Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 57 of 81

***********************
Bacci ɓarawo shiya sace mama a wannan dare cike da tunanin bebi aranta tana kuma yi mata addu,a tare da fatan zaman lafiya.
washe gari tunda asubahi.............

*manage bana da caji yau*
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *PART* 2

NAKUÆŠINE

*78*

Mama ta tashi su hassana akan suyi sallah sannan su fara haramar ɗora abin karin kumallon safiya sabida har zuwa wannan lokaci basu koma kamfani ba, Sanin halin Bebi na rashin tashi akan kari yasa duka ƴan uwan nata basu wani damu da tashin nata ba kowa ya miƙe yaje yay alwala suka dawo ɗaki sukai sallah.
Seda gari yaÉ—an soma shaa alamun haske sannan hussaina ta duba makwancin bebi taga wayam kallon mama tayi cikin mamaki tare da cewa.
"Mama ina bebi ne banganta a makwancin taba?"
Seda mama ta shafa addu'arta sannan ta dubi hussainar kana tace mata.
"Ai bebi tayi kwanan gidan mijinta kudai kubita da addu'a kawai".
Gaba É—aya É—akin shuru ya É—auka kowa yana jimanta rabuwa da bebi domin hassana har hawaye seda ya zubo mata.
"Amman mama mai yasa baki tashe mu mun rakata ba naga ai ana rakiya gidan amarya".
Inji hassana wadda take share hawayenta sabida Allah ya zuba mata ƙaunar Bebi akaf ƴan uwanta tana mugun son Bebi.
"Abinne yazo mana a gajarce amman usman yace zezo ya kaiku".
Cikin mamaki duka suke kallon mama kafin hussaina tace.
"Mama wai waye mijin Bebin munji kince ya usman?".
Murmushi mama tayi sannan tace.
"Ƙanin usman wanda sukazo rannan sunanshi Aliyu amman fa naji ance yana da mata kuma baiyi sati guda da auren ba"
Cikin tsoro hussaina tace.
"Tabb yasin nasanshi kice ZAKI bebi ta aura lallai wannan kuwa ze saita ta wallahi mama ranar dana ganshi kamar zanyi fitsari wannan aiya kusan haifar kamar bebi amman kuma ya aureta tabb wallahi mama nayi mamaki sabida gidansu fa suna da kuÉ—i Allah ya basu zaman lafiya ashe dai rabon mama tazama surukar mai atamfa ne yakaimu kamfani lallai na yarda komai silane tabbas rabon auren bebi ya kaimu talle kamfani'
TafaÉ—a tana murmushin murnar Æ´ar uwarsu ta sami gidan hutu.
Gyara zama mama tayi tana kallon Æ´aÆ´an nata sannan ta soma magana kamar haka......
"Ai daman komai kuka gani baya faruwa seda abu uku! na farko lokaci na biyu rabo! na uku kuma shine sila tabbas Allah ya rubuta Bebi zata auri wannan yaro sedai kuma ta silar tallen kune auren ze haɗu kuduba fa kuga yadda bebi taƙi tallen kamfanin tun farko ashe duk wannan zamiyar datake rabon auren ta yana can.............
Sannan kuma abu nagaba shine komai da kuka gani a rayuwa Allah ne ke tsarawa ta yuwu ta silar Bebi muji daɗi arayuwa ta yuwu ta silar Bebi muji takaici arayuwa, tunda na haifeta nake fama da ita itace ɗaukomin magana a waje tsokana faɗace-faɗace itace ƙin zuwa makaranta itace aljanu itace rashin son aiki, amman duka na hakura nacigaba dayi mata addu'a batare danayi fushi da itaba batare dana wareta cikinku ba, toga karshe dai jiba kuga yadda Allah ya nuna ikonsa akanta babu mamaki a farkon rayuwarta Allah ya nufa zansha wuyarta daga ƙarshenta kuma naji daɗi ajikinta, wannan dalilin yasa nake kira ga duk wata uwa data zauna ta fuskanci lamarin ƴaƴanta tai iya yinta wajan gwada musu dai-dai tare da binsu da addu'a domin uwa ita makarantar farkoce, ina roƙon Allah yasa yadda nagama da ita lafiya kuma Allah ya rabani daku lafiya Amin".
Jikinsu ne duka yayi sanyi ƙalau dajin wa'azani mama tabbas maganar mama gaskiyace sannan kuma bawai dan mahaifiyarsu bace tabbas da wuya ka sami mahaifiya kamar mama wadda zata zauna ta jajurce wajan kula da tarbiyar ƴaƴa mata har guda biyar cinsu shansu sutturarsu karatunsu uwa uba kuma basu tarbiya tabbas inda wata uwarce dafa tasami damar buɗe hannun jarine da ƴaƴan nata, amman ita ta zaɓi zaman basu tarbiya kula dasu batare data dubi wannan ba.
"Allah ya saka miki da alkairi mama haƙiƙa kincika uwa tagari Allah yabaki ikon cinye jarrabawar daya ɗora miki domin riƙonmu tabbas jarabawace agareki".
Cewar hassana tana goge hawayen tausayin mahaifiyar tasu tanajin tsananin kaunar mama acikin zuciyarta.
