Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 69 of 81

Iya ke tambayarshi hakan.
ÆŠago kansa yayi.
"Lafiyanta kalau ai bama gidane ita tacan É—ayan anguwar da gidana ke can insha Allah inna sami time senazo na kaisu can É—in".
YafaÉ—a yana kallon umma wadda take kauda kai gefe.
Shi dariya abin fa ya bashi ammi ko kaÉ—an bata kunyar surukanta wadda a haifema ta kusan haifar kamar maman amman ita jiba tama kasa kallonshi lallai yau yana ganin ikon Allah.
"To madallah Allah ya tayaka riko mungode sosai dan Allah kadinga hakuri da ita fa wallahi Bebi yarinya ce duka yanzu take ata sha bakwai se hakuri".
Murmushi yayi.
"Babu komai insha Allah, umma ni zan koma bakida saƙo?"
ÆŠagowa tayi sannan tace.
"Kace ina gaisar da ita kuma ta kula sosai, amman bara na zubo mata dambu akai mata".
Sauya yanayin fuskarshi yayi wadda ta nuna alamun rashin jin daÉ—i nan take.
"Umma har yau suna fita tallen ne?"
"A,a basa xuwa É—azu dai na saka akayi na dare"
Mayar da ajiyar zuciya yayi sannan yace
"Umma dan girman Allah kada su ƙara fita talle dan Allah umma, koda ban aureta ba tabbas inna sanku xan iya hana su fita talle to bare kuma yanzu da aure ya haɗani daku,insha Allahu da anjima zan aiko yarona yazo ya kawo muku saƙo sannan zan saka ai ma mai wannan gidan na gefenku magana naga ba mutane cikinshi se a haɗa a rushe da wannan a gyara muku pls umma karkimin fassara ta daban koda ba auratayya zan iya tallafar marayun Allah dan Allah karki musamin nagode"
YafaÉ—a yana mai kafeta da idanu yana hango tsantsar kamanninta da Æ´arta sedai ita mama akwai hakuri.
Kasa masa magana tayi seta miƙe tayi cikin kicin ta zubo mai dambun a ƙaton fulas ta kawo gabansa anan ta tarar da iya tana faman mai.godiya kamar zata ari baki.
Jin godiyar ike har ranshi dan haka da sauri ya mike tare da daukar fulas yana zira hannunshi cikin aljihunsa.
"Umma na tafi a turomin shahid ina waje".
Ya faÉ—i hakan sabida jin yadda bebi take ambatar sunan shahid shine yasa kai tsaye ya gane yaron
"Mun gode Allah ya tsareka Allah ya ƙara buɗi Allah ya rabaka da iyaye lafiya".
Mama ta faÉ—a tare da shiga É—aki sannan ta tura mai shahid É—in.
Fita yay ransa sanyi kalau sabida addu'ar da sukai mai yaji daÉ—inta ba kaÉ—an ba.
"Masha Allah maman Æ´an biyu arzikin ya soma sallama lallai É—an mutum mai rana komai tsiya haifi ka yar yara ku fito yau alkawairin Allah ya cika bilkisu ta haifu domin yau dai ga arzikinta ya fara doko sallama a gidan nan".
Muryar iya kenan wadda take faman zuba buɗa kamar zata zuƙo hancinta.............
AFUWAN NA YAU BA EDITINTG
11/14/21, 3:13 PM - Allah Akbar: *90*

Da sauri su hassana suka fito tsakar gidan kusan atare suka furta.
"Iya meya faru?"
Kafin kuma su nemi guri kusa da iyan suka zauna suna sauraronta.
"Hmm Æ´aÆ´an nan ba dole kuji ina buÉ—a ba wannan yaro anyi yaron arziki lallai Aishatu kinci wuyar Bebi a yarintarta ashe ga ranar daÉ—inta nan kowa zeji".
