Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 44 of 81
NA KUÆŠINE
*63*
Cikin hukuncin ubangiji idi ya soma karɓar kayan chaina yana rabawa ƴan kasuwa yana ɗora nashi, a shekarar ne kuma Allah ya azurta ayuba da samun ɗa namiji wanda yaci suna muhammadu, haihuwar matar ayuba da sheka matar salmanu itama ta haifi ɗiya mace, wadda taci suna salma.
Ganin haka yasa baffa ya kuma tafiya ɗanbatta ya aurowa idiris ƴar ƙanwar salma matarsa ( inna ) mai suna Bilkisu, shikuma yusufa ƴar abokin mahaifinshi malam muntari, mai suna ruƙayya, gida guda ya saya musu kowanne da sashensa, bilkisu mace ce mai matuƙar hakuri da kauda kai, saɓanin ruƙayya wadda tunda aka aurota take takalar bilkisu da faɗa, in inna tai magana setace ai dayake ita bare ce shiyasa zasu nuna mata bambanci.
Shekaru biyu bayan auren idiris da ƙaninshi yusuf wanda shi yusuf ɗin bayan ya gama makaranta seya sami koyarwa anan wata primary, se kuma ƙaninsu shu'aibu tare da karima, shima dai shu'aibun ƴar cikin dangi ya aura mai suna hanne, ita kuma karima ta auri ƙanin bilkisu mai suna shamsuddeeni, hankalin baffa ya kwanta sabida kowanne acikin ƴaƴan nashi ya sami madafa.
Sedai abinda ze baka mamaki duk cikinsu Allah yafi É—aukaka idiris sabida bayan aurenshi da bilkisu se samunshi ya ninka nada domin harya kai ga buÉ—e runfar anan kasuwa inda ya É—ora shu'aibu a wajan.
Shekarar su uku da aure matar idiris bilkisu tana da Æ´aÆ´a biyu duka maza ita kuma matar shu'aibu tana da Æ´a É—aya, Sukuma su ayuba suna da Æ´aÆ´a uku uku kuma ikon Allah ayuba duka yaranshi uku mazane shikuma salmanu mata.
Itama matar idiris duka mazane biyun, abubakar da umar, ita kuma matar yusufa, tana da rumassa'u.
Su abubakar nada shekaru shida aduniya ɗaukaka ta ƙara xuwarwa idiris domin tuni idanunshi ya buɗe akan harkar kasuwancin shi wanda harya soma tunanin ginin kamfani anan anguwar sharaɗa.
Kuma a shekarunne, yakai.iyayenshi tare da yayyenshi ƙasa mai tsarki domin sauke farali wanda baffa har kuka yay da hakan ada yanaƙin ɗan nashi a kasuwa, ashe anan ɗaukakarshi take.
Lokacin da bilkisu take ɗauke da cikin ɗana uku lokacinne ya sai ƙaton fili anan anguwar yahaya gusau, wanda ya bada order ginin gida mai part bakwai ciff, sannan ya kuma siyan wani ƙaton daban wanda yace in Allah ya raya ƴaƴansu kowa ya yanka ya gina wanda aka kareshi batare da angina shiba, part ɗin iyayenshi part ɗin shi, dana yayinshi harma dana mijin ƙanwarshi karima wanda a yanzu yake kasuwa tare da shu'aibu anan shagon idiris ɗin.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka kammala ginin tare da sabon kamfanin atamfar daya buɗe anan sharaɗan wanda zena sifirinta daga ƙasar waje zuwa nan yana bawa ƴan kasuwa sari, Komawarsu yahaya gusau tare da ƴan uwanshi ta kawo sauyi da dama, haɗin kai ne ya wanxu a tsakaninsu mai mugun ƙarfi domin su idiris basa ƙetare maganar yayansu ayuba wanda yanxu yara kece masa ( alhaji babba ) lokacin da bilkisu ta haifi ɗanta namiji na uku se aka saka masa usman sunan kakansu idi kenan, alokacinne kuma rashin lafiya ta kama Baffa wanda bai wani ɗauki lokaci mai tsayi ba Allah yay mashi rasuwa wadda ta girgiza ilahirin zuri'arshi dama sauran alumma, Tunda baffa ya rasu itama inna lafiya tai mata ƙaranci adaddafe seda