"Amin ya Allah hassana, sannan abu nagaba inason sanar muku da cewar kuma maganar auranku tana tasowa duk da nasan baku riga kun wayu da mazajen nakuba amman tun kafin rasuwar abbanku yabada wasiyar ke hassana a bawa Nuraddeen ke kekuma hussaina abawa Al-ameen. ƴaƴan wajan babanku ado sabida haka jiya malam ya tadarmin da maganar dan haka nan da karshen shekara za'ayi bikin kafin nan su yayyan naku sun kammala gininsu dasuye anan anguwar gaidar ƴankusa tunda kunga daman shi nura naji ance likita ya karanta kuma takaddar aikinshi ta fito, shikuma aminu lauya ya karanta kuma duka alhamdulillahi jiya iya datazo akan maganar auren bebi take cemin dukansu sun sami aikin gwamnati yanzu abinda ya rage musu ƙarasa gininsu da kuma haɗa lefe sannan kuma tacemin sunce anemi izinina zasu soma zuwa taɗi wajanku".
Tsitt ɗakin yay sabida yadda ƴan biyu sukai ƙasa da kansu alamun jin kunya yin duniya mama tayi maganar amman basu iya tanka mata ba( hmm kenan ƴan biyu sunfi Bebi kunya ohhhh! ).
"In baza kuyi magana ba kunga tashina arfa ihsan kuzo ku miƙa markaɗan koko kunji kukuma in kungama gulmar kwa saman wannan sunne kan bani zakuwa ba kuje kuyiwa iya ja'iran kawai".
ta miƙe ta saka ƴaƴanta agaba sukabar ƴan biyu a ɗaki suna faman sunne kai ƙasa.
seda suka tabbata mama tabar É—akin sannan hassana ta mike tai tsalle akan katifa.
"Wayyo! Allah nagode maka daka bani zaɓin raina kinsan Allah hussaina batun yau nakeson ya nura ba sabida shuru-shurunsa yana burgeni kinsan kwanaki dazemin allura daya matso gabana jinai kamar kada murabu".
Dariya hussaina tayi sannan ta dubi hassanar.
"Tabb ni ai kawai jin mama nake kenifa tuni ya Al-ameen yagama fayyacen komai kinsan Allah ko ranar da bebi tai iskar nan ma seda ya kirani waje mukai hira kinsan shifa daman barrister ne akwai surutu bai wani tsaya kwana kwana ba yagama fayyacen komai wai sabida kar ai masa shigar sauri nima ina sonshi wallahi ko banza mahaifi ƴaƴa farare kinga mu farare su yaya ma haka wayyo bebi itace mai miji baƙi".
Hussaina takai maganar cikin farin ciki.
Tashi zaune hassana tayi.
"Wallahi hussaina baki san kyau ba ai Bebi fa duka tafimu more miji sabida mijinta top class ne babu ƙarya ai ita tagama dace amman muma ɗin babu abinda zamuce da Allah se godiya amman ina gargadinki da kicire mijin Bebi a lissafinmu sabida yay mana gudun wuce sa'a daga mu har mazajan damuka aura kinji ko".
Dariya hussaina tayi kana tace.
"To mu madai mungode Allah kuma muna kuma godiya gareshi tashi muje muyi abin kari madam danni yau gidan Bebi zan wuni dan senaje na kashe kwarkwatar idanuna".
Kamar wasu ƙawaye suka jera daman su kansu ɗaya kuma komai nasu ɗaya hatta kama sedai hassana taɗanfi hussaina kama da Bebi domin hassana suna mugun kama da Bebi sosai inkaga bebi sekace hassana ce sakuwarta kasancewar Bebin duka tafisu girman jiki.
Ita kanta mama tayi mamakin yadda suka jima a É—akin sannan kuma tayi mamakin yadda suke wani nan nan da juna yau ta fuskanci bayyanar maganar aurensu tayi musu daÉ—i amman tsabar alkunya yasa basu nuna mataba sedai tagani a aikace domin hatta tafiyar aikinsu nayau yasha bam-bam da sauran ranaku domin tuni suka tace gasarar koko suka haÉ—a wuta nan danan suka haÉ—a koko da É—umaman tuwon karin kumallon safiya.
Tabarma suka baza a tsakar gida suka zubowa mama nata nasu kuma suka zuba a katon tire na shahid daban a wani É—an farantin roba sannan suka zagaye waje É—aya sunacin tuwon da kokon amman gefe guda hirar bebi suke.
Ihsan mai bin bebi itace tace.
"Mama ƙilafa bebi tana can tanacin farfesu yanzu".
Dariya mama tayi tace.
"Ba mamaki amman fa harna hango bakin mutuniyar".
Dariya suka kwashe da ita.
Shahid ne ya dubesu.
"Ai wallahi idona idon storen gidan Bebi senaje na É—ebo adadin idomie É—ina data cimin domin bafa zan bari ba".
Mama garin dariya seda ta kusan ƙwarewa.
"Kaikuma haka ake girman ai babu kyau É—iban kayan miji nidai bada yawuna ba kaje dai kaci iya cinka amman banda guzuri ni ba'a gidana ba ko ita ta É—ebo ta kawon nikuma zan kira Aliyu na gaya masa nakuma ce yazo ya kwashe kayansa".
Cikin dariya tai wannan furuci mai kama da wa'azi ga Æ´aÆ´an nata.
"Nama fa hana ana cin abinci ana magana nima kuma nazo na biye muku kuyi muci mugama muga kuma mezamuyi".
Cikin nutsuwa suka cigaba dacin abincinsu batare da wani ya kuma yin wani furuciba.
*******************
*CIKIN GIDA ƳAN KUSA*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.