Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 4 of 81

                       *ASALIN LABARIN*
Yana da kyau makaranci ya tsaya sosai yaji yaya asalin su Bebi yake dama Asalin labarin namu baki É—aya.
Kudai kuyi haƙuri kubiyoni a sannu domin har yanzu shinfiɗa muke a labarin bamu shigeshi ba.

*WAI WAYE ADON TAFIYA*

AUTAR MANYA👉👈
*COMMENTS*
*SHARE DOMIN ALLAH*ðŸ™
11/14/21, 3:05 PM - Allah Akbar: I just published "PART 4" of my story "AUREN BARE". https://www.wattpad.com/1108997175?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=autarmanya&wp_originator=wi7huBHWJ%2B5vI6y2TtE8NXp4yNS2NheTEBOWdGsVA%2FMsofq%2BYcMl0duvNSudokhBppbo6YX5Z0lR5IjfVeQqBBYg4U%2FLU6gjCjp67xDLnIiZheyApp4xToH52kSL8tqE

*AUREN BARE !!*🌹
    {  _HOT LOVE_  }
           

         NA
*AUTAR MANYA*

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

                          *004*

*ASALIN LABARIN*

Sunan mahaifin su Bebi  musa mai katifa haifaffen garin kanon dabo.
Cikin ƙaramar hukumar kumbotso anan wata ƴar alƙarya gidan iyayensa yake mai suna ƴan kusa.
musa ya taso cikin halin maraici tare da  tsangwamar matan mahaifinsa kasancewarsa maraya marar uwa, mahaifiyar sa Bilkisu Allah ya jiƙanta da rahamata tun wajan haihuwarsa ta rasu.
Rayuwarsa ta koma wajan matan mahaifinsa waɗanda suke azabtar dashi, inna hasiya matar Alhaji mai katifa ta farko tana da yara biyu maza sabi'u da Rabi'u se autar ta mariya,ita kuma  inna suwaiba tana da yara guda biyu maza, sani da tasi'u  se amaryar Alhaji mai katifa Bilkisu wadda ta kasance ƴar uwarsa ta jini wadda aka haɗasu auren zumunci kuma itama ɗin dai duk anan cikin ƴan kusan iyayenta, suke, waɗanda suka haifeta ita kaɗai bata da yaya bare ƙani ga kuma maraici domin Bilkisu bata da uwa bata da uba duk sun rasu, wannan ce ta saka Alhaji mai katifa yake mugun jin tausayinta tare da tsananin sonta.
Tunda Alhaji mai katifa ya auro bilkisu su inna suwaiba suka haɗe mata kai suda yaransu tsangwama xagi da hantara harta kai ga bata iya fitowa ko tsakar gida, cikin haka Allah ya bata ciki zokiga murna wajan Alhaji amman wajan su inna suwaiba kamar zasu kasheta sukeji, sabida baƙin ciki.
Tunda cikin nata ya taso Alhaji ya hanata koda girki, kasancewar Alhaji mai ɗan rufin asirine yasa yake tafiya wasu garuruwan kan harkokinsa na saida katifa, wanda kuma cikin hakan Allah ya nufi Bilkisu da fara naƙudar tsaye.
Ita bata san tana naƙuda ba,sabida ƙuruciya da kuma wauta amman su inna suwaiba sarai sun gane tana halin naƙudar sedai babu wadda ta kulata bare ta saka ran zasu tai maketa.
Kullum daren duniya setai kuka! sabida ciwon baya ciwon mara ga Alhaji baya gari bare ya taimaketa ranar dazata haihu tun safe take murƙususu a ɗaka amman an rasa wadda zata leƙo ɗakinta kodan taga halin datake ciki.
Tun tana ganewa hartazo hankalinta ya gushe, wanda A wannan lokacin Allah ya kawo Alhaji mai katifa gidan wanda zuwansa kenan yay cikin É—akinta.
Ganin halin datake ciki yasa ya fito ya rufe matan nasa da faÉ—a har yana kiransu da marasa imani, fita yay zuwa cikin gidan mahaifansa waÉ—anda suma suke babu rai, se dai akwai yayansa da matarsa agidan,matar yayansa ya kirawo suka nufo gidan nasa cikin sauri da ita.
Ganin halin da Bilkisu take ciki yasa matar yayan Alhaji cewar yaÉ—an basu wuri domin zuwa wannan lokacin har faya ta fashe kan É—a ya taho.
Bayan fitar Alhaji bilkisu ta soma nakuda ta gaske.
Wadda cikin mintuna goma ta haifi ɗanta ƙato dashi sedai yana cikin riga, seda matar yayan Alhaji mai suna gwagwgwo aya! tai da gaske sannan  ta yaga rigar ɗan kuwa ya canyara kuka! kallo ɗaya Bilkisu tayiwa jaririn nata Allah ya  karɓi ranta.
