Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 8 of 81
*HAR YANXU DAI AKWAI TAFIYA BAMU SHIGA CIKI BA, KUDAI KAR KU ƘOSA DANI...............*
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }
NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
*SANARWA!*
_Assalamu Alaikum barkanku da wannan lokaci naga saƙonku akan cewar ni na shiga gasar marubuta sabida kunga sunana a cikin group na 1 jerin suna na 4 To Alhamdulillahi bani bace an ɗan samu mistake ne wajan rubuta sunan inda aka saka *AUTAR MANYA* toba ni bace ƴar uwatace marubuciya mai suna *AUTAR MAMA* wadda itama nake mata fatan nasara fatan alkairi tare da fatan cin nasara acikin wannan gasar har da sauran ƴan uwana marubuta dake ciki dukansu Allah ubangiji ya basu nasara da sa,a Amin ina fatan kuma zakuje kuyi mata voting sabida marubuci ɗan uwan marubuci ne nagode_
*008*
Tunkafin suje gida jikin Bebi yagama ɗumama da zafi wanda atake anan ze baka tabbacin cewar zazzafan zazzaɓine ya shiga jikinta.
Suna gab da shiga cikin gida sukaci karo da iya hansatu wadda ta taho cikin tashin hankali mayafinta aka kamar ma batasan ta yafoshi ba dai dai ba.
Mama ta tare tana tambayarta.
"Maman Æ´an biyu, wai mai yasami Bebi ne yanzu naji labarin wajan salisa tazo aguje tana cemin Bebi ta faÉ—i?".
Iya hansatu ta faÉ—a duk jikinta yayi sanyi.
"Hmm kedai bari iya wallahi tsautsayi amman dai mushiga gida tukunna bama tsaya anan ba".
Cewar mama wadda taya fito iya da hannunta akan su shiga cikin gida.
Ranka yawa sukai atare zuwa cikin gidan da sauri sadiya taje É—aki ta É—auko tabarma ta shinfiÉ—a musu sannan ta taimakawa su hassanar suka aje Bebi wadda zuwa lokacin ta soma rawar É—ari.
Dukkansu zama sukai a tabarmar in banda ya Aminu dake tsaye yana bin hassana da kallo ganin har zuwa lokacin bata bar kukan! datake yiba.
"Hussaina samo min maganin zazzaɓi acikin kwabar kayan kwalliya seki zo ki samo mata ruwa abata".
Cewar mama wadda take tube mayafinta daga jikinta.
"To mama".
Hussaina ta faÉ—a tare da tashi da sauri tayi cikin É—akin.
Fita yaya Aminu yayi batare daya cewa kowa komai ba,lokacin daya dawo har anbata maganin hannunsa ɗauke da baƙar leda miƙawa hassana yay wadda ta daina kukan! yanzu sannan yace mata ta bawa mama magunguna ne ya siyowa bebi a chamist harda tsire gashashshe.
Bayan mama ta buÉ—e ledar godiya ta masa sannan yai musu sallama yabar gidan.
Mama ce ta kuma duban iya a karo na biyu.
"Wallahi iya nima ina zaune ihsan tazomin................,"
Tass! ta kwashe komai ta gayawa iya wadda take tafa hannu tana salati.
Sannan tacewa mama.
"Allah ya bata lafiya ai baxamu zauna ba sabida aikin iska yafi karfin tunani dole zamuje rimin gado dake gidan ƙanin mahaifina ya taimaka mana da roƙon Allah"..
Cewar iya wadda take kallon mama domin taji me zatace.
"To iya insha Allahu bari ƙarshen wata yazo semuje ɗin kafin nan kuɗin adashin dana saka na amsa".
Mama ta faÉ—i tana kallon iya.
"To babu damuwa Allah ya sawwaƙe ya nuna mana lokacin Amin".
Cewar iya wadda take ƙoƙarin miƙewa tsaye.
Bayan iya ta miƙe duban sadiya tayi wadda take gyangyaɗi.
