Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 75 of 81
*ZUMA A BAKI...!*🌹
{ Painful love Story }
_Shine sabon littafina da ze soma zuwa da zarar na kammale wannan kedai/kaidai maza ka hanzarta ka biya naka domin tun kafin na soma posting ɗinshi zan soma karɓar kuɗin masu son karantawa kai dagajin sunan kasan akwai rikita rikita wadda bazan ce komai ba amman rubutuna ze bayyana muku *Zuma A Baki* comming soon da izinin Allah ƙofa a buɗe take masu soma payment_
*ÆŠAN ÆŠANO*!
_Wannan karon tafiya nai mai mugun nisa har naje na zaƙulo muku ƙayataccen labarin masoya Biyu *Umar Muhammadu Sarkin-Gida* wanda jama'ar unguwa da abokai ke masa laƙani da ( *Cika Daji* ) Eh cika dajin ne mana sabida duk umar ba,a rago to hakance ta kasance ga shalelen inna kuma autanta wanda ya tsunduma a dafkin kogon soyayya da *Aishatul humaira* ɗiyar anty Har soyayyar tasu ta zamewa kowannen su *ZUMA A BAKI* Tabbas tunda nake rubutuna bantaɓa katari da labarin daya kwantamin ya tsayamin kamar ZUMA A BAKI ba! tabbas kodaga jin sunan kasan akwai rikita rikita kuda kawai kubiyoni nasan insha Allah bazan baku kunya ba_
*Hohoho! my fans nace muku painful wallahi da gaske wannan soyayyar mai zafice mai raÉ—aÉ—i ce duk wani masoyi yaci katari da wannan labarin nawa seya dara seya koka seya warwasa labarin ze Æ™ayatar ze tsaya arai ze nishaÉ—antar ze wa'azantar ze ilimantar kudai kubiyoni kawai*💃💃💃💃ðŸ¤ðŸ»
_kai ƙoƙarin ganin kayi payment domin zan soma sakin sane da zarar na kammale wagga_
~N~ *300*# *ta wannan account numbern 0078174806 starling bank show me your evidance of payment ta wagga numbern 08142105218 love you my Æ´an amana my Æ´an iya wuyata*
11/14/21, 3:20 PM - Allah Akbar: *96*
Alhaji mai gwall tare da iyalinshi zaune a falo suna hira, hankalinsu kwance kayan marmarine agabansu sunaci cikin nishaÉ—i da farin ciki da kwanciyar hankali.
Khalifa yana saman cinyar mamansa tana shafa kansa cikin kulawa shikuma alhajin yana ɓare apple yana saka mai a bakinshi.
Sam sun manta ma da lamarin wata ladi bare suyi maganar yaya ta kwana koko a wani hali take ciki? su kawai hankalinsu yana ga sabgar gabansu
Sallamar mai gadi ce tasa suka tsagaita da hirar tasu cikin ƙyamar talaka, ƙanwar khalifa take daka wa mai gadin tsawa.
"Kai miye zaka wani shigo mana falo kana wata sallama kamar mahaukaci kacikawa mutane kunne?"
Jikinshi yana rawa ya rissuna.
"Afuwan hajiya ƙarama ga wannan takardar wani yarone yace abawa alhaji"
Amsa tai a wulakance kana ta koma ciki daga tsaye ta mikawa alhajin sannan ta koma saman seater ta kwanta.
A fili alhaji yake karanta takardar.
_Kotun shari'ar musulunci dake zaune akan hanyar zaria road tana miko takardar sammaci ga, Khalipha Alhaji mai gwall, abisa yadda yay watsi da daraja da ƙimar aure bayan rattaba saki har biyu kai tsaye ga matarsa hakan bai masa ba kai tsaye ya afka mata kamar fyaɗe batare da sanin ƙimar ɗan adam ba, sabida haka wannan kotu mai adalci tana neman khaleepha shida mahaifinsu ranar litinin mai zuwa da misalin karfe taran safiya_
Wata dariya khalifa ya saki ta keta shima alhajin haka yayta dariyar harda kifawa.
Bayan sun gama jin komai daga wajan alhajin.