Anan ta fayyace musu dukkan abinda Aliyu ya cewa mama wanda kusan atare suka soma kabbara da hamdala ga sarki Allah.
Sumi-sumi mama ta fito daga cikin É—aki tana share hawayen farin cikin dake saukar mata zama tayi a gefen iya tana mai cewa.
"Ashe dai iya nima zan É—anÉ—ani daÉ—in hutu aduniya?".
Da sauri iya ta dubeta.
"Haba maman ƴan biyu sekace keba musulmaba? kintaɓa jin inda bawa yake yanke rahama a rayuwarsa? yoko Aljanna bawa baya fitar da rai da samunta bare kuma duniya, sabida haka ki ƙaddara daman can Allah ya tsara ta jikin ƴarki zaki sami jin daɗi da hutu ƴar takinma wadda kika fi cin wuyarta todai kinga yadda Allah ke juya lamuransa ko?".
Share hawayenta tayi tare da cewa.......
"Hakane iya amman wallahi nidai shekarun baya da suka wuce naci wuya kinsan girman Allah wani zubinfa abincin namu baya isarmu ni zan sha ruwa na hakura na basu sukuma waɗannan su hakura subaiwa ƙannan amman fa Bebi sabida jarabarta bafa zata bar ma kowa ba yadda arfa zata lamushe itama hakan takeyi wallahi iya saukinmu fa ɗaya lokacin da muka soma yin dambun nan ashema acikinsa silar firarmu daga wannan matsatsin take".
TafaÉ—a tana murmushin jin sanyi acikin ranta.
"Hakane daman Allah ya tabbatar mana da alkairinsa amin amman daman ai bayan wuya se daÉ—i insha Allahu shekara mai zuwa sekinje hajji a dalilin haihuwa".
Dariya suka kwashe da ita gabaki É—ayansu.
Nan da nan kuma hira ta kuma ɓarkewa cike dajin daɗi.

Shahid na fita ya hangi Aliyu harya kusan fita daga layin seda ya haÉ—a daÉ—an gudu sannan ya cimmai, Agaban motar Aliyu ya tsaya batare daya shiga ba sannan ya kalli shahid wanda ke kokarin russuna mai.
"A,a abokina baseka rissunamin ba, zaka iya bina kasuwar sunga, muje mu dawo kona haÉ—aka da mai napep zaka iya dawowa gida da kanka?"
Shikam dariyama maganar ta basa ina ne baya zuwa amman seya kame sannan yace mai.
"Ina zuwa har gaba da nan mama tana aikana dan haka babu matsala, amman dan Allah ka kaini nagano Bebi kafin nan".
Dariyar gefen baki yay yana mamakin yadda yaran suke son junansu sannan ya dubeshi.
"Ai ba,a kusa nake ba kafaÉ—i aiken naka zan gaya mata insha Allah, amman na sami lokaci duk zanzo na kaiku kuga gidan nata".
Dariya shahid yayi.
"Damafa ni zuwa zanyi naci ladan gaben idomie É—ina dataci min domin wallahi sena kwaÉ—eta".
Kama baki Aliyu yayi cike da mamaki ah lallai dole waccan yarinyar tai shirme yanzu wannan yayanta ne ke faÉ—in wannan kuruciyar kiri-kiri.
"To ai yanzu bazaka iya dukanta ba kamanta yanxu tanada aure, In indomie ce zan biyaka katan nawa kakeso abokina?".
Dariya shahid yay batare dayace komai ba, Aliyu ya bude mai mota suka shiga yaja suka nufi hanyar kasuwar sunga wadda ake sayar da kayan masarufi acikinta.
*************
Tunda Aliyu ya fita Bebi data shiga ɗaki tana masa dariya akan yace ze mata wanka bata kuma fitowa ba anan bacci ya kamata, daman kuma ga iskar gari wadda ake yawaita yinta kwanaki biyun nan sabida ƙarshen damuna dayazo sanyi yana kawo kanshi.