_Kullum nafsin zaikatul maut_
Mutuwar Bilkisu ba karamin girgiza Alhaji tayiba wanda seda akai da gaske ya koma walwalarsa.
Kwanci tashi babu wuya wajan Allah  yanxu haka musa ya cika shekaru goma da haihuwa wanda kawai sedai ace ikon Allah ne ya yarashi sabida yadda ya taso cikin halin tsangwama da hantara hatta ƴan uwansa cutar da shi sukeyi.
Awajan Alhaji kawai yake jin sauƙi wanda daman tunda ya taso bai sha nonon mahaifiyarsa ba sedai shayar da shi da ake da madarar shanu har Allah ya kawoshi waɗannan shekaru, bayan yaɗan soma zama saurayi ya soma fuskantar halin rayuwa  ganin babu wani sauƙi sena ubangiji yasa Alhaji ɗaukeshi ya kaishi can garin rimin gado makaranatar almajirai anan ya sami saukar alqur'ani mai girma, bayan yazama matashin saurayi alokacin ya sauke alqur'ani seya dawo nan ƴan kusa alokacin ne ya soma bin Alhaji kasuwa duk da su sabi'u na cutar dashi da haɗa masa sharri wajan Alhaji.
Amman shikuwa tsakani da Allah yakeson su kuma baitaɓa ƙullinsu acikin ransa ba.
Aisha ƴace a wajan baba sale yayan alhaji mai katifa, waɗanda suka fito uwa ɗaya uba ɗaya, wadda mahaifiyar aisha itace gwagwgwo aya mace mai kirkin gaske, kuma itama gwagwgwo aya daga kan aisha Allah bai basu wata haihuwar ba, tun tasowar aisha ta kasance kyakykyawar gaske nitsatstsiya marar son hayaniya, aisha tana da shekaru goma sha bakwai, Allah yaywa malam saleh rasuwa ,yayan Alhaji, wanda tsananin dukan rasuwar yasa Alhaji kwanciya rashin lafiya lokacin su musa sun girma domin dik su sabi'u sunyi aurensu shikuwa musa ya zama saurayi amman dai bai auren ba, bayan addu,ar sadakar bakwai Alhaji da kansa ya kirawo musa ya damƙa masa kyautar auren Aisha ɗiyar yayansa marigayi atake anan musa ya amsa batare dayay musuba, haka zalika itama aya dataji labarin tai matukar farin ciki.
Shirye shirye ne ya cigaba da gudana Aisha ma tai farin ciki sabida daman ɗan uwan nata yana burgeta cikin gidan Alhaji kuwa kamar ze ƙone sabida ashe tasi'u yana son aisha amman yay ƙauron baki har aka baiwa musa, wannan dalilin yasa su inna suwaiba sukai kamar su ƙona gidan seda Alhaji yay da gaske sannan suka nutsu.
Kwanci tashi babu wuya wajan Allah, an É—aura auren musa da aisha suma sun tare anan gidan Alhaji inda sauran Æ´an uwansa suke zaune da matansu zaman gidan Alhaji da Aisha da matan Æ´an uwan musa zamane na faccalanci marar daÉ—i.
Sosai aisha take kurɓar ruwan baƙin ciki awajan matansu sabi'u musamman wajan shafa'atu matar Rabi'u wadda take yin wani abun ma da gayya.
Haka dai aisha take haƙuri kuma koda wasa bata taɓa gayawa musa ba kasancewar ta mace mai kawaici, shekarun su Aisha biyu da aure da Musa Allah yaywa aya mahaifiyar aisha rasuwa wanda tsananin damuwa yasa seda musa yayta karɓowa aisha ruwan tofin dangana sannan ta sami nutsuwa.
Kwanaki naja lokaci na gudu katsam shima Alhaji aka wayi gari ya rasu wadda waÉ—an nan rashe-rashe ya girgiza musa tare da matarsa aisha amman ga sauran matan Alhaji da su tasi'u da matansu duniya ce ta buÉ—e musu sabuwa tare da buÉ—e shafin cin dukiyar alhaji wadda sukai kane kane kamar jira suke.
Abinda ze baka takaici shine kwanan Alhaji arba'in da rasuwa suka raba gado!...........  

*MANAGE*ðŸ™

*SHARE DOMIN ALLAH*
11/14/21, 3:05 PM - Allah Akbar: I just published "PART 5" of my story "AUREN BARE". https://www.wattpad.com/1109368451?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=autarmanya&wp_originator=FJq4nmGqNChIpjzeCYUID6TOo%2B5ljX4M5WXUf22BCkGUbwyUKvCCue%2F6EcHksmXWEzFi9umRgUcl0ZsLrIVeEGk1fro%2B%2Blba%2BwJwOWtHBuBCg6Xs%2BOukMT17%2BB5t45Dv

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.