Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 58 of 81
Kimanin karfe shidan safiya kawu rabi'u Kawu tasi'u da sauran ƴan uwan mahaifinsu Bebi suka hallara a ƙofar gida suna tsara maganar yadda zata kaya da ɗaurin aure shawara suke akan yadda lamarin ze kasance wasu suna ganin kawai a ɗaura anan ɗin wasu kuma suna ganin atafi can ƙofar gidan mama a ɗaura auren domin tuni alhaji mai gwall yace zasu zone da misalin karfe taran safiya.
Kawu sani shiya dubi kawu tasi'u tare da cewa.
"Uban ango uban amarya ina kake ganin ya dace a É—aura auren sabida kaine silar kafuwar auren nan?"
kawu tasi'u wanda yake dogon tunani akan jin shurun mutumin jiya mai tafiya da lefe shiya dubesu fuskarsa cikin damuwa sannan yace......................
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *PART* 2
NAKUÆŠINE
*79*
"Ina ganin kawai atafi can gidan uwarta a ɗaura mata auren domin mu baza,a barmu da yin tuwon ɗaurin aure ba gwara kawai in munje an ɗauro auren mu zame mu barsu acan su ƙarata".
Cewar kawu tasi'u kenan wanda ya faɗi maganar cikin ƙwarewa da mugunta.
Dariya sauran sukai sannan kawu rabi'u ya miƙe yana kaɗe babbar rigarshi.
"Hakan yafi kaga daganan seka É—auko mana lefe mu rabe tunda mekuma yay saura an rigada an É—aura".
Cikin kawu tasi'u ne ya bada sautin ƙuuuuuuu! sannan ya fakaici idanun ƴan uwan nashi ya watsa masu harara amman a bayyane se cewa yay.
"To!to babu komai Allah ya kaimu lokacin kumiyi mu tashi muje muyi wanka mu shirya kada suzo suna jiranmu kunsan manyan mutane basa son jira".
Kowa yay na'am da maganarshi dan haka duka suka miƙe tare da.shiga cikin gidan kowa yay nashi shashen domin yin shirin fita ɗaurin aure.
Ko a ɗaki kawu tasi'u yana zaune bakin gadon ƙarfen matarshi hannunshi ɗauke da man shawafa na mai gurguwa yana lakatowa yana mitstsikawa a fatar ƙafarshi matarshi wadda ke zaune daga gefenshi ita ta dubeshi.
"Amman baban ladi abin nan naka akwai lauje cikin naɗi acikinsa tsakani da Allah ga ƴaƴanka ƴammata a zaune babu manemi faccaloli suna mana habaici amman ka tsallakesu katafi can wajan ƴaƴan mamaci ka ɗauki ƴa guda acikinsu ka kaita gidan maiƙo kai ƴaƴanka ko oho kenan kafison sune akan naka koko wata sabuwar ƙaunace ta motsa? ko kuma ita aishan ka leƙa kagani kakeso shine kake ɗan biki?".
Dariya ya kece da ita kamar wani taɓaɓɓe seda ya kusan mintuna talatin yana faman yin dariyar kafin ya ɗago ya dubeta sannan ya aje man a gefenshi.
"Haba babar ladi ina son ki ƙara fahimtar waye mijinki, ke kintaɓa ganin inda kaƙi ɗanka ka kama na gaibu? to bara na feɗe miki biri har bindinsa".
Ya faɗa mata hakan tare da mikewa tsaye ya ɗauki sabuwar shadda fara ƙarr ya soma sakawa cikin sauri seda ya kammala sannan ya dubeta wadda ta haɗe rai tana jiran kota kwana.
"Wannan aure dazamu haɗa waccan ƴar iskar da wannan gantalallen yaron to ba dan Allah bane ba, wato kinsan Alhaji mai gwall da mugun sangarta ƴaƴa mu kammu hakuri muke da zama a ƙarƙashinsa sabida halin ƴaƴansa, to hakance tasaka garin sangarta ƴaƴansa yaje ya lalata ɗansa khaleefa wanda yaron bakiga ashararancin dayake agariba kowa fa kuka yake da ɗan ɗanda bai ganin darajar manya bai ganin darajar kowa akanme zan ɗauki ƴata ta cikina na bashi ɗanda kullum yake cikin maye ubansa na kuma ɗaure masa gindi naje wataran ya kashen ƴata, to bama tawan yagani ba waccan matsiyaciyar ya gani yace yana so Allah cikin ikonsa akai arashi ƴar tazo a ƴar musa namu kinga ai faɗuwa tazo dai dai daxama shine na shiga na fita na ƙulla auren domin a dabgi arziki dani to kinji yadda ta kaya".
Dariya matar tashi ta saki sannan ta dubi mijin nata.
"Yanzu naji batu ashe dai duk gayyar tsiyarce kaida ci arziki baban ladi amman su ladi se gani daga nesa kai amman aisha anyi sokuwar mace yoni inda nice ai baku isaba, kai yanzu dan Allah bakaji kunyar aisha ba dakaje a matsayin É—an uwan uban Æ´aÆ´anta kun manta irin cin kashin da kukai mata amman ita harta tsaya ta saurareku wallahi inda nice seka tawo da makahon idanu".
Haɗe ranshi yayi"kefa haka halinki yake jarabar masifar tsiya to seme nace seme mudai mune tilashin ƴaƴan kota ƙi kota so dan haka yanzuma muna gama wannan zamu ƙara famjamawa mu ɗaukowa sauran wasu ƴan ƙwayar mu game mu huta".
