Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 62 of 81
Sun jima cikin shuru harya kammala da kansa ya tashi yakai cup É—in kicin ya É—auraye ya kife sannan ya dawo ya zauna ya kalleta.
"Nagode ni zan ɗan fita ƙilan na dawo yau ko zuwa dare ƙilan kuma nakai gobe sabida haka duk abinda kike ciki ki sanar dani a waya banson yawan surutu pls ki zamanki anan banson ko part ɗin ammi kije da sunan kiran ƴan kwana domin akwai securties agidan wadatattu sannan kiyi addu'a Allah ne mai tsare kowa".
Yana gama faɗin haka ya miƙe tare da xube hannayenshi acikin aljihunshi yana kokarin saka kai ya fita daga falon.
"Allah ya tsaremin kai aduk inda kake amin amman ina zakaje har kwana?".
Basar da tambayar yay sabida bai shirya gaya mata sabon aurenshi ba sabida yadda ammi ta tsara dan yasan yana gaya mata seta gayawa umman ta ita kuma umma ta gayawa su alhaji daganan kuma abba yaji, sannan kuma bayajin ze iya yi mata ƙarya domin ba halinshi bane.
"Amin".
YafaÉ—a bai bata sauran amsar tambayar ba yasaka kanshi yabar falon se karar rufo kofarshi taji, Tattare wajan tayi sannan tai cikin É—akinta tanajin kewarsa amman sanin yadda sana'arshi ta business take na yawan tafiye tafiye yasa taji É—an dama aranta.
Kai tsaye part É—in ammi ya nufa har lokacin babu alamun mutanen gidan sun tashi sallama yay a falon ya tarar da ammi zaune tana amsa masa.
Zama yay a gefenta.
"Ammi har yau Æ´aÆ´anki basu tashi a bacci ba?".
Murmushi tayi kana tace.
"To babana ai yau basu da morning lecture kasan yau monday se wajan 1:00pm suke fita ita kuma amina ta kwana ciwon ciki itama bataje office ba wai zata huta shiyasa na barsu".
Sosa kanshi yay da keyn mota.
"Ammi da kamata yay su tashi suyi aikace aikacen gida wallahi mace setana miƙewa domin su ƙware karsuyi ƙazanta gidan mazajensu kinsan Allah yarinyar nan khadija na jinjina mata sabida tsaftarta hakannan naji ina ganin ƙimarta".
Murmushi ammi tayi tana kallonsa tana kuma gasgata maganarsa tabbas dukkan maganganunshi daya furta suna kan tubalin gaskiya mace duk yadda takai da girma da soyuwa a zuciyar mijinta wallahi in bata tsafta dole ze fara hangen wata daga karshe kuma yaji ta fitar mashi aransa idan kuwa baya sonta intana tsafta tana gyarawa tofa wataran za,a wayi gari aji tayi wuff da zuciyar mijin nata sabida babu wanda baison kyautatawa tare da kulawa wanda tsafta duk tana cikin waÉ—annan rikunonin.
"Babana ai tunda muka tashi da asubahi wallahi basu komaba seda suka haÉ—a break É—inda amaryarka taci É—azu sannan suka gyara part É—in abbanku sannan suka koma bacci waÉ—annan masu aikin daka gani munzo dasu É—azu girkin ma'aikata sukeyi banamu ba".
Se lokacin ya saki ranshi.
"Ammi harnaji daɗi dan banson naga ana kawo mana complain na ƙannenmu suna ƙazanta agidan mazajensu wallahi ammi banson mace ƙazama mai son jiki".
Yakai maganar har iya gaskiyarshi.
"To babana kai sa'ar khadija itama bilkisu ina maka albishiri da insha Allah tana da tsafta kuma zata maka biyayya kaidai fatana kazama jajurtaccen namiji wajan bawa iyalanka kulawa da adalci".
Murmusawa yayi yana shafa kansa da keyn motarshi.
"Amin ya Allah, ammi tana ina mu wuce kinsan fa se nama karɓi makullin key ɗinmu a wajan wani yarona acan ɗin".
Waigawa tai bata ga fitowar bebin ba.
"Jeka bedroom tana ciki tayi wanka ko tana jiranka ne".
Tashi yay tare da nufar bedroom É—in cikin sauri.
