Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 28 of 81
Itako Bebi babu laifi ta É—an samu baccin da tai fashinsa jiya, muryar ihsan dake faman kiranta itace tai mata caa a dodon kunnenta É—ago idanuwanta tai waÉ—anda sukai jajur sukai wani irin girmaÉ— sabida bacci tana makawa ihsan harara"dan ubanki ubanme zan miki dazakizo kina tashina?" bata karasa ba taji muryar mama daga tsakar gida wadda takejin yadda bebin ke zagin ihsan É—in"Ubanki zatai miki maza tashi daga wannan baccin ga dambu ya hadu ki É—auraye fuskarki kutafi da hussaina"..................
_Wallahi har yanzu ina zazzaÉ“i bana jin daÉ—i dan dai nai alÆ™awarine ma amman da bazaku samu update yauba amman gashi nayi da Æ™yar Allah ya bamu lafiya amin_ ðŸ™
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }
NA
*AUTAR MANYA*
_Albishirinku iyayen yara dama yaran baki ɗaya, shin ko kinsan shararriyar tashar nan ta youtube mai suna *Abdur-rahman* ta shirya tsaf domin baku gudunmawa wajan tayaku bitar karatun ƴaƴanku cikin sauƙi?, Kai dai/ kedai maza garzaya wannan shararriyar channel ɗin domin ki dannawa yaranki dansu karu da zazzaƙar ƙira'ar da *Abdur-rahma* ke gudanarwa wajan bitar karatun alkur'ani mai girma acikinta daman sauran littattafan addinin islama kada ki manta da danna *SUBSCRIBE* tare da ƙararrawar sanarwa mungode_
https://youtu.be/PFTnz8JGFfQ
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
*43&44*
Da gudu ta fito daga É—akin zaninta a hannunta bakin nan kuwa fall da miyon bacci seda ta wankeshi sannan tayo gaban mama ta wani baje, tare da haÉ—e hannayenta waje guda sannan ta soma zuba magiya,"Mama dan Allah ki barni agida wallahi ni haka kurum jikina baya bani alkairi atafiyata wannan tallan, gwara na zauna nayi musu wankin kawai" tafaÉ—a idanunta na kaÉ—awa suna yin wani irin jajur.
"Eh daman haka zaki ce mana, kuma nasan muddin na barki agidan bazaki musu wankinba, illah daga ƙarshema ki gudu gidan iya, nagaji da wannan halin naki wallahi yadda ƴan uwanki basu zaunaba kema kindaina min wannan kwanciyar wallahi sekin fita".
Mama takai maganar tana mikewa daga wajan damma karta sagar mata da ƙudurinta datai niyya.
Cike da jin haushi ta mike buja-buja ta shirya kanta cikin wata doguwar rigar yadi amman mai roba-roba bakaramin muhalli rigar ta samu ajikinta ba, tsabar matsetan datai yasa bata iya ƙwaƙwƙwaran juyi ma acikinta daga sama kuwa tai mata mugun sharp wanda ya baiwa kirjinta damar yowa sama ya fito sosai, ƙaton hijabi ta ɗauka mai kalar pink har ƙasa ta saka, shima kuma irin na yadin nan ne mai shara-shara, sedai bai nuna shatin jikinta ba matsalar ɗaya sedai idan tana tafiyane ze iya bayyana komai na jikinta.
Turare ta fesa ajikinta batare datai kwalliyaba ta kama hanyar waje sabida jin kiran mama datai akan motar dasuka tsadance da ita zata dinga zuwa tana É—aukarsu har mai motar ya karaso anma fitar da kayan Bebin kawai ake jira.
Fuwww tai waje batako tsaya jiran hussaina ba.
Da ƙarfi taja marufin motar ta shiga tana danna baki gaba.
