Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 74 of 81
*****************
*ZUMA A BAKI...!*🌹
{ Painful love Story }
_Shine sabon littafina da ze soma zuwa da zarar na kammale wannan kedai/kaidai maza ka hanzarta ka biya naka domin tun kafin na soma posting ɗinshi zan soma karɓar kuɗin masu son karantawa kai dagajin sunan kasan akwai rikita rikita wadda bazan ce komai ba amman rubutuna ze bayyana muku *Zuma A Baki* comming soon da izinin Allah ƙofa a buɗe take masu soma payment_
*ÆŠAN ÆŠANO*!
_Wannan karon tafiya nai mai mugun nisa har naje na zaƙulo muku ƙayataccen labarin masoya Biyu *Umar Muhammadu Sarkin-Gida* wanda jama'ar unguwa da abokai ke masa laƙani da ( *Cika Daji* ) Eh cika dajin ne mana sabida duk umar ba,a rago to hakance ta kasance ga shalelen inna kuma autanta wanda ya tsunduma a dafkin kogon soyayya da *Aishatul humaira* ɗiyar anty Har soyayyar tasu ta zamewa kowannen su *ZUMA A BAKI* Tabbas tunda nake rubutuna bantaɓa katari da labarin daya kwantamin ya tsayamin kamar ZUMA A BAKI ba! tabbas kodaga jin sunan kasan akwai rikita rikita kuda kawai kubiyoni nasan insha Allah bazan baku kunya ba_
*Hohoho! my fans nace muku painful wallahi da gaske wannan soyayyar mai zafice mai raÉ—aÉ—i ce duk wani masoyi yaci katari da wannan labarin nawa seya dara seya koka seya warwasa labarin ze Æ™ayatar ze tsaya arai ze nishaÉ—antar ze wa'azantar ze ilimantar kudai kubiyoni kawai*💃💃💃💃ðŸ¤ðŸ»
_kai ƙoƙarin ganin kayi payment domin zan soma sakin sane da zarar na kammale wagga_
~N~ *300*# *ta wannan account numbern 0078174806 starling bank show me your evidance of payment ta wagga numbern 08142105218 love you my Æ´an amana my Æ´an iya wuyata*
******************
Kamota yayi ya haÉ—e da jikinshi yana goga mata sajenshi na fuska.
"Wallahi Beby kinfi min mata ɗari, kina bani zumar danake manta kaina babu macen data isa ta kallan tace tana sona seke beby na haba ƙaramar ƙasa mai albarkatun man fetur"
Yafaɗa yana tsotsar mata ƙasan lip's ɗinta danasa lip's ɗin.
Sosai yasha wahalar shawo kanta kafin ta daina mai rigima, hijabi ta saka suka fita daga gidan da kuka suka rabu ya shiga mota shima yana share hawayen love.
Seda taci kukanta a ɗaki ta ƙoshi kana ta kamo kayanshi daya cire ta rungume gashi yaƙi bata waya bare ta kirasa.
Ahaka bacci ya kwasheta wanda rabi tunanin shine.
******
Akasalane yake driving komai ya tsaya mai cak a ranshi.........
*ZUMA A BAKI...!*🌹
{ Painful love Story }
_Shine sabon littafina da ze soma zuwa da zarar na kammale wannan kedai/kaidai maza ka hanzarta ka biya naka domin tun kafin na soma posting ɗinshi zan soma karɓar kuɗin masu son karantawa kai dagajin sunan kasan akwai rikita rikita wadda bazan ce komai ba amman rubutuna ze bayyana muku *Zuma A Baki* comming soon da izinin Allah ƙofa a buɗe take masu soma payment_
*ÆŠAN ÆŠANO*!
