Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 77 of 81
Mama ta mikawa hassana wayar wadda ta amsa tana murna.
Nanfa hira ta barke har hassanar ta bawa sauran suka gaisa sannan suka katse wayar kamar kada su rabu.
"Oh ni aishatu yaran yanzu babu kunya wai mijin bebi ne kecemin batada lafiya tana da ciki"
Dariya babar ladi tai da inna suwaiba kanwarsu abban bebi kana sukace.
"To ai zamanin ne se a hankali yaran yanzu kamar jira suke daga an haÉ—u se ciki, Allah ya raba lafiya wannan aure ashe rabone yasa akayishi cikin gaggawa".
Nanfa hirar lissafin cikin ta barke.
"Aini tun yanzuma zan soma haÉ—a kayan yajina kafin barkono ya tashi"
Cewar inna suwaiba kanwar abbansu bebin.
Dariya hussaina tai.
"mama zata goya jika Allah mai iko"
Mako mata hannu mama tai.
"Babu É—an dazan goya kowacce cikinku tai goyon abinta"
Sosai suka sake suna hirarsu har lokacin da suka tashi tafiya sukai sallama suka tafi, koda suka koma gida mama kamar tai tsalle dan murna lallai Allah ne abin godiya a koyaushe tana godiya ga Allah daya axurtata da Æ´aÆ´a mata nutsatstsu waÉ—anda ta raina ta basu tarbiya ingantacciya har Allah yasa yanzu zata soma amsar jika daga gurinsu.
********
Ita ko bebi tana gama waya da mama ta koma jikinshi ta kwanta tana lumshe idanunta.
Kamata yay suka koma falo tea ya haɗo mata data sha tasha magani taɗanci apple ɗin dayazo da ita, Anan sukai sallar isha'i ta koma kan cinyarshi ta kwanta hannunta ta saka tana ɗan jan gemunshi kamar yadda umman mufida ke mata lecture akan yawan wasa da sassan jikin mijinki amman inda yafi ɗaukar hankalinshi alokacin da kuke keɓance da juna,
"Kasan É—azu banji dadin wanki dakai ba"
Yaji maganarta.
"Saboda me?"
"Sabida Allah"
Murmushi yayi amatse yake da ita amman baison ya nuna mata hakan kodan lalurar jikinta, shiyasa ma shurun tasa tai yawa.
Hamma tayi tare da mikewa ajikinshi ta bankaro mai kirjinta tare da cewa.
"Bacci nikeji wallahi"
HaÉ—iyar miyau yay kana yace.
"Okey" ararrabe muryarshi can kasa alamun ya soma hawa network.
ÆŠaukarta yayi zuwa bedroom sauya kaya sukai ita ta saka wata half gown ta bacci shikuma ya bar only boxer'n jikinshi batare daya saka komai ba kwanciya sukai bayan ya shafe musu jikinsu da addu'ar tsari.
RuÉ—a mata jiki ya somayi da salonshi tare da haÉ—e bakinsu waje É—aya hannunshi zube a kirjinta yana sarrafa mata su,cikin kankanin lokaci komai yagama sauyawa soyayya mai tsayawa arai yake gwada mata sosai suka kasance tare har lokaci mai tsayi kafin ya zare jikinshi anata ya sunkuceta sukai bayi wanka sukai suka koma baccinsu.
Da asubahi ma da ƙyar ya barta yana dawowa suka koma ruwa wanda ranar ko office baije ba seda usman yay masa waya yace jinya yake, yinin ranar sallah cin abinci kaɗai ke tadasu sabida cikin bebi mai jarabar nacin mijine shiyasa baya gajiya itama kuma bata gajiya nan da nan aman ma ya tsaya hakannan zafin jikin nata ya dena kobai nemeta ba ita zata saka masa kuka ala dole seya kara abin har mama yake bashi, seda yay mata kwana biyu kamar na dija sannan ya soma kokarin komawa gida wannan karonma seda tai kuka sannan tabarshi ya tafi, koda ya koma gida shima a sukuku yake baya wani samun sukuni ga shige da ficen karar su khalipha wadda yau sauran kwana ɗaya ashiga kotu wanda ranar ta kama zagayowar girkin bebi.
