Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 12 of 81
*BONONZA BONONZA!*
*ÆŠAN MAJALISSA*
*RABON WANI*
*H A S K E*
KOBA SO*
*DA IZZATA*
_Dukkansu akan farashin naira 1000 document complt mai so seya tuntuɓi 08142105218_
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
  { _HOT LOVE_ }
     Â
     NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
           *14*
"Bebi kada fa ki makara a sallar asubahi nasan sarai kina jina Bebi".Cewar mama wadda ta miƙe daga wajan datake tsugunne domin tashin Bebi daga bacci, fita tsakar gida tayi domin haɗa sanwar awarar da tun ɗazu shahid yatafi kai markaɗanta bayan layi, Hassana ce ta idar da sallarta cikin sauri tayo tsakar gida ganin har gari ya soma haskawa ruwa mai sanyi ta ɗiba a randa cike da zafin nama taje ɗakin ta juyewa BEBI ajikinta shi tass, wani tsalle BEBI tayi tare da kwallah ƙara "Wayyo mama wannan wani ɗan.........", Sam hassana bata bari ta ƙarasa ba ta maketa "wai ke dan ubanki bakisan nagaba dake ba? toni na tasheki idan nima shahid ce",cewar hassana wadda ta zarewa Bebi Idanu daman hassana ita ba magana gareta ba sannan kuma bata fiye shiga sabgar bebi ɗinba sanin batada mutunci yasa bata bita kanta.
Tsitt tayi sabida tasan idan ta yadda muryarta tafi ta hassanar ɗaguwa tofa mama xata shigo haka kurum a zaneta da wannan sanyin safiyar shiyasa tai tsitt tare da tashi tana gunguni tayi waje, banɗaki ta shiga tafi mintuna goma aciki sabida jarabar kashin safiyar da Bebi take fama dashi kashin safe ya aureta duk safiyar duniya setayi aikuwa wari ya cika tsakar gidan sabida rashin wadatuwar faɗinsa, seda ta gama kashin sannan ta fito fuska jage-jage da hawaye wanda ba komai ke kawo matashiba se tsabar cin yaji shiyasa yake saka mata kashin ya riƙe yaƙi fitowa ta daɗi makilin ta lakata ta ɗora saman brush ɗinta tare da soma wanke baki sannan tayi alwala tayi cikin ɗaki aguje sabida sanyi.
ShinfiÉ—a abin sallah tayi tare da tayarwa tana idarwa tai azkar sannan taja hijabi ta koma baccinta hankali kwance.
Tsakar gida babu wanda yabi takan Bebi sabida idan da sabo sun saba da halinta, idanma suka tsaya tashinta tofa ransune ze ɓaci sannan ta ɓata musu lokaci a banza, shahid yana kawo markaɗan ya shiga wanka ita kuma mama tata ta somayi kafin ta ɗora tukunyar awara hassana tana dakan yaji hussaina tana wanke kayan da aka ɓata na abinci, su ihsan sukuma shirin makaranta suke ganin bakwai saura na safe, shahid yana fitowa shima shirin makaranta yayi, ragowar sauran tuwon jiya mama ta zubowa kowa amman banda su hassana sabida su ba fita zasuyi ba, iya shahid dasu ihsan ne kawai ta zubawa.
Suna gamaci sukaiwa mama sallama suka wuce makaranta.
Bayansu shahid sun fita, Hussaina dake kwaso kwanuka tana kaiwa kwando ita ta dubi mama tare da cewa.
"Mama wai ita Bebi ta daina zuwa makaranta kenan?,naga duk su sadiya suna xuwa".cewar hussaina wadda take kallon mama.
"A,a hussaina bata daina zuwa ba kuɗin jarrabawar datace nake son haɗa mata seta koma tukunna", mama ta faɗa tana yarfe gumin hayaƙin dayake keto mata idanunta yay jajur sabida zafin wuta.
"Lah wallahi mama ƙarya take babu wasu kuɗin jarrabawa kawai ita daman tace wai bazata kuma zuwa makarantar ba domin wai duk tafi ƴan ajin tsaho".
Cewar hassana wadda tagama daka yajin yanzu kuma albasa take yankawa.
"Au haka tafaɗa?,cewar mama wadda tsabar mamaki yasa ta miƙe daga sunkuyon datake."Eh wallahi haka naji tana faɗa jiya, amman nace zan gayawa yaya nura ko yaya Aminu". cewar hassanar.
"A,a barni da ita, jeki tasomin ita daga baccin datake".cewar mama tafaÉ—a cikin takaicin abin.
