Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 68 of 81

*Mai son littattafaina dana kammala complt documents akan farashin naira dubu É—aya ( 1000) waÉ—anda suke guda biyar ciff seya nemi 08142105218*

*RABON WANI*

*H A S K E*

*KOBA SO*

*ÆŠAN MAJALISSA*

*DA IZZATA*

_Gaba É—ayansu babu na yadawa siyan nagari mayar da kuÉ—i gida_ ðŸ˜
11/14/21, 3:13 PM - Allah Akbar: *89*

Driving yake cikin nutsuwa fuskarshi ɗauke da matsanancin farinciki wanda shi kanshi ya kasa gane kona miye ahaka harya ƙarasa fita daga cikin unguwar kanshi tsaye babban titi yahau wanda ya bashi damar ɗaukar hanyar sa ta gidansu.
Tafiyar mintuna masu yawa ya shafe yanayi asaman kwalta har Allah ya bashi sa,a ya shiga cikin unguwarsu lokacin gari yaɗanyi rana saɓanin ɗazu da hadari ya haɗo kamar za,a sheƙa ruwa.
Lokacin daya isa bakin gate É—insu har ansoma yin kiran sallah acikin waÉ—ansu masallatan, a nutse yake rage gudun motar tashi wadda take tafiya a slow harya zo daf da gate É—in kana ya danna horn.
Cikin nutsuwa ba kamar É—azu da zasu fita ba.
Cikin azama masu gadin gidan suka sheƙo aguje domin zuwa su buɗe mishi gate ɗin.
Seda suka ɗan leƙo da kansu suka tabbatar da shiɗinne kafin sukazo suka bude mishi suna masu ɗaga mai hannu.
Cikin nutsuwa yake jan kan motar harya idda shiga tafkeken ma'adanin motocin gidan nasu kana ya gyara parking ɗinshi tare da dai-daita motar sa'annan ya kasheta ya fito waje yana shaƙar iskar harabar gidan nasu tare da kamshin furran dake harabar wajan.
Jan ƙafafun shi yayi zuwa ainihin part ɗinshi seda ya kama kofar datake maƙale da gate ɗin sannan ya tuna cewar ya gayawa dija baze dawo yau ba, amman kuma dole ce ta sakashi dawowar tunda kiran abbanshi ne, buɗe kofar yayi kana ya zura kafafunshi cikin part ɗin nashi tare da ƙarasawa ya buɗe kofar falon ƙasa ya wuceshi kana ya haye samanshi, Buɗe ƙofar falon samanshi yay ya shiga bakinsa dauke da sallama, khadija ce ta amsa masa sallamar tana zaune a falon tana kallo jikinta sanye cikin vest da threequater vest ɗin jace shikuma wandon baki kanta babu kallabi se dogon kitson datai wanda ya zubo mata har wajan kirjinta waɗanda a kwana biyun nan suka ɗan tasa kaɗan.
"Lah yaya dama xaka dawo amman baka gayamin ba dana maka girki duk na É—auka se goben".
Ta faɗi hakan bayan ta tashi tsaye tare da nufarshi ta karɓi keyn dake hannunsa.
Murmushi yayi mata kaɗan wanda ya tsinci kansa acikinsa yau tun tashin sa kana ya dubeta cikin tsantsar kulawar da bata taɓa samunta a wurinshi ba.
"Na dawo dija abba ke nema na yasa na dawo amman ƙilan na koma anjima ko gobe".
Yana faÉ—in hakan ya nufin hanyar bedroom É—inshi.
Da sauri itama tabi mashi baya tana masa magana akan yadda tai farin ciki da dawowar nashi.
Se yau ta ƙarewa bedroom ɗin nashi kallo wanda babu wasu tarkacen kaya acikinsa komai tsaf, Bata tsaya ɓata lokacinta a kallon tsarin ɗakin nashi ba ta wuce cikin kofar data gani a gefe wadda take tunanin bathroom ne ruwa ta soma haɗa masa mai ɗan dalam dalam kana ta fito lokacin yana kokarin sanya rigar wanka.
"Yaya na haÉ—a maka ruwan wanka"
Juyowa yay tare da zuba mata idanu.