Babu laifi yana bawa dija kulawa itama irin ta auratayya, ranar daze koma gidan bebi cewa dija yay zeje legos, ze kwana biyu haka ya shirya ya nufi kotu wadda yau É—in za,a soma gabatar da karar da karfe goman safiya gaba É—aya kotun ta cika khalifa kaÉ—ai ake jira domin hatta ladi ma ta sami zuwa kotun wan aka É—aukota daga asibitin
Karfe goma saura alkali ya shigo wanda suma su kalifan suka shigo kotun shida ubansa da yan gidansu da lawyansu hakannan Ya nura tare da sauran lauyoyin da Ali ya É—auko suma sun hallara dan haka alkali ya soma magana kamar haka.............
*ZUMA A BAKI...!*🌹
{ Painful love Story }
_Shine sabon littafina da ze soma zuwa da zarar na kammale wannan kedai/kaidai maza ka hanzarta ka biya naka domin tun kafin na soma posting ɗinshi zan soma karɓar kuɗin masu son karantawa kai dagajin sunan kasan akwai rikita rikita wadda bazan ce komai ba amman rubutuna ze bayyana muku *Zuma A Baki* comming soon da izinin Allah ƙofa a buɗe take masu soma payment_
*ÆŠAN ÆŠANO*!
_Wannan karon tafiya nai mai mugun nisa har naje na zaƙulo muku ƙayataccen labarin masoya Biyu *Umar Muhammadu Sarkin-Gida* wanda jama'ar unguwa da abokai ke masa laƙani da ( *Cika Daji* ) Eh cika dajin ne mana sabida duk umar ba,a rago to hakance ta kasance ga shalelen inna kuma autanta wanda ya tsunduma a dafkin kogon soyayya da *Aishatul humaira* ɗiyar anty Har soyayyar tasu ta zamewa kowannen su *ZUMA A BAKI* Tabbas tunda nake rubutuna bantaɓa katari da labarin daya kwantamin ya tsayamin kamar ZUMA A BAKI ba! tabbas kodaga jin sunan kasan akwai rikita rikita kuda kawai kubiyoni nasan insha Allah bazan baku kunya ba_
*Hohoho! my fans nace muku painful wallahi da gaske wannan soyayyar mai zafice mai raÉ—aÉ—i ce duk wani masoyi yaci katari da wannan labarin nawa seya dara seya koka seya warwasa labarin ze Æ™ayatar ze tsaya arai ze nishaÉ—antar ze wa'azantar ze ilimantar kudai kubiyoni kawai*💃💃💃💃ðŸ¤ðŸ»
_kai ƙoƙarin ganin kayi payment domin zan soma sakin sane da zarar na kammale wagga_
~N~ *300*# *ta wannan account numbern 0078174806 starling bank show me your evidance of payment ta wagga numbern 08142105218 love you my Æ´an amana my Æ´an iya wuyata*
11/14/21, 3:20 PM - Allah Akbar: *98*
"Kotu tana buƙatar ganin ladi tasi'u tare da wanda take ƙara khalifa alhaji mai gwall"
Cikin rashin sabo ladi ta nufi ɗan gaban katakon nan da waɗanda ake tuhuma ke tsayawa khalifa ma ya nufi na gefenta ya tsaya, alkaline ya dubi mai gabatar da ƙara kana ya bashi umarni akan ya karanto ƙarar.
Tiryan tiryan mai karanto kara ya karanto komai na abinda barrister nuraddin ya shigar sannan kotu ta nemi lauyan wanda ake kara koyana da abinda zece.
