Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 14 of 81

*MANAGE BA CAJI*
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
    {  _HOT LOVE_  }
           

         NA
*AUTAR MANYA*

_Albishirinku makaranta littattafan hausa shin ko,kunsan shararriyar marubuciyar nan *FEENAR MATAR SOJA* wadda ta saba gwangwajeku da zafafan littattafanta masu matuƙar ratsa zuciya ta ƙara zuwarku muku dawani zazzafan littafin, Mai suna *AUREN GADO*  kadafa ku manta Feenar tayi fice wajan baku nishaɗi faɗakarwa ilimantarwa acikin littattafanta, Kamarsu *MUƘADDARI AUREN SOJA*,  *ZANYI BIYAYYA* *WANAKE AURE* dama sauransu toyau ma gata nan tafe da wani sabon wanda ta shirya tsaf domin ta nishaɗantar daku acikin sabon littafinta mai suna *AUREN GADO* na kuɗine akan farashin Naira 500 ga wanda ya shirya biya seya nemeta ta wannan number 09011251444 maza ku hanzarta koda kuɗinka seda rabonka_

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

                       *16*

Dariya Amina ta saki ahankali tare da kallonsa"Yaya kaima dai Allah ya yanke maka haka, musha biki ai wallahi nayi farin cikin wannan haÉ—in dasu abba sukai". tafaÉ—a cikin farin ciki, HaÉ—e rai yayi sosai fiye da yadda yake da tare da kallonta da idanunsa waÉ—anda suka saka ta sami kyakykyawar nutsuwa akan dariyar datake yi,"Ke ni tsaranki ne?".yafaÉ—a cikin serious magana babu alamun sassauci, Gintse dariyar tayi tare da haÉ—e hannayenta waje guda.
"Allah ya baka haƙuri".tana faɗin haka ta miƙe tayi ɗaki da gudu sabida tsoron karya kai mata mari tasan halinshi da zafin zuciya tare da saurin hannun tsiya, tsaki yayi a fili batare daya ce komaiba ya lumshe idanunshi yana tasbihi ga Allah buwayi gagara misali, wani irin sassanyan ƙamshi ne mai ratsa zuciyar ma'abocin jinsa ya ratsa ilahirin falon, sallamar wata farar macece tas! marar jiki kallo ɗaya zakayi mata kaga bafulatanar asali sanye take cikin shigar jan legos less wanda yaji uban kuɗi mai tsada se zobuna da sarƙa dayaji a wuyanta da hannunta jikinta rufe da farin mayafi mai tourching ja ajikinsa, ɗago da lumsassun idanunshi yayi tare da ƙawata fuskarshi da murmushin dayayi masa kyau fiye da tunani, "Amin wa'alaikissalam Ammina" yafaɗa tare da ɗan karkatowa ya tashi daga kishingiɗen dayake, yana kallonta cikin so da ƙaunarta.
Itama faɗaɗa far'arta tayi tare da janyo tum-tum guda marar tudu ta zauna akansa tare da kallonshi, "Yau dai lafiyarka naga duk jikinka amace?".ta tambayesa cikin kulawa, Ɗan langwabar da kanshi yayi tamkar ƙaramin yaro tare da matsowa gabanta ya ɗora kansa akan cinyarta, tura bakinshi yayi gaba kaɗan wanda yay matuƙar bani mamaki ganin yadda yakewa, Ammi kamar ƙaramin yaro, cikin nutsuwarsa wadda tagama bin jikinsa ya furta"Wallahi ammi yau jina nike duk babu daɗi, amman inaga yanayin aikin yau ɗinne".yafaɗa yana ɗago idanunshi yana kallonta,Cike da kulawa ta kuma dubansa itama,"Kaje kiran Alhaji babba kuwa tun ɗazu yake aikosu fahad dan Allah dan Annabi babana kaje kada ka kuma jamin cin zarafi akaro nabiyu tunda sunce ninake ɗaure maka gindi kowa ganin laifina yake".tafaɗa cikin nutsuwarta.
