Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 9 of 81
"Hakane mama amman wallahi idan har wannan yarinyar tace haka zataje taiwa mijinta kullum kuwa seyaci ubanta".
Cewar shahid wanda haushinta yagama cikashi.
"Kaikuma ina ruwanka sarkin baƙin baki ni bama zanyi auren ba sedai duk kutafi ku barni da mama ina cin daɗi na".
Kallon ƙuruciya mama takewa Bebi tare da ayyana yanayin girman jikinta wanda tsaf idan aka kalleta za,a iya ɗauka itace gaba da ƴan biyu.
Sannan tace.
"Kema ƙuruciya ke ɗibanki bana miki fatan zaman gabana kema Allah ya kawo miki mijin arziƙi na aurarki na huta".
Tsirenta ta lamushe tare da miƙewa tai ɗaki tana gunguni itafa bata son aure inama take da saurayin bare wani aure tabb bata ma san maye soba bare auren.
Kwanciya tayi aÉ—aki tana tunanin gobe yadda siba ze kalleta awajan sayar da awarta sabida rashin m É—in data karta masa.
Tanajin sautin hirar mama dasu hassana ganin baccin baizo mata ba yasa ta miƙe zuwa gaban sif ɗinsu kayanta ta cire tai tik, tare da ɗauro zani a kirjinta sabida anyi ruwa garin yaɗanyi sanyi ita kuma bata kaunar kwanciya da kaya.
Harta koma kan katifar xata kwanta sekuma ta kuma komawa gaban sif ɗin tare da ɗaukar wata ƴar shimi wadda tsayinta ya kaimata dai dai ƙwaurinta.
Tube zanin jikin nata tayi domin aranta take faÉ—in gwara ta saka rigar sabida mama ta hanata kwanciya da zani domin tsakar dare zanin kama gabansa yake.
Ƙurawa farar fatar jikinta idanu tayi musamman wajan cinyarta inda har wani jajur tayi sabida farin wajan fatar ta irin lugwi-lugwi ɗin nan ce wadda idan ka dubeta bazaka taɓa zaton ta taso gidan wahala ba, sabida gogewa tare da murjewar fatar jikinta.
Bebi tana da wani irin baiwar kyau mai fisgar hankali, farace ita tas mai ɗauke da wani irin kyau mai ƙayatarwa matsagaiciya ce itaba doguwa can ba, kuma ita ba gajeraba, gashin kanta, irin mai curewar nan ne wanda yake bawa mutum wuya wajan kitso, domin mugun taurinsa shiyasa bata ƙaunar taɓa wannan kan ko kaɗan, kuma babu laifi tana da cikar sumar sedai rashin tsahonta.
Tana da gashin idanu zara-zara haka zalika girarta acike take,halittar kirjinta acike take sabida nononta irin mai ƙasan ƙwaryane waɗanda suke a tsaye ƙyam babu alamun zubewa atare dasu, gasu cikakku farare tas sedai ko kaɗan basu fidda kai ba saboda ƙarancin shekarunta.
Daga ƙasanta tana da cikar hip's wanda idan zata saka skirt wani zubin seda tsalle.
Bebi tana da kyawunta dai dai misali mai ƙayatarwa.
Saka rigar tayi ajikinta tare da nufar katifa tai kwanciyarta bata jimaba barci mai daÉ—i ya fisgeta.
Ko shigowar su mama bataji ba seda Asuba dataji mama tana tashinta a barci........................
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }
NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
*10*
Tsadaddiyar motace ƴar gaske black colour haka zalika window ɗinta ma tinted ne, irin wadda ake cewa sedai na ciki yaganka badai kai ka ganshiba, Fake take awani tangamemen bakin gate wanda aka rubuta *MAI ATAMFA INVESTMENT NGR LTD* da manyan harufa, cikin sauri tare da zafin nama irin na cikakkun maza masu jini ajikinsu matashin saurayine wanda baze gaza shekaru talatin da bakwai da haihuwa ba, dogone sosai mai murɗaɗɗan jiki irin na majiya ƙarfi hasken fatarsa baƙar fatace,mai ɗauke dawani irin gogewa tare da ɗaukar hankali, kallo ɗaya zakayi masa kaji ya kwanta maka acikin zuciyarka, sabida yadda Allah yayi masa baiwar cikar haiba tare da kamala, da ƙaton tabon abin sallah nafara cin karo shinfiɗe a saman goshinsa wanda har wani irin kurji kurji yayi sabida bayyanarsa.