Cikin kasaita wani kakkauran mutum ya mike.
"Sunana barrister salim mai goro, nike kare khalifa Alhaji mai gwal abisa shaidar kwararan hujoji...........nan ya soma karanto karya da gaskiya domin ya kare khalifa daga karshe ya É—ora da cewa sharri sukaiwa khalifan su basu san komai nakan lamarin ba.
Kana ya koma ya zauna.
Cikin tsanaki alkali ya dubi ya nura.
"Barrister nura ko kana da wata hujjar tare da shaidar gani da ido?"
Cikin nutsuwa ya nura ya mike.
"Assalamu Alaikum, sunana barrister nuraddin adam rimin gado nike shigar da karar khalifa abisa cin mutuncin wannan baiwar Allah dayay bayan ya aureta a ranar yay mata cin zarafi ajikinta kana yazo ya rattaba mata saki har biyu wanda abinda ya faru da ita seda ya saka har aka kwantar da ita a asibiti sabida haka inada shaida ƙwaƙwƙwara daga wajan nurse ɗin data dubata aranar"
Ya numfasa sannan yace.
"Ina neman kotu mai adalci data bani damar bayyana shaidar nurse tare da drivern gidan wanda agabanshi akai komai"
"Kotu tana neman nurse É—in data ma ladi dinki tare da drivern gidan alhaji"
Cewar alkali.
Cikin nutsuwa wannan nurse É—in data soma duba ladi ta bayyana tiryan tiryan ta bayyanawa kotu komai daya faru sosai mutan cikin kotun suka firgita da abin hakanan drivern gidan alhaji wanda su Aliyu suka shawo kansa da kyar shima ya bayyana nasa shaidar.
Nan da nan zufa ta karyowa kalifa idanunshi ya soma raina fata.
"Ko lauyan wanda ake kara yana da abinda zece?"
Girgiza kansa yayi sabida baya da abinda zece.
"Br salima baka da abinda zakace? khalifa kuma fa?"
Nan ma shuru.
Kotun ce tai tsit shikuma alkali ya sunkuyar da kansa a ƙasa yana rubutu a farar takarda.
Yana kammalawa ya É—ago.
"Abisa yadda kotu ta yanke hukuncinta cikin adalci, kotu ta yankewa khalifa hukuncin zaman gidan kaso na natsayin shekaru uku tare da horo mai tsanani Batare da bada beli ba, tunda aikine yay na ganganci, sannan ze bawa ladi tarar kuÉ—i naira miliyan goma"
Kana ya tashi nan fa kotu tahau tsine yan sanda ne suka sakawa khalifa ankwa aikwa nan alhaji ya zube atake anan ya suma mahaifiyarshi kwa binsa tai tana kuka.
Dakatawa yayi yana kallon mahaifiyar tasa.
"Momcy nayi nadamar zuwa a ɗanku domin kuba mahaifan ƙwarai bane tunda baku bamu tarbiyar kwarai ba duk abinda mukeso shikuke mana ashe akwai ranar dazan girbi abinda najima ina shukawa kuma ba kowa yajamin ba face ku, momcy naji na amince zanje domin na gyara halina ko Allah ze yafan laifukana dana jima ina aikawata in baba ya farfaɗo kice masa kadama yay wahalar fito dani domin nayi nadama gwarama ya barni naje na girbi abinda na shuka acan sannan ku rokarmin ladi ta yafemin"
Ƴan sandane suka saka keyarshi a mota sukabar mamansa tana kuka!
Da taimakon Æ´an sanda aka saka Alhaji mai gwall a mota aka nufi asibiti dashi domin barin jikinshi ya tabu koda aka kaisa asibitin ma taimakon gaggawa aka soma bashi sedai duk yadda akaso a dai daita lamarin Allah baiba sabida zuciyarsa ta sami bugawa tare da cutar barin jiki cikin mintuna goma Alhaji yace ga garinku nan ya rasu da tsananin takaicin halin daya jefa É—ansa ya rasu da takaicin yadda abinda yake ganin yafi karfi gashi shiyazo yafi nasa karfin.