Tashi yayi daga saman cinyarta tare da aro nutsuwa sosai sannan ya dubeta"Zanje Ammi amman dominki bada ban keba na rantse babu wani zuwan dazanyi haba wallahi abinda ake acikin gidannan baya dacewa" Riƙe baki ammi tayi cikin ɗunbin mamakin halinshi sam baya da rufi maganar data fito masa a baki ita yake yafaɗi baya rufa rufa musamman idan ranshi yana ɓace."To naji dan Allah karaba kanka da wannan zafin ran babana bana sonka dashi, sannan kuma idan kaje kasan maganar dazaka faɗa musu sabida daga ƙarshe dai kasan meze biyo baya" tafaɗa itama fuskarta babu daɗi, Lumshe idanunshi yayi tare da furzar da zazzafar iska daga cikin bakinshi.
"Naji Ammina Amman harga Allah bana son wannan yarinyar har zuciyata".Haɗe ranta tayi sosai,"Kace muma duka baka sonmu, Nikuma duk duniya banida kamar khadija tunda ta iya buɗar baki ta furta maka so naji ina sonta".Ammi tafaɗa tana kauda kanta gefe,Dariyar gefen baki yayi, batare dayace komai ba, ni mamakinshi ma nayi yadda naga ya sake sosai da mahaifiyar tashi suna magana kamar ba wannan miskilinba,"Ammi kin sauke dambun?".taji amon! Muryarshi acikib dodon kunnenta, "A,a da saura na saka Habiba ta dubamin".Haɗe rai yayi"Ammi dan girman Allah kidaina baiwa masu aiki suna taɓa mana abinci, gwarama su baba amman waɗancan yaran duk ƙazamai ne".dariya! tasaki "To baban ƴan ƙyamƙyami naji wannan dai na bata tayi sabida inada uzuri, inxakaci to idan bazaka ciba kai kasani" girgiza kanshi kawai yayi tare da ɗaukar wayarsa wadda ya mayar da ita slient, ganin misscall ɗin Abbansu yayi wajan 5 jikinshi na rawa ya fara neman layin ringing! 1 abban nasu ya ɗaga, Sallama yay cikin nutsuwa tare da furta "Afuwan abba wallahi banji kiranka ba".daga cikin wayar abban nashi ya ɗanyi murmushi"Naji Babana babu komai, yaya gida da aiki?",yafaɗa cikin kulawa, cikin nutsuwa shima ya basa amsa da "Lafiya ƙalau alhamdulillahi, Abba ya legos ɗin?". shima daga nashi ɓangaren numfasawa yayi"Lafiya ƙalau Abubakar bai gaya maka saƙona ba?. ya lumshe ido tare da warasu akan Ammi wadda take kallonshi"A,a abba bai gayamin ba, amman yana hanyar gida, sabida bamu haɗuba yau"."Ok daman sonake kazo nan legos ranar saturday akwai kayan dazasu biyo jirgi, sabida umar ze tawo gida week end sekai ka karɓeshi nima kuma gobe zan wuce chaina kaga baze yuwu abarsu bilal su kaɗaiba semuga ba dai dai ba". shafo sumar kansa yay wadda bata cika yawa ba sabida askin dayake mata na saisaye tare da furta"To babu komai Allah ya kaimu zan biyo jirgin dare ranar friday".yafaɗa cikin bin umarnin mahaifin nashi.
"Allah yayi maka albarka Aliyu bantaɓa neman abu wajanka kayi musuba koda hakan bai maka daɗiba, yadda kakemin biyayya kaima Allah ya baka masu yi maka" Amin ya Allah" yafaɗa cikin jin daɗin addu,ar mahaifin nashi wadda idan da sabo yasaba jinta wajan dukkan mahaifan nashi guda biyun.
Katsewa yayi tare da kallon Ammi,"Pls ammi ki ɗan zubomin naci na tafi ɗaki kinji nan da jibi zan wuce legos".murmushi tayi tare da kallonshi "Toya zakai da baƙin dazasu zo muku ranar lahadin naji kace kuma sabbin costumers ne?"shafa kanshi yayi tare da ɗan jim kaɗan"Babu komai xan haɗasu da ya usman duk da dai ni suka sani awajan". yafaɗa cikin comfidance,"A,a ba,a haka kaga dai suɗin baƙine meze hanaka kace masa yabari ranar lahadin ko da daddare seka tafi can ɗin?".waro idanunshi yayi"Haba ammi ai babu wani uzirin daze katse naku awajena kedai ki sakani acikin addu'arku kawai".yafaɗa cikin ladabi, "Addu,a kullum cikin yi maka ita muke tare da ƴan uwanka baki ɗaya Allah yayi muku albarka amin".Ammi ta faɗa cikin jin tausayinshi sabida kaf ƴaƴanta yafi kowa ƙulafucin iyaye yana da mugun rauni akan iyayenshi yana sansu over.

