Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 7 of 81

*DAWOWA LABARI*

*COMMENTS*
*VOTE*
*SHARE*
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }

NA
*AUTAR MANYA*

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

*007*

_Dawowa Labari_

Duk irin yadda Bebi takewa Sadiya raɗa akunnen nata ashe malam hadi yana kula dasu seda ya gama dukan ƴan makara tas sannan ya juyo garesu tare da haɗe fuska tamau kamar bai taɓa dariya ba.
"Bilkisu Musa Mai katifa! Sadiya Ado Rimin gado". yafaÉ—a tare da haÉ—e ransa..........
"Dukan ku kufitomin nan tunda Ku bakwajin magana kullum cikin surutu kuke".
Cikin tsananin tsoro sadiya ta soma raba idanu amman mutuniyar kuwa ita ko ajikinta sema fitowar datayi gaban malam ta rissuna tana tura baki gaba tare da yatsine fuska.
"Gani".
Abinda Bebi ta faÉ—a kenan tana tsare malam hadi da idanunta babu alamun jin tsoro ko kaÉ—an a idanun nata.
"Wai ke kuwa Bilki aljanu gareki ne?, kullum burinki kiyi surutu a aji har ki shafawa wasu".
Muryar malam hadi kenan wadda ta saka Æ´an ajin yin tsit sunajin gulma.
Seda Bebi ta juya ta makawa Æ´an ajin harara sannan ta juyo.
"Nidai Malam sunana Bilkisu idan yay maka yawa kace Bebi amman ubana bai raÉ—amin suna da Bilki ba, kukuma munafukai ubanku kuke kallo?" .
Gaba É—aya ajin shuru ya É—auka ita kuwa sadiya wata gudawa ce ta zo mata sabida kowa yasan halin malam hadi yau shikenan Bibe ta ja musu jaraba.
Ran malam hadi yayi mugun ɓaci cikin zafin rai ya kira monita tare da ce masa yaje ya ɗauko masa dorina mai baki biyu a ofishin shugaban makaranta.
Jiki na rawa monita ta tashi hartana dariya sabida Bebi ta addabi kowa a ajin babu wanda take ragawa daman ta jima tana jin haushin Bebin shiyasa ranta yay fes dajin hakan.
Mintun Biyu monita tazo da dorina jiki na rawa ta rissuna ta miƙa wa malam hadi.
Wani kallon zamu haɗu dake Bebi ta mata tare da sunkuyar da kanta a ƙasa duk da tana da jin tsoron duka amman batajin zatai kuka! kuma batajin xata bashi haƙuri bare aga galabar ta.
Muryar sadiya ce ta karaÉ—e wajan.
"Malam dan girman ubangiji kai haƙuri wallahi Bebi ce ke magana bani ba, dan Allah malam karka dakeni".
TafaÉ—a jikinta yana rawa.
Wani irin haushine yazowa Bebi wuya da kallon ɓacin rai ta dubi sadiyan amman bata iya ce mata komai ba.
"Jeki zauna ki barni da wannan tsagerar marar kunya".
Da sauri sadiya ta koma ta zauna tana godiya.
Tabar Bebi tana gunguni tana mitar zuci wadda sautin har waje yake fitowa.
Tattare hannun rigarsa yay tare da zuba mata dorinar agadon bayanta wanda dukan har wajan fuskarta haka ya zage ya dinga lafta mata bulalar ajikinta seda yay mata guda goma sannan yace ta miƙe hakan nan ya kuma zuba mata guda biyar a ƙafafunta.
Wata iriyar banƙara Bebi tayi tare da kurma wata shegiyar ƙarar! data amsa makarantar baki ɗaya tare da zubewa a ƙasa tana wata iriyar haniniya tana fidda dafara.
Kallo É—aya zaka mata ka gane tana fama da bugun iskane wanda kuma hatta mama data haifeta bata san da wannan aljanun na bebi ba haka zalika kowa ma, bai sani ba se yau É—innan da malam hadi yay wannan dukan.
Cikin sauri ragowar malaman suka shigo ajin kasancewarsu maza yasa suka nemi Æ´an ajin mata akan su É—agata wadda take kamar gawa su kaita offishinsu.
Mutum kusan biyar ne matan ajin suka xo kan Bebi zasu É—agata amman duka seta ta watsar dasu.
Sadiya kuka! take aguje tayi ajin su Æ´an biyu tana gaya musu cewar suzo Bebi ta mutu.
Hassana mai saurin kuka! tuni ta É—ora hannu akanta tana ihu hussaina kuwa gudu ta saka zuwa ajinsu Bebi tana share zubar datake yanko mata.

