Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 39 of 81
***********
Yajima acikin bathroom É—in yana wanke jikinshi..........
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
  { _HOT LOVE_ }
     Â
     NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
            *57*
Kafin ya ɗauro babban tawul a ƙugunshi, kayan jikinshi kuma daya tube ya zubasu acikin washing maching, fitowa yay jikinshi na zubda ruwa sabida baiyi amfani da ƙaramin tawul na goge jiki ba,gaban ƙaton dressing mirrow'n shi ya tsaya tare da miƙa hannu cikin jerin cream's ɗin dake shaƙe bisa gaban mirrown agurguje ya ɗauki wanda yake using dashi ya goga a saman golden skin ɗinshi mai ɗauke da wani irin laushi da sulɓi, body perfumes ya fesa ajikinshi, gaban close set ɗinshi ya ƙarasa tare da ɗauko wani milk ɗin yadin tisue tare da singlet and boxer, shirya kanshi yay cikin yadin mai ɗauke da ɗinkin tazarce wanda yazo mishi har gaba da ƙwaurinshi, sabida shara-sharan yadin yasa har ana iya hango white singlet ɗin dake jikinshi, seda ya kuma yiwa kanshi ɓarin perf kana ya zira black shoe mai rufewar sama ya ɗibi wayoyinshi tare da makullin motarshi ya fita daga cikin bedroom ɗin lokacin ana ƙoƙarin tayar da sallar azahar domin yaji ƙarar loudspeaker masallacin cikin gidan nasu.
A daining area ya aje makullin haɗi da wayoyinshi da sauri ya sauka down stair har yana gudu sabida jin ana tayar da sallah, abakin famfon ƙofar part ɗinshi yay alwala da sauri ya nufi cikin masallacin tare da bin sahun jam'in sallar, Cikin nutsuwa suka gabatar da sallar azahar, bayan sun idar yajima yana addu'oinshi kafin ya nufi part ɗinshi upstair ya haye bakinshi ɗauke da sallama, Cikin azama khadija dake cikin kicin taɗan leƙo da kanta cike da mamakin yaushe ya fita? amman se bata nuna mishi mamakin nata ba, ganin saman goshinsa da ƴar ƙasa alamun sallah yayi yasa ta fito baki ɗaya daga kicin ɗin hannunta ɗauke da ludayin datake juya miyar cabbage ɗin datakeyi sannu da zuwa tai mishi kafin ta koma kicin ɗin.
Tunda ya hauro saman mayen ƙamshin girkinta yagama cika mishi hanci sosai ƙamshin girkin nata yay mugun fisgar tunaninshi, wata irin muguwar tsohuwar yunwar dayay ta dakonta ce take taso mashi, Cike da kasala ya ƙarasa gaban daining site ɗin ya ɗauke makullinshi da wayoyinshi saman three seater yazo ya baje yana shaƙar ƙamshin girkin nata wanda azahiri ka dubi face ɗinshi bakka cewa wai shaƙar ƙamshin yakeyi amman shi can cikin zuciyarshi shikaɗai yasan yadda yake son yaga mema take dafawar, daman last time bayan dawowarshi daga uk usman ya taɓa cemasa khadija ta iya girki sabida time to time tana kamawa ammi, amman seya gwasale usman ɗin bai bawa maganar mahimmanci ba, To seyanzu daya shigo ya tarar tana girkin dakuma yadda mugun ƙamshin girkin nata yagama kashe mishi hancinshi yasa yasoma gasgata zancen usman ɗin duk da baya tunanin ko ze iya kai lomar abincin nata cikin bakin shi.
Kwanciyar rigingine yay kanshi yana kallon white rufin pop ɗin falon nashi while hannunshi guda yay matashi dashi, ɗayan kuma ya rufe idanunshi dashi.
Yay kusan minti talatin ahaka, kafin yaji daddaÉ—ar muryarta wadda aka haÉ—ata da iyayi akai mata kwas-kwas ta doki cikin dodon kunnenshi.
"Assalamu Alaika habibina na barka kai É—aya afuwan".
TafaÉ—a tana haÉ—e hannayenta duka biyun waje É—aya, abinda yasa adukkan lamuranta take aro muguwar nutsuwa idan agabanshi ne sabida tasan shiÉ—in oga cin ubaka ne, bayason baragada abu kaÉ—an zaka masa ya kai maka hannu.