tai shekara ɗaya tana fama da lalura kafin kuma itama Allah ya ɗauki ranta gidan seya zama dagasu sesu da yaransu babu uwa babu uba,idiris ya mayar da hankalinshi akan kamfaninshi wanda daga kano har legos yana fita, ya tura kaya, Alokacin babu irin ƙiyayyar da rukayya matar yusufa bata nunawa bilkisu duk da dai yanxu ba part ɗinsu ɗaya ba amman bakin ciki yasa rukayya taji bata kaunar balkisu sabida yadda tafita ƴaƴa tafita da miji duk da ba miji guda suke aure ba, amman kullum burin rukayya ta zuga yusufa mijinta akan ƴan uwanshi amman dayake shi yusuf baida matsala sam baya kama maganarta
Bayan haihuwar usman da shekara uku balkisu ta kuma haihuwa É—a namiji kyakykyawan gaske sedai shi bakar fatane kamar mahaifinshi haihuwar data zamarwa idiris farar haihuwa domin ribar daya daya samu a kamfaninshi tafi ta ko yaushe wadda ta haifafa mashi fara sabon gini wani kamfanin na atamfa anan anguwar mundaÉ—u, Ranar suna yaron yaci sunan mahaifin idiri ALIYU, son duniya idiris ( abba ) ya É—auka ya É—orawa Aliyu domin ko bacci zeyi sedashi a kirjinshi yadda Aliyu ya saba da abbanshi bai saba da mahaifiyarshi ba daga abba se usman kaÉ—ai Aliyu ke sakewa aduniya amman kosu abubakar baya sakewa dasu sosai.
Aliyu yana da shekaru biyu, aduniya abubuwa nacigaba suka kuma samun abba, alokacinne alhaji babba ya kira ƙaninshi salmanu( abban bauchi ) wanda shi baya zama anan garin sabida aikinshi yana bauchi amman inyay hutu yakan zo da iyalinshi nan kano gidan da abba ya gina musu suyi hutunsu a part ɗinsu sutafi.
Zama sukai tare da Æ´an uwanshi ayuba ( alhaji babba ) salmanu ( abban bauchi ) idiris ( abba ) yusufa ( baba yusufa ) shu'aibu ( baba shu'aibu ) se kanwarsu karimatu ( anty karima ) addu,oi sukaiwa mahaifansu sannan Alhaji babba yay gyaran murya sannan ya soma yi masu bayanin abinda yasa ya tarasu.
Ya kirasu ne akan yana tayasu murna na samun rufin asiri tare da iyalai masu albarka domin alokacin alhaji babba yana da ƴaƴa biyar uku maxa biyu mata abban baucima biyar duka mata, se abba yana da huɗu maza baba yusufa ɗaya mace, se baba shu'aibu yana ƴan biyu duka mata , se karima datake da maza biyu, Cikin nutsuwa ya shigar musu da ƙudurinsa na cewar.
kakansu marigayi malam usman shi kaɗai mahaifanshi suka haifa yazo shima ya haifi mahaifinsu shi ɗaya shikuma mahaifinsu yazo ya haifesu su shida cikin hukuncin Allah suyanzu gashinan ƴaƴansu sunkai kusan 30 dan yanason su ringa ƙulla alaƙar Auratayya a tsananin ƴaƴan nasu kamar yadda mahaifinsu baffa yay ya dinga ɗauko ƴan uwanshi na ɗanbatta yana aura musu inka cire rukayya matar yusufa wadda ita kaɗaice bare, domin itan ƴar abokin mahaifinsu ce.
Kowa yay na'am kuma yay murna da hakan domin ta hakan ma zumuncinsu ze kara ƙarko.
Anyi taro lafiya angama lafiya wanda aka yanke hukuncin haɗa ɗan gidan alhaji babba mai suna muhammadu da ƴar gidan abban bauchi salma, anan aka yanke maganar za,a na ɗaukar mace ɗaya daga wannan ɓangaren namiji ɗaya ana haɗasu aure sannan alhaji babba ya nuna baya son ɗaya daga cikin ƴaƴan nasu ya AURO BARE! gwara kowanne ya duba anan cikin gida ya aura, da haka aka tashi ataron dayake su abba basa musa maganar alhaji babba kamar yadda mahaifinsu ya basu wasiyya wannan dalilin yasa kowa ya amsa mata dato.