Ganin ƴar uwarsu cikin halin rai ko mutuwa yasa hassana fita aguje tayi hanyar gida.tana gaf da kaiwa ta haɗu da ya Aminu. cikin sauri yake tambayarta ina xataje a ahaka atake anan take gaya masa abinda ya faru baiyi ƙasa a gwiwa ba wajan binta makaranta yace karta gayawa mama lokacin da sukaje har an kori ƴan ajin sabida an kasa ɗagata dan haka malaman sukace kawai ai mata roƙiyar anan ajin nasu.
Daga sadiya se hussaina tare da sauran malamai hassana da ya aminun suka shigo ganin halin datake ciki yasa hassana ƙara volume ɗin kukanta!
Seda malama hadi ya buga mata tsawa sannan tai shuru.
Karatu malam najahi ya shiga rerawa akunnen Bebi wanda seda ya shafa mintuna biyar sannan ta soma tari wata iriyar banƙara take tare da kaiwa malam najahi shaƙa, wadda da ƙyar su malam hadi suka ɓamɓareshi sannan malam najib ya amshi karatun tare da ɗaga murya da ƙarfi, kowa ya dubi Bebi yasan bata hayyacinta sabida wannan uban ƙarfin ansan bana ta bane sabida aljanun nata irin masu mugun ƙarfin nan ne duba da yadda suka taki kanta da mugun ƙarfin gaske.
Birgima ta fara a tsakar wajan kafin ta dage iya ƙarfinta ta yaga kayan jikinta ganin suna ƙoƙarin fidda mata da tsiraici yasa hussaina nufarta a guje ta rungumeta tsam ajikinta ahaka sukaita birgima tare suna kaiwa hussaina yaƙushi da ciwo amman taƙi sakinta harseda karatun yagama jigata su sannan suka soma magana da ƙarfin gaske.
Alokacin malam hadi yacewa hussainar ta cikata, duk da haka seda hussaina ta saka mata hijabin jikinta ita kuma ta warware ɗankwalinta ta yafa sannan taja baya, tabar malaman da mamakin ƙarfin halinta tare da zumunci irin nasu.

Tambayar farko da malam hadi ya somawa aljanin dayake magana shine yaya sunansa? sannan wani jinsi ne shi tare da addininsa.
Amsa ya bashi sunansa musa kuma shi musulmine kuma anan birnin sin yake, kuma dalilin shigarsa jikin Bebi kawai tana burgeshine yadda bata barin kota kwana amman shi ba macuci bane ƙarewa ma akwai dalili mai ƙarfi dayasa ya shiga jikinta wanda hakan yazama sirrinsa.
ÆŠaga murya malam hadi yayi.
"Babu wata soyayya a tsakanin ku da bil adam, sabida haka mu bamu gamsu da bayaninka ba dan haka ka fita daga jikinta".
"Nifa ba tun yau nake jikinta ba, hasalima najima ajikinta nagaya muku inada dalilin dayasa na shigeta, yanxu ma banyi niyyar haurowaba dukan dayake matane naga ze cutar da ita shiyasa nazo dan na kare dukan".
Yakai maganar cikin wani irin sauti.
"Bamu yarda da zamanka ajikinta ba, domin hakan cutarwa ne dan haka tunda kai musulmine kasan girman Allah, to karabu da Æ´ar mutane".
Cewar malam hadi.
"Nasan girman Allah kuma zan tafi insha Allahu, amman dan Allah kuma ku dinga haƙuri da halinta tunda ita a haka Allah yayota dukan da kuke mata ze iya sakawa mazumuntan mu su sami faragar shiga jikinta".
"Insha Allahu, Malam musa Mungode".
Cewar malam hadi wata iriyar birgima tayi tare da banƙara tare da sakin atishawa nan ta koma luff ta kwanta kamar gawa.
Ruwa malam najib ya umarci sadiya ta samo, data kawo yay addu'oi cikinsa sannan ya bawa hussaina ta shafa mata harma ta bata abakinta, domin ita hassana bata aikin komai sena kuka!.
Seda sadiya ta taimaka aka É—agata aka shafa mata sannan ta buÉ—e idanunta da sukai wani irin jajur kamar gauta.
"Sadiya lafiya kuke shafamin ruwa?".
TafaÉ—a cikin rashin sanin halin data faÉ—a a É—azun.
"Lafiya ƙalau suma kikai".
Cewar yaya aminu wanda yake tsaye, ganin ya aminu awajan ya bata mamaki watakan dukan malam hadine ya sumar da ita.
Ganin batada lokacin tambaya yasa ta nufi ta miƙe tsaye anan ƙafa tace bata san da wannan ba.
Domin fafur taƙi takuwa wani irin rintse idanu tayi tana salati da sauri da sauri.
Ganin haka yasa malam najib ya sunkuya dai dai ƙafar tata ya tofa mata addu'oi sannan fa aka samu ƙafar ta miƙe amman da duk da hakama tana mata zafi dan seda ta dafa su hassana, suka nufi gida.
Kowa se binta yake da kallo.
Suna fita bakin gate É—in makarantar sukaga mama cikin sauri duk hankalinta atashe sadiya wadda take gabansu mama ta tara.
"Sadiya ina Bebin take?,yanzu ihsan tazo tana min kuka! agida wai Bebi ta rasu?".
Tafaɗa duk hankalinta a matuƙar tashe seda sadiya ta matsa sannan mama ta hangosu da sauri ta ƙarasa ta rungume Bebin tana shafa kanta.
Malam hadi wanda ya biyosu a baya shiya É—an yiwa mama magana akan yana son ganinta mintu biyu.
Sakin Bebi tayi ta nufi wajansa.
Bayani yayi mata yadda zata gamsu.
"Allah gani gareka ni Aisha Bebi da aljanu, Allah ka taimakeni kada ka jarabci wannan yarinya bata da wani gata se naka".
TafaÉ—a muryarta na rawa amman kana ganinta kasan ta kaÉ—u amman haka ta daure taiwa malam hadi godiya suka nufi gida tare da sadiya ya aminu dasu hassana, cikin nutsuwa su hassana ke tallafe da Bebi ajikinsu haka suka nufi gida da ita..........

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.