"To Auta tashi maza mutafi gida anfara taskar labarai darefa yayi".
Tura bakinta tai gaba tare da cewa...
"Ni dai dan Allah iya ki barni yau É—aya nai jinyar Bebi".
Tafaɗa kamar zatayi kuka! mamakin shaƙuwar Bebi da Sadiya iya take kullum suka haɗu se anyi faɗa amman ɗaya baya ƙaunar yaga ɗaya cikin damuwa.
Ko cuta Bebi take tofa sadiya setayi aminai ne na ƙut amman duk wannan amincin nasu baya hana aci uba idan ta ɓaci.
"To masu jinya Allah tashemu lafiya".
Iya ta faÉ—a tana dariya! mama ce tabi bayanta domin ta mata rakiya suka nufi kofar soro.
Sun jima suna tattaunawa akan lamarin lalurar Bebin sannan iya taiwa mama sallama, ta nufi gidanta.
Mama tana ƙoƙarin zama Shahid na doko sallama gidan.
Turus yay da baho akansa sabida ganin Bebi lulluɓe tana rawar ɗari ƙarar sautin kuma har kunnensa.
"Mama meya sami wannan yarinyar?"
Yafaɗa yana aje bahon a bakin rariya sabida tuwon ya ƙare tas.
"Hmm aika zauna tukunna kodaga tsayen zakaji mai Æ´ar uwa?".
Mama ta faɗa tana mamakin shaƙuwa irinta ƴaƴan nata.
Jiba kamar ba,aci uba ita dashi ba É—azu amman jiba dayazo ya tarar ta ahaka duk yabi ya É—aga hankalinsa.
Motsin! zaman shahid akusa da mama ya dawo da ita daga tunanin data afka na lamarin Æ´aÆ´an nata.
"Mama kimin shuru lafiyarta ƙalau kuwa?"
Yafaɗa yana yaye lulluɓin Bebi yana taɓa jikinta dayay zafi rau kamar gaushin wuta.
Da sauri ya janye hannun nasa yana yarfewa.
"Kai mama ai wannan babu lafiya zazzaɓi ne bara na siyo mata magani inada kuɗi ajikina".
Yafaɗa yana miƙewa tsaye jikinsa yana rawa!.
Wannan kalamin na shahid shiya saka mama hawaye.
Nima kaina mai rubutun seda naiwa yaron hawayen tausayi.............
_GUNTUN PAGE KUYI HAƘURI PLS_
*AFUWAN YAU INA UZURINE WALLAHI DA ƘYAR NAI MUKU WANNAN SHAFIN AMMAN KU TARENI ZUWA DARE INSHA ALLAHU RABBI, NAGODE DA BIBIYATA DA KUKE*ðŸ™
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }
NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
*009*
Kamo hannayensa mama tayi tare da jawoshi jikinta.
"Zauna É—an albarkata, ka kwantar da hankalinka, yanzun nan yayanku Aminu ya siyo mata magani insha Allahu babu wata matsala".
TafaÉ—a bayan ta zaunar dashi daga gefen jikin nata.
Zama yayi amman duk jikinsa yayi mugun sanyi, ciro kuɗin cinikin tuwon yayi tare da miƙa mata.
Ƙirgasu tayi cif suke babu ƙwandala data ɓata koda yake daman tasan shahid baya ɓatar da kuɗi, ko Bebi ma kawai tsabar sakarcin tane.
"Allah yay maka albarka É—a É—aya tamkar da goma, maza tashi kaje shago ka kwanta kaga gobe munada sammakon safe".
Shahid na ƙoƙarin tashi seya fasa ganin Bebi tana yunƙurin tashi daga kwanciyar datayi.
Gaba ɗayansu zuba mata idanu sukai harta miƙe batare datayi musu magana ba, gaban rariya taje ta wanko bakinta sannan ta dawo duk jikinta yana mata zafin zazzaɓi, amman ina bata damu ba, hankalinta yanaga wannan baƙar ledar data ƙyallah idanu ta hangota gefen mama, daman ita ciwo baya hana ta kai loma.