_Wannan karon tafiya nai mai mugun nisa har naje na zaƙulo muku ƙayataccen labarin masoya Biyu *Umar Muhammadu Sarkin-Gida* wanda jama'ar unguwa da abokai ke masa laƙani da ( *Cika Daji* ) Eh cika dajin ne mana sabida duk umar ba,a rago to hakance ta kasance ga shalelen inna kuma autanta wanda ya tsunduma a dafkin kogon soyayya da *Aishatul humaira* ɗiyar anty Har soyayyar tasu ta zamewa kowannen su *ZUMA A BAKI* Tabbas tunda nake rubutuna bantaɓa katari da labarin daya kwantamin ya tsayamin kamar ZUMA A BAKI ba! tabbas kodaga jin sunan kasan akwai rikita rikita kuda kawai kubiyoni nasan insha Allah bazan baku kunya ba_
*Hohoho! my fans nace muku painful wallahi da gaske wannan soyayyar mai zafice mai raÉ—aÉ—i ce duk wani masoyi yaci katari da wannan labarin nawa seya dara seya koka seya warwasa labarin ze Æ™ayatar ze tsaya arai ze nishaÉ—antar ze wa'azantar ze ilimantar kudai kubiyoni kawai*💃💃💃💃ðŸ¤ðŸ»
_kai ƙoƙarin ganin kayi payment domin zan soma sakin sane da zarar na kammale wagga_
~N~ *300*# *ta wannan account numbern 0078174806 starling bank show me your evidance of payment ta wagga numbern 08142105218 love you my Æ´an amana my Æ´an iya wuyata*
11/14/21, 3:20 PM - Allah Akbar: *95*
Da wani irin mutuwar jiki yake driving É—in shi kaÉ—ai yasan yadda zuciyarshi take tsananin jin kewar yarinyar da gaske tana da mugun shiga can cikin ran É—an adam yana jin yana mata wani irin azababban so na fitar hankali, bayajin ze iya rintsawa batare da itaba.
Ya jima yana driving kafin ya isa gida, dayake khadija tasan da zuwan nashi tuni ta kammale komai na gida gashi kuma alhamdulillahi É—an satin dayay bai nan ta samu damar gyara jikinta sosai da magungunan da anty ruma ta kawo mata.
Kai tsaye wajan ammi ya nufa ya tadda ita a falo tana zaune waya a hannunta ganinsa yasa ta aje wayar fuska ba sukuni take amsa mai gaisuwar daya ke mata.
Kafin ta haÉ—e rai tahau surfa masa masifa kamar zata ari baki.
"Sannu baba nace sannunka da shuka yanzu kai haka adalcin naka ike? kawai katafi masha Allah kabarmu da matarka baka ko leƙo mana ba?"
TafaÉ—a tana mita sosai.
Seda ya jira ta gama faɗanta sannan ya kwantar dakai kamar ƙaramin yaro yana bata Haƙuri.
"Ammina kiyi hakuri, wallahi mai sunaki ce batada lafiya shine na zauna sabida babu wani kusa da ita"
YafaÉ—i hakan domin yasan ta hakanne kaÉ—ai zata rabu dashi.
Sosai ammi ta washe haƙoranta.
"Masha Allah baba amman dai kunje asibiti ko?"
Sosa kanshi yayi.
"Ban kaitaba amman inna koma zamuje"
Murmushin ta kumayi, sannan ta dubeshi.
"To inka huta kaje kaiwa É—an uwanka barka zainab ta sami Aliyu jiya ta haihu ganin dare yasa ba,a gaya maka ba ubansa yay maka takwara, Sannan ankawo lefen su amina fa harda Æ´an biyu abbanku yace sun gama school gwara an haÉ—a dasu tunda sunada mazajensu a hannu an saka rana nan da two weeks"
Ƙayataccen murmushi ya saki yana furta.
"Kai dik dai ammi masha ALLAH, Allah ya raya takwarana amman ni usman bai faÉ—amin ba?"
Murmushi ammi tai.
"Ance maka dare ne yayi shima fa yayanku umar fa humaira ta haifi mace yau kwana biyar kasan suna can legos É—in duk se biki zasu tawo"
A wannan karon kabbara yake bakinshi É—auke da far'a sosai yake jan addu'a a bayyane ammi tana amsa mai kana ya mike.