Ba ita ta shiba seda taji bugun gidan yayi yawa.
Tashi tayi tana zare idanunta waɗanda sukayi jajur dasu, sannan ta miƙe miyau fall bakinta seda taje ta zubda sannan ta wanke fuskarta, kana ta nufi wajan bugun buɗewa tayi tare da raɓewa,gefe tana kallon wata bakar mace wadda bazata gaza shekaru 30 ba marar jiki doguwa amman gani ɗaya zaka mata kasan cewar ta haɗa jini da ƴan mai duguri domin ga zanenta nan na kanuri ya fito a saman goshinta, ƴar gayuce ajin farko domin babu abinda jikinta keyi se faman zuba uban ƙamshi mai kwanciya a zuciya, se su mufida a bayanta.
Hannunsu É—auke da ledoji masu zane waÉ—anda alamun kayan miyane a hannun nasu.
Da far'a take cewa.
"Au mufida se yanzu kuka shigo min kun barni gida ni É—aya?".
TafaÉ—i hakan kamar ta jima da sanin yaran.
Gaba tayi suka bita abaya seda suka shiga tsakar gida sannan suka gaisa a mutunce da wannan matar kana tace mata.
"Ai su aymana suntafi islamiya ne yanzu suka shigo, Nice mamarsu sunana Nafisa amman ana cemin umman mufida, ni kaɗaice yaren hausa a gidannan ragowar dukkansu ƙabilune ma'aikatan kamfanin mijinki hausawan suna ɗayan gidan nashi na bayan layin nan".
Washe baki Bebi tayi tare da cewa.
"Kai amman naji daÉ—in kasan cewarmu anty nafisa Allah ya haÉ—a kammu amin".
Gaba tayi suka bita zuwa falon.
"Yawwa Anty Bebi ga wannan saƙon inji babansu yace ogane yace akawo kayan miyane amman bara na saka mufida ta gyara miki idan babu damuwa zan tafi dashi can naga da yawa senai miki dubara na dafa miki su yadda bazasu lalace ba".
Kallonsu tayi da murmushi.
"To anty nafisa nagode amman ku zauna mana naga kun tsaya kamar ba gida ba".
Dariya umman mufida tayi.
"Haba amarya magariba ta gabato naga ko gyaran gidan yamma ma bakiyi ba hala baccin gajiya kikene nasan ansha mota".
Hamma tayi kana ta fice waje tana ce musu tana zuwa.
Alwala tayo tazo ta tayar da sallar la'asar tana idarwa ta janyo É—ayan ledar abincin.
Babu yadda batai dasu ba akan suzo suci amman fafur sukaƙi sema faɗan da umman mufidan keyi na damme bata aiko an karɓa mata burabusko ba amman anjima zata aiko mata da abincin dare.
Godiya tai mata nan da nan taji ta aminta da umman mufida mace mai tsafta da gayu jitai ta ɗauketa kamar mama sabida yadda taga tana mata kamar ƴar uwarta ta jini( Allah ka haɗamu da mutane nagari masu halin girma masu sonmu domin Allah Allahumma Amin ) Harta gama cin abinci umman mufida tana zaune ba dai tai wata magana ba amman tana nazarin yarinyar wadda tashi ɗaya taji Bebin ta shiga ranta jinta take kamar ƴar uwarta ta jini, nan da nan taji aranta ta samu ƙanwa a kano tunda dai ita,ba ƴar garin bace kuma bata da kowa anan ɗin, Tunanin yanayin Bebin ne yaɗan bata mamaki taga yarinyar ƙaramace sannan kuma daga gani bata san komai na game da aure ba se tsabar wauta da zumuɗi kuma idan bazata mance ba kwanakin baya taji baban mufida yana ce mata oga yay aure ya auri cousins ɗinsa ba dai ta da masaniyar komai bayan wannan dan haka tasha alwashin koyar da Bebi wasu abubuwan kafin Allah ya rabasu domin tasan zaman nasu baze daɗe agidan ba kamar yadda mijinta ya gaya mata, ta ɗauki alwashin bawa bebi training na musamman akan rayuwar aure da tsafta da gyaran jiki kai harma da girki domin ɗa na kowane itama bata san mai mufidatan zata zama gaba ba.