Sosai iyalinsa suka gigice suna kuka ba khalifa ba alhaji nanfa duniya ta juya musu baya a rana É—aya lallai Allah abin tsorone.
Haka aka naÉ—o gawar akayo gida da ita.
Ladi kwa gida aka wuce da ita tare dasu Aliyu sosai su kawu tasi'u kewa Aliyu da nura godiya su Ali na kokarin tafiya gida sakon rasuwar mai gwall ya samesu sosai sukaji abin tare da nema masa gafarar Allah kana sukai sallama dasu kawu suka tafi.
Itama ladi maman su bebi tabi can gidan tace ita ta koma wajan Æ´an uwanta.
Daga ƴan kusa, Aliyu gidan bebi ya wuce sabida yanzu yanajin ya sami nutsuwa dayaga ya kwatarwa yarinyar can hakkinta sedai gefe ɗaya kuma tsananin tausayin kalifa ya kamasa na rashin mahaifin dayay ga kuma yadda rayuwar ta koma masa shiyasa ake son kawaita addu'a akan ƙaddararka Allah yasa tazo maka a mai kyau.
Dama tun safe umman mufida ta wankewa bebi kanta da karkashi dasu ƙwai da zuma, zaman kitso sukai inda tai mata kananun kitso mai kyau irin na ƴan maiduguri, lalli tai mata ja wanda ya haska farar fatarta.
Da taimakonta suka haÉ—a masa abincin gargajiya wanda suka haÉ—a mai burafusko da miyar taushe gyara gidan bebi tayi ta kunna turare kana ta gyara kanta cikin wasu shegun riga da wando.
Jera mai kayan tai a falo kana ta harde a saman sopa tana kallon kofa.
Aikwa tanajin budewar É—akin tai maza ta mike ta nufeshi ta rungume shi tana furta.
"Barka da zuwa i missing you" tafaÉ—a tana kwanciya akirjinshi.
Shafa kanta yayi tare da É—ora bakinsa a goshinta yana sumbata.
Da taimakonta yay wanka ya shirya sannan ta haÉ—a mai kayan abincin yana ci yana tambayarta ya ajiyarshi kuma koda wasa bai nuna mata cewar ga lamarin dake faruwa da gidansuba domin duk hidimar dayay musu da karar kalifa da komai bai sanar da itaba haka zalika bai gaya mata shiryawarsu da dangin mahaifinsuba.
Sedai hirarshi akan bebinsa ne na ciki da kuma hirar love.
Seda ya kammala komai na game da cin abincinshi sukai sallah sannan ta haye saman cinyarshi tana nuna masa lallanta.
Hannun ya kama ya zira yatsan a bakinsa yanasha kamar alawa, zame É—an kwalin kanta yayi yana shafo kitson nata.
Hannunshi ya saka ya zagaye ƙugunta yana hura mata hiskar bakinshi cikin kunnenta.
"Ummi kinyi kyau kamar na cinyeki nikaÉ—ai nasan mi nakeji ajikinki pls ki karamin yawunki nasha na koshi".
yafaɗa yana mai bude bakinta ya zira harshenshi yana zuƙe miyan bakinta yana lumshe idanunshi,hannunshi ya ɗora a kirjinta yana matsa mata na shanunta dasukai wata mahaukaciyar cika kamar xasu fasa kirjin nata, lumshe idanunta tai tana jan ajiyar zuciya tana fesar da numfashi, ganin wankin hula na neman kaisu dare yasa ya sunkuceta yay bedroom da ita a haukace yake rudata da zafafan romancig ɗinshi kafin ya kama hanyarshi inda nake jiyo kukan daɗin bebi danashi.