"Ammi banaje na gano my boy, wallahi sena ganshi zan wuce kafin na kawo ragon suna takwara ai ba wasa ba"
YafaÉ—a yana nufar hanyar fita.
Da fatan alkairi ta bisa tana yabon haÉ—inkan zuri'arta sosai take kuma godiya ga Allah akan hakan.
A bakin part É—in ammi ya tsaya yay wa ya umar waya yay mashi barka harda É—an mitarshi akan yadda bai gaya masa ba hakuri ya bashi sannan sukai sallama ya tafi, bayan yay masa transper kuÉ—i wai a saiwa takwarar ammi pampers.
Cike da annashuwa ya isa part É—in usman duk yan uwansu suna zazzaune a falo ana yiwa yaron wanka sosai suke kwasarshi yana wani basarwa dayake duk abokanan wasane yasa suke mashi hakan.
Bayan angamawa yaron wanka aka naÉ—oshi a tawul aka mikawa Aliyu shi, addu'a yay masa sannan ya mike suka jero da usman.
"Man kai kaga yadda kai wani fresh so masha Allah, amarya ta amsheka"
Usman yafaÉ—a yana dariya.
Shima Æ´ar dariyar yay kaÉ—an sannan yace mai.
"Bazaka gane ba amman dai nina san yanzu nayi aure fa, Alhaji kaikaga yadda ake tattalina"
YafaÉ—a yana shafo gemunshi.
"Dama ai irin waɗannan sunfi daɗi yar shila malam amman da ana baka kana ƙin amsa"
Murmushi yay mai kana yace.
"Bazaka gane irin son da nakewa beby ba wallahi usman ka gama min komai a rayuwata Allah kaima ya faranta maka kamar yadda ka faranta min"
Sosai usman yake dariya ganin yadda ƙanin nashi ya zarme da yawa tab daman akwai ranar da Aliyu ze iya sauke jida kanshi yace yana son mace lallai so ba wasa bane ba.
Ganin usman ze mayar dashi sauna yasa ya wuce part ɗinshi shima bakinsa kunshe da dariyar yabar usman dashe a wurin yana dariyar ƙeta.
Sosai ya sami tarba a wajan madam dija kuma shima É—in bai mata irin Wannan shariyar da yake mata daba sabida yana son ya kwatanta adalci gudun fushin ubangiji.
Da taimakonta yayi wanka ta tayashi ya kintsa, se wani maƙele mai take ajiki shikuma yana wani basarwa abinci ta haɗa masa mai rai da lafiya, kaɗan yaci ganin tana wani irin mirmir da idanu ya gane mai take nufi ɗaukarta yay cak ya nufi ɗakinsa da ita sosai ya ruɗa mata jikinta da salonshi kafin ya kama hanyar dayafi kauri.
Babu laifi baiji wannan azabar dayaji kwanaki ba sedai ko kaÉ—an bai sami É—anÉ—anon daya samu wurin bebi ba domin ita bebi kusan haukacewa yake inya tare da ita.
Bai wani jimaba ya rabu da ita ya mike yaje ya tsarkake jikinsa yazo ya shirya kanshi cikin wani marun boyel mai manyan zane, yana fesa turare ya dubi dija datake kwance kamar gawa bama ta da niyar tashi.
"Dija ki tashi mana ki tsaftace jikinki"
Taji amon! muryarshi acikin kunnenta da ƙyar ta mike tana ware ƙafafu ta fita daga ɗakin tanajin kamar an mata shegen duka domin ta gurzu.
Dariya yay afili kana ya furta.
"Tabb lallai kinada aiki banyi good 30 mnt ajikinki ba kike wannan gandar, lallai dija raguwace, waccan yarinyar semu wuni muna abu ɗaya bata taɓa gajiya ba sedai intaji yunwa taci abinci mu koma, amman ke daga sau ɗaya se ragwanci tabb,itako umminah ka daɗi ga dauriya wayyo i miss"
yafaÉ—a yana dafe jikinshi da hannunshi, a gaggauce ya shirya ya nufi masallaci sukai sallar azahar sannan ya É—auki mota ya nufi gidan mama sabida tunda yaje sau É—ayama bai koma ba.
