Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 37 of 81

*******************

Se wajan ƙarfe uku hussaina ta sauke alalen daga wuta...............

[ _afuwan jiya nai mistake number xan saka 53-54 sena saka 52-53 se kawai na soke na bar na jiya a 53 kaÉ—ai yau ga 54 kuji daÉ—inku ina yinku my fans_ ]

*INA ƘARA GAYA MUKU DUK SANDA KUKAJI SHURU KUMIN UZURI INA TARE DA MARAR LAFIYA TO LOKACIN TYPING BAI DA YAWA AFUWAN MASOYA WANNAN LABARI YA WUCE INDA KUKA KAISHI KUDAI KUCIGABA DA SUBURBUƊO MIN CMNT KOTA INA KUCIKAMIN WAYA NIKUMA IN CIGABA DA BAKU NISHAƊI INSHA ALLAH*
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }

NA
*AUTAR MANYA*

_Writter of_
*ÆŠAN MAJALISSA*
*H A S K E*
*KOBA SO DA AKWAI ƘAUNA*
*RABON WANI*
*DA IZZATA*

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

*55*

Juyoshi tayi baki ɗaya acikin madai-daicin farin bokiti sannan ta juye manjan cikin ɗan kwanon suyar mai, ta ɗorashi akan gaushin wuta, minti biyu manjan ya soyu, seda ta fara miƙowa mama alalen sannan ta koma ta ɗauko kwanon suyar man wanda seda tayi amfani da ƙyalle kafin ta ɗauko sabida gudun ƙonewa.
Kwanikan cin abincinsu, ta ɗauko duka acikin ƙaton faranti ta jero sannan ta koma gaban mama ta ajesu itama ta nemi guri ta zauna.
"Sannunki Allah yay miki albarka ya baki masu yi miki kamar yadda kikai min".
Mama tafaÉ—a cikin nutsuwa, kana ta buÉ—e marufin bokitin.
"Bani farantin ku, seki bani kwanika biyu".
Cikin bin umarninta hussaina ta miko mata ƙaton farantin da sukecin abincin, sannan ta kuma miƙo mata wasu kwanikan guda biyu, kamar yadda ta buƙata.
Dai-dai yadda zasu ƙoshi ta zuba musu sannan, ta zubawa shahid nashi,itama ta zuba, Bebi ta sami bacci dan haka seta bar mata nata cikin bokitin.
Manja ta zuzzuba musu wadatacce yaji ko, tura musu tayi tana cewa............
"To dai kuyi a hankali wallahi babu ni a rakiyar ban É—aki".
Dariya! dukkansu suka kwashe da ita musamman hussaina wadda har ƙwarewa take dan dariya, kafin kuma ihsan tace.
"Daman mama aimu bama zabga yaji acikin abinci wannan se Bebi gata kuma da ɓataccen ciki daga taci se gudu zuwa masai".
Dariya duka suka kuma kwashewa da ita.
"Nidai babu ruwana kinsan ta sarai kotana ciwo bata raina masifa dan haka kiyi kina sani".
Mama tafaɗa cike da barkwanci, wannan hali na mama yana burge ƴaƴanta sabida mama mace'ce wadda tasan haƙƙin yaranta sam bata nuna bam-banci ko wariya, a tsakaninsu tana bawa kowannen su haƙƙinshi, bata matsa musu wajan ƙwauran abinci, ko suttura muddin kaga mama bataiwa su Bebi abu ba tofa sedai, bata dashi, amman ankon maulidi kayan sallah, duka basa wuce su haka nan kuma idan tana camama zata ɗan siyo musu namansu ko kifi adafa kowa yaci, mama takan hana kanta wani abun domin ƴaƴanta, wani zubin har tausayi take basu idan zatai musu wani abun wannan dalilin yasa basa takura mata akan tai musu kaza-ko kaza sabida sun san tana iyakacin bakin ƙoƙarinta indai Allah ya hore mata.
Danma yanzu Alhamdulillahi shahid yana É—aukewa kanshi wasu abubuwan dan wataran da ribar gawayinshi ma suke cefane, da sauran sabgogin cikin gida,wannan dalilin yasa kowanne acikin yaran nata burinshi ya taimaketa sabida yadda itama take zage damtse wajan tallafa musu duk da maraicinsu amman bata bari sunyi kuka! ba sannan bata bar rayuwarsu ta salwanta ba, domin inda wata uwarce yadda Æ´aÆ´an nata suke duk mata kuma.masu kyau da tuni ta bude hannun jari dasu Allah ya kyauta.
"Mama aini yadda naga Bebi ma jiya tana rawar É—ari wallahi ban É—auka yau xata iya zuwa asibiti ba".
Hassana tafaÉ—i tana kokarin kai loma bakinta
"To kuyi shuru muci abinci kar amanta da ambaton sunan ubangiji mai girma tare da korar shaiÉ—an".
Mama ta faÉ—a cikin bada umarni.
Tsitt tsakar gidan yay babu abinda kakeji se sautin taunar su cikin nutsuwa.
Sun ɗan jima suna cin abincinsu kafin su kammala arfa ƴar ƙarama ita ta ɗauke farantin takai gaban rariya ta zuba omo ta wanke tass.
