Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 46 of 81

Yana da tsari a rayuwarshi wanda komai nashi a tsare yake tun yana karami yake da nutsuwa wadda tabi jikinshi har zuwa girmanshi, wannan dalilin yasa baya shiri da mutum mai rawar kai sabida shi mutum ne nitsatstse sau tari sukan yi faÉ—a da usman akan surutunshi.

Akaf Æ´an uwanshi yafi shiri da usman sun shaku komai nasu É—aya hakanan Aliyu da usman sukanyi sirrinsu batare da kowa yajiba.
Aliyu yana son usman sosai hakanan shima usman É—in nason Aliyu wani zubinma har Æ´an biyun ammi ake ce masu.

Ko kaÉ—an baya son khadija har cikin ranshi amman yadda mahaifanshi suka bashi umarni akan ya aureta yasa bai masu musu ba.
Sabida a tsarinshi baison karamar mace yafison babba wadda ta mallaki hankalin kanta, duk da khadija ba yarinya bace kuma tana da hankalinta amman shi baison mace irinta ko kaɗan bata burgeshi, sabida khadija akwai iyayin tsiya tare da shige masa shikuma mutum ne wanda baida son zaƙewa a rayuwa.

Khadija doguwa ce amman bacan ba farace tass wadda harta É—an fara É—ashewa batada wani jikin kirki domin yanayinta kamar ta tsinke, tana da rashin magana, dan baza,a sakata ajerin masu son mutane ba don ko a makaranta batada kwashe-kwashen kawaye ita dai barta da iyayinta.
Tana da mugun kishi akan abinda takeso wannan dalilin yasa bata yarda da wata tazo gidansu bare suyi katari da Aliyu.
Tana da tsafta hakanan batada son jiki domin tasami ƙwarewa akan girke girke kala kala tare da kyaran jiki da gayu sabida umman ta gaskiya tanada tsafta.
Tana son Ali sosai wanda har bata iya ɓoye sonshi a ko ina.
Sedai gefe guda harda kwaÉ—ayin abinda Aliyun ya mallaka domin arayuwarta tanada son fantamawa tafison taga tafi kowa acikin familyn su tafison tashiga jerin matan dasuka amsa sunansu mata tafison taga ta mallaki manyan kaddarori waÉ—anda zata shiga cikin jerin mata first class masu kuÉ—i da jin daÉ—in rayuwa, wannan dalilin yasa ta rike wuta harseda burinta ya cika akan Aliyu taga ta mallakeshi a matsayin mijinta gashi kuma burin nata ya cika na mallakar Aliyun bara muga kozatai nasarar mallakar zuciyar tasa..

Kunji tarihin ALIYU yanzu kunsan waye shi da kuma zuri'arsu.