Ranarma sunyi matukar jiyar da junan su daÉ—i bakaÉ—an ba harda asubahi suna tare kafin suyi wanka ya wuce masallaci.
****************
Legos washe garin talata Alhaji idiris mai atamfa zaune a airport na legos yana son ya dawo kano yau sabida yadda bayajin daÉ—i kwana biyu na jikin nashi cikin farin ciki Alhaji isyaku shima wanda ke kokarin zama a gefen abba ya dubeshi.
"A,a mai atamfa nake gani anan ne kamar kwa kasan ina nemanka wayarka bata shiga, nima yanzu haka kanon nayi wallahi aminina Alhaji mai gwall ne ya rasu jiya"
Cikin jimami abba kewa haji isyaku ta'aziya sannan ya karasa da cewa shima zeje kano ne unexpected sabida bayajin dadin jikinshi.
Hira suke da Alhaji isyaku kafin a soma kiran sunaye.
Sabida suna a waiting room ne.
"Niko Alhaji idiris ina son nai maka murna kuma Allah bai ba, ashe baba Ali yayi aure to Allah sanya alkairi ai munje ma kofar gidan matar tasa har ina karyata auren nasa sabida nasan zuri'arku bakwa AUREN BARE! amman yadda naji tabbacin auren ne yasa na yarda ai yarinyar nasan har mahaifanta Æ´an mafuta ne"
Murmushi abba yay.
"Alhaji isyaku auren Aliyu yazone a kure kasan yar gidan kanina marigayi ya aura, amman har yanzu muna kan bakammu na rashin AUREN BARE! Aliyu Æ´ata ya aura ai"
Murmushi haji isyaku yayi.
"Kasan girman Allah Alhaji idiris Ali ɗanka yay aure kuma yarinyar daya aura ita ɗan gidan marigayi mai gwall yaso aura se Aliyun ka ya rigashi yanzu ma haka akan case ɗin yaron fa mai gwall ya sami heart attack"..............tiryan tiryan Alhaji isyaku ya zayyanewa abban Aliyu komai batare daya rageba hatta ƙaryata mai unguwa da haji isyaku yay seda ya gayawa abba, ( in baku manta ba alhaji isyaku shiya karyata mai unguwa lokacin daurin auren kalifa da bebi ku duba shafukan baya kuma isyaku kunsan abokin abba ne daman bashine harya kira layin abba yaki shigaba).
zuface take karyowa abba kota ina yana ina hakan ta faru?
Maganar isyakuce ta karade masa kunne.
"Yakama Alhaji fa ku daina wannan al'adar ta rashin AUREN BARE sabida ba addini bace kama godewa Allah dayasa aure yay ba karuwa ya aje ba bana gaya maka wannan maganar dankai fushi da ɗanka ba nagaya makane domin kuyi saurin gyara ɓarakarku kafin a haifi ɗan da baya da idanu"
Yana gama faÉ—in haka ya tashi domin an kira sunanshi, seda aka zo kan abba shima ya tashi ya shiga cikin jirgin jikinshi yay sanyi kalau.
Koda suka sauka kano ma baiwa kowa wayaba haka ya dauki napep har gida a falon alhaji babba abba ya yada zango lokacin karfe goman safiya sosai Alhaji babba yake faɗa lokacin da abba yagama shaida masa komai nan da nan aka kira meating na gaggawa iyalin mai atamfa ƙwansu da ƙwarƙwatarsu sun hallara a falon alhaji hatta khadija dasu usman wanda cikinshi ya duri ruwa.
Abba rike da waya yana kiran layin Aliyu amman anki É—agawa secan ya É—auka cikin ladabi yake gaida abba.
"Bana bukatar gaisuwarka Aliyu maza kazomin da wannan yarinyar daka aura yanzu ina falon alhaji"
Ƙittt ya katse wayar zuface ta soma karyowa Aliyu rana dubu ta ɓarawo..
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.