Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 5 of 81
*AUREN BARE !!*🌹
  { _HOT LOVE_ }
     Â
     NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
              *005*
Abinda ze baka takaici guda ɗayane kwana arba'in da rasuwar Alhaji mai katifa, su sabi'u da tasi'u da sani da rabi'u harma da mariya wadda take aure acan gaida suka ɗauko alƙali wanda suka gama siyansa da kuɗi yazo yay rabon gado.
Wanda inda kaga yadda aka raba aka bawa musa nasa kason sekai kuka! sabida ko arziƙin soron gidan Alhaji mai katifa musa bai samu ba.
Duk da kasancewarsa ɗansa na jini amman hatta mariya datake mace taci wani kasafin acikin gidan amman musa dan tsananin ƙinsa bai sami arziƙin zaman cikin gidan mahaifin nasa ba.
Kwana uku da kammala rabon gadon Rabi'u ya fito gadaga yacewa musa yakamata tunda an bashi kasonshi ya tattara shida matarsa ya bar musu gidansu.
Se asannan musa ya sami zarafin zubda hawayen takaici tare da baƙincikin yadda zumuncin yanzu ya kama uban ɗakinsa.
Lokacin Aisha tana tsaka da laulayin haihuwar farko haka ya haɗe musu tarkacensu suka baro cikin unguwar ƴan kusa cike da baƙin ciki.
Koda sukazo fita ma daga gidan amai makon su Rabi'un su rakosu da addu,ar fatan alkairi a,a ina se fatan tsiya tare da mugun baki ne ya rakosu, wanda bada ban musa da Aisha sunada haƙuri ba dase anyi ɓatacciya sabida yadda ƴan uwan musan suke jifansu da muyagun kalami.
Anan cikin gaida ya kama musu hayar ɗaki guda a wani gida waishi gidan sabil, abinda kuwa yasa aka sawa gidan wannan suna sabida yadda yawanci masu zaman gidan masu ƙaramin ƙarfine haka zalika shi kansa mai gidan yana dai saka mutane ne kawai sabida Allah amman kuɗin gidan yafi haka.
Zaman Aisha da musa sedai muce zamane na haƙuri, saboda komai na musa ya tsaya cak! kasancewar daman ƴar kasuwar dayake zuwa ta ƴan katifa wajan mahaifinsa ne to tunda ya rasu kuma sesu sabi'u suka rufe shagunan dan tsabar mugunta ma basu sakasu a rabon gado ba, ko da Ado abokin musa wanda sukai karatu a rimin gado tare yazo yaga halin da suke ciki kuma yaji komai se ransa ya ɓaci haryana ƙiƙi rarin cewar musa ya ɗaukaka ƙara.
Shi kuma ze tsaya masa duk inda za,aje aje, amman ga mamakin ado se musa ya buÉ—i baki yace.
"Haba Ado dawani idon zan dubi alƙali nace masa nakawo ƙarar ƴan uwana akan gado?, Nikam na haƙura na barsu da sakkowar rana da faɗuwarta".
Numfasawa ado yayi tare da kallon abokin nasa cikin tsananin damuwa mai cin zuci sannan yace.
"Amman banji daɗin hakan ba, amman babu komai insha Allahu bazaka zauna haka ba, ni zan koma ƙauye zan haɗo kaddarata, tas nazo nan na sama mana abin da zamu dingayi muna rufawa kammu da iyalanmi asiri".
Sabida tsabar jin daɗi musa seda yay ƙwallar farin ciki, daman haka rayuwar nan take bare can seya rufa maka asiri amman ɗan uwanka yakasa rufa maka shi.
Koda sukai sallama musa yana zuwa gida ya shaidawa Aisha wadda tacika da tsananin farin cikin da seda tai ƙwallah.
Malam Ado abokin musa yana zuwa ƙauyen rimin gado ya samu dukkan kaddararsa ta ƙauye ya siyar daman mahaifansa sun rasu kuma shi kaɗai suka haifa kuma sun tafi sun bar masa tarin dukiya mai yawa, matarsa guda ɗaya, Hansatu se ƴaƴansa maza guda biyu Aminu da nura.
Haka ya sakosu agaba, sukayo nan cikin kano, agidan musa suka soma zama ɗakin Aisha shikuma suke kwana da musa a wani shagon maƙota har Allah yasa komai ya dai-daita.
Dayake musa yana da fuska kuma yasan jama'a a nan kasuwar ƴan katifa hakan yasa basuyi ƙasa a gwiwa ba wajan garzayawa kasuwar, cikin hukuncin Allah suka sami baba lado aminin Alhaji mahaifin musa wanda daman yasha zuwa gidan Alhajin neman musan amman baya samunsa se su Rabi'u waɗanda suke jifansa da baƙaƙen maganganu saboda yazo wajan musa kamar ba abokin mahaifinsu, ba anan musa ya kwashe komai ya gayawa baba lado wanda tsananin tausayin musa yasa baba lado zubda hawaye.
Anan baba lado ke basu labarin ai satin daya wuce ma su Rabi'un sukazo da dillalai suka sayar da shagunan Alhajin baki É—aya.
Sosai musa ya kaÉ—u da wannan lamari, amman seya share haryay wa Æ´an uwan nasa addu,ar shiriyar Allah domin duniyar ba madauwa ma bace ba.