Hannu ta saka tana kici-kicin janyowa cikin É—unbin mamaki hassana take kallonta.
"Ke BEBI yanzu duk nauyin dakika zuba mana ɗazu garin ɗauko ki kina makyar kyatar zazzaɓi baze saka ki mana godiyaba, sedai ki ɗauki leda burinki kenan?".
Cewar hassana wadda haushin ko in kular data musu yaÉ—an bugeta.
"Hmm kema dai hassana da ɓata bakin ki, kike kin manta da wadda kike magana kenan?".
Cewar hussaina wadda take hararar
Bebi domin gabaki É—ayansu tayi mugun basu haushi.
Ko kallonsu batayi ba sema zazzage ledar datayi.
Ganin tayi idanu Biyu da tsire a fake a baƙar leda daban yasa ta zabga wata shegiyar shewa!
Kafin muryarta ta karaÉ—e É—an tsakar gidan nasu.
"Ahayye! shagali ni ai wannan duka na malam hadi da goshi yazo mini ko banza nayi brush da tsire".
TafaÉ—a tana buÉ—e ledar wadda har yawunta seda ya É—iga a saman takardar.
Sosai ta basu dariya da mamaki har seda mama ta dara afili tabbas ta yarda É—iyar tata nada iska, duba da yadda watarana take acting É—inta kana gani kasan seda uzuri.
"Kekuwa Bebi meyasa wataran baki da kan gadone, daga ganin abu babu tambaya har kin É—auka gakuma dare yayi amman kike wannan shegiyar shewa kamar tsohuwar bazzawara".
Cewar mama wadda take kallon Bebi É—in.
"Toni mama meye ruwana da dare, amman dai nasan wannan garar babu ta kowa face tawa, wayyo! ni ƴar abbanta yau zanyi ƙaramin party da tsire".
Tana faɗin haka ta ɗauki ɗaya ta saka abakinta ta lumshe idanu tana luma haƙora tana tanɗewa kamar wata kura.
"Wayyo Allah na masu kuɗi suna shagalinsu, aini Allah yay min arziƙi tofa kullum semunci tsire mun donge ƙullinki mamata daban".
TafaÉ—a tana kuma É—aukar wani gudan ta afka abaki tana tanÉ—ewa tana lashe hannayenta.
"Waike wace irin yarinya ce?, watakan ke ɗayace mai rai agidan kenan kanki kaɗai kika sani, wallahi ina jiye miki wannan halin naki na sonkai ai ko ƙannenki kya sanwa amman kiketa faman ci ke ɗaya".
Mama tafaɗa tana warce ledar seda ta bawa kowa sannan ta miƙa mata yanka biyu.
"Ke amshi wannan tunda kinci biyu".
Tura baki tayi gaba nan da nan idanunta suka sauya kala.
"Ni wallahi wannan yamin kaɗan haba mama jibi fa dan Allah ki ƙaramun anaki".
"Bazata ƙaraba malama idan bakya ci ajeshi anan banza marar hankali"..
Cewar hassana cikin ƙufula.
"Nidai ba banz........,
"Kull É—inki Bebi inji kin rama, kekuma ban hanaku zage zagen nan ba?".
Cewar mama ta juya tana kallon hassana.
"Yi haƙuri mama wallahi Bebin ce da abin haushi komai ita kanta ta sani kina kallon jiya da malam ya aiko mana da fura da nono kafin kizo ki fiddawa kowa tasa itafa harta sha fiye da rabi".
TafaÉ—a cikin jin haushin abinda Bebin ke musu wataran.
"To hassana tunda haka Allah yayota aise haƙuri wataran se labari ina gaya muku a kullum cewar kada ku ɗauki wannan rayuwar da muke a madauwamiya wataran komai ze zamo tarihi idan babu mutuwa akwai aure kowacce rayuwarta ba mai ɗorewa bace ba anan gabana nafi muku fatan kuje can kuyi rayuwa da mazajenku lafiya".
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.