Murmushi kurum tayi batace masa komaiba amman har cikin ranta ta jinjinawa aisha duk da bata son maman su bebi ko kaɗan amman setaji ta bata tausayi sabida yadda taga maxajen nasu na shirin ƙara jefa rayuwar ƴaƴan nata cikin gadar xare.
Harya fita baice da ita komai ba sabida haushin data bashi na yadda taji tausayin maman biyu, bayan ya manta su daman mata ababan raunine da wuya mace taga Æ´ar uwarta mace acikin wani yanayi bata taimaketa ba wannan abun yana matukar wahala kasancewar mata akwai tausayi da rauni koda baka bawa wanda kagani cikin wani hali agajiba tofa acikin ranka zakaji raunin hakan tare da zafi.
Abakin kofar gidan duka suka taru tare da sauran maƙota daƴan tsirarun dangi dasuka gayyata domin halartar ɗaurin auren.
Ƙarfe tara saura suka nufi sharaɗa can anguwarsu bebi lokacin tawagar Alhaji mai gwall tuni itama tayi gaba domin Khaleepha ya riga yasan gidansu bebi shiyasa basu sha wahalar gane gidan ba, Kusan a tare suka haɗu a ƙofar gidansu Bebin wanda har yawan mutanan wajan yaywa kofar gidan kaɗan.
Ƙarfe tara da rabi duk waɗanda suka kama zasu haɗu a wajan ɗaurin aure sun haɗu dan tsabar isa harda tabarmai suka taho dasu aka shinfiɗa a ƙofar gidan.
Cikin sauri shahid ya shiga gida yake shaidawa mama halin da ake ciki awaje domin shiya É—auka ma rasuwa akai sabida baida masinyar komai.
Murmushi mama tayi sannan tace.
"Mugunta fitsarin faƙo maza jeka kira malam tare da mai unguwa dan Allah banda sanya ka faɗa masa halin da ake ciki sabida kada a ɗaura aure akan aure".
Shahida bai jira mama ta ƙarasaba ya danna kai aguje ya tafi wajan malam lokacin dayaje ma tuni maganar ta isa kunnen malam ɗin zaman jiran mai unguwa ma yake yazo su nufi wajansu kawu tasi'un shahid baiko zauna ba mai unguwa yazo suka rankaya atare cikin sauri zuwa wajan ɗaurin auren.
Mama tana daga cikin gida tanajin ana addu'ar fara É—aurin aure babu abinda take se hamdala ga Allah wato cin zarafin dasukai niyyar mata kenan Allah ya tsallakar da ita.
Lokacin dasu malam suka ƙarasa wajan lokacin ne kuma yay dai dai da sanda limamin dasu alhaji mai gwall suka tawo dashi ya miƙe tsaye yana ambatar sunan tasi'u akan ya fito wajan wakilcin auren ɗiyarshi.
Jiki na rawa kawu tasi'u ya mike zuwa wajan domin shine waliyin bebi.
Cikin nutsuwa mai unguwa yay sallama a tsakiyar wajan.
Sabida shurun da wajan ya É—auka sakamakon gabatowar É—aurin auren yasa kowa yaji sallamar mai unguwa.
"Yawwa ina son na sanar da dukkan al'ummar dake wajan nan cewar, su dakata da wannan É—aurin aure domin ko anyishi bai halatta ba".
Cikin hargagin masifa kawu tasi'u ya mike tsaye.
"Sabida mai bai halattuba munafuki nace sabida me sabida kai ubanmu ne bamu nemi izinin kaba kaga kada kaga kaifa mai unguwane bazaka nuna mana halin iko muda Æ´armu ba ehe".
Murmushi mai unguwa yayi tare da karɓar loudspeaker dake hannun liman wadda akazo da ita irin mai amfani da batir ɗinnan ce sabida kowa yaji komai.
"Ba dan ni mai unguwa bane ba yasa nace aure bai É—auru ba sedan musulunci yadda yay mana nuni da hani da É—aura aure akan aure bi ma'ana ita wannan yarinya bilkisu yau take kwana É—aya tal agidan mijinta na sunna wanda nima na kasance É—aya daga cikin waÉ—anda suka zama shaidun É—aura wannan aure wanda kuma ba kowane ya kasance mijin nataba se ALIYU IDRISS MAI ATAMFA:MD MANAGER NA MAI ATAMFA TEXTILES! Wanda nasan in wani bai sanshi a wajannan ba tofa wani ya sanshi".
Mai unguwa yana gama faÉ—in haka ya juya zebar wajan.
"Ƙarya kake nina fi kowa sanin suwaye familyn mai atamfa ko ƴaƴan manyan masu kuɗi alhaji idi baya barin ƴaƴansa su aura sabida basa AUREN BARE azuri'arsu bare kuma wannan kucakar ƴar matsiyata kawai inzaku fito mana da yarinya ku fito mana da ita wannan shine magana sabida ni ɗinnan abokin cinikin alhaji idine babu yadda za'ai ɗan sa baba Ali yay aure mukasa sani wallahi ƙarya ne duk da kwanakin nan inna kira layin haji idi bana samu amman nasan kota egmail ɗinsa ze turo mana".
Mai unguwa yaji saukar muryar wani kakkauran dattijon mutum baki yana faÉ—in wannan magana a zuciye.
"Iya gaskiyar lamarin kenan amman inzaku É—aura ku É—aura ammanfa kusani kun É—aura banza domin angaya muku gaskiya malam zomu wuce duk wanda yake da tamtama acikin wannan lamari seyaje ya tambayi shi ALIYUN".
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.