*DAWOWA LABARI*
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *PART* 2

NAKUÆŠINE

*66*

_CIGABAN LABARI_

Aliyu bai san bidirin dasu usman sukai ba hasalima bai san komai akan faruwar lamarin auren ba.
Shidai jiya sun rabu da usman akan cewar zega mai yuwuwar samawa yarinyar gurbin makarantar kwana mai tsada yasan intai nisa da gida babu mai takurata bare ai mata wannan auren.
Abinda kuma usman ya raɗa mashi jiya a mota shine xasu san yadda sukai ta dawo wajan ammi da zama inyaso in ta dawo hutu tai zamanta a wajan ammi da wannan dabarar suka rabu da usman ( lallai akwai ƙura ! )
Bai tashi a baccin shi ba se wajan 12 Na rana salatine ɗauke acikin bakinshi yana miƙe ƙafafunshi waɗanda ya saukesu daga saman gadonshi, jikinshi sanye da guntu wando kasancewarshi bamai kwanciya da kayaba, koda ya zira kayan bacci tofa cikin dare seya tubesu kuma baya son rufa yafi bukatar ya kwanta a haka.
Rabonshi da bacci tun karfe huÉ—un asubahi daya tashi yay nafila, ya wuce masallaci bai shigoba se shiddan safiya wajan motsa jiki yaje yay morning training bai shigoba gida ba se wajan 8 ruwa kurum ya watsawa jikinshi ya kuma kwanciya shine bai tashiba se yanzu.
Gaban kofar bathroom É—inshi yaje ya É—auko katon towel mai kalar dark blue daurashi yay a west É—inshi bayan ya zame guntun wandon dake jikinshi cikin bathroom É—in ya shiga yay brush tare da watsa ruwa ajikinshi.
Yafito dukkan ilahirin jikinshi yana É—igar da ruwa.
ƙaramin towel ya ɗauka ya tsane ruwan jikinshi tare da nufar gaban AC controll ɗin ɗakin ya ƙaro ƙarfinta janyo stool yay ya zauna gaban mirrow yana shafa cream a skin ɗinshi cikin sauri.
Æarin body spray, yaywa kanshi sosai yabi kowani saÆ™o da lungu na jikinshi ya goga turarenshi na arabian uod, sannan ya gyara kwantaccen sajenshi mai haÉ—e da gemunshi, tashi yayi ya nufi gaban close set É—inshi.
Ɗanyen farin boyel mai yankan gidan sugar ya ɗauka wanda akai mashi ɗinki da golden ɗin zare dogayen kayane har ƙasa, shirya kanshi yay cikinsu still ya kuma yima kanshi barin turare.
Phone É—inshi dake yashe bisa saman bedside ya É—auka tun jiya bai kunnata ba yanzun ma kuma baida niyya kunnawa sabida baya son yawan damu yanajin dukkan jikinshi ya gaji babu abinda yake bukata se hutu, sakamakon yawan zirga zirgar dayake yi bai samun xama shikam kusan kullum yana kasuwa ko yana wani uzirin a office.
Taka ƙafafunshi yay a saman lallausan chanies carpet ɗin dake malale a center'n ɗakinshi handle ɗin kofar ya bude ya fita falo.
Tundaga bakin room ɗinshi wani irin daddaɗan kamshi ne ke mashi well come! mamakine ya kamashi lokacin da idanunshi sukai arba da ƙayataccen tiren sliver a tsakiyar table ɗin dake falon, an jere falasai a samanshi gawata ledanan irin ta rafin an rufe tiren da ita da alamun kayan break fast aka jere a kan tire ɗin.
Zama yay akan one seater tare da kallon tvn dake kunne ana wani indiyan film mai kyau.
Kimanin mintuna biyar yayi yana kallon film É—in yana kuma jin dadinshi sabida shiba ma'abokin kallace kallace bane ba amman wannan film É—in yay masa kyau tare da daÉ—i sabida soyewar da ake cikinshi.
Baƙon sassanyen kamshine yake kusantoshi rintse idanunshi yay yana kuma kwantar da kanshi a gefen hannun kujerar harta karaso gabanshi.
"Assalamu Alaika"!
TafaÉ—a tana tsugunnawa gabanshi.
Can cikin makoshin sa yace mata.
"Amin wa'alaikissalam".
Domin seda tai da gaske taji abinda yace É—in.
"Yaya barka da safiya fatan ka tashi lafiya naga hidima jiya nagode Allah ya ƙara buɗi da ɗaukaka amin".
Da sauri ya wara idanunshi yana kallonta.
Sanye take cikin atamfar holland ja wadda akai mata ɗinki rafa na riga da zani setai wani irin firit acikin kayan sabida batada ƙiba.
Dariyace taso kamashi ganin yadda tai kamar kace mata kett ta arce gawani irin burum datai acikin riga da xani domin ko kaÉ—an basu amsheta ba, dogayen riguna sunfi mata kyau.
Amman sanin zataga kamar yay mata cin fuskane seya kanne ya basar tare da barin dariyar can kasan ranshi.
"Yaya the break fast is ready"!
TafaÉ—a tana nuna mashi da É—ayan hannunta.
"Tun É—azu nai niyyar tashinka naga time yana wucewa amman sanin kayi zirga zirga kaji wahala yasa na barka kasami hutu".
Tafaɗa tana miƙewa daga gabanshi wajan kayan karin taje ta soma sauko dasu kasan carfet.
"Yaya abinda yasa ban kaisu daining ba sabida nasan sekafi jin daÉ—in yin break a kasa nima banciba kai nake jira".
Mamaki take bashi na wannan rawar kan datake mashi.
Amman bai magana ba, sedai can cikin ransa yaji dadin yadda tai mashin danshi yana son a girmamashi a riritashi aji dashi a waje musamman wajan matarsa ta sunna.
Yanajin yadda ta karramashi inya ƙi cin abinci kamar ya zuba mata kasa a idanunta ne.
Dan haka cikin nutsuwa ya taso daga kan kujerar tare da komowa kasa ya zauna gabanta yana facing É—inta yana ganin yadda take sarving break É—in acikin plate cikin nutsuwa tare da tsantsenin tsafta.
Kallon yatsun hannunta yake ta kasan idanunshi wanda yake hango zallar tsaftar khadija a cikinsu sabida yadda suke a yanke ƙar-ƙar dasu, aransa yakejin kodan tsaftar dake gareta ze iya cin abinda ta bashi.
plate biyu tai na soyayyen dankalin turawa tare da miyar source É—in hanta agefensu kamshinsu ne ya cika masa hanci.
Tura mai nashi tayi gabanshi tare da É—auko cokali mai yatsu ta saka aciki.
"No ki fara bani black tea nasha"!
yafaÉ—a kamar an tilasa mashi.
Cikin jin daÉ—i ta amsa masa tare da janyo tea flaks É—in dake gefenta.
Ta É—auki white tea cup ta bude flaks É—in ta fara zuba mashi ruwan tea É—in data masa hadin su na'a na'a dasu kanun fari, tun tana zubawa kamshin kayan hadin yagama cika falon harta kammala ta saka tea spoon ciki tare da miko mai gabanshi.
Dayake da sugar take dafa shayi domun yafi ji tare da kara lafiya.
Mamakin yadda ta iya sarfa girki yake cikin ranshi tare da tsaftar ta amman bai ce komai ba seya karba tare da ajewa gabanshi.
"Nagode!"
YafaÉ—a tare da yin bisimillah ya fara shan tea É—in wanda bakaramin daÉ—i yay mashi ba............

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.