Seda ihsan tacewa mama ai Bebin tana mota sannan mama ta sallami hussaina da tana kicin ma tana nanatawa hussaina lissafin duk abinda suka tafi dashi daki-daki ita kuma hussainar tana gefe tana karashe cin tuwonta É—umame na karin safe, itako daman Bebi tai kaurar zuci yau bakin cikin talle yahanata karyawa.
Bayan hussaina ta gama ta wanko hannunta taiwa kowa sallama na gidan nasu sannan ta fita.
Aiko ta tarar da Bebi kamar xata fashe bata kulataba daman hussaina bata ragawa Bebi tuncan wannan yasa tafita a harkarta har mai motan yaja suka É—auki hanyarsu.
Tafiyar mintuna kaÉ—an ya kaisu sharaÉ—a Æ´an kamfani, kamar kullum a bakin tangamemen gate É—in kamfanin _Alhaji idrissa mai atamfa_ motar taja ta tsaya cikin azama drivern ya taimaka musu wajan fiddo da kulolin dambun da kular alalen, sannan sukai sallama yaja motarshi yabar wajan, aiko driver yana tafiya babu yadda hussaina batai da bebi ba akan ta taimaka mata su shigar da kayan ciki amman yarinyar nan taki harseda wani security yazo ya saka baki sannan ta É—auki robar manja ta wuce shikuma ya taimaka musu da kula É—aya sabida yana ganin kirkin Æ´an biyu yasa yay musu hakan.
Lokacin da Bebi ta saka ƙafafunta cikin shahararen kamfanin mai atamfa seda tazama ƴar ƙauye sabida yadda taga ginin glass da glass wanda aka kuma ƙawata ko'ina na kamfanin da wasu irin filawowi masu birgewa gawajan adana motoci daban kai kowanima dai sashe ( word )akwai inda xakabi ka taddashi sosai kamfanin ya ƙawatu gakuma girmanshi daya baiwa Bebi tsoro lallai waɗannan ma'mallaka wannan kamfanin akwai ruwan kuɗi duba da yadda taga ma'aikata kota ina wasu na shiga can wasu na fita banda zafafan motocin dake fake can gefe, sannan data ɗaga kanta sama kusan shidewa tai sabida yawan hawan benen ciki a ƙalla akwai kusan hawa uku, to ita inata taɓa ganin hakan indai ba'a film ba shima kuma film ɗin takan shafe shekaru bata gani ba sabida basuda kayan kallo.
Cikin jin haushi hussaina ke kiran Bebi amman madam tai nisa harseda hussaina taje tagama haɗa komai sannan Bebi tasami damar gama kallon nata ta soma karasawa can inda taga ƴar uwar tata tayi tofa ko a wajan dazasu zauna ɗinma seda bebi tabaiwa idanunta abinci sannan taja ƙafafunta, ta karasa gaban hussaina amai makon ta zauna a benchin dataga hussainar nakai, a,a seta koma can gefen wata bishiya ta zauna a saman tudun wajan tana kuma juya idanunta kallon ko ina take sosai sabida itafa ganinta take ba'a wannan duniyarba ta ɗauka awata ƙasa take wai a shirmen bebi shiyasa tace gwara ta kalli komai ta more kafin ta koma gida.
Habawa baƙin ciki kamar xe kashe hussaina har wani ruwane ya tarar mata a idanunta wannan wani irin sakarcine inda tasan hakane wallahi da gwara tazo da ihsan yanzu jiba ƴan siyan dambu sun soma zuwa ga ƴan alale tama rasa yadda zatai dasu sabida babu mai taimakonta.
Cikin ikon Allah baban nazir yazo domin su gaisa kamar kullum.
Sallama yay mata lokacin tana zubawa wani staff dambu a leda seda ta kammala sannan ta ƙarasa gabanshi ta rissuna tana gaisar dashi, cike da farin ciki yake amsa mata kafin yace.
"Ke nifa ban ganeku ina É—ayar take naga yau aikin duk yay miki yawa?".