"Hoho talaka bawan Allah ni yau talakan dake kasana ze shigar ƙara tabb lallai sun taro faɗa dani"
Alhaji ya faÉ—a yana fiddo wayarshi lowyern shi ya kira yana dariya yake sanar dashi.
Shima lowyern alhajin dariya yake kana yace mai subar mai komai ze bincika case É—in.
Katse wayar yayi yana mai cewa inama ai shari'ar gobe domin ze gwada musu karfin kuɗine, khalifa kam dariya yake domin ya riga ya saba lalata ƴan aikin gidansu ma koda kwanaki uwar wata yarinya daga cikin masu aikin nasu yayma ƴarta ciki data kaisu ƙara a ranar aka kori case ɗin sabida sunyi toshiya da kuɗi.
Dan haka wannan bai É—aukeshi abakin komaiba domin yasan tunda sunada kudi sun gama komai kilama reshe ya juye da mujiya.
A ɓangaren ladi kuwa sosai take samun kulawa sabida yadda Aliyu ya saki kuɗi komai yana tafiya mata cikin sauki hatta ɗinkin ma da aka mata yanzu ya fara cirewa, haka zalika matsalar abinci ma basu da ita sabida yadda Aliyu yasa aka kai masu kayan abincin can gidan su na ƴan kusan sannan yayma samarin gidan alƙawarin aiki a kamfaninshi na tokarawa da zarar an fara aiki.
Ranar dasu kawu tasi'u suke jin maganar kotu da kuma wannan aikin daya samarwa Æ´aÆ´ansu har kuka sukai suna cewa.
"Da ɗa da dukiya ba,a musu mugunta domin baka san wanda zaka mora ba ada sun ƙyamaci ƴaƴan ɗan uwansu ashe ajikinsu zasu huta rayuwa kenan"
Kamar zasu ari bakin godiya wajan Aliyu ranar har seda yaji babu daÉ—i sannan yay masu sallama ya tafi gida ranar ma baijewa bebi ba sabida gajiya ko khadijama bata ganshi ba ya kulle kansane a É—aki yana faman tura sakonni na ordern kayanshi na kamfani dayake son yaje ya tawo dasu nan da wata biyu.
Ya kai wajan karfe biyun dare yana abu É—aya kafin ya kashe system É—in ya kwanta.
Wa shegari ranar talata nanma sun sami baƙi daga kamfaninsu bai shigo gidaba se dare.
Zama yay a gefen gado yana cire safar kafarshi sannan ya tube suite É—in jikinshi.
Wayarshi ya zaro ya lalubo numbern goma ringing É—aya goma ya É—aga bayan sun gaisa yake cemai yana son ya bawa mufida waya ta kaiwa Bebi.
Cikin bin umarni goma ya bawa mufida wayar ta kai mata.
Tana kwance saman sopa tana faman baccin daya zame mata jiki tunda ya tafi bata da aiki sena bacci umman mufida ke aiko mata da abinci da daddare kuma su mufida suzo su tayata kwana.
Sallama mufida tai sannan taÉ—an bugi kafarta.
"Anty ki tashi ga waya inji abbanmu"
Cikin magagi ta amsa tana yamutsa fuska.
Mufida juyawa tai aikwa nan wayar ta hau ringing.
Seda ta fita waje ta zubda miyaun daya cika mata baki sannan ta É—aga.
"Assalamu Alaikum"
TafaÉ—a cikin muryarta mai alamun bacci.
Lumshe ido yay yana shafa sajenshi.
"Amin wa'alaikissalam matar haidar"
Gabanta ne ya faÉ—i jin muryarshi kaÉ—ai ya hargitsa mata lissafinta.
"Umm kamanta dani ko?"
Zaro idanunshi yay waje kamar tana gabanshi.
"Bebyna ashe zan manta kaina, hope kina lafiya dai?"
Tura mai baki tai kamar yana gabanta.
"Amman yau kwana uku, bana tare dakai ko waya bakai ba?".
Rarrashinta ya somayi cikin so da kauna nan da nan ta soma dariya tana tambayarshi yaushe ze dawo.
