Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 38 of 81

"Hahahaha"!!
Sautin dariyarsu.
"Bamuda lokacin ki Aisha inma zaki mike muci arziki tare to in kuma zaki tsaya gaddama ne to muzuba mugani kinsan taƙadirancin mu haka zalika kinsan muɗin kosu waye mu zuba mudake rana ita yau zata bayyana kanta"!!

KaÉ—a babbar rigarsu sukai suka fice tare da turo yaran É—azu suka kwashe masu kayan da suka zo dasu.
Da baya tasi'u ya dawo ya kwashe kudin auren.
"Bazama mu baki komai ba matsiyaciya kuma wallahi semun É—aura wannan aure kozaki mutu....................

_MEKUKE TUNANI_ ?

*INA JIRAN SHARHINKU*
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
    {  _HOT LOVE_  }
           

         NA
*AUTAR MANYA*

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

                        *56*

Da baya mama taja tana dafe bango kafin kuma ta zube a ƙasa tana fidda numfashi sama-sama, tanayi tana jan wata irin ajiyar zuciya mai ƙarfi,cikin tashin hankali duka yaran nata sukayo kanta suna kuka! ɗagota hassana tayi tare da aza kanta bisa cinyarta, Bebi wadda taji dukkan zazzaɓin jikinta ya sauka sabida ganin halin da mamansu keciki ita take kiran sunan maman.
"Mama dan Allah kidaina wannan ajiyar zuciyar kar wata cutar ta kama mana ke mama ke kaÉ—aice garemu".
Kuka! Suke suna kallon mahaifiyar tasu wadda babu abinda take face faman sakin ajiyar zuciya ta jima ahaka kafin tabi hussaina da kallo.
"Maza ki ɗebomin ruwa nasha innalillahi'wa'inna'ilahirraju'un"! maman ke faman faɗi afili tunma kafin takai Bebi tariga hussaina isa gaban randa kofi ta saka ciki ta kindimo ruwa tazo gaban mama ta tsugunna tana zubar da ƙwallah ta miƙa mata.
Seda tasha sosai sannan ta miƙe daga jikin hassana ta shiga ɗaki minti ɗaya ta fito ɗauke da mayafi da kallo tabisu.
"Zanje gidan malam ku gyara gidan kafin na dawo".
Tana gama faÉ—in hakan ta fita ranta duk babu daÉ—i duk jikinsu babu daÉ—i suka bita da "to".
Da sauri Bebi taja mayafin ihsan ɗan ƙarami ta yafa a saman doguwar rigar  jikinta tabi bayan mama cikin ɗaga murya hassana tana kiranta akan tazo ta sauya mayafin sabida ko bayanta bai rufe ba amman sam taƙi dawowa.
Abaya abaya   takebin mama ko tafiyarta ma a hankali takeyinta har mama ta shiga gidan malam wanda lokacin ana gab da kiran sallar magariba ne domin malam lado ma yana kofar gida yana alwala ze shiga masallaci dalilin dayasa mama bata kulashiba ma kenan dan haka ta shige gidan.
Sallama mama tayi acikin gidan bayan ta shiga.
Babace ta fito daga banÉ—aki hannunta rike da buta tana amsawa mama sallamar cikin karamci.
"A,a maman biyu kece da magaribar nan to lale maraba shigo kiyi alwala  malam ɗin yana waje".
Baba tafaÉ—a tana kokarin É—aukowa mama tabarmar dake jingine a gefe É—aya.
"Eh! Naganshi ai awaje shiyasa banyi mishi magana ba nima bara nayi alwalar"
"To ƙaraso a,a wanake gani kamar mai gado? kice tare kuke da ita?".
Cewar baba......
Se asannan mama ta lura da bebi wadda take buya a lokon tsakar gidan.
Girgiza kai kurum mama tayi tarasa wannan ƙulafuci na bebi.
Zama Bebi tayi akan tabarma sabida tana fashin sallah gobe dai take saka ran wanka tunda ya É—auke, ita kuma maman ta É—auki buta ta shiga banÉ—aki domin É—auro alwala.
Bayan ta fito ta shiga É—akin baba tai sallah.
Bayan sun idar  baba ta fito musu da fitila ta aje itama maman ta fito waje kusada bebi ta zauna, mintuna kaɗan baba ta dawo hannunta ɗauke da kwano wanda ta zubo musu tuwo a saman kwanon se miya a ƙasa.