"Nagode dija".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ba naje na sama maka abu marar nauyi domin nasan tundaga tean safiya da ƙyar idan kaci wani abun"
Bata jira cewarshi ba ta fice a É—akin murmushi yayi kana ya faÉ—a cikin bayin wankan kusan awa guda yay tare da É—auro alwala ya fito duka jikinshi yana É—igar da ruwan damshin wankan.
Gaban mirrow ɗinshi yaje ya tsaya yana goge ruwan dake jikinshi tare da shafa cream sama sama turaruka masu daɗin kamshi yayma kanshi ɓari sannan ya nufi gaban kayanshi ya shirya kanshi cikin wata ɗanyar dark blue gezner wadda aka mata ɗinki half body wanda ya fito da tsantsar baiwar cikar halittar da Allah yayi mishi seda ya kuma watsawa jikinshi wasu turarukan sannan ya ɗauki agogonsa fari na rolex ya saka,a tsintsiyar hannunshi takalmin fata ya saka wanda yay marching da kayan jikinshi hakan nan hular dayay amfani da ita ta tangaran itama mai shigece da kayan na jikinshi.
Masha Allah! Anan ya fito a ainihin Aliyun shi kuma a ainihin shigar al'adarshi ta yaren hausa fulanin usul.
Gemunshi yaÉ—an janyo kaÉ—an yana shafawa kana ya fita daga É—akin yana barin kamshinsa acikinsa.
Gaba É—aya falon nashi ya É—auki mugun daddaÉ—an kamshin girkin da dija keyi zama yay akan É—aya daga cikin royal chair din dake falon yana mai É—aukar remote ya tsaida tv É—in dakeyi sabida kiran sallar da ake yi a masallacin cikin gidan nasu.
Yana zaune bini bini ze É—ago hannunshi ya duba agogo sabida bai son abba yay sallah ya dawo basu haÉ—u ba.
A haka ta shigo falon hannunta ɗauke da plate wanda ta zubo ƴar jallof ɗin cous-cous ɗin data yi mai wanda tai decoreting ɗinshi da kayan vegitables masu ƙayatarwa, da ɗayan hannun ta janyo table ɗin dake tsakiyar falon ta aje mai plate ɗin akai sannan ta tura mai gabanshi tana mai cewa.
"Ga abincin nan ina zuwa".
Kallon abincin yayi sau É—aya ko kaÉ—an baya son cous cous amman sabida bai son yaga ya jisgata yasa ya É—anja spoon É—in tare da faÉ—aÉ—a shi sabida yaÉ—an huce.
Babu laifi ya daina wannan tururin dan haka yay Bisimillah.
Kana ya É—auki spoon É—in ya soma É—iban shi kaÉ—an yana kaiwa bakinshi kuma girkin yayi daÉ—i sedai baya son cous cous shiyasa lomarshi É—aya ya ture duk da tsananin yunwar da yake ji.
Tawowa tayi hannunta É—auke da wani É—an medium jug se cup guda gabanshi ta aje a gefen plate É—in tare da tsiyayo mai lemon kwakwar data haÉ—a yanzu seda ta cika tamm sannan ta tura mai gabanshi sannan ta nemi guri ta zauna tana kallonshi tana yaba kyawun dayayi tare da jin kishin wannan kwalliyar kada mace ta gansa a waje.
"Sannu nagode".
YafaÉ—i tare da É—aukar cup É—in data haÉ—a mai lemon kwakwar ya kafa a bakinshi yana mai jin daÉ—i sabida garÉ—i da daÉ—in lemon a zuciyarshi.
Seda ya shanye gaba ɗaya sannan ya miƙe yana mai ɗaukar phone ɗinshi.
"Kije É—akina ki É—aukon keyn mota".
Taji maganarshi cikin sauri taje ta É—auko mai ta kawo masa.
"Zan fita any way dai zamuyi waya".
Yana faɗi mata haka yabar falon sejin ƙarar fitarshi tayi.
Tattare wurin tayi ta shiga sabgarta tana jin ranta sakayau na yadda yau ta sami kansa.