Kallonta umman mufidan tayi cike da kulawa.
"Anty bebi yaushe angon naki ze dawo?"
Æata fuska tayi.
"Haba anty nafisa dan Allah kidaina cemin anty nifa wallahi Æ´arkice kicemin Bebina kawai"
TafaÉ—a tana rufe idanunta.
"To naji Bebi" umman mufida ta faÉ—i tana dariya.
"Yace ko anjima ko yaushe ma oho mishi".
Tafaɗa tana tura bakinta gaba wanda ya ƙara fiddo mata da tsantsar kuruciyarta.
"A,a Bebi, mufida kutashi anan kuje gida ku gyaramin kayan miyar nan akai markaÉ—e".
Tafaɗa tana mai basu umarni, wanda ba musu suka miƙe suka fita daga ɗakin.
Kamo hannun Bebi tayi ta riƙe da kyau tana fuskantar ta.
"Haba Bebi mijin kine fa ta yaya zakice bakisan ranar dawowarshi ba, bakida wayane?".
Tura bakinta tayi.
"Eh bani da ita"
"Shekarunki nawa Bebi?"
"Sha bakwai"
Ta bata amsa.
"Masha Allah Bebi nasan kinyi karatun addinin ko? kinsan haƙƙin mace akan mijinta kamar yadda namijin shima keda hakki akan mace wanda ya haɗa da, kulawa kyautatawa bin umarninshi sauke haƙƙin aure da sauransu, domin shi aure bautar Allah ne wanda se mun haɗa da hakuri a yayin zamanshi.................yanxu kin shiga sahun manya komai na hakkin aure ya wajabtu akanki tsafta kulawa kyautatawa da sauransu".................Sosai ta zauna ta fayyace mata komai na dangane da aure ta jaddada mata tsafta tafi sau uku tare da gyaran jiki dana muhalli, gami da iya girki.
Nan da nan jikin Bebi yayi sanyi har tanajin karayar zuciya.
"Ko kina son ya ƙaro miki amarya wadda zata na basa kulawa?"
Amamakinta setaga Bebi ta girgiza kai ma'ana bata so har tana haÉ—e ranta.
"To ki rage son jiki ki dage wajan kyautata masa kinji ko?"
ÆŠaga kanta tayi sama alamun yarda da maganar umman mufidan.
"Yanxu tashi muje kicin ki duba aga mai za,a dafa masa".
Anan wajan dariya tayi kana tace mata.
"Kai anty nifa ba wani iya girki nayi ba amman dai na iya taliya"
Dariya anty nafisan tayi atare suka jera suka fita tsakar gidan da taimakon anty nafisa aka haÉ—a gas É—in wanda daman an riga an zuba gas É—in acikinsa.
Kunna mata tayi ta taimaka mata da ɗan blanding ɗin kayan miya, batai gigin taɓa mata girkin ba amman ta tsaya akanta tana nuna mata yadda zatai harta haɗa jallof ɗin taliya wadda aka baza mata kayan ƙamshi tare da na ɗanɗano ga uban kifi, Bebi tana zuba taliyar cikin fulas tana haɗiyar miyaun ƙwaɗayi harta gama, anan umman mufidan ta kuma ce mata tazo su haɗa mai lemon abarba tofa mai hali baya fasa halinsa seta tura baki gaba ta soma dira ƙafa kamar a gaban mama.