Yana da manyan idanuwa masu haske tare da ɗaukar hankali, waɗanda kallo ɗaya zewa marar jin magana dasu ya hukuntashi hancinsa dogone mai ɗan faɗi kaɗan tare da ɗan baki ma daidaici, mai ɗauke da fararen haƙora tarr gwanin sha,awa, saman sumar kansa irin askin nan yay na manyan maza wato saisaye seɗan gemun daya bari kaɗan tare da sajen daya ƙara ƙawata masa kyawun fuskarsa,Sanye Cikin wata azabbiyar shadda wadda ta amsa sunan ta shadda mai kalar golden yake batare daya saka hula akansa ba, se takalminsa mai buɗaɗɗan sama wanda ya bada kala da ruwan shaddar jikinsa, cikin sauri ya buɗe marufin motar ya fito kunnensa kare da wata tsaddiyar waya mai mugun kyau, Hannunsa nabi da kallo wanda yaji manyan zobunan azurfa guda biyu gawata irin kwantacciyar gargasa databi saman hannun nasa har wajan tsakiyar yatsunsa ta lafe gwanin sha,awa da ita.
Cike da zafin nama yake taka ƙafafunsa wanda yabani tabbacin cewar cikin wannan kamfanin ze shiga duba da yadda ya nufi ƙaramar ƙofar datake kusa da gate, ɗin,fuskarsa babu wata far'a yake doka ƙaramar ƙofar da ɗayan hannunsa wanda bai riƙe wayar dashi ba.
Cikin sauri wani security yazo yaɗan leƙo da kansa ta ɓular datake tsakiyar ƙofar ganin wanda ke buga musu ƙofar yasa jiki na rawa yazo ya buɗe masa ƙofar tare da rissunawa yana masa barka da zuwa, cikin sauri ya wuce security ɗin batare daya amsa masa ba sedai hannunsa ɗayan daya kuma ɗaga masa still alamun baze iya magana ba, sabida wayar dake kare a kunnensa.
Tunda ya shigo cikin kamfanin ma'aikatan cikinsa ke kawo masa gaisuwa kowa ya gansa seya rage tsayinsa sedai kaji ana "OGA ALIYU barka da fitowa" wannan kalamin yana matuƙar ɓata masa ransa tayaya zasu dinga masa haka, bayan sunsan cewar duk ɗaya suke, wallahi jiyake aransa inda yanada yaddaze ya datse wannan girman da suke bashi dase yayi sabida sam bayaso amman rashin maganarsa da tsabar miskilancinsa yasa yagaza furta musu abinda yake ran nasa, to inama yake da lokacinsu bare ya tsaya yi musu bayani.
Wata ƙofa yabi mai girma wadda take ɗauke da wani ƙaton office wanda aka rubuta *MD ALIYU IDRISS MAI ATAMFA* da manyan baƙi, cikin sauri sakataren sa ya tawo gabansa yana zubewa tare da fara gaisar dashi cike da tarin ladabi hannun dai yakuma ɗaga masa tare da raɓewa yanufi cikin wannan office wanda yake ɗauke da table ɗin takardu daban wajan system daban ga kuma wani ɗan medium room nan duk acikinsa, saman wata one seater ya nufa tare da zama, yana cigaba da sauraran wayar dayake har seda ya ɗauki mintuna kafin yay sallama.
ÆŠago idanunsa yay waÉ—anda nima kaina seda nakusan yada abin rubutu na saboda kyawunsa daya gigitani, zubawa sakatare idanu yay wanda yake gurfane gabansa yana jiran yaji meze ce masa.
