Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 45 of 81

NAKUÆŠINE

64

Sosai abin yake damun su abba ganin yadda Aliyu yay buris da zancen aure, kuma basu kaÉ—ai ba hatta Æ´an uwanshi abin yana damunsu domin a yanzu haka nusaiba mai binshi tana da yara uku! ya abbakar Æ´aÆ´a huÉ—u, ya umar kuwa yana da É—aya, yanzu kuma matarshi tana da wani cikin ga kuma usman shima matarshi tana É—auke da cikin fari danma batai haihuwar wuriba domin yanzu haka kusan shekarunsu biyar da aure amman se yanxu akai cikin fari, Amina ansaka mata rana, tare da É—an gidan abban bauchi, yanzu haka kuma aminar nurse ce, tana aikin asibiti.
Ƴan biyu suna lavel 2 a university, kuma suma duk da mazajensu a hannu kuma suma ɗindai ƴaƴan cikin familyn ne.
Ruma yayar khadija ita kaɗai ke aure a kaduna tana auren ɗan ƙanwar ummansu wanda umman ta kawo mata tace ta aura ganin jinin ummanne yasa su alhaji babba suka amince a shekara guda akai bikinsu da nusaiba mai bin Aliyu ita ruman tana nan kaduna yanzu yaranta huɗu.
Rayuwar Aliyu ƙalilan ce acikin gidansu sabida tunda ya dawo bai zama kullum yana hanya fita ƙasashen waje domin kawo samfir in kuwa yana kasar nan tofa yana cikin kasuwa suna harka da ƴan kasuwa sabida suna rabawa ƴan kasuwa kaya su haɗa masu kudinsu sannan ƴan kasuwan na zuwa wajansu, sari amman basa harkar komai se atamfa.

