Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 26 of 81

NA
*AUTAR MANYA*

_Albishirinku iyayen yara dama yaran baki ɗaya, shin ko kinsan shararriyar tashar nan ta youtube mai suna *Abdur-rahman* ta shirya tsaf domin baku gudunmawa wajan tayaku bitar karatun ƴaƴanku cikin sauƙi?, Kai dai/ kedai maza garzaya wannan shararriyar channel ɗin domin ki dannawa yaranki dansu karu da zazzaƙar ƙira'ar da *Abdur-rahma* ke gudanarwa wajan bitar karatun alkur'ani mai girma acikinta daman sauran littattafan addinin islama kada ki manta da danna *SUBSCRIBE* tare da ƙararrawar sanarwa mungode_
https://youtu.be/PFTnz8JGFfQ

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

*37&38*

Saman kwalta yahau É—oÉ—ar yana fafaka uban gudu, saboda zuwa wannan lokacin har ansoma yayyafi kaÉ—an-kaÉ—an ga kuma dare yayi motocin ma jefi-jefi ne suke wucewa, yana wajan kwanar ganduje, goslow ya rikesu har lokacin bai cewa Ali ci kanka ba shima kuma Aliyun bai tankashiba dama ya lafiyar kura.............
Seda aka sakesu usman É—in ya kuma jan motar dawani irin gudu azuciye kamar ze zubar dasu sannan ya É—ago yana kunshe dariyarshi.
"Haba angon zee baban ƙarnin gobe, meyay zafi ba wuta ba? zaka nemi ka zubar damu, dan kai kanada wanda ze maka addu'a aciki".
YafaÉ—i hakan cikin tsokana.
Aikuwa kamar jira usman yake yahau sababi.
"Yanzu dan tsabar baka da mutunci har ka iya fitowa kabarni a wannan bakin lungun inda Æ´an sara suka sunmin illah fa?, mezaka cewa my zee kai mata asarata kome?".
Murmushi yayi yana sauke ajiyar zuciya"kagama? daman akan wannan É—an abin kake tada jijiyoyin wuya?".
Yaja fasali tare da furzar da hucin cikin bakinshi.
"Wai nikam anya kaiko ɗan ammi ne? kai ina tantama, idan banda wauta irin taka kai baka san mata ba, baka taɓa ganinta ba daga ɗorin ɗosano ya haɗaku zakaje gidanta da wannan tsohon daren kamar kwarton daya rasa katanga..............,
Abin nakama bai tsaya a waje ba shine harda shiga gidan tare da zama kana zuba kamar famfon daya rasa maɗauri, kasan girman Allah! bada ban kajani ta ƙarfin cin tuwo ba babu abinda ze shigar dani cikin gidan mutane dan Allah ka dinga kintsa kanka wallahi wannan kwashe kwashen naka wataran seka ɗauko mana aljanu, haba kaga yanzu ka duba kagani ita kanta matar taji babu dadi da yarta ta fito ta samemu, amman kai ko ajikinka amai makon kabaro musu gidan ka fito waje a,a sema sake bajewar dakai nidai nagaya maka ka sauya halinka wallahi, kawai dan tsabar shirme zage zage damu muwani shige gidan mutane da wannan tsohon daren nikam ka cuceni wallahi ka cuceni".
Yafaɗa cikin daure fuska tamau kamar betaɓa dariya ba.
Wata shegiyar dariya usman ya saki sannan ya dubeshi.