Sabida yafison suyi sutafi kada lokaci ya ƙure.
Zaune take abakin gadon ammi ta ware ƙafafunta a dai dai saitin fanka kamar wadda akama kaciya tana faman haɗa zufa batare data saka komai ajikinta ba, baki ɗaya fuskarta ta gama jiƙewa da ruwan hawaye dana majinar kukan zafin wuta...............
# *Autar Manya*
11/14/21, 3:13 PM - Allah Akbar: *83*
Wata irin azaba takeji acikin dukkan cinyoyinta sabida wutar turaren data gama ratsa mata jiki,wanda hakan ne ya kuma bawa fatar wajan damar ƙara yin wani irin jajur kamar jini ze zuba ajikinta.
Gaba ɗaya fuskarta tagama jiƙewa da ruwan hawaye dana majina se faman tura baki take gaba, tana kuma gunjin kukan da sautinshi baya fita sosai, sabida azabar datake ji acikin jikinta,wannan shine ma dalilin daya sa ta zauna a gefen gadon ta ware ƙafafun nata tare da ɗan zame tawul ɗin jikin nata tana karɓar sanyin iskar fanka dana Ac'n dake ratsa mata jikinta ko ta sami salama da irin yadda takeji ɗin.
Cikin nutsuwa ya murɗa handle ɗin ƙofar room ɗin, tare dayin sallama ƙasa-ƙasa wadda ko ita dake cikin ɗakinma bataji sallamar tashiba sabida yadda yay amfani da ƙaramin sautin muryarshi wurin fitar da ita.
Daga bakin ƙofar ya tsaya tare da zube hannayenshi acikin aljihun jeans ɗin dake jikinshi tsananin ɓacin rai yaji acikin zuciyarshi.
Tayaya shi yana can yana sauri domin su wuce sabida baya son abba ya tashi ya tarar da shi acikin gidan amman dan tsabar rainin shine tawani zube anan ko shiryawa batayi ba.
Tsaki yaja kaɗan yana mai tako ƙafafunshi izuwa gareta, Yana zuba mata kaifafan idanunshi masu cike da haiba gami da kwarjini, Tsabb ya kare mata kallo acikin daƙiƙun da basu gaza biyar ba.sannan kuma yagama fahimtar halin datake ciki amman a irin miskilancin sa seya basar kawai yana mai tsayawa agabanta ya tsareta da idanunshi yana kallon fuskarta.
Wani irin faÉ—uwar gaba taji acikin kirjinta sakamakon tsayawarsa agabanta wanda har hakan yasa ta kasa É—agowa gareshi kuma ta kasa motsi sema wani ruwan hawayen dake kara kaini bisa saman fuskar tata.
"Baki shirya ba?".
Taji saukar sassanyar muryarshi tana mata amo! acikin dodon kunnenta.
Daka ta amsa masa, ma'ana ta ɗaga masa kanta sama tana taɓe bakinta irin yadda yara ƙananu keyi in suna cikin rashin jin daɗin yanayi.
"Bana hanaki amsa min magana daka ba? kinason tun yanzu nasoma tsinin baki akanki ko?".
YafaÉ—a cikin kwantar da murya sabida yaga take-taken yarinyar baya son ya fiye É—aga murya akanta domin ya fahimci irin yaran nan ne masu mugun saka mutane yawan magana tare da basu ciwon kai.
"Ammi ce tabani turare nayi shine na ƙone anan sena zauna fanka tana huramin".
Yaji muryarta cikin rawa tana wassafo masa waÉ—annan bayanai kamar a cikin tsoron furucin.
"Ikon Allah to garin yaya kika ƙone ina wutar ba,a wannan abun naku na turare take ba?".
Yajefa mata tambayar cikin tuhuma
"Anan take man niba cemin tai na turara sosai ba".
Shi dariyama yarinyar ta bashi amman seya basar.
"Dayake ke shasha,shace yasa kika tura cikin ƙafafun naki ko?"
Mtssss! "Allah ya sawwaƙe ki maza ki shirya na baki five minutes ina falon ammi wallahi na kuma dawowa naganki haka sena bugeki".
Yafaɗa yana ƙoƙarin juyawa
"Nifa wallahi zafi suke man toba bani akai ba nikuma zance mata baniyi ne wallahi bazan iya tashi bani".