Seda yaje masallaci sukai sallah sannan suka jero tare da usman wanda ke faman yi mai tsiya bai tankashi ba har sukaje part É—in abba a falonsa suka haÉ—u anan suka zauna sukai maganar da zasuyi sannan ya wuce mota.
Bai sami zarafin leƙa ammi ba sabida akwai inda ze biya.
Koda ya fita daga gida kai tsaye harba hancin motarshi yayi zuwa unguwar sharaÉ—a.
Abakin layin gidansu Bebi yaja ya tsaya seda ya kintsa komai sannan ya fito daga motar ya shiga cikin layin da ƙafafunshi.
A ƙofar gidansu Bebi ya tsaya yana faman leken kozaiga ɗan aike cikin haka shahid yazo ze shiga a mamakin Aliyu seyaga yaron ya tsaya tare da rissunawa yana gaisarshi.
Tsira mai idanu yay yana hango tsabar kamar yaron da Bebi hatta haskensu kusan kai É—ayane.
"Dan Allah ƙanina kacewa mama ga ɗanta yazo".
Zaro idanu shahid yay kamar yadda bebi keyi kana ya juya batare daya ce komai sedai iya acting É—inshi kaÉ—ai ya fahimtar da Aliyu cewar yaji mamakin furucinsa ne.
Mintuna biyu shahid ya leƙo "wai tace ace ka shigo".
Cikin kamala yaja katon bugun da aka lulluɓe soron ya shiga yana mai sallama kana ya bayyana a tsakar gidan.
Mama wadda take zaune akan kujerar tsugunno iya kuma tana kan tabarma ƴan biyu suna ɗaki suna faman shirin zuwa gidan bebi harma da sadiya.Ita ta amsa sallamar duk azatonta usman ne ma amman ganin Aliyu yasa ta gyara mayafinta sosai tare da sunkuyar da kanta ƙasa bakuma tayi masa magana ba se iyace tai saurin gyara mai tabarmar ya zauna.
Muryarshi mai sanyi ita ta karade kunnuwansu, yana gaisar dasu.
Seda ya soma gaisar da iya sannan yace.
"Umma barka da yamma ya gida?".
Ta cikin mayafi mama ke amsa masa sabida itafa Allah ya zuba mata jin kunyar surukai kosu ya aminu ma tunda taji kanun maganarsu da Æ´an biyu yanzu bata sakewa da su ko kaÉ—an.
Mama tasan Aliyu iya kuma bata san shine mijin Bebi ba sedai tayi mamakin ganin yadda mama ta koma tsit dan haka iya ta kada baki tace.
"Mamam Æ´an biyu yanaji kinyi bako kuma kin masa shuru kodai surukin namune?".
Se lokacin taÉ—an É—ago kaÉ—an.
Batacewa iya komai seta soma cewa.
"Hassana! hassana zo mana".
Sannan ta É—an dubi Aliyu wanda tsabar mamaki ya kamashi tace.
"Toya gidan naku dafatan dai bata maka wannan shirmen nata ko, Allah ya saka maka da alkairi angode".
TafaÉ—i maganar a rarrabe.
Atare su hassana suka fito dukkansu har sadiya.
hussaina ce ta sanshi dan haka cikin sakin fuska tace
"Lahhh umma fa Ya Aliyu ne mijin Bebi wallahi shine ina yini?".
TafaÉ—a cikin far'arta.
Ba yabo ba fallasa yace
"Lafiya"
Haka hassana da sadiya wadda ta saki bakin mamakin haÉ—uwar mijin kawarta ta suka gaisar shi.
Se lokacin shahid shima ya fahimta aikwa cikin sauri ya xare jikinsa mintuna biyu sega shi ya dawo hannunshi É—auke da bakar leda ya mikawa hassana.
Ta karɓa lemo ne da ruwa ta juyo a saman tire ta kawo masa kana suka bar wajan suka koma cikin ɗaki.
"Haba maman biyu base kice min surukin namu bane ko yau karar akansa ta motsane bafa shi bane na farko".
Iya ta faÉ—a tana dariya.
"To dafatan dai Bebi tana lafiya? domin yanzu da ake shirin tura Æ´an uwanta su gano mana ita"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.