsaya tana xare idanu batare data xauna ba.
Zumbur ya mike ya nufi hanyar bathroom alwala ya dauro tare da fitowa sumar kanshi jike da ruwa.
Tsareta yay da idanunshi.
"Jekiyo alwala muyi sallah"
Musgutawa tai a tsayen
"Inada alwala sabida banjima da sallar isha'i ba".
Murmushin xakici uvanki yay mata sannan ya É—auko dadduma ya shinfiÉ—ata.
Sallah yajasu raka"a biyu bayan sun idar ya jima yana addu,a sannan ya juya ya mata tambayoyi akan addininta sosai ta bashi amsa wadda daman bayada haufi akan hakan sabida babu laifi sun sami ilimin addini mai kyau.
Tashi yay tare da hayewa saman gado yana kallonta cikin mugunta.
"Naga kina matse har kina kokarin yimin fyaÉ—e last time ok maza zona baki karki saka uwata ta tsinan".
YafaÉ—a yana janyota ya zare mata mayafin jikinta.
"Baki isa kinga jikina ba sabida mai tsadane amman xan baki abinda kike muradi".
Yafaɗa yana fisgo bakinta da karfi cikin mugunta yake sucking lip's ɗinta hannunshi duka biyun suna aje kan mitsi mitsin boobs ɗinta yana murzasu cike da xallar mugunta tun tana kukan zuci harya fito fili babu abinda yake mata se xallar mugunta hatta numfashi da ƙyar take fisgoshi, lokacin daya tubeta ya ɗora bakinshi saman kirjinta, Ihu ta saka sabida harga Allah cizo kawai yake kaimata akan nippy ɗin nata sabida mugunta, rage hasken ɗakin yay yana karanto addu,ar saduwa da iyali kafin ya ɗauki hanyarshi ɗoɗar bai tunawa da itan budurwace haka ya gama sha'aninsa batare da armashiba sema ƙaro wutar jarabarshi dayay domin takasance mishi babu wani test ko kaɗan agaretan, sabida irin matan nan ne masu mugun sanyin daya musu illah har suke rasa ni'imarsu, itako tsantsar azaba ta saka ta suman wucin gadi kafin ta farfaɗo a cikin ruwan daya ɗagata ya sakata aciki bayan yagama bidirinsa, ɗan stain ɗin jinin daya bata bedshit ɗin yasa ya tattareshi ya watsa a washing maching lokacin karfe biyun dare ya kusa dan haka ya barta a bathroom domin ta kintsa shiko ya shiga na ɗayan room ɗin domin bayajin ze iya nuna tsiraicinshi gavanta.
Allah ya taimakeshi ya sami jallabiya acikin Carbet sabuwa dall fara dan haka yay using da ita bayan ya fito, alwala ya dauro ya kwanta sabida duk jinsa yake wani iri duk da ya sameta a É—iya mace amman sam baiji wani dadin da abokanshi kecewa ba sema jarabar zafin da abarshi ke mishi adaddafe bacci ya kwashe sa.
Itakuwa khadija tai kuka kamar babu gobe kasancewarta ba yarinya ba yasa ta gyara kanta wajan ruwa biyar tai na xafi ta shiga sannan taÉ—anji dadi kana ta futo tana É—ingishi ta sauya kaya ta haye gado tana curewa waje guda.
Koda asubahi daya tashi ya shiga É—akinta da gyar ya ita tada ita tai sallah sannan shima ya wuce masallaci daga nan kuma yaje yayta jigilar kwaso kayanshi nacan part É—in yana fiddosu ta kofar baya, har wajan 7am yana faman abu É—aya seda yay setting close É—inshi tsaff a bedroom É—in dayake can gefen na khadijan wanda yake nasa sannan yay wanka ya shirya cikin bakin yadi mai farin xare wajansu abba yaje suka gaisa sannan yaje ya gaisar da mutan gidan, daganan bai koma part É—inshi ba parking lot yaje tare da karbar mukullin motar wata black prado 018 ya shiga tare da bata wuta yabar harabar gidan tare da nufar gaban gate masu gadi suka bude mai ya fice.......
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.