Sosai yay mamakin yadda aka ƙere gidan bayan haka kuma masu aikin sunyi mugun sauri.
Harda É—an gate a kofar gidan ga wani uban fanti mai azabar kyau da aka yima gidan.
Parking ya gyara yana neman wanda ze aika.
Kamar daga sama sega shahid akan lifan dinsa da Aliyun ya sai masa sabida zuwa makaranta.
Yana washe baki ya ƙaraso gabansa ya rissuna yana gaisar da shi.
"Yaya Aliyu barka da rana, yanaga ka tsaya a waje yakamata ka shiga ciki aikaima É—an gidane"
Murmushi yayima shahid sannan yace.
"Kai dai shiga kacewa mama ina waje"
"Tom bara na sanar da ita daman lefensu hassana aka kawo fa É—azu, ansaka biki nan da sati uku"
Murmushi ya kuma sauke masa.
"Kai shahid da sauri haka za,a É—ebewa mama Æ´aÆ´anta?"
"Wallahi yaya da ai shekara aka saka to kuma su yaya nuran sesuka ce tunda sun gama gininsu kuma sun sami aiki su kawai suna so ai da wuri"
Zaro idanu Aliyu yayi kaÉ—an wanda yake kara masa kyau kana yace.
"To Allah ya nuna mana lokacin Amin"
Shahid seda ya sanar da mama wadda tahau shi da faÉ—a damme baze ce ya shigoba sebarsa a waje.
"Mama fa seda na gaya mai shikuma yace nadai sanar dake"
Sannan ya fita wajan suka tawo tare da Aliyun
Sosai gidan ya burgeshi babu dai wani girman kirki sabida wanda aka siya ɗinma bawani babba bane sedai tsarin fasalin gidan ya ƙayatar kana shiga tsakar gidane da bayi.
Se ƙofar falon mama da aka zuba mata kujeru ma dai daita da ƴar tv ta bango harda ƙaramin frij, se kicin acikin falon se ɗakuna guda uku na shahid ɗaya na mama ɗaya na su hassana kuma duka da toilet cikinsu,se ƙaramin store sosai aka ƙayata gidan kamar ba shiba, kuma badaga wajan kowa wannan sauyin yake ba sedaga wajan Aliyu domin shiya wakilta wani yaronshi akan komai na gidan hatta saitin kayan ɗaki na kicin dana sakawa duk an kawo musu sabbi domin ɗakin mama gadone da sif da madubi hakama sauran ɗakunan su shahid ɗin bakaramin kuɗi fa gidan ya lashe ba, amman shi baiji komai ba sabida bebi ta bashi abinda yafi wannan daraja.
Sallama yayi cikin nutsuwa ya shiga falon iskar fanka tanata kaÉ—awa.
Mama wadda take zaune saman kujera tai saurin amsa masa tana gyara zaman hijabinta yatsunta jajur da lalle.
A ƙasan center carpet ya zauna yana gaisar da ita.
Tana amsa masa itama cikin kunya sannan ta mike taje frij ta É—auko mai pure water ta zuba a plate ta kawo mai kicin ta wuce ta zubo masa alkubus da miya acikin kwanuka wadda miyar tasha naman kaji sabida yadda Aliyu ke sakawa a kawo musu kayan bukata akai akai.
Gabansa ta aje sannan ta wuce É—aki.
ta É—auko carbinta ta dawo ta zauna.
"Mama yaya gida yasu ihsan? mama kozaki bamu arfa ne na kai mata sabida gidan yay mata faÉ—i ba kowa ni kuma na tawo nan"
Yakai maganar kansa a sunkuye.
"Kadai ci abincin tukunna bara na baka waje"
TafaÉ—a cikin kulawa ta mike ta nufi É—akinta.
Janyo plate yayi ya zuba alkubus É—in guda biyu ya zuba miya bai saka nama ba.