Koda hassana ta shiga ɗakin seda suka kai ruwa rana kafin Bebi ta miƙe ta fito tana hamma fuskarta duk tai wani irin alamun bacci.
"Mama ina kwana?,Gani angama abincin safe?".tafaÉ—a tana tsugunnawa agaban mama,
"Ban gama ba uwata nace baiwar bata gama ba, yanzu abinda kikai kinmin daidai Bebi rana zafi inuwa ƙuna ina tsaye dan ganin na rufa mana asiri ashe ke dan gidanku ƙarya kike ba,ace kuzo da kuɗin jarrabawa ba kika ƙi zuwa makaranta kinfison kullum kina ɗaukomin maganar jama'a?".
Cewar mama tana kallon Bebi cikin tsananin ɓacin rai.
"Nifa Mama nafi ƴan ajin tsayi, rashin kunya sukemin suna min dariya idan na daki ƴa seta kaini malaman suyita dukana", tafaɗa tana danna baki gaba dan bebi taƙi jinin zuwa makaranta sam arayuwarta.
"Aiseki zauna anan É—in ko kiyita zaga layi É—aukar awarar ma bawani abin kirkin kike ba".
Murmushine ya suɓuce mata sabida taƙi jinin makaranta tafi son tai zamanta gida wannan kalamin na mama baƙaramin daɗi yayi mata ba.
"Mama haka zaki barta, dan Allah mama kada kibiye mata wallahi seta koma ai ba ita ta haifi kanta ba".cewar hussaina cikin ƙufula tayi wannan maganar sabida bakaramin haushi Bebi ta bata ba.
"Dama Hussaina ai bazanbi ta kanta ba ita ɗin banza nadai saurari tatsuniyarta ne kawai kuma tayi ƙurun ƙus saura dame kuma?".
Mama tafaÉ—a tare da juyawa gaban tukunyar awararta tana buÉ—ewa sabida yadda yayo sama alamun tafasa.
"Kekuma ina ruwanki idan nai karatun hala ba kaina nayiwa ba?".
TafaÉ—a tana tura bakinta gaba.
"Malama rufe mana baki anan in ba hakaba Wallahi in zubdar miki da haƙora banza wadda bata san mutuncin kanta ba,ke kodan maƙiya bakya zauna kiyi karatuba.kinfison kullum fita tallah ana kallonmu ana zinɗanmu, ai kema kya samu ko candy ne kiyi kamarmu".duk wannan maganar hussaina ce kewa bebi ita cikin tsananin jin haushinta.
Mama tana jin hussaina tana mamakin kaifin hankalinta tabbas tasan yaran nata na tsananin son karatu sedai kuma ana takai waketa kaya.
Bebi batace komaiba illah juyawar datayi gaban tukunyar É—umame batare data tambayi nawa dana wa bane ta tsoma hannu ciki tana ci, "Lahh! mama wallahi bamuci bafa kinga harta kusan cinyewa".cewar hassana wadda tazo aje albasar hannunta wadda ta wankota,juyowa mama tayi tare da tafa hannu tana rafka salati, "Kubarta ana ranarta dan wannan tuwon rai ukune kinci harna rana kuma kika fita tallan awara kikaci Wallahi sena zane miki jikinki".Ko ajinkinta dan wannan tuwon jinsa take har cikin ranta daÉ—insa yana mata mugun yawa,tafarar É—aya tagama dashi tayi bakin rariya ta wanke hannu taje gaban randa ta É—ebo ruwa a kofi ta kafa baki tahausha gyatsa!tayi tare da hamdala ga sarki Allah kana ta juya zata tafi cikin É—aki.
"Dawo malama ubanwa kika aje ya wanke tukunyar?".mama wadda take zuba awara a mataci dan ta tsaneta itake wa Bebi wannan maganar,sanin batada gaskiya yasa ta juya tafi minti goma akan tukunya É—aya harseda mama ta kuma magana sannan ta É—aurayota ta zo ta ajeta"Hahaha cikin muka kawo duniya kasa uwar Æ´an bacci acici kenan babu abinda ake saurin ganin himmarki akai, kamarci".cewar mama kenan tana kokarin É—ora É—an murfin tukunya akan awarar sabida ta tsane ta yanka ta soma suya ganin lokaci yana ja kada su makara a tallan nasu.
Tana ƙoƙarin shiga ɗaki tajiyo muryar mama tana magana"Yau dai babu lokaci amman gobe ki shirya dan Aminu ko Nura zasu rakaki makaranta kimaji da kyau"! turo baki tayi "Nidai mama gwara an mayar dani aji huɗu kawai ko asamarmin aikatau natafi can na dinga kwana tunda bakwa sona".tana faɗi ta shige ɗaki tare da birkito da kayan kwalliyarsu tana son shafa powder ne domin tayi shirin fita tallansu...............