Khadija tun tana ɓoye damuwarta akan Aliyu hartazo ta soma bayyana fili domin juyin duniya anyi da ita akan ta fidda miji taƙi haka xalika a family in ankawo mata setace bata so seta saka kuka! su alhaji babba da abba suna tausayin khadija fiye da xato sabida maraicinta.
Dan haka basa takura mata karatun ma dasu amina suka fara da Æ´aÆ´an alhaji babba su hidaya amman tsabar tunani harya kai ga sun fice sun barta da gyara exams.
Wannan abin takaicin ya dami umman khadija rannan dai ta sakata gaba har seda ta gaya mata abinda ke ranta.
Da kirsa da komai seda umma ta cusa khadija wajan ammi harta kai ga tana kwana tare dasu ƴan biyu, umma ta ɗauki ƙudirin setayi mai yuwuwar ƴarta ta auri Aliyu, sabida tun rasuwar yusufa taso abba ya aureta amman abin yaƙi ( kuji fa ) wai sabida suma su dandali arziki( hmmm banda wanda kuke ci mutum kenan)dan haka taci alwashin cusa wa ɗansa khadija wanda daman tun kafin khadija tazo mata da maganar take saka abin aranta.
Rawar kai kala kala babu wanda khadija bataiwa Aliyu amman shikam bata ko gabanshi.
Harkar gabanshi kawai yake domin yanzu kulada harkar dukiyar mahaifinsu itace akan gaba, ga hidimar gida domin alhaji babba yay ritaya haka xalika abban bauchi shima haka duka iyayen nasu basa fita abbansu ne kaÉ—ai yake tafiya legos ko waje domin shigo da kaya shima kuma yakan jima bai fitan ba domin yabarwa Ali wannan jigilar.
Duk da yaransu alhaji babba kowa yana aikinshi na gwamnati domin baifi mutum biyar ne a karkashin kamfanin abba ba, amman hakan bai saka abba yafasa dasa su Ali direwa kowani part kayan abincin wata ba, haka xalika sutturu karatun yara zuba mai a motocin daya zube duka abba ya dauke musu, sannan kuma babu wanda bai É—auka yakai saudiya sauke farali ba.
Su kansu ƴaƴan abba su ya abbakar sunada mugun kuɗi, sosai, ba kamar Aliyu a kaf cikinsu sabida shi bai laru da aikin ƙarƙashin kamfanin mahaifinsu kaɗaiba, sabida a kullum yana ayyana kuɗin bana sabane shi ɗaya, wannan dalilin yasa ya raba ƙafa yana lura da kamfanin mahaifinshi a matsayin amana da biyayya gefe ɗaya kuma shima yana lura da harkokinshi na kasuwanci wanda ya haɗa da kawo motoci, tare da atamfofi yana bawa manyan ƴan kasuwa wanda ko iya wannan ribar tashi kaɗai zata iya riƙe gidansu,kuma Allah yasaka masa nasibi a harkokinshi domin gidajen kansama daya gina ya bada haya sunada yawa banda kaddarori tare da ƙaton ginin kamfanin sayar da atamfofi dayake ginawa anan Tokarawa!wanda shi kansa abba daya ga ganin seda ya sarawa ɗan nashi.
Yanxu haka rabinshi yana harkar kulada kaddarar abbansu rabi kuma yana zuwa tokara domin ganin ginin kamfaninshi na ƙashin kanshi wanda ze dinga sauke dillar atamfofi lesuna shaddodi harma da takalma danshi yace baxe tsaya a atamfa kaɗai ba.
Iya tsaruwa kamfanin ya tsaru sabida ɓangaren atamfofi daban! na shadda daban! na lesuna daban! na takalma da mayafai daban! domin bakaramin kudi yake narkawa ba.
Kuma babu ko silan abba ciki da iya tsantsar guminshi dayake business É—inshi yake gina kayanshi yakai su ya abbakar sun gani dasu alhaji babba wanda suka dawo gida suna santin wurin tare da jinjinawa Aliyun.
Ranar dasu ammi da umma da su hajiya matan alhaji sukaje ganin a daren umma batai bacci ba dan kuwa seda ta dangana da wajan Alhaji babba karya ta lafta masa akan cewar khadija bata cin abinci bata shan ruwa akan soyayyar Aliyu.
Babu kunya bare tsoron Allah haka taita lafta karya harda kukan kada su bari khadija ta rasa ranta su taimaka mata su biyu ta haifa ga khadija marainiyace.
Rarrashinta Alhajin yay kana ya hau faÉ—an akanme khadija xata kashe kanta ita da É—an uwanta cewa umma yay ta tashi taje ciki zasu tattauna akan maganar da Æ´an uwanshi.
Washe gari alhaji ya kirasu abba ya gaya masu a ranar abba ya kirawo Aliyu tare da khadija ya gabatarwa da Aliyu khadija a matsayin matar dasuka zaɓa masa.
Kamar ze kuka haka ya amsawa abban tare da tashi yabar wajan itako khadija ranar batai bacci ba sabida farin ciki.
Tuni magana ta karade family wanda wasu daga cikin Æ´anmatan famiyn suke cewa inama sune sukai dace haka.
Wasuko tausayi take basu sabida sun san baida wasa.
Tundaga lokacin yawanci khadija take zama a falon ammi tare da bin ammi kicin ta tayata aiki wanda ta sami wannan karatun daga wajan ummanta.
Sosai ammi take yabon khadija shiko gogan ko dariyarsa bata taɓa gani ba tunda shi daban bamai yawan far'a bane wannan se usman shine mai yawan far'a da sakin fuska.........................