Bisimillah yayi ya soma ci ai ina tuni Aliyu ya manta a ina yake sabida azabar daÉ—in da abincin yayi masa, seda yaci sosai yasha ruwa sannan yay hamdala kana ya koma gefe É—aya yana jin cikinshi ya cika damm.
Zamansa da mintuna biyar su hassana sukai sallama falon jikinsu sanye da hijabi har ƙasa,daga ganima daga unguwa suke.
Ganinshi yasa suka tsugunna suka gaishe shi sannan suka wuce É—akin mama da kallo ya bisu yana yaba nutsuwar yaran.
Arfa ya janyo da hannunshi yarinya ƙarama mai mugun kyau tana matukar kama da bebi.
"Ajinki nawa a makaranta?"
Basa amsa tayi da cewa.
"Primary one ita kuma ihsan three"
Sabida su daman tun asali a wata private school mama ta sakasu mai saukin kudi.
"A islamiyya kuma munkai izifi sha biyar"
Zaro idanu yay yana cewa.
"Kai masha Allah"
"Su yaya Bebi kuma sauka zasuyi fa aka mata aure anma kusa shine da aka mata aure tai ta yiwa mama kuka"
TafaÉ—a da suffar yarinta.
"Suma su anty hassana ma aure za,a musu sunata yiwa mama kuka, kuma yanzu mama bata saida dambu kullum inaji tana yiwa wani yaya Aliyu addu'a intayi sallah muma tace kuma muyi masa waishi ya mayar mana da gidanmu sabo yake aiko mana da abinci"
TafaÉ—a batare data san cewar shiÉ—in bane.
Dariya yakewa yarinyar sabida yaga irin yaran nan ne masu faÉ—i ba,a tambayekuba.
Cikin haka mama ta dawo falon
"Aliyu harka gama ka haÉ—u da arfa sarkin surutu ko?"
TafaÉ—a tana zama a saman kujera.
"Lahh mama daman shine kikace muna masa addu'a yanzu nake gaya masa ankawo lefen su anty hassana, lah mama daman shine yayanmu mai kyau"
Ta faÉ—a tana naÉ—ewa jikin Aliyu.
Da sauri hassana ta fito ta maketa aikawa ta saka kuka tayi É—aki aguje.
"Haba da baki duketa ba yarinya ce ai"
Ya faÉ—awa hassana wadda ta saki murmushi ta koma É—aki.
"Haka suke fama dasu damma dodon tasu bata nan aisu hassana basa duka Bebi ce mai azabar saurin hannu"
Dariya ya saki kaÉ—an.
"Mama yanzu bebi tana dukansu?"
Gyara zama mama tayi.
"Ai Aliyu bebi ko ƙoface ta bugeta wallahi seta koma ta rama sedai fa hannunta ya fashe kaga tana ƙarama intai faɗa aka duketa kwana take kuka! ai duk yarana Aliyu babu mai rashin haƙuri kamar bebi, nasha wahala akan bebi Aliyu gashi ta soma ciwo babu mai rintsawa duk yarana bebi tafi shiga ran jama'a sedai fa tafi kowa rashin ji"
Dariya yake sosai yana hango yadda take masifar jin tsoronsa amman ashe agida ba kanwar lasa bace.
"Ai Aliyu bazan iya baku arfa ba wallahi matarka seta sumar min daƴa daman sunata murna ta tafi, Bebi akwai saurin hannu babu ƙaddarar da zata saka na baku autata wallahi"
Marai raicewa yayi yana faman magiya amman mama taƙi fafur sabida sanin halin ƴar tata.
Kallonshi mama tayi cikin nutsuwa.
"Aliyu nagode nagode Allah ya saka maka da aljanna ka sauya rayuwarmu daga ƙunci ta koma farin ciki ka gyara mana gida ka bamu kayan abinci kai mana ɗinkunan suttura, wai ashe har malam ma seda ka aika masa da kuɗi da kayan abinci duka dai nagode Allah ya biyaka"
Sosai ta bashi kunya sukewa wanima bare surukansa,.