Sunkuyar da kanta tayi ƙas sosai tana zana kasa a ƙasa sannan tace.
"Wanki mama tace tayi amman munzo da Bebi".
ÆŠan jimm yay kana yace.
"Yoni ai bana rabewa daku kusan duk kamanninku guda wacece haka?".
Ya tambayeta yana É—an waige kozega Bebin.
"Bilkisu! fa gata can"!
Ta juya ta nuno mishi bebi wadda take kallon saman benen wajan.
Sakin Baki yayi cikin mamakin ganin yadda Bebi ta girma masha Allah sannan ya soma kiranta.
"Bilkisu! Bilkisu!! yaki nan dan gidanku ƴar ƙauyen banza kina can a zaune kinbar yayarki tana aiki ita ɗaya ko".
Wani sanyi hussaina taji hartana murmushi.
Wanda adai dai wannan lokacin itakuma Bebin tazo wajan kiran nashi sabida ta ganeshi domin tana ganinshi gidan baba.
Gabansu tazo tare da rissunawa tana gaida shi.
"Toni aike Bilkisu idan zanganki a hanya bana shaidakiba, sabida girmanki harkinfi Æ´an uwanki masha Allah".
Yafaɗa yana rike haɓa, burus tai dashi bata ce komaiba harya gama mata nasiha akan tabar wajancan ta koma wajan ƴar uwarta ta taimaka mata suyi sugama sutafi gida.
Ciki-ciki ta amsa masa da "To" sabida itafa haushima ya bata amman sabida ba,a basu tarbiyar musuwa babba ba yasa ta miƙe zuwa saman benchin dataga ƴar uwar tana kai.
Zamanta yayi dai-dai da ƙarasowar usman wajan lokacin ita kuma hussaina tana gaban baban nazir yana yimata ƴan nasihohi akan hakuri da ɗan uwa kada taga bebi nayin haka taji wani abu kuruciya ce kowa da irin tasa.
"Assalamu Alaikum ƴar ƙanwata barka da safiya ya mamarmu?".
YafaÉ—i hakan cikin barkwanci dukshi ya É—auka hussaina ce ko hassana sabida lokacin tai kasa tana gyara zamanta.
ÆŠago da dara-daran idanunta tai tare da zuba masa su batare sata saki fuskarta ba.
"Tsarki ya tabbata ga ubangijin halitta"!
Abinda ya fito daga cikin bakin usman kenan yayin dayay tozali da fuskar Bebi wadda tai tamau da ranta.kamar an aiko mata da sakon mama ta rasu.
Basarwa yay amman cikin ransa yay santin kyawun halittar Bebi amman santin bana soyayyaba sedai yaji yarinyar ta shiga ransa lokaci É—aya.
"Ina Æ´an uwan naki suke?"
YafaÉ—a yana saita nutsuwarsa.
Amai makon ta bashi amsa setai saurin tsugunnawa.
"Ina kwana?, gata can wajan baban nazir".
Tafaɗa kanta a ƙasa still kuma tana tsugunnan.
"Kai masha Allah! rabbi ya sakawa da uwa mahaifiya da alkairi, bisa jajurcewa wajan tarbiyantar da ƴaƴanta waɗanda suka tashi cikin halin maraicin rashin bango! agidansu wato mahaifi amman hakan bai hanata jajurcewa wajan basu tarbiya ta ƙwarai ba".
YafaÉ—i hakan yana numfasawa.
Lokacin hussaina ta karaso itama ta rissuna ta gaisarshi.
Cike da tsantsar farin ciki ya amsa sannan ya mayar da hankalinshi ga Bebi wadda har yanzu bata mike ba.
"Ƙanwata kekuma maye sunanki?".
Miƙewa tai ta zauna.
"Bilkisu"!
Wata Æ´ar zabura yay kaÉ—an.
"A,a kice mamarmu ce wallahi sunan amminmu kenan masha Allah suna mai kyau".