Hoda ta shafa asaman fuskarta tare da jan baki raɗau da kwalli acikin idanunta tayi kyau babu laifi, kaya ta sauya tare da saka hijabi ja ajikinta fitowa tayi tsakar gida lokacin mama harta fara suya, cikin sauri ta ƙarasa gaban ɗan bokitin da mama ke tara awarar zata ɗauka mama ta doke hannunta, cikin lokaci kaɗan ta kammala suyar tare da bawa su hassana wadda zasu karya saboda su basu sami tuwonba suma shiryowa sukai cikin hijabinsu tare da fitowa kowacce ta ɗauki tata awarar sukaiwa mama sallama suka tafi.
Bayan su hassana sun fita tattare gida mama, ta somayi tare da ɗan gyara inda ya ɓaci.
Bayan ta kammala komai zama tayi akan tabarma tana, tsince waken dazatayi abincin rana dashi, sallamar mace ce ta karaÉ—e É—an tsakar gidan nasu.
"Assalamu Alaikum mutan gida sannunku".cikin sakin fuska mama ta juyo ta amsa sallamar tare da saurin tashi ta kawowa matar tabarmar tana cewa.......
"A,a Rahane barka da zuwa yau agari ai rabona dake tun wancan adashin seda mukai magana da baba kwanaki tace wai kinje kauyene".mama ta faÉ—awa Rahane wadda ta shigo gidan yanxu:Rahane É—iyar malam lado ce ta biyu wadda take aure anan wajan fanshekara,
"Eh wallahi maman biyu, munje garinsu mijina ne,babarsa ce bata da lafiya yanxuma daman wata magana ce ta kawoni wajanki Allah yasa zaki fuskanceni".rahane tafaÉ—a tana kallon mama cikin nutsuwa.
Wuri-wuri mama tayi da ido"Kai gashi ba yara bare asayo miki pure water munan na randa muke sha keko baƙuwace".murmushi rahane tayi "A,a in xansha kya bani sabida nasha agidan baba yanxudai kibani hankalin ki nan kusa". tafaɗa tana kallon mama,"To ina saurarenki".mama tafaɗa tana baiwa rahane dukkan nutsuwarta.
"Yauwa kinsan babansu naxir yana aiki a kamfani ko?,to kinga da yana tsohon kamfanin mai atamfa ne yana musu aiki, yanzu kuma kwanan nan da yaran mai kamfanin suka dawo nan kano seya kuma, buɗewa anan sharaɗar kamfanin nika, da yaran nasa suna legos ne a ɗayan reshensa nacan, tsohon kamfanin sa na nan kuma babban ɗansa ke wajan to wannan sabon daya kuma buɗewa shine ya kwaso ƴaƴansa guda biyu suke riƙe dashi, to kuma se aka rago ma'aikatan wancan tsohon na mundaɗu, to daga cikinsu harda babansu nazir kinsan ya jima yana musu aiki, yanzu haka a wannan sabon sun ƙara masa matsayi, to matsalar abinda ke damunsu yanxu shine abinci, wajan yay ciki da yawa babu masu abinci, ma'aikatan wajan suna buƙatar masu kai musu abinci kinsan kamfanine na sarrafa atamfofi suna fitarwa ana kuma shigo musu da ita daga ƙasashen waje anan kuma suna hulɗa ne da manyan diloli na ƴan kasuwa daga jahohi kala kala, kin gane?".ta tambayi mama "Eh nagane mana haba waye bai san kamfanin mai atamfa ba, haba ai inajin sa a redio sosai".cewar mama wadda take sauraron rahane.
"Yawwa to shine babansu nazir ya tambayi ogansu akan suna son kawo mai cinikin abinci wajan, sabida su sami sauƙi kinsan aikin kamfani babu hutu kuma su manyan wajan babu ruwansu tunda su order suke yowa ko akawo musu daga gida, tokinga matsalar tana wajan ƙananun wajan tunda su babu wanda ze basu yace wallahi watarana sedai su sha lemo da biscut ko dai wani abun babu abinci ko kaɗan awajan, to ogan nasu ya amince yanxu haka da nice zan dinga kaiwa amman ya hana shine nace meze hana ki gwada sa,arki ma'ana ƴan biyu suna kaiwa can inkin dafa wataƙil Allah ya buɗo muku ciniki sosai kinga yafi wannan saida warar da batada ribar kirki............ amman ya kika gani dan seda na tambayi baba kuma tai murna babansu nazir kuma yana wajan kinga baze bar wata ɓaraka ba insha Allahu".
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.