ÆŠago da mayun idanunshi yay waÉ—anda suke saka marar jin magana saurin nutsuwa.
Ya zuba matasu, wanda sauran kaÉ—an ta shiÉ—e sabida zautuwa.
Can cikin ƙasan maƙoshin sa ya furta.
"Jeki sallah".
Kana ya mayarda idanun nashi ruf ya rufe kamar bashi yay maganar ba.
Jikinta har yana rawa wajan nufar hanyar bedroom É—inta sam kaifin idanunshi ya mantar ta cewar tayi sallar harseda takai ga shiga cikin room É—in nata sannan, ta tuna ganin sallayar datai sallar a shinfiÉ—e bata ninke ba.
Sintiri ta somayi acikin katafaren É—akin nata wanda aka narka dukiya cikinsa.
Har wajan mintuna biyar tana faman saƙa da warwara acikin zuciyarta na yadda zata siye zuciyar Aliyu, batare data bar ƙofar wata ƴa mace ta shigo cikinta ba.
Sannan kuma tanason ta jawo hankalinshi zuwa gareta domin har yanzu bin umarnin ammi kaɗai, take gani acikin idanunshi amman bata ganin ƙwayar soyayyarta ko guda acikin idanun nashi, tofa sedai da gaske domin ta jawo hankalinshi gareta babban burinta yau ai second round ko Allah zesa ya bata kulawa kamar yadda ya kamata.
Jin kamar ƙaurin miyarta yasa tai saurin fita aguje, batabi ta cikin falon ba, setabi ta gefen kujerun har ta isa kicin ɗin nata cikin zafin nama ta sauke miyar, tata wadda ta wadata kayan lambu da nama acikinta, farar shinkafar data fara gamawa wadda ta adanata acikin katon flaks mai kyau ita ta ɗauko ta aza bisa babban farantin jera kayan abinci sannan ta ɗauko karami nanma ta zuba miyar, plate na cin abinci ta ɗiba guda biyu se saving spoon tare da spoon guda biyu se glass cup guda biyu duk haka ta jerasu akan babban farantin, ta nufi cikin falon bakinta ɗauke da sallama, akan center carfet ɗin falon, ta soma ajewa, kana ta mike a nitse zuwa daining area ta ɗauko ledar shinfiɗawa a saman carfet wadda akecin abinci akanta ta soma bazawa tsakiyar falon a hankali ta gama ta soma kwaso flaks da sauran kayan abincin ta jeresu reras tai decorating ɗinsu gwanin sha'awa.
Tsira mishi idanu tai aranta tana ayyana.
Ali xaki nawa ga tsoro ga ban tsoro nagama girkinnan amman na rasa yadda xanyi.
Gyaran murya tai! cike da salo takai hannunta dai dai saman yatsarsa guda tajashi daɗan ƙarfi, duk abinda take yana kallonta ta witsiyar idanunshi yana kuma mamakin yadda batada kawaici wajan miji.
"Habibi wake up food is ready!!." tafaÉ—a cike da salo.
Gyarawa yay yaÉ—an É—ago kaÉ—an yana ayyana ze saita mata burki.
ÆŠago mata jajayen idanunshi yay yana kallonta dasu waÉ—anda suka gama cika da xallar gajiya tare da bacci.
"Barni dan Allah bacci zanyi".
Da sauri taga ya koma ya kwanta.
"H........., bai barta takaiba yaÉ—an É—ago da hargagi.
"I said leave m......,Bata gamajin hargagin nashiba ta miƙe tai ɗaki jikinta na shacking, tana ayyana tsananin masifarshi wataran.
Tsaki yaja da ƙarfi aranshi yana cewa....
Yarinya se jaraba jibeta kamar tsinke amman jitake kamar ta cinyeni, bazanma ci abincin nakiba bare ki lalubeni ki kuma min illah cikin dare( hoho Aliyu É—an duniya kunjifa takuma masa illah cikin dare bama yay mata ba! Umm khadija anemi maganin sanyi domin ki rama abinda Aliyu yace ).
Mirginawa yay baijima ba barci mai nauyi ya kwashe sa.
Bar farkaba se ana kokarin kiran sallar la'asar wannan al'adarshi ce duk yadda yakai ga bacci ana kiran sallah seya tashi.