"Mama babu komai fa wannan ba wani abu bane ai anzama ɗaya, insha Allahu zan aiko a ɗebi amaran ma akaisu ceɗi su zaɓi kayan ɗakuna ashe an kawo lefe"
"A,a Aliyu haba É—awainiyar da kai mana ma ta isa abin ai seyay yawa"
TafaÉ—a muryarta tana rawa.
"Wallahi mama bata isa ba nifa karki damu bawai kuba ko wani kuka kawo zan masa mama sabida ina son Bebi, sosai, ai kun gama min karshen karamci da kuka bani ƴa guda baku duba cewar koni wanene ba wallahi nagode kuma xan riƙeta bisa amana insha Allah"
Kunyace ta kama mama lallai yaran zamani se abarsu yanzu agabanta yake furta mata yana son Æ´arta, shiko ko ajikinshi haka ya cigaba da janta da hira har yake gaya mata matar usman ta haihu,
****************
Bai iya komawa wurin babar ladiba kai tsaye gida ya wuce yayi kwanan zulumi washe garima haka ya koma shagon wannan mutumin mai kayan lefe anan yakejin labari wai ashe mutumin ɗan damfarane wai sunje sunyiwa wani mutumi irin yadda sukai masa ashe mutumumin ɗan sandane shine ya baza jami'ai har aka ganosu ashe grp ne guda dasu na irin wannan damfarar suke karɓar hayar shago a kasuwa insun yi sesu gudu se wannan lokacin dubun su ta cika.
Aka kamesu aka haÉ—a da masu basu hayar shagunan yanxu haka suna gidan horo na musamman.
Awajan kawu tasi'u ya zauna yana kuka wiwi gadai karshen wannan mutumin yadda ya koma yasan shikam kayan lefen nan nasa sun dulmiya.
A daddafe ya koma gida nan É—inma ya tarar da Æ´an uwanshi cirko cirko duk jiki a sanyaye.
Ga Æ´aÆ´a sunci duka wajan Æ´an sanda.
"Tasi'u ina ganin lokaci yayi da zamu saduda fa lokaci yayi da zamu aje maka man yaƙinmufa shekaru suna ƙara ja iyayenmu sun rasu mun cutar da ɗan uwanmu akan gadon damu bai mana ƙarkoba tunda musa yabar gidan nan muke ganin bala'i da masifa wani cigaba muka samu a rayuwarmu? to nidai na gaya muku yanzu xan tashi naje wajan aisha ta yafemin ƴaƴanta ma haka ko Allah ya duben ya yafen laifukana".
Kawu sani yafaÉ—a yana kuka kamar ranshi ze fita.
Atake anan kowa yay na'am da hakan shawara suka yanke akan su fara tunkarar gidan malam lado tukunna.
Aikuwa nan da nan suka haÉ—u cif tare da Æ´aÆ´ansu maza sukayi sharaÉ—a gidan malam lado sukaje yana soro yana karatu se ganinsu yay akansa kamar an korosu.
"A,a tasi'u salisu Rabi'u sani! zuwa kukai ku kasheni kome?"
YafaÉ—a a rikice.
Jikinsu a matuƙar sanyi suka zauna a gefen tabarma.
"Malam ba wannan ya kawomu ba, munzone akan mu baka hakuri sannan kai mana jagora wajan aisha wallahi bala'i yayi mana yawa"
Dariya malam yayi.
"Kodai kunzo cin arziki kunji labarin yanzu aisha ta wuce raini ai kaÉ—an kuka gani azzaluman Allah kuma jira sakamakon ku"
Rantse rantse suka hau masa akan su wallahi basuma san da sauyin da mama ta samuba.
Ganin yadda sukai namada ne sosai yasa jikin malam yayi sanyi.
Da kansa ya aika aka kirawo su yaya aminu da sukazo ya zauna yayi musu bayanin komai.
Dayake Æ´an bokone tuni, suka nuna murnarsu suka kuma yi na'am da tuban da kawunan amaren nasu sukai dan haka sukai musu jagora zuwa gidan mama.