Suko su hussaina wanko hannayen su sukai tare da nufar É—aki sabida yau zasu kaiwa gidan baba lado( malam ) ziyara sabida kwana biyu talle bai barsu sunje gaidasu baba'ba.
Hassana ita ta fara shiga wanka bayan ta fito ta É—auro alwalar sallar la'asar sannan hussaina itama ta shiga.
Saman tabarma hassana ta zauna tana shafa mai.
Mama kuma tana kuncewa ihsan ɗaurin zanin datai na baya wanda yaƙi suntuwa ta sauƙi, sabida itama maman tagama cin alalen nata harta wanke hannunta tasha ruwa tare da godiya ga sarki Allah.
Sallama sukaji daga soro cikin É—an É—aga murya kaÉ—an mama take amsa sallamar kafin taga yara kimanin guda uku.
Suna shigowa da manyan buhunan shinkafa guda biyu, juyawa sukai cikin sauri sega wasu kwalayen nan na macaroni guda uku taliya uku jarkar manja data man gyaɗa manya ɗai ɗai, se manyan ledoji,guda uku abinka da ƙaramin gida nan da nan tsakar gidan ya cika da kaya.
Mama sakin baki tayi tana kallon ƙudirar ubangiji haka zalika sauran ƴaƴanta ma haka.
Yaran dasuka shigo da kayan abincin ne suka juya suka fita.
Cikin izza da taƙama baba tasi'u da rabi'u suka shigo gidan ko sallama babu, gaban mama ne ya faɗi amman seta daure bata nuna firgicinta a fili ba.
Seda ƙyar kamar an musu dole tasi'un yay sallama tare da tsayawa a tsakar gidan yana bin ko ina da kallo yana ƙyafe bakinshi kamar yaga gashi.
Cikin gadara da nuna isa irinta wasu dangin uban Rabiu ya laluba aljihun wandon jikinshi.
Sabbin ƴan dubu dubu ne ƙarr kamar yanzu aka bugosu kimanin naira dubu ɗari biyu, ya fito dasu waje tare da watsawa mama su a saman fuskarta, "ga sadakin gantalalliyar ƴarki nan a matsayin mu na dangin mahaifinta shaƙiƙansa, mun zauna munyi nazari da yawon ta zubar ɗin datake gudun karta ɗauko mana abin kunya yasa mukai mata miji nan da sati ɗaya tall rana mai kamar ta yau zamuzo nan ƙofar gidan mu ɗaura mata aure, suma waɗannan ƴan biyun na gabanki mun baki nan da wasu gajerun lokuta maza ki nemo musu mazajen aure idan ba hakaba tabbas zamu haɗasu da koma suwaye , ga kayan abinci nan inji sirikinmu uban mijin ƴarki yace abaki mota guda ya bamu muka raba gida biyar muka baki kaso ɗaya dan kici arzikin, sannan abu nagaba ki saita ƴarki sabida yaron ze zo anjima ya ganta duk abinda ya nema wajanta kartai masa musu domin shiɗin ɗan madarane baison wahala ba babu kuma irin gatan da ubansa Alhaji isa mai gwal bai mishi ba dan haka ku taka a sannu mun barki lafiya".
Gaba É—aya kan mama ya daure tunaninta ya tsaya cak, wasu keson yiwa aure da É—an gidan Alhaji isa mai gwall wanda babu wanda bai sanshi ba afaÉ—in anguwar sharaÉ—a mutumin da baida mutuncin baisan darajar talaka ba, koda ba shige shige take ba amman labarin shaiÉ—ancin yaron Alhaji isan babu kalan wanda basaji a wajan matasan anguwar hatta shahid yana yawan bata labarin É—an gidan alhaji isan dan ma tana taka masa burki ne to tayaya ma suka san alhaji isan har suka haÉ—a É—anshi aure da Æ´arta sannan su yaya basu bawa Æ´aÆ´ansu sun aura ba se nata Æ´aÆ´an?
"Nifa ban fahimta ba wai dawa kuke son haɗin wannan aure ne tasi'u karku saka ƙafa a ƙofar gidan nan harse kun ɗauke waɗannan kayan dan ban bukatarsu".
Dariya ya kece da ita.
"Dawa kwa xasu dace ban da BALKI wadda nagani ta sauka daga mota rannan ai tunda tambaÉ—É—É—iya ce to ga dai dai itanan na samo mata sabida haka idanma bakida labarin Khaleefah Mai shanawa! kije ki nema sabida ki shirya yadda yarki xata zauna dashi mudai mun gama namu sauran ke"!
"Dakata! Tasi'u!!!"
Mama tafaɗa da ƙarfi wanda sautin muryarta ya tayar da Bebi a firgice ta mike tana raba idon rashin sanin abinda yake faruwa su hussaina ko kuka kawai suke duk jikinsu yay sanyi.
"Babu wanda ya isa yay wa BeBI auren dole ama rasa da wa za,a haɗamin ƴa seda wannan ragowar cutar ƙanjamau ɗin waye bai san maishanawa ba tayaya zaka ɗaukoshi ka haɗashi da Bebi na rantse duk toshiyar bakinda macucin ubansu ze baku bata isa tasa na bashi ƴata ba kuma ku ɗaukemin waɗannan kayan daga gabana tun kafin mu raba abin faɗa".
mama tafaɗa cikin ƙaraji!

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.