*NAKUÆŠINE*
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *PART* 2

NAKUÆŠINE

*65*

ALIYU IDRISS MAI ATAMFA shine cikakken suna shi, ɗane na uku a wajan Alhaji idriss mai atamfa, yana da kimanin shekaru talatin da bakwai ciff a duniya, ya sami saukar karatun alqur'ani mai girma tun yana da shekaru goma a duniya, hakanan yay haddarshi yana da shekaru sha ɗaya a duniya, ya sami karatun addinin islama cikakke ya karanta manyan littattafan addini, a ɓangaren karatun boko yana da matsayin masters wanda ya sami iliminshi akan harkar kasuwanci business accounting, tun bayan dasuka kammala secondry ɗinsu mahaifinsu ya ɗebe su shida ɗan uwanshi usman ya fitar dasu ƙasar uk anan wata jami'a dake ƙasar suka sami damar yin karatun su tundaga matakin digree har zuwa masterring, batare dasun kuma dawo gida ba koda da hutu, har seda suka kammala karatunsu sannan suka dawo ƙasarsu ta gado cike da ɗunbin nasarori, daga nan ne kuma kowa ya kama aiki ganga ganga a karkashin kamfanin mahaifinsu.
Har zuwa wannan lokacin da shi ALIYU yakai ga soma gina kamfaninshi na ƙashin kanshi banda wasu sabgoginshi dayake na harkar kasuwancin shi da jarinshi.
ALIYU mutum ne mai riƙo da addininshi domin baya wasa da ibada hatta azumin nafila ko wanne baya wuceshi hakanan yana da miskilanci na gaske baida sakin fuska sosai, gefe ɗaya kuma harkar gabanshi kaɗai yake baida saka idanu akan lamarin wani, Dogone sosai mai suffar ƙarfafan maza baƙine shi amman irin kalar nan mai ƙyalli, yana da manyan idanu masu firgita marar jin magana mai ɗauke da dogon hanci wanda bai cika siranta ba, sedai yana da tsaho da ɗan faɗi kaɗan, bakinshi madai daici haƙoran ciki farare ne tass ajajjere dasu, yana da wani ƙaton tabon abin sallah a saman goshinsa wanda har wani turzawa yayi yay wani irin kurji-kurji yana saɓa, gashin girarshi mai gazar gazar ne, wanda ya cure a saman doguwar fuskarshi mai ɗauke da wani irin haɗaɗɗen saje wanda ya haɗe da gemun daya bari a fuskar tashi.
Baya barin suma a kanshi duk da yana da yalwarta amman bai barinta sedai yay askin saisaye batare daya bar suma akanshi ba, haka nan Aliyu mutum ne mai tsananin tsaftar gaske ko kaɗan baison ganda bare ƙazanta haka xalika baya son sanyin jiki komai nashi da zafi-zafi yakeyi da ƙarfinshi da lafiyarshi, domin ko shiryawa ze baya wuce mintuna goma ya gama, ya fice yana da mugun zafin nama, yana da rashin son magana sedai inka taɓoshi akwai zafin rai da zuciya tare da taurin kai, wannan dalilin yasa ƙannenshi suke mugun shakkarshi hakanan kuma ma'aikatan su suna ganin girmanshi sabida iya mu'amalarshi da jama'a sam baya nuna girman kai ko izza baya nuna cewar shi mai kuɗine a kullum yana nuna cewar shidasu ɗayane, suna matukar jin daɗin tafiya da shi sedai yawan rashin maganarshi kaɗai ke haɗasu dashi amman iya adalci da tausayi yana dashi.
Yana da biyayya sosai domin duk abinda ammi da abba suke so yakan hana kanshi farin ciki domin ya samarwa mahaifanshi yakan aje lokacinshi mai mahimmanci akan ya kyautatawa mahaifanshi, wannan dalilin yasa suma mahaifan nashi ke ƙoƙarin ganin sun kyautata mashi.
Aliyu yana cikin jerin mazaje masu mugun ƙarfin sha'awa tsananin zurfin cikin shi ke sakawa bai nuna halin dayake ciki illah mutum ɗaya dr mijin kanwarshi nusaiba, wanda suka taso a tare ɗan wajan alhaji babba shine kaɗai yasan halin da abokin nashi ke ciki shima kuma dalilin yana karɓar magani wajan shine.
Duk halin daze shiga a ɗakinshi shi kaɗai yake gama murƙususun shi na azaba batare da wani ya sani ba, sedai ƙwayar idanunshi ta nuna wadda kusan kullum take a lumshe wadda gazar gazar ɗin gashi suka rufeta ruff gwanin sha'awa don kafin kaganshi ya buɗe ƙwayar idanunshi tarr akan mutum da wahala inko yay hakan sedai inyana cikin ɓacin rai wanda inya kalleka da ita seka kusan fitsari dan firgici! sabida yadda Allah ya bashi wani irin ƙwarjini da haiba, ma'abocin son ƙamshine wannan dalilin yasa kamshin ya sami wuri ajikinshi ya kama kullum yazo waje zakaji kamshi wataran ma kafin yazo wajan kamshinsa ze fara maka sallama.
Yana da kyakykyawar mu'amala a tsakanin shi da Æ´an uwanshi, sedai inda ammi ke fama dashi rashin shiga cikin jama'a sosai sau tari yakan zauna ne a É—akinshi yay ayyukan gabanshi koya É—auki carbinshi na yatsun hannunshi yayta tasbihi ga ubangiji yakance hakan yafi masa yayta zuba surutun da baida amfani.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.