Abinda ya kawosu kasuwar suka gayawa baba lado, wanda anan take baba lado yay musu garanto wajan kama hayar shago É—aya wanda zasu dinga saro katifa suna sayarwa.
Seda suka kammala komai sannan suka bawa baba lado kuÉ—in sarin sabida musa ya yarda da baba lado kasancewar sa kamar amini ne wajan Alhajinsa.
Koda baba lado ya rakosu hanya anan yake tambayar musa yanzu yana ina, anan musa yake ce masa aishi bai sami arziƙin samun kaddarar mahaifin nasa ba se kuɗin da suka bashi waɗanda basu ishe shi koda yankar farcan susa ba.
Sosai baba lado ya tausaya masa.
Kuma anan take yay masa albishir daya bashi kyautar gida guda wanda yake cikin sharaÉ—a sedai gidan É—aki É—ayane tal se shago a waje.
Tare da kicin da banÉ—aki amman yanzu haka Æ´an hayane aciki se nan da wata biyu zasu tashi idan yaso idan suka tashin seya shiga, wanda daman daga gidan da baba ladon ya bashi zuwa gidan baba ladon layuka ukune tsakaninsu.
Sabida tsabar farin ciki musa harda kuka! haka zalika ado shima seda yay hawayen murna.
Wanda shima ya nuna yana buƙatar idan da hali baba ladon yay masa hanyar siyan gida anan kusada abokin nasa musa.
Ganin garin yana yamma yasa baba lado ce musu su koma gida gobe sa dawo hakan ce ta kasance musu suka koma gida anan musa yake gayawa Aisha abinda ya faru, sosai Aisha ta shiga murna harda kukanta itama hansatu taimurna ranar kwanan zaune sukai dan farin ciki.
Washe gari tun wuri suka iske baba lado acan sharaÉ—an gidan sa wanda har seda suka shiga ciki suka gaida baba matarsa mace mai kirki haka tai ta jan musa ajiki tana masa wasa,kasancewar baba lado bashi da Æ´aÆ´a maza se mata kuma duk sunyi aure yasa baba jin tsananin son musa aranta.
Anan baba ta shiga zayyanawa musa irin taimakon da Alhaji yaywa baba lado aduniya, seda suka sha kokon da baba ta tilasta musu sannan baba lado ya ɗaukesu suka shiga cikin unguwar cikin ikon Allah suka sami gida wanda tsiran layi guda ne tsakanin gidan da ado ya samu ze saya dana musa ciniki akai cikin sauƙi aka kammala wanda su zasu ma riga musa tarewa.
Komai ya kammala sedai gidan ado yafi na musa girma kaÉ—an.
Cikin satin suka kammala komai ado ya dawo nan sharaÉ—a da zama haka suka soma tafiya kasuwa komai yana tafiya musu dai dai misali.
Kwanci tashi babu wuya wajan Allah yanzu haka shima musan ya dawo nan gidan da baba ladon ya bashi kuma suna tafiya kasuwa a tare da ado kuma babu laifi suna samu rufin asirin Allah dai dai misali.
Lokacin cikin Aisha ya tsufa, cikin wannan lokacin su Rabi'u sukaji labarin yadda Allah ya rufawa musa asiri wanda basuyi ƙasa a gwiwa ba wajan zuwa ciwa musa da ado da baba lado mutunci tas harda cewa insha Allah se gayyar ta watse.
Ko da wasa baba lado yaƙi barin su musa suyi magana har su Rabi'u suka gama cin mutuncin su suka tafi.
Zumuncin ne ya ƙarfafa a tsakanin hansatu da aisha da kuma baba matar baba lado wadda suka maidata uwa haka zalika ƴaƴan baba mata guda uku dasuke aure suma baƙaramin zumunci suke dasu Aisha ba.
Sukuwa su musa da ado sun zama kamar yaya da ƙani wanda suka ɗauki baba lado uba domin duk ƴan unguwama sun ɗauka cikinsu guda.
Ranar wata laraba Aisha ta haifu wanda ta haifi yaranta mata masu kyau tabarakallah.
Guda biyu baba da hansatu sune suka gyarata tsaf haka aka cigaba da zaman biƙi wanda baba ita take kula da Aisha.
Har tsawon kwana arba'in sosai musa yake kula da matarsa da yaransa waÉ—anda sukaci suna Hassana da Husaina.
Ƴan biyu suna da shekara ɗaya ta kuma haifar namiji mai suna muhammad ana ce masa shahid saboda sunan Alhaji mai katifa yaci.
Ƴan biyu sun taso cikin kulawar uwa da uba wanda suke cewa Aisha ( mama) musa kuma ( abba ) hansatu kuma ( iya ) kamar yadda ƴaƴanta ke gaya mata ado kuma ( baba ado ) baba lado kuma ( malam ) baba kuma matarsa sukan ce mata ( baba ) ƴan biyu sunada shekara biyu shahid yana da ɗaya mama ta kuma haifar ƴa mace sabida haihuwar kwanika take.
Yarinya ta haifa fara tas kyakykyawa ajin farko, lokaci ɗaya ta shiga ran Abba wanda atake anan ya saka mata suna BILKISU wadda suke ɓoye mata da BEBI saboda sunan mahaifiyarsa ne.
Abba ya É—auki son duniya ya É—orawa BEBI...............
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.