Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 64 of 81

*ÆŠAN MAJALISSA*
*H A S K E*
*RABON WANI*
KOBA SO*
*DA IZZATA*

_Kowannensu akan farashin 300 waÉ—anda suke documents complt, gabaki É—ayansu kuma naira 1000, maiso seya nemi,08142105218, haka nan mai son wannan littafin shima dai seya nemi wannan numbern ta sama domin ya saya_
11/14/21, 3:13 PM - Allah Akbar: *85*

*Assalamu Alaikum ina miƙo saƙon ban haƙuri zuwa ga ɗunbin masoyana masu bibiyar wannan littafin na yadda kuka jini kwana biyu shuru abinne ya haɗemin mun ɗan shiga hidima ne amman yanzu alhamdulillahi na kammala komai sabida haka zamu ɗora daga inda muka tsaya waɗanda suka kirani domin suji lafiya da waɗanda sukai min magana ta watsapp inbox duka nagani kuma nagode da yadda kukai min uziri Allah ya saka muku da ɗunbin alkairinsa amin summa amin nagode*

Gaba É—aya hannayenta suna naÉ—e acikin hijabin daya umarceta ta saka tun a cikin falon Ammi.
Tana tafiyane cikin mutuwar jiki kamar wadda ƙwai ya fashe mata acikin jikin nata, ba kuma wani abunne ya saka mata wannan yanayin ba face wannan zumar da ammi ta bata ɗazu ta sha wanda tun a ɗakin takejin baƙon yanayi acikin jikin nata amman bai tasiri kamar na yanzu ba.
Gefe ɗaya kuma tsananin mamakin girman gidan tare da haɗuwarshi sun kuma kamata ashe jiya bataga komai ba domin a dare suka shigo ko ina ma'aikatane cikin blue ɗin uniform sunata faman kaiwa da komowa domin ganin sun tsaftace gidan daga yawan dattin bushashshun ganyen bishiyun dasuke faɗowa gefe ɗaya kuma ga masu faman baiwa fulawowi ruwa ga masu wankin motoci daga can tsakiyar wasu rumfuna, har harɗewa take sabida fargaba, ahaka ta ƙarasa tsakiyar farfajiyar gidan sama ko ƙasa bata ganshi ba, waige take tana raba idanu acikin jerin manyan tsala tsalan motocin dake harabar wajan amman sam bata ganshi ba.
Aranta take ta mamakin yanayin saurin sa domin ace daga wannan ƴar tafiyar harta nemesa ta rasa sekace ƙiftawar idanu.
Tsayawa tayi kamar wata doluwa tana ta zare idanu tunani take kamar ta juya ta koma wajan Ammi amman tuna yawan faÉ—anshi gareta yasa ta tsaya tana jiran tsammanin ganin shi.
Wata azababbiyar farar mota wadda taci baƙin glass ce ke faman doko mata horn wadda take daga can opposite da gaban gate, Cikin sassarfa Bebi ta waiga tana kallon motar jikinta na tsananin rawa take taku har zuwa gaban motar wanda taga murfin gefen da drivern motar ke ciki a buɗe ɗan zira kanta cikin motar tayi cikin sauri kuma ta ɗago sabida haɗuwar datayi da kaifafan idanunshi waɗanda suke tsaye suna kallonta, jan murfin motar tayi ta shiga ciki ta zauna sanyi Ac gami da ƙamshin turarensa dana motar sukaima hancinta sallama.
Tsintar kanta tayi da jingina da seat É—in kujerar cikin motar tare da lumshe idanunta tana jan ajiyar zuciya sabida mutuwar da jikinta ya kumayi.
"Malama ki rufo mana motar mu wuce kin wani tsaya kinata kalle-kalle kamar wata sokuwa tun É—azu ina jiranki"
YafaÉ—a cikin É—an zafin rai kaÉ—an, ko cikanka bata ce masa ba, sabida tafiya duniyar tunanin datayi, wanda hankalinta ma baya garesa.
Tsakinsa ne yajawo hankalinta gurinsa tsintar idanunshi tayi yana maka mata ƙatuwar harara kafin ya haye kanta a sukwane yajanyo murfin motar da ƙarfi kamar ze ciresa har yana haɗewa da hijabinta.
"Dan tsabar iskanci ina miki magana kinmin banza sabida kin mayar dani sa'anki to wallahi karkiga nasha miki baki É—azu kiga damar rainani ina gaya miki wahala zakisha".
Ta tsinci muryarshi acikin kunnenta.
Mamakin yawan faÉ—anshi take ji acikin zuciyarta maye na wannan masifar dan kawai bataji abinda yace ba.
Shuru tayi masa aguje yaja motar kamar ze tashi sama, sabida takaicin wawan data mayar dashi lallai yazama dole ya taka mata burki domin shi ba sauna bane ba.
Wani mahaukacin horn ya danna a gaban gate É—in wanda seda ya cika ilahirin gidan da gudu masu tsaron gate É—in suka antayo suka wangale masa shi suna É—aga masa hannun dabai da niyyar mayar musu.
Aguje ya saka kan motar ya nufi waje yana faman sake É—aure ranshi tamau kamar wani kumurcin zaki.
Tsorone fall a zuciyar Bebi addu'a take Allah yasa kada ya zubar dasu ya cuceta abanza yabar mamanta da jinya gefe É—aya kuma tsoronshi ne fall acikin ranta na yadda taga kamar ma harararta ikeyi.