"Eh amman akan cemin,Bebi".
Ta bashi amsa kanta tsaye.
"Ok masha Allah nice name momynah! oh jiya kece muga gani kenan?"
YafaÉ—a yana duba wayarshi "Eh"!
Tabashi amsa tana mamakin ashe daman jiya sune sukaje gidansu? wato idan ta fuskanta wannan shine mai surutun nan na tsiya! shiko É—ayan waye? sanin batada mai bata amsa yasa ta watsar da maganar tanajin yana tsokanar hussaina har yana cewa tabbas wataran dole ammi taga bebi takwararta anan yake baiwa hussaina labarin jiya ai yaje gidansu amman baigan suba.
Sosai taga suna magana da hussaina kamar sun jima har lokacin da masu siyan dambu suka zo.
"Ƙanwata zan koma office amman banyi break ba, pls ki bawa momyna ta mikomin yau masinjana bai nan, tahau sama hawan ƙarshe daga hannunta na dama ta duba room 2 nan ne office ɗina, amman yau alale zanci sabida manjan nan ya burgeni".
YafaÉ—a yana dariya cikin sauri kuma ya juya yay tafiyarshi batare daya tsaya jin mai zasu ce ba.
Murmushi hussaina kurum tayi aranta tana yaba kyawawan halaye irin na usman gashi dai mai kudi amman sam baida girman bare izza kullum ƙara jansu ajiki yake tamkar daman can yajima da saninsu.
Cigaba sukai da zubawa jama'a dambun wanda har Bebin taÉ—an saki sabida faÉ—anda baban nazir yay mata da kuma zuwan usman wanda hussaina taga Bebi tai na'am sosai da usman É—in.
Ƙarfe ɗaya da rabin rana suka dakata da cinikin famfon dake can baya hussaina ta nufa tayo alwala kamar kullum akan wani ɗan dakali ta shinfiɗa dardumar dasuke zuwa da ita ta soma yin sallah, itako Bebi da wannan damar ta sami ƙaton flate ta shaƙe da dambu harda pure water sabida azabar yunwar datake ji, ganin babu yawan mutane a wajan duk suna masallaci suna sallah yasa ta ɗorashi a saman cinyarta tahauci hannu baka hannu ƙwarya.
Tana gab dagama ci, Shikuma Aliyu ya dawo daga masallaci saboda duk hanyar ɗayace kusan a haɗe sedai kwanonin da suka rabu wanda yabaiwa kowani ɓangare damar nufar hanyarshi, Tundaga Nesa yake kallon duk abinda yarinyar takeyi sosai yake mamakin yarinyar mace budurwa ta zauna a center jama'a tana kai abinci cikinta, seda yakusan shiga corridow ɗin daze kaishi word ɗinsu yagane masu dambun nan ne da usman ke santi, to tayaya tsafta ta samu anan wanda harze saka yay gangancin kai dambun cikin bakinshi, Baiga fuskar yarinyar ba amman ya shaida hijabinta, harya karasa office ɗinshi mamakin wannan al'adar yarinyar yake wadda tsananin rashin kamun kanta ya bashi mamaki domin babu kamunkai ga maicin abu a hanya,Watsar da zancen yayi sabida tarin aikin dake ganshi wani file ya ɗauko wanda ya saka dole seyaje office ɗin usman yay masa bayaninshi kafin ya saka hannu kasancewar kwana biyu bai nan shi.
Tashi yayi da ganshi batare daya nemi sakatarenshi ba, domin daman shi ba komai yake zama seyay aike ba, kasamcewarshi mutum mai zafin nama yasa baya zama kusan dakanshi yake gabatar da komai.
Fita yayi zuwa office É—in usman anan ya sami usman É—in suna waya da zee seda ya gama sannan ya nemi waje usman É—in ya soma yi mishi bayani kan file É—in wanda harya shafe lokuta wajan usman É—in.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.