Direwa tai tana cewa..........
"To mai gado ga tuwon baba tunda kwana biyu kinƙi zuwa bare kici abokiyar faɗa".
Dariya! mama tai kaÉ—an.
"Ai mutuniyar taki babu lafiyane kwana biyu anyi zazzaɓi gakuma makaranta data koma sabida, taƙi bin ƴan uwan nata".
ÆŠan sauya fuska baba tai.
"Allah sarki ai banida labari da banzo dubiya ba, abinka da mai garin jiki bata faÉ—a ba sedai idanunta daya zurma ciki kaÉ—an".
Nan dai suka cigaba da tattaunawa ita kuwa Bebi jan kwanon tai gabanta, tare da tashi ta wanko hannunta tazo ta zauna ta bude tuwone miyar kuka babu wata wata tasoma cin abinta sabida daman kwana biyu bataci abinci ba, duk da bata ƙaunar tuwo amman tana son tuwon bana yana mata daɗi.matuƙa.
Sallamar malam lado ita tasaka suka tsagaita da hirar tasu.
Cikin sakin fuska tare da mutun taka malam ya ƙaraso suka gaisa da mama sannan tace.
"Daman wajanka nazo".
Murmushi yayi irin nasu na manya sannan yace.
"To'to shigo daga ciki Aishatu, Ince dai yaran duka lafiya?". yamike ya shiga É—akin nashi tare da kunna fitilar wayarshi.
Miƙewa tai tana cewa "Lafiya ƙalau muke wallahi".
Ta bishi cikin É—akin.
Zama tayi agaban malam suka kuma gaisawa sosai sannan ta kalleshi cikin nutsuwa ta wassafa mishi duk abinda ya faru tass bata raga ba kuma bata ƙara ba.
Seda yagama jin duk abinda ta faÉ—i sannan yace.
"Banyi mamakin abinda sukai ba sabida suɗin marasa kunya ne to inba rashin kunya ba tayaya, se bayan da kika gama wahalar ƴaƴanki sannan suzo suce zasu miki ƙarfa-ƙarfa akansu ina baze yuwu ba, wannama maganar banza da wofi ce Aishatu".
YafaÉ—a yana hucin takaici.
"Ni duk bama wannan ba malam kasan dawa suke kokarin haÉ—ata?, wai É—an gidan Alhaji mai gwall na nan bakin sharaÉ—a".
Cikin sauri malam ya xaro idanunshi.
"Wannan yaron mara kunya Allah ya kiyaye ki bari gobe insha Allahu zanje can Æ´an kusan wajansu muyi magana duk yadda muke ciki sena gaya miki".
Da kallon tausayi tabi dattijon.
"A,a malam ka bari zan nemesu ai bakaje da tsufanka canba haba ai kaine gaba damu".
Murmushi yay.
"Babu komai ki bari dai Aishatu Allah ya shiga lamarin namu amin, sekuma maganar Æ´an uwan nata ina dai kinsan da wasiyar marigayi ko?".
Jim mama tai cike kuma da ƙarfin gwigwa tace.
"Na sani malam hassana daman ita Aminu aka baiwa ita kuma hussaina nura ai maganarsu tana nan mun bari zuwa karshen shekarane kafin nan kaga duk yaran sun kammala bautar ƙasarsu se ai magana, tunda kaga iya mazan nema suka sani amman ƴan biyun ma basu sani ba".
Cikin gamsuwa yace.
"To madallah babu komai Allah ya kaimu lokacin Allah ya rufa asiri amin".
Sallama sukai sannan ta fito tsakar gida tanaiwa baba sallama Bebi harta soma bacci mama ta tayar da ita "Karfe takwas na dare kin soma bacci maza muje gida".
Sallama sukai da baba suka fita bayan sun ƙarƙare da malam akan gobe  zeje can ƴan kusan ainihin gidansu mahaifin Bebin inda su tasi'un suke ciki yaje akan soke maganar  auran da suka zo dashi.
Tafiya suke ga garin babu nepa ko ina duhu adai dai gidansu sadiya Bebi ta coke"Mama dan Allah zanje gidan iya sabida maganar ankon maulidinmu kinga kwana biyu banje makaranta ba kar naje ko an fitar bana nan".
TafaÉ—a tana kokarin shiga gidan.
"To kada ki daÉ—e kinji ko sannan kar kicewa iya tare muke sabida ni bazan shiga ba nasan na shiga gidan se wajan goma zan fito".
Mama ta faÉ—i tana wucewa, ita kuma Bebi ta shige gidan aguje!.......

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.