Tsitt ko ina acikin unguwar yake babu sautin komai bare ka saka ran zakaji maganar ɗan adam, saɓanin unguwarsu da tun asubahi ma zakaji mutane nata kaiwa da komowarsu amman ita wannan unguwar dayake ta masu hannu da shunice jiba bakajin komai acikinta.
Tafiya mai É—an tsayi yayi kafin yahau babban titi alokacinne kuma ya saka hannu ya kunna redion cikin motar yana sauraran labaran safiya.
Ƙasa tayi da kanta tana sauraran redion itama bakuma tayi gigin ɗagowa ba.
Tafiya suke kamar ta kurame sabida yadda kowa yay shuru gwarama shi tanajin sa'i da lokaci yana ɗaga waya wadda kuma bata gane komai a maganganun nashi sabida yadda muryarshi tai ƙasa sannan kuma yawancin ma da yaren harshen turanci yake maganar tashi.
Cikin haka bacci ya kwasheta wanda batayi tsammaninshi ba.
A tsakiyar cinyoyinta ta cusa kanta tanayin baccinta cike da fargaba.
Shiko baima bi takanta ba, kawai tuƙinshi yake ya matsu ya ƙarasa da ita ya kuma juyowa ya komo gida sabida baya son abba ya tashi basu haɗuba domin wajan gobe yaji abban na maganar ze koma legos, gakuma maganar dazasuyi ta fitarshi waje wadda yasan in abban ya riga ya koma tofa da wuya ya dawo yanzu dole ze ɗan jima acan legos ɗin.
Wannan dalilin yasa yake sauri yaje ya kaita ya koma gida inyaso in sunyi maganarsu da abban still ya kuma dawowa nan ɗin domin yaga mai ze saya mata na abubuwan buƙatar gida.
Tafiyar kusan awa guda damma da go slow a hanya ita takaisu cikin unguwar tokarawa can wajan Æ´an kaba.
Wadda take shaƙe da manya manya kamfanin nika gefe guda kuma akwai yawan manyan motocin ɗibar kayan kamfani acikin unguwar wadda yawancinta ƙabilu sunfi zama acikinta sekuma masu abincin saidawa sabida yawan masana'antun dake unguwar.
Titin cikin unguwar ya shiga tare da miƙa cikinsa sosai yake tafiya hannunshi ɗaya na riƙe da sitiyarin motar ɗayan kuma yana duba wayarshi cikin lokaci kaɗan ya soma magana.
"Hellow goma yaya akai? nacefa gani nan cikin unguwar ina zan ganka na karɓi keyn part ɗin?".
Cikin sauri tare da ladabi yusuf goma wanda ya kasance yaron Aliyu ne tunba yanzuba kuma shiya wakilta anan domin ya kula masa da sabon kamfanin nasa na nan É—in domin goma yana da amana.
yace.
"Oga ai inama gida sekun ƙaraso kawai Allah ya kawoku lafiya".
Katse wayar Aliyu yay tare da maida hankalinshi ga tuƙinshi.
Dayake goman shima yana cikin nan gidan da Bebi zata tare ɗin shida matarshi da yaranshi, kuma bama shi kaɗai ba akwai mutane wajan biyar agidan waɗanda kuma duk yaranshi ne da suke lura da gyare gyaren kamfanin nashi na nan ɗin waɗanda ya zaɓa ya kuma bawa kowanne acikinsu part guda shida iyalinshi sabida gidan kamar irin gidane na haya haka tsarinshi yake ƙaton gate ne se ƙofa ƙofa wadda kana shiga kowacce akwai tsakar gida da toilet tare da ciki da falo se kicin haka kowanne part yake agidan waɗanda biyar daga ciki akwai mutane ragowar ukune babu kowa cikinsu yanzu kuma Bebi zata zauna a ɗaya ragowar na kusa da ita guda biyune su kuma babu kowa cikinsu.
Gaban farin gate ɗin gidan ya tsaya wanda ƙarar sautin horn ɗinshi ne ya tashi Bebi ta ɗaga jan idanunta daya cika da bacci tana faman kalle-kalle unguwar kamar sabuwar anguwa domin babu wasu gidajen kirki a wajan daya tsaya ɗin.
Kashe motar yayi tare da buÉ—e murfin ya fita waje, wanda itama cikin sauri ta bude nata tare da fita wajan itama tana kuma kallon unguwar kamar za,a sace mutum.
Gaban wannan farin gate taga ya nufa batare daya kulata ba, itama bin bayanshi tayi cikin sauri harda É—an gudunta.
BuÉ—ewa yayi ya shiga ciki wanda harabar gidan take ba komai se Æ´an ciyayi da tafasa,wayarshi ya É—aya tare da kira.
"Goma ina waje".
YafaÉ—a tare da kashe wayar.
Ba'a jimaba wani magidancin mutum wanda ze kusan sa'a dashi ya fito daga wani É—an lungu hannunshi É—auke da makullaye masu yawa.
Cikin sauri ya karaso gabanshi suka gaisa sannan ya bashi.
"Oga ga wannan amman sedai abuÉ—e wancan na farko É—in sabida wannan na gabanmu kwanaki ankashe maciji acikinsa baya da kyau gaskiya".
Yafaɗa yana nuna ɗayan ƙofar ta farko wadda kusan a tare da nunin hannunshi nashi suka tafi da yadda cikin Bebi ya bada sautin ƙuwwwww. na tsoron bala'i daya kamata....................
11/14/21, 3:13 PM - Allah Akbar: *BARKA! BARKA!! DA RANAR TAKUTAHA TA ANNABI S.A.W INA YIWA ƳAN UWANA MUSULMI BAKI ÆŠAYA MURNAR ZAGAYOWAR WANNAN RANA ALLAH YA ƘARAWA ANNABI DARAJA AMIN BARKA BARKA BARKA ƳAN UWANA MUSULMI* ðŸ˜ðŸ˜ðŸ’ƒ

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.