Bakinshi ɗauke da salatin annabi muhammad (s.a.w)ya farka, sauko da kafafuwanshi yay dayakejin sun ƙage sabida yaywa kujerar tsaho, baibi takan wayoyinshi ba, room ɗinshi ya koma still watsa ruwa yay as usual, Ali kamar agwagwa yake dason wanka,Wannan karon dakakken light blue ɗin yadin wagambari ya saka ɗinki half body, yaywa kanshi ɓarin ƙamshi ɗangaske, hular tangaran ya kafa akanshi mai kalar ruwan sararin samaniya itama seyay amfani da agogon zallar fata mai kusan shigen kalar kayan jikin nashi haka xalika takalmin dayasa ma kusan hakan, bakaramin mugun kyau guy ɗin yayba da gaske shigar ta amsheshi kamar wanda zashi gaisuwar surukanshi haka ya fita yana baza uban ƙamshi.
Yadda yabar komai na falon haka ya dawo ya tararsu wayoyinshi ya kwasa tare da car key É—inshi, harya nufi sauka seya tuna, da sauri ya nufi hanyar room É—inta.
Cikin nutsuwa, ya tura ƙofar bakinshi ɗauke da sallama.
Zaune take saman sopa tai tagumi abin duniya duk yagama yi mata yawa jin sallamarshi yasa ta miƙe a matukar tsorace.
Kokawa take da numfashinta sabida yadda yake mata barazanar ɗaukewa sakamakon tozali datai da gwarzon mijin nata wanda ya haɗa uban kyau mai cike da tsantsar kamala da haiba jitake kamar taje ta rungumeshi.
Jitake kamar ta dauwama ahaka tana kallonshi sakato tai da baki kamar wata sakarai tana kallonshi.
"Kin wani tsareni da ido kamar zaki cinyeni ni zan fita".
Yafaɗa a dake dominshi bai san lallashi ba kodan bai taɓa soyayyaba ne oho? shi ƙarewama ƴanmatan dake sonshi suke lallashin nashi.
Itako acikin ranta cewa take.......
Indama zan sami damar lashekan aida aikine mai sauƙi.
Amman afili seta ƙwaɓe fuska kamar zatai kuka tawani marai raice mai.
"Nayi maka abinci bakaci ba, Sannan kuma a ƙa'ida washe garin tariya ango ai bai fita".
Ɗage mata girarshi yay ta ƙasa kaɗan wadda ta saka khadija jada baya kaɗan tana ayyana you will kill me da wannan kallon naka.
"Hmmm inna zauna mizaki min tell me mizaki min Deejah?".
Yafaɗa dawani irin salo na yaudara yana ƙoƙarin cilla mata kaifafan idanunshi cikin nata wanda dasu yake gano weak ɗinta akanshi.
Wani irin armashi garsashi taji acikin dukkan sassan jikinta bata taɓa jin wanda ya kira sunanta da daɗi kamarsa ba wayyooo!! ze kasheni daso.
TafaÉ—a aranta.
Amman a bayyane setace.
"Nidai...nidai...kaci abincin to".
tafaÉ—a rabe.
Murmushin dabai shirya ba yay mata yana noticing ɗin mood ɗin datake ciki.
Ya hango tanada muguwar jaraba yarinyar domin ga ƙwayar idanunta nan harta harba sedai baya tunanin tana cikin jerin mata masu juriya domin daga jiya yaga zahiri.
"Bazanci abincinki ba, sabida yau ko break banyi ba nafita, so kuma bancin abinci kai tsaye dole sena É—ansha ruwan zafi, amman fa na yaba abincin naki dan naita haÉ—iyar miyau É—azu sedai dole zanje wajan ammi tabani ruwan zafi nasha ko hanjina ya warware ni zan fita zanzo miki da kazarki ta jiya da ban kawo ba, ai min afuwa".
YafaÉ—a direct sabida shi mutum ne sak! wanda bai rufa rufa ko gulma, sabida baya son barin abu cikin ranshi ko kaÉ—an.
Adashe yabarta harya fice bata zaunaba sema shaƙar mayen ƙamshinsa na gado datake.
Komawa tai ta zauna tana dafe saitin zuciyarta tare da matse cinyoyinta sabida azababben feeling É—inshi datakeji dole yau yasan yaze kumayi da ita domin ai ita shuka seda ban ruwa.......