"Mekika tanadar min na dawowar?"
Cikin sakarci tace mai.
"Tabb nifa wallahi tunda katafi bana girki"
Gabansa ne ya faÉ—i cikin sauri kuma yace mata.
"Subuhannallahi meyasa?"
"Ni wallahi bana son warin gas ɗin ranar da katafi na kunna zan ɗora tea kasan har amai nayifa shine umman mufida ta hanani girkin, ita take kawon kumani bana son komai inba tuwonta ba, se kuma kaina yayta min ciwo da zazzaɓi naita amai da safiya da magariba naita bacci wallahi wani bin mafa akan sallaya nake baccin"
Lumshe idanunshi yayi luff yana shafa kwantaccen gashin kirjinshi laso ƙasan laɓɓansa yake waɗanda suka ɗan bushe kaɗan.
Kobai karatun likitaba yasan abinda take nufi.
"Alhamdulillahi kina son mu sami boy mai sunan abbanki?"
YafaÉ—a cikin raÉ—a
"A,a"
Ta bashi amsa kanta tsaye.
Gabansa ne ya faÉ—i cikin sauri ya buÉ—e idanunshi
"Sabida me kika cemin haka?"
Ya tambayeta.
"Sabida bana son haihuwa gaskiya haka kawai salon in anganni da ciki asan abinda muke dakai a É—aki, ni wallahi bazakaja aitamin kallon..............".
Dariya yake harda riƙe ciki ƙuruciya tuburan lallai maza suna morewa in suka auri yarinya karama domin anan zasu san takan wauta da kuruciya
"Asan me madam?"
YafaÉ—a yana kunshe dariyarsa.
"Asan abinda kakemin mana, kai yanzu bazakaji kunyar ammin kaba?"
Dariya yay kaÉ—an wadda inba itanba babu maijin irin dariyar dayake.
"Kunya a raya sunna? aure fa sunnace mu tayaya akai aka samemu? haba amaryarta ki daina faÉ—in haka plssssss"
Tura mai baki tai gaba.
"Nifa wallahi bazan iya wankin kayan kashiba sannan yaro yayta shamin nono haka kawai nifa bana so"
Nutsuwarsa ya gyara.
"Nidai nasan nai ajiya amararki sabida haka ki kulamin da kanki sosai kafin nazo, semuje asibiti, in banda abinki nimafa nasha bare bebyna daman ai dammu akayi shi nida yarana kaÉ—ai"
Dariya tayi har tana rufe idanunta.
Sosai ta sake suna hira batare daya fahimtar da ita abinda yake hasashe ba sedai koda wasa bai nuna mata tana da shigar cikiba sabida yaga take takenta na kuruciya acewarsa kartai masa wasa da kaddara.
Seda ta soma hamma sannan ya katse wayar anan wayar ta kwana wajanta seda safe mufida ta tafi da wayar wajan abban nata.
Shiko a daren kwanan sallah yay yana addu'ar Allah yasa hasashen shi yazama gaskiya.
Bebi nada cikinshi lallai Allah mai yadda yasone da bawansa wato dai aurenshi ma harda rabon haihuwa shiyasa Allah ya kawo auren gab babu jan lokaci.
Duk da bashida tabbas amman da safe kowa agidan ya shaida farin cikinshi sabida yadda ya dinga rabon kuÉ—i ga ma'aikatansa hatta khadija ranar taga gata da safe.
Haka nan ko a office sosai ya sake yake harkoki da jama'a haka nan lina wannan tsohuwar budurwar tasa datake sonshi ita kanta dataje office É—insa yau É—in taga sauyi anan take bashi card É—in bikinta tana yi mai bayanin ta karbi musulunci dan haka aure zatai zata auri musulmi É—an nan ma'aikatar.
Sosai yayta farin ciki harya sa ta kira angon nata yay musu kyautar maƙudan kudi sannan ya masu fatan alkairi suka tafi.
Koda ya tashi daga office daman kamar akan ƙaya yake kai tsaye gidan bebi yayi bayan ya gayawa khadija cewar yana da uzurin daze kaishi safiya bai dawo ba..................
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.