Cikin nutsatstsiyar muryarsa mai É—auke da kamala, wadda sam baya É—agata wajan fidda magana yace.
"Am sorry nura inaiwa baƙinmu bayani ne".
Yafaɗa ataƙaice.
Sosa kai nura sakatare yay tare da kallon ogan nashi kana yace.
"Haba dai oga wani irin nai haƙuri ai kafi ƙarfin haka,Yau ai naga baka shigo office da wuriba nace ko lafiya sabida oga usman ma yazo kusan sau biyar bai gankaba yace ya kira wayoyinka swich off".
Lumshe idanunsa yay tare da mayar da kansa baya kaÉ—an yana É—an sosa saman kan nashi da key É—insa dabai riga ya ajeba.
Tsaki yaja kaÉ—an.
"Motana ta samu problem ne yanzun haka tana bakin gate nima banso nai lates ba saboda nasan akwai new vistors dazamuyi yau".
Yafaɗa tare da zira hannunsa acikin pocket ɗinsa, counter ya ɗauko ya saƙala yana motsa baki a hankali wanda yabani tabbacin tasbihi yake ga sarki buwayi gagara misali.
"Haba nidai nasan oga inba wannan matsalar ba baka kaiwa har 12 baka shigoba Allah dai ya tsare mana kai".
Nura sakatare ya faɗa tare da kuma russuna kansa ƙasa.
Bai tankawa nuran ba kamar yadda nuran yasan da haka, sema ƙara mayar da kansa baya dayay sabida ko kaɗan shi mutum ne marar magana yafi buƙatar yayta istigifari a fili dazuci akan ya zauna yayta maganar da bazata amfane shiba, shiyasa yake mamakin jarabar surutun usman.
"Nura shigomin da files".
Abinda ya faÉ—a kenan tare da rintse idanunsa yana cigaba da tasbihinsa.
"Angama oga".
Nura yafaÉ—a cikin sauri ya tashi ya fita zuwa office É—in kusada dana ogan nasa.
Mintuna uku nura ya shigo hannunsa shaƙe da manya manyan files asaman table ya zubesu tare da rissunawa kana yabar office ɗin.
Wayarsa dake gefe itake ringing!
Da kallo yabita ganin mai kiran yasa ya danna busy.
Sannan yay dial number.
"Assalamu Alaiki, Eh naje Ammi ok, zan kira letter I'm busy now!"
YafaÉ—a cikin tattausar murya kana ya datse kiran ya nufi gaban kujerar dake fecing É—in wannan table É—in ya zauna tare da soma abinda ke gabansa.
Yajima yana gudanar da ayyukan dake gabansa.
Kafin yaji ana knocking dorr É—insa.
"Yes come in"!yafaÉ—a idanunsa kan takardun dake gabansa.
Wani magidancin mutum ne ya shigo bakinsa dauke da sallama.
"Haba tuzurun Ammi yau ina kashige ne kaƙi fito mana aiki da wuri gaskiya semunci tararka".
Cewar wannan magidancin daya shigo office É—in yanzu.
Wata harara ya zabga masa tare da haÉ—e rai tamau saboda ya tsani sukirashi da wannan sunan, baya so ko kaÉ—an amman yaga alamar yayyen nasa so suke su mayar dashi wani bitacan dan jiyama yana jin ya abbakar yana gaya masa hakan but amman bai tankaba.
"Kaga malam rabu dani in gama aikina wallahi gobe Abba ze dawo kada ka haÉ—ani dashi".
Dariya magidancin ya saki tare da furta..
"ALIKON ABBA kaima kasan abba baze maka komai ba, yau inda dai mune da mun banu".
Bai tanka masa ba kuma bai É—agoba illah cigaba da aikin gabansa dayake sabida yasan ya biyewa É—an uwan nasa USMAN sesu wuni ba,ai uwar komai ba.
"Oga Aliyu.................
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
  { _HOT LOVE_ }
     Â
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.