TafaÉ—a cikin sangartar data sabayi agidansu.
Juyowa yay tare da sakin baki yana kallon yadda take fici-fici da idanu tana murzasu kamar wata yarinya tsintar kansa yay da kureta da idanunshi yana kallonta seyaji yanayinta ya sakashi nishaɗi arayuwa yana son mace wadda ta iya shagwaɓa sabida shi feeling ɗinsa yafi karkata ga nan ɗin bare ita wannan da salon yay masifar bi da ita ya karɓeta ba kaɗan ba domin zata iya sakawa ya lalace mata anan yana kallonta.
Ahankali da wani irin sanyin jiki ya komo gabanta ya tsugunna adai dai saitin yatsun ƙafafunta tare da ƙuresu da idanu yana kallon tsarinsu acike suke musamman ta wajan agararta wanda yana da tabbacin tana daga cikin mata masu ni'ima tare da yawan buƙatuwa.
Itako ganinshi gurbane gabanta yakuma dagula mata lissafin dake cikin ƙwaƙwalwar kanta wani irin ƙullewa cikinta yay domin atunaninta ma dukanta zeyi shiyasa ta rintse idanunta gam-gam tana jiran taji saukar duka ajikinta.
Hannunshi guda ya ɗora akan ƙafar tata dai dai wajan ƙwaurinta batare dayay gigin ɗaga idanun nashi ba, sekuma can yaɗan ɗago kanshi tare da jefa idanun nashi asaman ƙwaurin nata yana son ganin ƙunar data ce tayi amman bai gani ba, wannan dalilin ne yakuma bashi damar kai ƙwayar idanunshi saman cinyarta wadda take jajur kamar ka taɓa jini ya fita.
Kusan a tare laushin cinyar da kuma azababban ƙamshin mayen turaren da ammi tace tayi suka bugi zuciyarsa hancinsa dakuma hannunshi daya ɗaga ya ɗora a saman lallausar cikakkar cinyar tata.
*AUREN BARE PART 2 NA KUÆŠINE IN KINA BUƘATA KI TUNTUÆI WAGGA NUMBER 08142105218*
Cikin furgici ta É—ago idanunta dake rintse ta zuba akan hannunshi dake saman cinyarta wanda yake cike dawani irin kwantaccen gashi wanda harya kusan xagaye yatsun hannun nashi se manyan zubban azurfa farare guda biyu, tare da wani irin agogon bakar fata dake É—aure bisa tsintsiyar hannun nashi.
Mayar da idanunta tayi ta rintse tana jiran taji kome ze mata a wajan.
Cikin wani irin dagulallan lissafin dabe taɓa ƙirga irinshi ba yake yawo da hannunshi bisa saman cinyar tata tare da ware faffaɗan tafin hannunshi adai dai saitin dayaga shatin jan tabon wutar.
Cikin wata irin cakuɗaɗɗiyar murya wadda tagama cika da zallar shauƙi ya furta mata.
"Rufe idanunki sosai zanyi maki addu'a a wajan Plsss".
YafaÉ—a a rarrabe yana jan ajiyar zuciya mai zafi.
Cikin tsananin tsoro ta kuma rufe idanun nata gam tana sauraran addu'ar tasa gareta.
Bakinshi ya É—ora a tsakiyar cinyar tata tare da saka hannunshi guda yaÉ—anja tawul É—in wanda yakuma basa damar ganin manyan cinyoyin nata waÉ—anda suke free babu komai jikinsu.
Jikinshine ya ɗauki wani irin zafi kamar gaushin wuta tare da wata irin tsuma kamar maijin zazzaɓi, kwantar da kansa yay duka a saman cinyar tata yana mayar da numfashi jin mararshi tayi wani irin ɗaurewa gam kamar zata rabe biyu, wanda tsananin zafin da jikinshi yaɗauka ne yaha naashi aiwatar da abinda ke zuciyarsa illah kwantar da kansa kurum dayay a saman cinyarta yana murza kansa a cinyar kamar yaro ƙarami.
Furzar mata da wata irin zazzafar iskar bakinshi yake wadda ita kanta tanajin hucin zafin fitar iskar bakin nashi sedai tsananin tsoro yahanata ta É—ago bare ta buÉ—e idanunta taga halin dayake ciki...................
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.