"A,a nida gidanmu aini kuma naga wuri aiko nemata kukai baku ganni ba to kutafi can cigiyata wallahi tun tasowata bantaba ganin mace mai kirkin mamanmu ba".
"Sabida tai maka dambu, koko sabida jarabarka zaka dinga shige mata kana kalle mata Æ´aÆ´a a sadaka?".
YafaÉ—a batare daya kalli side É—in usman ba.
"Kai kasan wannan baya tsarina inada mata kamar zee aiduk mata fankone awajena, kaine ma dai nake ganin wannan ta É—azun taso tada maka da tsohon tuzurancika".
Wata shegiyar dariya ya saki ta rainin hankali sannan yace.
"Wa kenan? au ashe da wasu matan bayan ita mai dambun ai ban sani ba tell me plsss" yaja maganar yana haÉ—e hannunshi.
Haushine ya kama usman daman yasan rainin hankalin Aliyu seyay abu yay kamar bashi yay ba shariya tana ɗaya daga cikin halin sa wadda take mugun batawa usman rai ayau Aliyu ze ganka gobe ze iya nuna kamar bai taɓa ganinka ba.
Amman hakan yafi yiwa mata kodan yaga yanada farin jininsu ne oho.
"Bazaka gane abinda nike nuna maka ba harse wataran kaje ta liƙa maka wata acikin yaran nata tunda har tana ƙirga maka su, Allah yasa abaka wannan ballagazar marar kamun kan da kunya".
YafaÉ—a idanunshi rufe.
"Ban gane ba? kamar yaya kai harka zauna dasu duka kasan halin kowa?".
Murmushi yayi.
"Ko É—aya hasalima bani da sanin gaibu wannan Allah kaÉ—ai keda iliminshi".
yaja ajiyar zuciya ya furzar da iskar cikin bakinshi yana shakar sanyin motar.
"Amman kasan komai yana da alama, bana da tabbas É—in rashin kamun kai agareta amman akwai karancin tarbiya da kunya".
YafaÉ—i maganar kamar an fusgota.
"Akwai karancin kamun kai da kunya?"!!!
Usman ya nanata yana mamakin wannan maganar ta Aliyu, shifa baiga wani illah wajan yarinyar ba amman jibi uban Æ´an sharrin nan shi harya fassarata.
"Baxaka gane ba, matar ta bani tausayi a wannan zamani a rasu a barka da waÉ—annan yara ai tamayi wallahi".
Usman yafaÉ—a yana karya kwanar gidansu sabida harsun karaso ma.
"Seka aureta ka rike mata Æ´aÆ´an baki É—aya ubansu! Mtswwwwww ina familynsu sekai zarbai?".
YafaÉ—a yana É—aga kanshi sama yana kallon saman motar.
"A'uzubillahi nasan ba haramci amman ita É—in uwace agareni yakamata ka adana waÉ—annan bakaken maganganun agabana domin na hango tsana acikin idanuwanka daman kai katsani mutum ai yabanu, pls ka lafa musu".
Bai tankawa usman É—inba har suka shiga cikin gidan da taimakon masu gadin dasuka wangale musu gate É—in.
Cike da sauri ya fice a motar baiko tsaya É—aukar kayanshi ba usman ya bashi haushi over yadda yake wani xagewa akan waÉ—ancan mutanan shi sam baison shigewa mutum.
Tundaga bakin kofar falon ammi ya watsar da maganganunsu domin ya dauki abun shirme dan haka ranshi sakayau ya nufi cikin main falon ammi yana yin sallama abakinshi..............