Tun a bakin gidan su kawu tasi'u suka soma xare idanu katari da shegiyar motar Aliyu a kofar gidan ya kuma basu tsoro.
Malam shiya soma shiga sannan sauran suka bisu.
Mama tana zaune suna hira da Aliyu taga shigowarsu malam da sauri ta sauko kasa ta basa kujera ya zauna.
Su nurane suka karaso suma tare dasu kawu.
Gaisawa sukai da Aliyu inda mama ta sha jinin jikinta takuma haÉ—e ranta tamau ko gaisuwar dasu nura ke mata a ciki ta amsa falonne yayi shuru.
gyaran murya malam yayi.
"Aisha ni waye wajanki?"
YafaÉ—a yana kallonta.
"Kai ubane na ƙwarai wanda ya tallafi rayuwar marayan Allah"
"Da kyau kiramin Æ´aÆ´anki"
Tashi tayi ta kirawo su hassana bebi ce kaÉ—ai babu.
Aliyu ya mike zebar falon malam ya dakatar dashi.
"Zauna mana Aliyu ai kazama É—an gida kaima ma haÉ—u mu bawa babar taka baki"
Zama yayi yana murmushi.
"Aisha nazo na baki hakuri ga iyayen Æ´aÆ´anki sun gane kurensu sunzo akan su baki hakuri kucigaba da zumuncinku, kamar yadda zumunci yake daman jijiyane daga Allah wanda ya sadashi Allah ze sadashi da rahama, wanda kuma ya yankeshi Allah ze yanke masa rahama, kin dai gani da idanunki yadda Allah ya nuna musu ko?"
Kuka mama tasa awajan.
"malam da ciwo fa malam kaga cin zarafin da sukai mana nida abbansu bada ban kaiba ina zamuje a kano malam a shagofa muke kwana nida Æ´aÆ´ana"
TafaÉ—a tana kuka.
Aikwa nan da nan Æ´an biyuma suka hau kukan kamar rasuwar abbansu ce ta dawo sabuwa.
"Naji aisha Allah ma ana masa laifi ya yafe bare kuma mu Æ´an adam ina haÉ—aki da girman Allah akan kiyi hakuri ki bar maganar, kinga ga surukanki nan a wajan bai dace kina kuka ba"
Malam ya faÉ—a mata hakan cikin kwantar da murya.
Suma su kawu tasi'un kuka suka saka.
"Tabbas mun cutar da musa amman aisha muna rokonki da kiyi mana afuwa ki bamu damar gyara zumuncin mu"
ÆŠago kanta tayi.
"Na yafe muku, nidai sauran Æ´aÆ´anku gasu nan, suma Æ´an biyu atake anan suka yafewa dangin mahaifin nasu nan kuma hira ta barke cike da nishaÉ—i sunayi suna kuma bata hakuri kamar zasu ari baki.
Wayar kawu tasi'u ce tahau ringing yana É—agawa ya dire yana furta.
"Innalillahi wa'innah ilaihir raju'un ganinan"
YafaÉ—a a firgice
Gaba É—aya tambayarsa aka hau yi mai ya faru.
Da kuka yake shaidawa malam abinda ya faru da ladi da khalifa.
Zaro idanu Aliyu yayi yana jin jina rashin imanin khaleefa shiko nura tashi yayi tsaye.
"Kawu ina ganin zan shigar da ƙara kotunmu dan wannan bai isa ya taka doka mun barsa ba sunana barrister nuraddeen adam rimin gado sabida haka zan tsaya maka insha Allah harse na kwatar maka hakkin yarka nike neman auren hussaina ga kuma ɗan uwana Dr aminullah adam rimin gado shikuma shike neman auren hassana, se wannan Md Aliyu idiriss mai atamfa nasan kunsanshi shine mijin bebi na gabatar muku da kammu amatsayin surukanku dasuka auri ƴaƴan ƙaninku dan nasan baku sammu ba"
Sosai su kawu suka rude da lafazin nura.
