Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 48 of 81

Mama tana shiga É—akin taga bebi ta kifa kanta tana kuka!
Ƴan biyu duk sun xagayeta suma gwanin tausayi sabida sunajin duk abinda ya faru.
Cikin rarrashi mama taje gabanta.
"Bebi maye na kukan tunda ALLAH ya ƙetarar dake auren wancan yaron, ina ba godiya xakiba da Allah ya kawo maki sauyi tare da fatarwa kanki Alkairi".
ÆŠagowa tayi tana kallon mama.
"Mama banfa sanshi ba, kenan auren dole kukai min sabida bakwa sona?"
Shafa kanta mama tayi.
"Koma waye zaki ganshi kuma a sannu zaki bam bance komai".
Kukan ta cigaba dayi.
"Mama nida ko miyar kuka ban iyaba sannan kumin aure".
Duk da mama tana cikin damuwa amman seda ta dara da shirmen bebi tana raya Allah yasa Aliyu ya iya da shirmen Æ´ar tata.

Can kuwa gidansu tasi'u matansu ne suka shirya tsakar gida tare da shinfiɗa manyan tabarmai na karɓar baƙi ƴan kawo lefen da za,a ɗaura auren gobe, ƙarfe ukun yammacin ranar............

*Afa shirya daren nan yaya Aliyu zeji maganar É—aurin auren da usman yay masa jagaba ayi? wanda shi bai san dashiba? hohoho harna hasko madam bebi tai ido biyu da gadanga a wannan dare a matsayin mijinta*...............................

SU TASI'U KUNA RUWA FA
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *PART* 2

