Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 21 of 81

_LEGOS_
Safiyar asabar kwance yake.............

_MUTARA A NEXT PAGE FANS_
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }

NA
*AUTAR MANYA*

_Afuwan my fans nayi mistake É—in number wancan shine 25&26 wannan kuma 27&28 afuwan_

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

*27&28*

_LEGOS_
Safiyar asabar kwance yake a saman sopa ya miƙe ƙafafunshi waɗanda har zubowa ƙasa sukai sabida tsahonsu ya wuce tsayin sopar, jikinshi sanye da milik ɗin jallabiya mai yankakken hannu sam bashi da niyyar tashi bare yasan abinda zeyi, gashi tarin abubuwa masu mahimmanci sunyi mishi caa! agabanshi gashi a yau ɗin yakeson wucewa kano, ko bokking ɗin jirgi baije yayi ba, amman yana ganin hakan babu matsala sabida yana da mutane a airport ɗin yasan dayayi waya za,a tanadar mashi, saukinta ma yau ya umar ze biyo jirgin dare shima ya tawo nan ɗin abbansu kuma shima dai still yau ze biyo jirgin dare daga chaina zuwa kano,ɗago ƙwayar idanunshi yayi wadda saman idanun nashi ya cika da yalwatacciyar suma zara zara, ya dubi tamfatsetsen agogon dake manne da bangon ɗakin, cikin sauri ya miƙe yana fito da manyan idanunshi waɗanda suke saurin saka maraji nutsuwa, ganin har 11am tayi ya sakashi miƙewa gaba ɗaya da sauri ya saka hannunshi ya gyara jikinshi sabida yadda reaction ɗinshi ya bayyana tun jiya yake fama da ciwon mararshi wadda ta zame mishi jiki a kwanannan, tunda yazo legos ƙarfin hali kurum yakeyi amman shikaɗai yasan yadda yake fama da sassan jikinshi babu abinda yake buƙata a halin yanxu kamar mace acikin rayuwarshi shima mutum ne kamar kowa ba dutse ba, inda Allah ya rufa mishi asiri shiba mazinaci bane sannan kuma yana da kokarin yawaita azumin nafilar daya zame mishi jiki a halin yanzu kusan kullum shiyake yi yake samun sauki acikin jikinshi.
Ɗan cije lip's ɗinshi yayi kaɗan tare da nufar gaban trolly ɗinshi ta kayan dayazo dasu, tawul ya ɗauko, faffaɗa tare da ajeshi a gefen gado, rigar jikinshi ya cire wadda ganin surar jikinshi kaɗai ta saka nakusan yada birona, sabida yadda yake da murɗaɗɗan jiki irin na maza majiya ƙarfi waɗanda training ya gama ratsa jikinsu,kasancewar shi mai yawan zuwa wajan motsa jiki baya zama haka kurum, ƙwanjin hannunshi kaɗai mace ta kalla seta firgita sabida yadda yake a murɗe babu alamun sako sako, kirjinshi irin faffaɗan kirjin nan ne wanda daga ƙasan mararshi ya tsuke, yalwatacciyar sumace baƙa siɗik kwance a saman kirjin nashi wadda ta gangaro har wajan cibinshi ta xagaye har zuwa ƙasan mararshi, nipple's ɗinshi masu girma cikakku kosassu dasu waɗanda gashi yabi ya zagesu gwanin sha'awa haka xalika dukkan ilahirin sassan jikinshi gargasace tabi ta lafe a ko'ina kallo ɗaya mace xatayi mishi taji ya burgeta musamman mai raunin sha'awa tana kallonshi zataji tana bukatar kasancewarta dashi, ɗaukar tawul ɗin yayi ya ɗaura a saman west ɗinshi tare da zame gajeran wandonshi na ciki batare daya bari sirrin girmanshi ya bayyana ba, ya ɗauki karamin tawul ya ɗora saman kanshi tare da nufar bathroom, ruwa mai ɗumi ya haɗa, ya soma wankanshi wanda yakai kusan mintuna 40 a cikin bathroom ɗin kafin ya kammala ya fito jikinshi yana ɗigar da ruwa, karamin tawul ɗin saman kanshi ya saka yana goge jikinshi tare da ɗauko cream cikin jakarshi a gurguje ya shafa tare da fesa turare sama-sama hmm da gaske fa Aliyu namijine sabida cikin mintuna goma ciff yagama shirya kansa sabida shi baya cikin maza masu sanya komai nashi da zafi-zafi yake yinshi cike da zafin namanshi babu sanyi ko kaɗan komai yana yin shine da karfinshi da lafiyarshi, cikin wani milik ɗin yadi mai sharara domin ana hango farar singlet ɗin jikinshi, ya shirya kanshi se, black shoe daya saka a ƙafafunshi, tare da ɗaukar system ɗinshi da wayoyin shi ya fita cikin sauri yana rufe ɗakin sabida akwai abinda yakeso yayi a office kafin ya taho kano, seda ya rufe ɗakin sannan ya fiddo da wayarshi guda wadda take cikin aljihunshi kana ya soma kiran wanda ze kira a airport ɗin seda ya tabbatar ze samu jirgin dare zuwa kano sannan ya nufi parking space inda tarin motocin gidan suke sabida abbansu ya zube musu motoci masu dama agidan sabida kowanne ya sami saukin fita office.