"ni ina aiki anan kotun dake court road,a matsayin lauya, se yayana yana aiki a asibitin malam aminu kano, ƙwararren likitan matane, wannan kuma nasan kuna da sanin ɗane wajan Alhaji idriss mai atamfa textiles kuma shine director manager na kamfanin mai atamfa wanda ke sharaɗa kamfani nasan dai ko baku sanshi ba kunsan sunanshi a redio"
Ya nura ya faÉ—a yana mai fiddo da wayarshi.
Rudewa su kawu sukai tsoron Allah ya kuma kamasu lallai baka raina mutum domin baka san mai Allah ze masa ba, jiba aisha bata da ƴaƴa maza manya amman Allah ya bawa ƴaƴanta mata maxaje na nuna sa'a lallai ka tsayama ka bawa ɗanka tarbiyar ƙwarai jarine yanzu inda ta saka ƴaƴan a gurbatacciyar rayuwa da bazasu taɓa xama haka ba.
"Aisha mungode da samun uwa kamarmi kin jajurce wajan bawa ƴaƴan ɗan uwanmu tarbiya wadda tasa har Allah ya basu mazan ƙwarai madallah da samun uwa marar son abin duniya kamarki"
Suka faÉ—a a tare.
"Ni yanzu zan koma asibiti wajan ladi sabida yanzu ance ana bukatar jini da allurai wai tana ta wani abu kamar jijjiga"
Mikewa sukai mama ta bisu tana musu sallama tana kuma jin tausayinsu sabida yadda duniya ta murxasu.
Cikin sauri Aliyu ya bisu yaran sune suka tafi gida sukuma ya É—aukesu a mota suka nufi asibitin harda ya aminu ma.
Transper suka É—auka zuwa wani asibitin daban wanda Aliyu ne yay bill kuÉ—i har wanan dubu É—ari ukun ta jiya seda ya biya.
Asibitin kudi mai kyau aka mayar wanda nan da nan Aliyu ya sakar musu kudi aka soma bata taimako fiye da wanda aka bata abaya.
Bai baro asibitin ba seda ya biya kudin komai kana ya cikasu da kuÉ—i yanajin idan yay musu kamar mahaifin bebi yayma ne.
Fitowa yay kawu tasi'u da rabi'u suka biyoshi suna faman masa godiya hatta babar ladi seda tai kukan daÉ—i.
"Kaga ikon Allah ko tasi'u? suda muka walalanta ashe ajikinsu zamu huta"
Rabi'u yafaÉ—a yana murmushi.
Sosai suka saduda da lamarin rayuwa kuma sukai nadamar abinda sukai abaya.
Mama da daddare sukazo harda abincinta koda taga ladi seda tai kuka su inna suwaiba kamar zasu lashe mama har wajan taran dare suna can seda ya nura yakai iya sannan suka tawo tare.
Shiko Aliyu tea kawai yasha yay sallah ya nutse agado gobe yana da office gashi kuma yana son su haÉ—u da nura akan zancen case É—in khalifa domin uban yaron yana da kuÉ—i dole se Aliyu ya haÉ—a nura da manyan lauyoyi kafin a tunkari abin yana son a nunawa alhaji mai gwall cewar basuji buluss ba.
haka ya kwanta da gajiya da tunanin bebi aransa.
Washe garima mama ce ta aika shahid ya kai musu kayan karin kumallo A asibitin sabida ladi zata É—auki wajan wata É—aya a sibitin ana bata treatment.
Wajan 10 Aliyu suka haÉ—u da nura sukai abinda zasuyi kana suka shigar da karar khalifa na yadda yaywa ladi, sannan ya haÉ—a nura da manyan lauyoyin daya cikasu da mahaukatan kudi akan case É—in.
Office ya wuce.
Ranar ma baije gidan bebi ba sabida gajiya bai kuma kirata wayaba ya bari gobe inyaje yama kaita ta dubo ladi.
A kotu an gama komai ranar monday za,a soma zama, amman kafin nan anbawa maga takarda takardar sammaci gidan Alhaji mai gwall..............
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.