_KUYI MANAGE DA WANNAN BADAI YAWA AMMAN ZE TAYAKU HIRAR DARE_
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }

NA
*AUTAR MANYA*

_Albishirinku iyayen yara dama yaran baki ɗaya, shin ko kinsan shararriyar tashar nan ta youtube mai suna *Abdur-rahman* ta shirya tsaf domin baku gudunmawa wajan tayaku bitar karatun ƴaƴanku cikin sauƙi?, Kai dai/ kedai maza garzaya wannan shararriyar channel ɗin domin ki dannawa yaranki dansu karu da zazzaƙar ƙira'ar da *Abdur-rahma* ke gudanarwa wajan bitar karatun alkur'ani mai girma acikinta daman sauran littattafan addinin islama kada ki manta da danna *SUBSCRIBE* tare da ƙararrawar sanarwa mungode_
https://youtu.be/PFTnz8JGFfQ

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

*39&40*

Cikin haɗaɗɗan takunshi irin na cikakkun maza, yaywa falon ammi dirar mikiya, Ammi zaune a saman carpet tana ɓarewa Abba banana ta juyo fuskarta tana ɗauke da ƙayataccen murmushi take amsa mishi sallamar dayayi, Abba wanda yake zaune daga saman one seater idanunshi sanye cikin medical glass sabida hasken computer dake aje asaman cinyarshi yana dannawa shima ɗagowa yay tare da aje computer a gefenshi fuskarshi ɗauke da murmushi shima yana yiwa Aliyu barka da zuwa.
Cikin wata iriyar sangarta wadda tai matuƙar bani mamaki takuma ƙamar dani har na tsawon wasu daƙiƙu, naga Aliyu ya nufi gaban abba da sauri shikuma abban yajawo hannunshi ya ɗagoshi ya mannashi ajikinshi cike da tarin farin ciki yake furta "Babana sannunka da zuwa! Babana yau ka sakamu cikin damuwa tun wajan 9 muke jiranka wallahi yanzu nake ayyana zan kira wancan yaron yabimin kai( abbakar kenan yayansu wanda su abba basa faɗin sunanshi sabida karar ɗan farko ).
Zame jikinshi yayi tare da jada baya kana ya tsugunna har ƙasa, ya juya gaban ammi wadda itama fuskarta take shaƙe da ɗunbin murmushin dake nuna zallar missing ɗin ɗan nata datai na two days sannan ya soma gaisar da ita cikin ladabi, yana kuma tambayarta yaya gidan?, sosai ta sake tana amsa mishi sannan ya juya gaban abba shima ya gaisarshi tare da tambayarshi yaya ya baro chaina cikin farin ciki abban yake amsa mishi da Alhamdulillahi, yana yi yana tsokanarshi.
Zama yayi a ƙasan carper tare da tanƙwashe ƙafafunshi yana jin gwara sunyi wani lissafi da abban yanzu tunda yana available akwai order ɗin dayakeson kamfaninsu na nan zeyi, cikin wannan watan daze kama to daman ya jima yana dakon abban bai sami ganinshi available ba kamar yau shiyasa yakeson yay amfani da damar daya samu ayanzun.
"Am abba daman zancen.......,
Bai barshi yakai ba.
"No babana kaje tukunna ka huta ai ina nan har zuwa satin daza,a É—aura maka aure, bazan koma ba. takanas na sami wannan hutun sabida auren ka, maza tashi kaje ka huta abincinka yana falonka na sama zuwa gobe semuyi maganar Allah yayi maka albarka kaida sauran Æ´an uwanka baki É—aya".
Ƙayataccen murmushi ya sauke wanda yake bayyana tsantsar kyawunshi sannan ya mike yana kallon iyayen nashi.
"To Allah ya bamu alkairi nagode ƙwarai".
YafaÉ—a yana rissunawa kaÉ—an sannan ya zira takalmanshi daya aje su a bakin falon tun sanda ya shigo hanyar samanshi ya nufa yana jin wata gajiya tai mashi caaa!
Abba ne ya dubi ammi cikin farin ciki yana cewa....
"Banida ra'ayin bambanci acikin Æ´aÆ´ana amman har ga Allah wannan yaron yafi kwanta min araina".
Fuskantar shi ammi tayi kana ta miko mishi bananar ya karba ya luntsumata abakinshi yana sauraranta tana cewa.
"Daman bambanta Æ´aÆ´a aishike kawo rabuwar kai, sedai kuma zakaga akwai wanda yafi faranta maka tokoda kana jin dadin hakan seka bar abin aranka kasan Æ´aÆ´a da kishi yanzu sekaji kai ya rabu, amman kowa yana son mai kyautata mishi ai abinda wasu iyayen basa ganewa kenan sakaga kiri kiri suna nuna bam banci acikin Æ´aÆ´ansu wanda hakan bakaramin tarwatsa kan zuri'a yake yi ba, nikaina Aliyu ya shiga raina fiye da tunani sedai ina dannewa sabida banson Æ´an uwanshi suga na nuna musu bambanci a tsakaninsu, sabida yaron nan iya gwargwado yana nuna mana mahimmancin mu na iyaye kasan girman Allah ko kaÉ—an baison wannan aure amman yadda yaga mun dage akai tuni yabi ya hakura da ita".
Ammi takai maganar tana kuma baro wata bananar, amman a wannan karon nata bakin taiwa masauki da ita.
"Haka ne Bilkisu! Allah yayi musu albarka baki É—ayan su".
Da amin ta amsa sannan sukaci gaba da hirarsu ta fahimta ita da mijin nata wadda rabinta akan Æ´aÆ´ansu suke yinta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.