Tundaga wannan lokacin zuri'ar MARIGAYI ALHAJI ALI MAI ATAMFA! suka soma auratayya a tsakaninsu, kuma abba shiyake gina masu sashe acikin wannan ƙaton filin daya aje na cikin gidan, a shekaru biyar seda akai auren mutum huɗu ƴaƴan alhaji babba maxa biyu mata na abban bauci kuma duk suna cikin gidan sedai kuma yawancinsu suna aikin gwammanatine, domin lokacin alhaji babba ma yay ritaya awajan aikinshi.
Seda Aliyu ya shekara goma sannan balkisu ( ammi ) ta sami ciki watan cikinta tara ta haifi É—iya mace nusaiba, wanda a shekarunne kuma aliyu ya shiga secondry sukuma su abubukar sun kammala jami'a har abba ya É—ebesu zuwa kamfaninshi sabida business suka karanta.
Aliyu ya taso dason kasuwanci kamar abbanshi dominshi haryafi abbanshi son neman kudi.
Wannan dalilin yasa yana gama secondry abba ya fitar dasu UK shida usman domin su karanci, Business, bayan tafiyarsu ammi ta haifi Amina daga amina se Æ´an biyu, daga nan kuma haihuwa ta tsayawa ammi, wanda alokacin da ammi ta haifi amina kusan atare suka haihu da rukayya wadda itama ta haifi mace wadda taci suna khadija ammi tana da Æ´aÆ´a8 ita kuma rukayya ( umma ) take da Æ´aÆ´a biyu ruma da khadija.
Bayan tafiyarsu abubuwa sun faru daga ciki kuwa harda auren su, abubakar wanda abubakar ya auri Æ´ar gidan alhaji babba, shikuma umar lokacin abba ya buÉ—e kamfani a legos tose ya tura umar can anan ya gamu da wadda yaso aura amman dayazo gida da maganar se alhaji babba yace masa sedai yabar musu gida domin su baza suyiwa kowa a Æ´aÆ´ansu AUREN BARE ba, bakaramin damuwa umar yay ba daga karshe aka bashi Æ´ar abban bauchi humaira wadda take sa'arsu amina da khadija ya aura ya wuce da ita legos É—in.
Nusaiba kanwar Aliyu itama É—an gidan anty karima mujahid ta aura,duk dai Æ´aÆ´an gidan kowanne inya taso baya rasa wanda za,a haÉ—asu aure.
Lokacin dasu Aliyu suka dawo daga kasar waje, Abba yaso yi musu aure amman Aliyu yaƙi, se usman ne aka haɗashi da zainab ƴar gidan baba shu'aibu kuma itama ɗin sa'arsu amina ce dai, Aliyu kuwa baki ɗaya ya mayar da hankalinshi ne akan harkarsu ta kasuwanci wanda a wannan lokacin yana legos wajan umar suna gudanar da kasuwancin tare a kamfanin abba nacan, ganin ƙwazon yaron yasa abba ya dawo dashi kano, cikin haka suka kuma gina wani sabon kamfanin na nan kusa da anguwarsu Bebi wanda abba ya damƙawa Aliyu matsayin MD na nan ɗin sabida ƙwazon shi wanda haryafi ƴan uwanshi ƙwazo da gudanar da aiki yadda ya kamata.
Cikin Haka Allah yaywa yusufa rasuwa, bayan Æ´ar rashin lafiyar dayay zokuga kuka wajan umman su khadija tun daganan komai nasu ya koma kan abba, hatta khadija dasu amina take tafiya makaranta wadda tun ranar dataga Ali taji tana masa mugun so, tunda ita bata sanshi ba seda ya dawo daga waje.
Amman yadda taga baya kulata baya wasa da ita yasa takejin mugun tsoronshi.
Faɗan duniya alhaji babba yayi akan ALIYU yaki aure sabida lokacin har ƙannenshi maza na familyn wasu sunyi aure amman shi in aka kirashi seyace akara masa lokaci.
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *PART* 2
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.