( *Wayyo Hannuna wallahi kamar ya cire dan Allah karku fitarmin da page É—innan bani da lafiya haka nake daurewa domin na kyautata muku dan Allah kuji tausayin marainiyar Allah* )
"Nifa wallahi anty nafisa na gaji duk uban wannan kifin shi kaÉ—ai aka jibgawa komai shi komai shi nifa bazan haÉ—a mai wani lemo ba yaci haka".
Dariya anty nafisa tayi tana mata kallon ƙuruciya.
"To ina zuwa fitar da wannan kular anan sena gyara miki kicin É—in, kaita can falonki naga shi base an share ba".
ÆŠauka tayi fuska fall murna ta fice harda gudunta takai ta aje, cikin mintuna kaÉ—an maman mufida ta gyara kicin É—in.
Kana tai saurin komawa gidanta ta ɗaukowa Bebin turarukansu na can ƙasar maiduguri masu sirrika na musamman.
A falon ta tarar da ita batada alamun ko motsi.
"Ah bebi tashi maza ki shiga wanka ga wannan turaren ki zuba a rikita oganmu sabida oga ya gama mana komai Allah ya gani komai zamu mai baxamu biyashi ba".
Da taimakon maman mufidan ta shiga wanka tana fitowa ta kuma bata wata humra ƴar ƙarama tace mata ta shafa a ko'ina na jikinta, bayan ta shafa tace mata taje ɗaki ta shirya.
Wasu shegun ƙoɗaɗɗun kayanta na gida ta saka wanda seda umman mufida tai mata da gaske sannan ta koma ta ɗauko jakar kayan ta dire mata tana tura baki gaba.
Da kanta ta zaɓa mata wasu shegun riga da wando jajaye waɗanda jikinsu yake na karen miski.
Dama kayan a gumama ta taɓa siyosu lokacin an kwance a bayan layinsu to mama seta hanata sasu sabida yadda suka kame mata jikinta, shine ta ɓoye kayanta cikin ƙasan jakarta se yanzu da umman mufida ta ɗauko matasu.
"Ungo waÉ—annan ke waya gaya miki ana saka manyan kaya da daddare maza amsa kiyi ki shirya na gudu kar oga yazo ya ganni".
Dariya tayi tare da amsa haÉ—i da jakar tayi cikin É—akinta.
Sabida tsabar yadda kayan suka amsheta basu bata damar saka bra ba domin bata da muhalli a wajan sabida yadda kayan sukai mugun matseta wandon kwa da ƙyar ya shigeta sabida yadda hips ɗinta suka wani baje acikinsa daga baya kuma mazaunanta sukai wani irin tasawa daga saman rigar kwa baki ɗaya na shanunta sunyi wani irin ɓullutsowa kamar mai juna biyu.
Kallon kanta take sosai da hasken windon É—akin seda ta sami mayafi ta yafa sannan ta iya fita.
"Wow ƴata amman fa kinyi kyau masha Allah yau akwai drama keda oga ungo wannan shafa a kunnen ki da tsakiyar kirjinki, da kowani saƙo na jikinki"
ÆŠakin ta koma ta shafa azababban turaren wanda ya cika É—akin gaba É—aya.
"Yau Æ´ata bara na koma gida tunda komai ya kammala idan yaso gobe zan shigo na kuma gwada miki wasu abubuwan dan Allah kar aiwa oga musu"
ÆŠaga kai tai tare dayi mata sallama ita dai ta bitane amman bata gane ko musun mai take nufi bama.
Umman mufida na fita itama ta koma É—aki taÉ—an karkaÉ—e katifar ta gyaro É—akin sannan ta sako hijabi tare da fita ta É—auro alwala ta dawo ta xauna tana karanta azkar.
Amman tsorone fall ranta ga babu nepa ga kuma duhun magariba yasoma ƙaratowa.
Raɓewa tayi a saman sopa tana addu'a tare da neman tsarin Allah akan dukkan sharri gaba ɗaya mugun tsoro ya gama.cikata ga babu fitila gidan ga su mufida shuru.............

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.