Tashi tayi da kanta taje ta haɗo mashi dambun cikin madai daicin flate sabida shiɗin ba ma'abocin cin abinci da yawa bane, zaman ammi kaɗan wani magidancin namiji ya shigo wanda ya girmi Aliyu nesa ba kusa ba sedai shi baikai Aliyu kauriba kuma shi yana da hasken fata kamarta Ammi, sallama yayi hannunshi riƙe da wata farar Beby mai kyau, da sauri yarinyar tayo gaban Aliyu ta rungumeshi "Uncle ina yini kasiyomun choculate ɗin?.tafaɗa cikin shagwaɓa ɗagata yayi yana mata wasa "A,a Afrata har an dawo daga school da wuri haka".yafaɗa duk hankalinshi yana kanta yama manta da wanda ya shigo ɗin seda yaji muryarshi yana mashi magana"A,a tuzurun ammi kaine anan?".yafaɗa yana dariya kaɗan ɗan haɗe ranshi yayi"Ya Abbakar dan Allah kudaina wallahi bana so".dariya wanda aka kira da ya abbakar ɗin yayi"Ai yanzu nasaka ka magana miskilin banza".yafaɗa yana neman wajan zama"Ammi pls kibamu abinci yunwa yau kowa yakeji agidan",yafaɗa cikin kwantar da kai"kai nifa nagaji kaje can kana siyo muku wannan laulayin na matarka inaga vaze barni na huta da dahuwa ba".ammi tafaɗa tana kiran "Amina ko hassana wani yazo".Cikin sauri ƴammatan ɗazu sukazo ganin ya Abbakar yasa suka tsaya awajan amman babu wadda tai gigin kallon saitin gadanga wanda ya ɗora afra akan cinyarsa yana cin dambun yana bata batare daya kalli kowa ba, yana gama cin abincin ya tashi baki ɗaya kafaɗarsa ɗauke da afra.
Wadda tayi bacci miƙawa amina ita yayi ganin yadda suka cika falon suna hira da ya abbakar kamar wani sa'ansu bakaramin bashi haushi hakan yayiba dan haka fita kawai yayi batare daya kula kowa ba.
Yana kokarin kai kanshi part ɗin Alhaji babba yaga usman na kokarin kutso kanshi cikin part ɗin nasu ɗan dakatawa yayi harya karaso"Kai kuma ina zuwa haka?" usman ya tambayeshi cikin barkwanci"Wajan wancan tsohon zanje wallahi ya riƙe wuta".yafaɗa rai ahaɗe Dariya usman ya saki"Aikin Alhaji yana kyau shine maganin manyan tuzurai maza jeka na khadija bada kanka asare" yafaɗa tare da maƙe dariyarsa, batare daya dubi usman ba yaja ƙafarsa yabar wajan cikin hukuncin Allah yana kokarin kai kansa cikin part ɗin alhajin ya hango tashin motar fahad ɗan gidan alhajin wanda yake zaton tare dasu Alhajin suka fita ƙila wani wajan zasuje.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da barin part É—in Alhajin baiyi gigin bita part É—in Abban bauchi ba, sabida gudun yawan magana sulalewa yayi ya koma part É—insu
Tun daga farkon falon kakejin hayaniyar su ya abbakar da usman wanda dagaji tsabar hirace tai daÉ—i a falon ammin amman shikam baiyi gigin shigaba haka yaja kafarsa ya haura samansa, Alwala kurum yayi tare da nufar masallacin dake cikin gidan nasu.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.