NAKUÆŠINE

*68*

Ilahirin matan su tasi'u sun halarci zaman karɓar lefen har faɗa ake a tsakanin matan wannan tana cewa in aka kawo a ɗakinta za,a aje wannan nacewa in aka kawo a ɗakinta za,a aje sabida baƙin ƙudirin dasuka saka aransu na in aka aje a ɗakin kowacce zata saci wanda ranta keso.
Matar tasi'u ce ta miƙe tare da kallon sauran matan.
"Waini wannan maganganun da kuke duk kunsan na banxane sabida wannan dai aure mijina shine sanadin sa dan haka ko wacce taja gefe babu wadda zamu aje komai a É—akinta".
Tafaɗa tana girgiza kamar wata ƙaura, shewarsu ce ta karaɗe tsakar gidan kafin ƙanwarsu tasiu mai suna suwaiba ta janyo matar tasiun tana mata magana.
"Haba keko lantana wannan fiffiƙa da kike duk bai daceba yanzu a misali kina cikin wannan faɗan matan dazasu kawo lefen su shigo dan Allah bakin bamu kunya ba".
Wata harara lantanar ta watsowa suwaiba tana cewa.
"Kinga nifa bazaki min ƙasa da muryar munafurciba duka ay gayyar mun santa kowa soyake arzikin yaje ɗakinsa dan haka ni banƙi suzo su ganni anan ba maye to abinda lefen rabewa zamuyi agidan".
Dariya duka sauran matan sukai tare da buÉ—a sannan kuma wajan ya kaure da cece kuce sabida suwaiba tace lantana tayi mata rashin kunya.
Sosai wajan ya hargitse da faɗace faɗace har seda rabi'u ya fito daga majalissar dasuka dasa ta zaman jiran karɓar lefe ya shigo gidan ya tsawatar masu.
Tare da rufe suwaiba da faÉ—a yana cewa ina ruwanta da matansu, tana babba ai seta kama girmanta.
Ataƙaice dai suwaiba harda kukanta awajan tana cewa ai sun firfita matansu akanta, da ƙyar ƴarta dasuka zo tare ta rarrasheta sannan tai shuru shikuma rabiun ya fita ya barsu.
Ni kaina abinda na fahimta su kansu a junansu su tasiun babu shiri sosai a tsakaninsu kawai ta ciki na cikine.
Ƙarfe ukun ranar manyan santala santalan motoci masu kyau da tsari har guda uku sukai dafifi a ƙogar gidan marigayi alhaji muhammadu mai katifa.
Cikin rawar jiki tasi'u ya sheƙa a guje gaban baƙar siyanar farko ya buɗe yana zabgawa wata gajerar mace baƙa kirari tare da fadanci irin na masu maula.
Cikin yauki da gwalli wannan matar ke umartar shi daya kirawo yara su kwaso akwatunan, kafin wasu mata suma guda biyu suka fito daga bayan motar.
Ragowar matan cikin sauran motocin suma suka fito tare da xuwa gaban wannan matar suka tsaya cikin rawar jiki tasiu ya kirawo sauran ƴan uwanshi cike da ƙawa zuci suka buɗe boot ɗin motar suka soma fito da akwatuna masu kyau har guda goma sha biyu.
Banda manyan jakunkuna na gana masgo, guda uku da sauri suke shigar da kayan cikin gida har suka gama abinda ze baka mamaki yadda waɗannan matan suka tsaya ƙyam a wajan batare dasun shiga cikin gidan ba a ƙyamace wannan bakar matar tace
"Base mun shiga ba wannan zuwan ma dan Alhaji ya takuramu ne, mun saka biki nan da gobe ina amaryar zamu tafi can da ita sabida gyaran jiki?"
Wani gumine ke ratsowa tasiu sannan ya aro jarumtar cewa.
"A,a ai tana can wajan uwarta dama se goben zamu É—auko muku ita".
Batare data kula da maganarshi ba taja tsaki kaɗan tare da faɗawa mota sauran ma suka mara mata baya haka ta badesu da ƙura tabar wajan.
Jan ajiyar zuciya yay mai ƙarfi tare da baza rigarshi yayi cikin gida, daman bai bada damar taɓa akwatunan ba harse da ya shigo gidan hakanan sauran suma suka shigo cikin gidan, zama tasi,u yay agefen akwatunan tare da fito da wayarshi waya sukai ta mintuna goma kafin ya miƙe ya fita waje.
Se gashi nan tare da wani magidancin mutum, buÉ—e masa akwatunan yay yana É—aga masa kayan dasuka kusan zauta jama'ar wajan seda mutumin ya gama É—aga dukkan kayan sannan yaÉ—an jawo tasiu suka fita waje.
"Kayan sunmin daman kasan akwai wanda ya bani order haÉ—a mashi lefe nan da sati biyu".
Cikin murna tasi'un yace.
"To yanzu yaya kenan kuÉ—insu xasu kama sabida nagaya maka ni kudin nakeso ko?".
Murmushi mutumin yay tare da cewa.
"No karka damu kayan sunmin kuma zaka sami alkairi mai yawa sabida kayan masu kyau ne".Batare da ɓata lokaciba sukai cinikin kayan lefen cikin farashi mai tsada wanda harya saka tasi'u suman wucin gadi.
"Yanzu naxo da motana xan É—ibi kayan inya so gobe wajan yamma sekazo shagona nan inda ka ganni seka amshi kudin naka ko?".
Cikin zumuÉ—i tasi'un yace.
"To!to babu matsala muje semu taimaka maka da É—auko ragowar".
Cikin jin daɗi mutumin ya shiga gidan yana marawa tasiu baya, su rabiu suna zaune sukaga anan fitar da akwatun suna tsoron suyi magana tasiu yaƙi rabon kuɗi dasu.
Har suka gama kwashe kayan sannan, sukai sallama da mutumin yaja motarshi yabar gidan.
Seda ya shigo yana share zufa sannan sani ya dubeshi.
"Ni naga ankwashe kayan nan ina zaka kaisu?".
Murmushin mugunta yay sannan ya dubesu.
"Dukkan abinda ze kawo mana ɓaraka bana sonshi dan haka na kirawo maƙocin gidan da aishan take akan yazo ya ɗauki kayan nan ya kai masu can kunga gobe ƴan ɗauri aure kowa zega lefen nan daganan semu kwashe kayanmu kunga mun fita ko awajan alhajin ne koya kukaga?".
Dariya matarshi ta sheka sannan ta rangaÉ—a buÉ—a.
"Kai lallai banyi auren banza ba nagode Allah daya bani makirin miji tabbas wannan shawara taka haka take baban ladi da larai".
Ragowar matan ma da mazan dariya sukaitayi suna yaba wayon tasi'u tare da dubararsa suna kuma ɗaukin ganin gobe kodan yadda zasuyi babakere da wannan dukiya da aka sheƙo masu ta banza.
Kallon marasa wayo sakarkarun banza yake masu yana danne abinda ke ranshi ya tsallake yabar tsakar gidan yana saƙa mugun nufin dake ranshi.
Ni zasu É—auka wawa naje nayo farauta sannan muyi raba dai dai to baku isaba waÉ—annan kaya sun tafi har abada, nidai fatana kawai mu haÉ—u gabaki É—ayanmu mu É—aura wannan aure daganan kuma watan rashin mutuncina ze motsa akanku, sabida amfaninku ya kare gareni, shiyasa wancan ma kudin farkon na raba komai gida biyu na danne rabin na barmaku rabin mahaukatan banza da wofi, nan kwanaki uwata data rasu rasa wanda ze sai mana kokon zaman makoki akai acikinku ko kun xata ni wawa ne.
Yana tafe yana faÉ—in wannan maganar a ranshi harya karasa wajan mai tsiren dayake zama lokaci zuwa.lokaci ya zaro gudar dubu sabuwa dal wadda ya zare acikin kuÉ—in daya danne irin wanda ake sakowa asaman kayan lefe batare daya bari sauran sun ganiba tsirenshi aka yanka masa yaja gefe yana cin abinshi hankali kwance.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.