Wajan ammi yaje amman kafin nan seda ya leƙa part ɗin umman khadija ya gaisarta, tare da karɓar accnt number ɗinta yay mata transper ɗin kuɗi masu kauri akan ta sallami ƴan biki aikuwa umma baki har kunne ta baje tana godiya, aranta tana yanzu muka fara tatsarka tai tunanin duk daɗin ƴartane yasa yay mata wannan kyautar sedai daman can Ali mutum ne mai kyauta dason kyautatawa amman rashin zaman guri ɗaya yasa umman bata fahimci hakaba, kuma babban dalilin dayasa shi yi mata hakan sabida bin umarnin iyayenshi shikuma yaga baya iya tashi batare dayay mata ihsani ba shine yasa yay mata wannan kyautar amman ita umma ai ta girmama abin harda yiwa ant ruma waya bayan ta bata labari ta kira khadija wadda itama abin ya daure mata kanta, duk da tasan kyauta halinshi ce amman tai mamakin daya baiwa ummanta kuɗi kodai ya soma sonta ne? da wannan farin cikin ta ware taci tasha ta cigaba da sabgar tarbar angon nata a karo na biyu........daga wajan umman khadija masallaci ya koma yay sallar la'asar bayan yay amfani da famfon bakin masallacin yay alwala yana idarwa yay part ɗin iyayenshi.
Lokacin dayaje part ɗin ammi babu kowa cikin falon nata, dan haka seya wuce falon abba zama yay suka gaisa da abba, cikin hikima abba ke kara nusar dashi hakurin zaman aure tare da kyautatawa iyali haɗi da fita haƙƙinsu sosai jikin Aliyu ya kuma yin sanyi duk da yana da ilimin hakan akanshi amman yadda mahaifin nashi yake kuma tunasar dashi yasa yakuma jin soyuwar mahaifin nashi acikin ranshi, Ahaka ammi tazo ta samesu itama zama tai suka gaisa dik da yunwar dake cinshi amman tsabar zurfin cikin tsiya ya hana yacewa ammi ta bashi abinci.
Seda ta haÉ—owa abba tea mai kayan kamshi sannan abban ya umarceta akan ta haÉ—owa Aliyun.
Aikuwa babu musu ya amsa bai dire cup É—inba seda ya shanye tass gumi ya keto mishi hamdala yaywa ubangiji, sannan ya mayar da hankalinshi ga tv inda ake watso labarai a tashar cnn.
Suna hirarsu da iyayenshi suna kallonsu cikin hikima ammi take kara nausarshi tare da nuna mishi mahimmancin auren dayay.
Har akai magariba yana tare dasu kafin su miƙe da abba suka fita, zuwa masallaci sabida shi yana da alwalarshi abbane kawai yay suka shiga cikin masallacin.
Bayan an idar da sallah suka fito tare da abba yana adai dai parking space yake cewa abba ze fita yaje ya dawo addu'a abba yay mishi ya wuce.
Yana ƙoƙarin shiga cikin motar sega usman ya fito daga wajan part ɗinshi, da sauri ya karaso bai tsaya wata wataba ya bude ɗayan side ɗin ya faɗa yana cewa.
"My man kai ga kanga kuwa wannan sheƙi haka kodai kodai".
HaÉ—e rai yay yana tada motar.
"Malam nifa nisa nai dalla fitarmin a mota karka cikani da surutu"
YafaÉ—a yana fisgar motar.
"Eh! nima fitar zan É—anyi amman tunda na sami driver kawai sena huta driving na shigo taka marar kunya ai yanxu dai dai kake damu tunda kaji abinda mukaji".
YafaÉ—a yana dariya.
Tsaki Aliyu yaja yana danna horn.
Cikin azama suka bude musu gate É—in ya fita daga harabar gidan tare da hawa titi.
"Malam ina ka nufa? ni nasarawa magaji rumfa kai a ina zan sauke ka?".
YafaÉ—a idanunshi tsaye bisa kwalta.
"Ni sharaɗa zaka saukeni zanje duba ƴan biyune sabida kwana biyu babu dambu madam ta riƙe wuta".
Tsaki! yaja tare da ƙarawa motar gudu...........
***********
Da sallama mama ta shiga cikin gidan nata Æ´an biyu suna tsakar.........
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.