Gaban Wata Black Venz ya buÉ—e ya zuba system É—inshi a front side kana ya koma driver side ya shiga bakinshi É—auke da addu,a kana yaja ya nufi bakin gate mai gadi ya bude mashi gate É—in ya fita zuwa office.
Sosai yake gudanar da abinda zeyi a office É—in har zuwa six na yamma sannan yay off tare da sallama da ma'aikatan wajan ya nufo gida, koda yaje sosai yayi mamakin ganin ya umar harya sauka tare da matarshi humaira.
Cikin barkwanci ya umar yace.
"Kawani saki baki kana kallonmu to kaima kaje dan yau mukaga ammi tanata haɗa kayan lefe inaganin ma ƙila sunkai tuzurun banza kawai".
Shiko tsananin mamakin yadda yaga yaya umar yawani baje a babban falo suna ciye ciye shida humaira matarshi yayi wadda tirtsetsen cikin jikinta yakusan fitowa duniya, sabida baya sakin jiki gaban matan yayin nashi bare su raina shi,( kuji fa ) ya saka kai yana kokarin ratsesu yana daya sanin ta ɗayan falon ya biyo bata nan ba"Ya Aliyu ina yini".yaji muryar humaira matar ya umar tana gaisar dashi, cikin ƴar ɗaga murya kaɗan ya umar yace"Kai dan ubanka nifa gaba nake dakai kasan Allah matata baxata kuma gaisar dakai ba, tunda ko sannu munfi karfin kayi mana, bare ka tambayi wayaje ya ɗauko mu".shikam mamaki yayyanshi suke bashi yadda suke wani rawar ƙafa akan matansu kamar zasu taka cikinsu ɗan siririn tsaki! yaja kaɗan kana ya juyo cike da tsantsar miskilancinshi"Lafiya"! yafaɗa yana kallon humaira kaɗan sannan ya saka kai.batare daya tankawa ya umar ba( wayyo my fans! ga wanda yafi Aliyun fati nan miskilanci RABON WANI ), sakin baki humaira da ya umar sukai.
"My love nidai wallahi senaji ina tausayin khadija har raina, wallahi ta É—aukarwa kanta aiki nifa harga Allah wani xubin ya Aliyu tsoro yake bani, sabida ko kallo baka isheshi ba amman ita tarasa wazata É—auka seshi, ammanfa wannan shine dai dai da mace marar ji sabida kallo guda yay mata zatasan da maza a wajan".
TafaÉ—a tana kallon shi tare da kwanciya a saman cinyarshi tana É—ora hannunshi saman cikinta.
"Kuma fa baki san wani abu ba kinsan Allah da kike ganinshi haka irinsu mugayen jarababbune wannan miskilin bari kiga ya sami mace a É—aki se buzunta".
Dariya ta saki tana faÉ—in.
"Ai duk kanwar jace kaima ai haka kake babu sauki a room,".
Haka dai suka cigaba da tattauna a kan halin Aliyu na shariya da miskilanci.
Wanda cikin haka ya fito jikinshi sanye da ƙananun kaya se zuba ƙamshi yake se ƙatuwar jakar kayanshi a kafaɗarshi hannunshi guda rike da wayoyi, takowa yay har gaban ya umar tare da yi mashi sallama a daƙile ko kallon inda humaira take baiyi ba ya saka kanshi ya fice daga falon.
"Allah dai ya yaye maka wannan ƙuncin domin ciwone wannan yaro inda kaine gaba damu damunga mugunta tuzurun banza".cewar ya umar yana kallon Aliyu wanda harya bude ƙofarshi ya fita bai tanka mishi ba.
Seda yay sallah acikin masallacin gidan sannan ya fita batare daya É—auki mota ba.saboda airport ze wuce babu wanda ze dawo da motar.
Ƙarfe bakwai na dare tayi mashi a babban filin sifiri da sauka na jahar legos wanda cikin lokaci kaɗan ya sami abin hawan daze kaishi can ɗin.
Zaman mintuna ƙalilan sukai tare da sauran fasinjojin dazasu taso kano suma dan har sallar isha'i ya tashi yaje yayo sannan ya kuma zama cikin haka aka soma kiran sunaye, mintuna kaɗan jirgin ya cika da fasinjoji kana ya tashi zuwa kano ta dabo cigari!.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.